nigeria reading and access research activity primary 2 ... · primary 2 teacher’s guide. nigeria...

184
Jagoran Malamai - Aji 2 Nigeria Reading and Access Research Activity Primary 2 Teacher’s Guide

Upload: others

Post on 30-Apr-2020

24 views

Category:

Documents

2 download

TRANSCRIPT

Jagoran Malamai - Aji 2

Nigeria Reading and Access Research ActivityPrimary 2 Teacher’s Guide

Abubuwan Da Ke CikiGodiya iWaɗanda Suka Ba Da Gudummawa iiGabatarwa iiiHanyar Koyarwa Ta RARA ivAbubuwa Biyar Na Koyar Da Karatu Da Rubutu v

Fahimtar Ƙwayoyin Sauti vTsarin Baƙaƙen Harshe vIya Karatu vKalmomi viFahimta viManyan Hanyoyin Koyarwa Na Tsarin Koyar Da Karatu viKoyo A Tare viGwajin Yau da Kullum viiIn Yi, Mu Yi, Ku Yi viiKunnenka Nawa viiHarshen Baka: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti Da Sanin Kalmomi viiFahimtar Tsarin Rubutu viiRarrafen Karatu vii

Gwaji viiiGwajin Jagoranci Koyarwa ixƘaidojin Amfani Da Allo xDabarun Iya Rubutu xiAlamomi xii

Zango Na 1 1

Manufar Malamai Da Ɗalibai 2

Mako Na 1 - Darasi Na 1 da Na 2 6Mako Na 2 - Darasi Na 3 da Na 4 12Mako Na 3 - Darasi Na 5 da Na 6 18Mako Na 4 - Darasi Na 7 da Na 8 24Mako Na 5 - Darasi Na 9 da Na10 30Mako Na 6 - Darasi Na 11 da Na 12 36Mako Na 7 - Darasi Na 13 da Na 14 42Mako Na 8 - Darasi Na 15 da Na 16 48Alamomi 52

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na 2 53

Manufar Malamai da Ɗalibai 54

Mako Na 1 - Darasi Na 1 da Na 2 56Mako Na 2 - Darasi Na 3 da Na 4 62Mako Na 3 - Darasi Na 5 da Na 6 68Mako Na 4 - Darasi Na 7 da Na 8 74Mako Na 5 - Darasi Na 9 da Na10 80Mako Na 6 - Darasi Na 11 da Na 12 86Mako Na 7 - Darasi Na 13 da Na 14 92Mako Na 8 - Darasi Na 15 da Na 16 98

Alamomi 104

Zango Na 3 105

Manufar Malamai Da Ɗalibai 106

Mako Na 1 - Darasi Na 1 da Na 2 108Mako Na 2 - Darasi Na 3 da Na 4 114Mako Na 3 - Darasi Na 5 da Na 6 120Mako Na 4 - Darasi Na 7 da Na 8 126Mako Na 5 - Darasi Na 9 da Na10 132Mako Na 6 - Darasi Na 11 da Na 12 138Mako Na 7 - Darasi Na 13 da Na 14 144Mako Na 8 - Darasi Na 15 da Na 16 150Mako Na 9 - Darasi Na 17 da Na 18 156

Rataye 170

Abubuwan Da Ke Ciki

Jagoran Malamai - Aji 2i

GodiyaYunƙurin Aikin Binciken Karatu Da Samun Gurbi (RARA) da kamfanin RTI ke gudanarwa, wanda Hukumar Raya Ƙasashe Ta Amurka (USAID) ta ɗauki nauyi, suna miƙa godiyarsu ga dukkan waɗanda suka tallafa wajen samar da Jagoran Malamai na Hausa don amfanin aji biyu na firamare. Ba wai jagora ne ga malamai don koyar da karatun Hausa kawai ba, littafin ya ƙunshi abubuwan da ke cikin manhajar Hausa ta makarantun firamare, wadda ake amfani da ita a makarantun Jihohin Bauchi da Sokoto, kamar yadda Hukumar Bincike Da Bunƙasa Ilimi (NERDC, 2012), ta samar.

Haka kuma, muna godiya ga Ma’aikatun Ilmi ɗa Hukumomin Ba Da Ilimin Bai-ɗaya (SUBEB) na jihohin Bauchi da Sokoto, domin ba da gudunmawar ma’aikata da shawarwari, abin da ya tabbatar da aiwatar da ayyukanmu cikin sauƙi.

Daga ƙarshe, muna jinjina wa ilahirin marubuta, da editoci, da ma’aikatan bayan fage, waɗanda suka sha famar aiki wajen samar da littafin a cikin harshen Hausa. Godiya ta musamman zuwa ga ƙwararru, kamar Kwamitin Ba da Shawara Kan Koyar Da Karatu na Jihohin Bauchi da Sokoto, waɗanda suka taimaka wajen samar da wannan Jagoran Malamai.

RARA

Jagoran Malamai - Aji 2 i i

Waɗanda Suka Ba Da GudunmawaSunaye Wurin Aiki

Ahmad Alh. Umar State Universal Basic Education Board (SUBEB), Sokoto

Alison Pflepsen RTI International

Bilyaminu Inuwa Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA)

Dahiru Yalwa Mohammed College of Education, Azare

Dubeck, Margaret (Peggy) RTI International

Hadiza Salihu Koko Shehu Shagari College of Education, Sokoto

Lauwali Ibrahim State Universal Basic Education Board (SUBEB) Sokoto; Bodinga LGEA

Muhammadu Bello Yusuf Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA)

Phyllis Hildebrandt Technical Advisor (Consultant)

Prof. Malami Buba Hausa Language Consultant

R. Drake Warrick Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA)

Raphael Aiyedipe Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA)

Safiya Bala State Universal Basic Education Board (SUBEB) Bauchi; Bauchi LGEA

Swadchet Sankey Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA)

Yahaya A. Umar State Universal Basic Education Board (SUBEB), Bauchi

Zahra'u Abubakar Maishanu Nigeria Reading and Access Research Activity (NRARA)

Akanbi John Norj Illustration Consultant

Godwin Ondoma Desktop Publishing Consultant

Salisu Abdullahi Tsiga Hausa Language Consultant

Jagoran Malamai - Aji 2

Iya karatu da irin abin da ke biyo bayansa, ke sanya yawaita muhawara kan ingantattun hanyoyin bayar da ilimi. Gwamnatocin Jihohin Bauchi da Sokoto tuni sun fahimci cewa, iya karatu da rubutu ga ɗalibai ginshiki ne wajen haɓaka ci gaban karatunsu. Wannan yana da muhimmanci, ba wai wajen samun takardar shaidar kammala karatunsu ba kawai, har ma wajen gudanar da sauran harkokin zamantakewarsu. Sai dai, binciken da aka yi na baya-bayan nan ya gano cewa, yara ƙanana ba sa iya karanta komai a cikin harshensu balle a harshen Ingilishi. Wannan sakamako barazana ce, wadda ke nuna cewa yaran Bauchi da Sokoto baza su cim ma burin samun ilmi na bai-ɗaya ba, sai an sami tsararriyar hanyar koyar da su karatu.

Lallai akwai buƙatar sa hannun shugabanni a haɗa kai don bada gudunmawa wajen inganta harkokin koyarwa. Hukumar Raya Ƙasashe Ta Amurka (USAID) da gwamnatocin Bauchi da Sokoto, sun ƙulla yarjejeniya, inda suka gudanar da binciken gano fahimtar iya karatun ɗalibai a makarantun farko (EGRA), a aji 2 da 3 na firamare. Wannan aikin binciken koyar da iya karatu, wato RARA, ana yinsa ne domin gwada sahihan hanyoyin taimakawa da kuma samar da kayan aiki, domin inganta tsarin ilmi, ta yadda zai kawo ingancin iya karatun ɗalibai cikin harshensu (Hausa). Za a tabbatar da cim ma wannan buri ta hanyar horar da malamai domin a dasa tushen amfani da:

a. Fahimtar ƙwayoyin sautib. Tsarin Baƙaƙen Harshec. Kalmomid. Iya Karatue. Fahimta

A ƙarshen wannan yunƙurin, muna fatan samun haɓakar iya karatun Hausa ga ɗalibanmu, tareda bunƙasa dabarar koyar da iya karatu ga malamanmu. Haƙiƙa ya zama wajibi mu tallafa waaiwatar da yunƙurin RARA a makarantu, don samun cikakkiyar nasara.

Kwamishinan Ilimi Na Jihar Sokoto Kwamishinan Ilimi Na Jihar Bauchi

i i i

Gabatarwa

Alhaji Bello Yusuf Danchadi Ibrahim Mohammed Aminu

Jagoran Malamai - Aji 2 iv

Hanyar Koyarwa Ta RARA Da Farko dai, shi wannan tsari daga binciken manazarta ya samo asali, kuma yana da nasaba da wasu ingantattun tsare-tsare, tare da yin la’akari da darussan da aka koya wajen gudanar da ayyukan tallafi a Najeriya.

Abu Na Biyu shi ne, tsarin yana amfani da muhimman rassan koyar da karatu don taimaka wa ɗalibai su iya karatu. Su waɗannan rassan guda biyar ne: furta sautin baki, bambanta baƙake, karatu mai ma’ana, gina kalmomi da kuma fahimtar karatu. Dukkansu na da tasiri a wannan tsarin na koyarwa.

Abu Na Uku kuma, shi ne, wannan tsari na koyarwa ya yi amanna da cewa maganar baka ita ce jigo wajen koyon iya karatu da rubutu. Shi ya sa wannan shiri yake ba da ƙarfi kan harshen gida, wanda shi ne Hausa.

Na Huɗu, tsarin da ake bi yana ƙarfafa maganar cewa iya karatu da rubutu a wani harshe yana taimaka wa ɗalibai su iya karatu da rubutu a wani harshen na daban. Wannan bayani ya zo daidai da hanyar nan ta ɗora sabon aiki kan abin da aka koya a baya. Abin nufi a nan shi ne, tsarin yana taimaka wa ɗalibai su koyi iya karatu a cikin harshen gida, wanda suka fi iya magana da shi tun farko, kafin su koyi karatun a harshen da ba su sani ba.

Na Biyar, tsarin na RARA, yana jaddada muhimmancin yin bayani filla-filla, daga tushe zuwa rassa, na darussan da za a koyar. Abin da ake nufi da irin wannan bayani shi ne cewa koyarwa takan fara daga sauƙaƙan ayyukan horarwa kafin a kai ga masu tsauri. Tsarin na koyar ɗalibai sabon aiki a bayyane yake, ta yadda za a fara gabatar da dukkan muhimman abubuwan da ake son a koyar tun da farkon farko. Shi kuma yin bayani filla-filla hanya ce da malamai zasu shiga gaba suna aiki, ɗalibai na biye suna kwaikwayonsu. Bayan haka, sai su ɗaliban su ci gaba da koyon aikin da kansu, malamai suna dudduba su.

Na Shida, wannan tsari yana ba da fifiko kan amfani da littattafai iri-iri. Ɗalibai suna buƙatar samun damar amfani da littattafan koyon karatu da suka dace da shekarunsu. Sannan kuma suna da buƙatar jin karatu daga bakin waɗanda suka iya karatu, domin su ma su kwaikwaya.

Na Bakwai, tsarin ya fahimci muhimmancin gwajin ɗalibai, kuma ya shigar da gwaje-gwajen a cikin ainihin darasi, domin ya faɗakar da malamai wajen koyarwa.

Na Takwas, tsarin yana sane da cewa malamai suna da buƙatar tallafi da jagora wajen koyar da karatu. Saboda haka ne ma aka tsaro shirin da aniyar ba da horo, da yin jagora da samar da manyan abokan aiki, da kuma ba da damar musayar ra’ayi dangane da koyo da koyarwa.

Na Tara, wannan tsari ya yi imani da muhimmmancin sa-idon iyaye ga karatun ’yan azuzuwan farko. Ana mai da hankali kan bai wa ɗalibai ’yan ayyukan karatu da za su gwada yi a gida.

Abu Na Goma, shi ne a fahimci cewa Tsarin RARA na Koyarwa, hanya ce ta koyar da ’yan azuzuwan farko da ake kan gwajinta. Ba a tsiro ta da niyyar maye gurbin manhaja ba. Abin da dai muke kyautata zato, shi ne, idan aka bi wannan tsari, za a ɗora ɗalibai kan tafarkin koyon da zai kai su ga nasarar zama gwanayen karatu da rubutu.

Jagoran Malamai - Aji 2v

Abubuwa Biyar Na Koyar Da Karatu Da Rubutu GabatarwaMaganar masana ta zo daidai a kan cewa akwai abubuwa biyar da ya kamata duk wani

ingantaccen shirin koyar da karatu ya ƙunsa domin taimaka wa masu koyo su zamo gwanaye wajen karatu da rubutu. Akwai bukatar koyar da waɗannan rassa a tsarin da aka fayyace shi a bayyane.

Fayyacewa: Ana nufin ka yi aiki a fili don a koya.

A kula: Ana nufin koyarwarka ta kasance ta fara daga aiki mai tsauri zuwa mai tsauri, ba tare datsallake muhimman ayyuka ba.

Abubuwan biyar su ne:a. Fahimtar ƙwayoyin sautib. Tsarin Baƙaƙen Harshec. Iya Karatud. Kalmomie. Fahimta

1. Fahimtar ƙwayoyin sauti Manufa: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti na nufin iya gane ɗaiɗaikun sautukan da ake amfani da su wajen gina kalmomi. Akwai buƙatar taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar ƙwayoyin sautin da akan gina kalma. Ɗaliban da ba su da wannan masaniya za su sha wahalar koyon karatu. Kafin mai koyon karatu ya san manyan rassan sautuka, kamar gaɓa, kalma, da jimla, ya kamata ya sa ɗaiɗaikun sautukan haruffa.

Dalili: Ɗalibai na buƙatar fahimtar muhimmancin ƙwayoyin sauti domin taimaka wa karatu da rubutunsu.

Hanyar Koyarwa: Ana iya bunƙasa fahimtar ƙwayoyin sauti ta hanyar amsa-amo da waƙoƙi, tare da aiki da ɗaiɗaikun baƙaƙe. Ɗaliban da ke da fahimtar ƙwayoyin sauti na iya gane kalmomin “mace” da “mama” dukkansu suna farawa da sauti iri ɗaya /m/.

2. Tsarin Baƙaƙen HarsheManufa: Iya karatu na buƙatar fahimtar tsarin baƙaƙen harshe - (wato, su baƙaƙe da makamantan su), wakilan sautuka ne a cikin kalma. Wannan tsari na koyarwa, hanya ce ta horar da masu koyo yadda za su kamanta rubutacciyar kalma da sautinta.

Dalili: Koyar da ilimin sauti zai bai wa ɗalibai damar furta sauti da baƙin kalmomin da ba ka koyar ba.

Hanyar Koyarwa: Malamai su taimaka wa ɗalibansu ta hanyar koyar da su ɗaiɗaikun haruffa, da zanen haruffa, da kuma gaɓar kalma. Haka kuma, ya dace su ba su damar koyon haɗa baƙaƙe da rarraba su. Masu koyon da aka koyar da su iya furta sautin baƙi na iya karantawa da kiran sunan baƙaƙen baƙuwar kalma, kamar ‘gwamma’, ko da ko ba su san ma’anar kalmar ba.

3. Iya KaratuManufa: Iya Karatu, shi ne iya karanta rubutu bisa ƙa’idojin rubutu na harshe.

Dalili: Yakan taimaka wa ɗalibai tsakuro ma’ana cikin rubutu. Haka kuma yakan taimaka musu su zamo suna sane da tsarin jimla, wanda hakan ke taimaka wa rubutunsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 vi

Hanyar Koyarwa: Gwargwadon yin ma’amalar ɗalibai da rubutu, gwargwadon zamansu gwanayen karatu. Gwama karatun amshi da karatu tare da karatun raɗa zai taimaka wa ɗalibai su ƙara ƙwarewa a karatu. (dubi akwatin bayani a ƙasa). Gwanaye a karatu za su iya karya murya da hanzari, don yin daidai da tsarin kalma da na ƙa’idojin rubutu.

Karatun amshi: Ana amfanin da shi a lokacin da aka gabatar da sabon rubutu. Da farko, malamai za su karanta, su kuma ‘yan aji su amsa.

Karatun amshi: A nan kowa zai karanta rubutun a lokaci guda. Muryar malami /ma ta taimaki ɗalibai.

Karatu Tare : Za a ga ‘yan koyo da dama suna karatun rubutu tare.

Karatun raɗa: ‘Yan koyon karatu ba su da isasshiyar ƙwarewar iya karatu a asirce. Sai dai suna iya yi wa rubutu ‘karatun raɗa’, wato a tsanake, kuma ba mai jinsu.

4. KalmomiManufa: Kalmomi kan taimaka wa masu koyo wajen fahimtar abin da suka saurara, ko sukakaranta. Haka kuma, kalmomi suna taimaka musu koyon karatu da iya magana da kuma rubutu.

Dalili: ‘Masu koyo na buƙatar sanin tarin kalmomi domin fahimtar abin da suka karanta, da kuma iya magana mai ma’ana.

Hanyar Koyarwa: Za a iya koyar da kalmomi kai tsaye ko kuma a fakaice. Darussan da ke gwama koyarwa da motsin jiki (TPR), da amfani da hotuna, da karatun bayyane, suna bai wa masu koyo damar jin kalmomi da amfani da su. Ya kasance, ajinku cike yake da harshen koyarwa, inda akwai rubutu ko ina a baje domin amfanin masu koyon karatu. Ɗan koyon da aka koya wa karanta kalmomi zai fi gane yawancin abin da ya saurara, ko kuma ya iya karantawa. Haka kuma, ɗalibai na iya amfani da kalmomi a lokacin rubutunsu.

5. FahimtaManufa: Fahimta ita ce iya ganowa da bayyana ma’anar labari. Fahimta iri biyu ce. Fahimtar Zahiri ita ce wadda ke nuna iya ba da bayanin abin da ke bayyane a cikin labari (kamar launin rigar wani cikin labari, ko kuma abin da ya faru a ciki ). Fahimtar hasashe kuwa ita ke buƙatar mai karatu ya tono wani bayani da ba ya cikin labari (kamar yadda yake tsammanin wanin cikin labari ke ji, ko a bin da su za su yi da a ce su ne wani a cikin labarin).

Dalili: Shi ne babban dalilin yin karatu.

Hanyar Koyarwa: Ya kamata a koyar da fahimta ga masu koyo, kome ƙurciyarsu. Ana koyar da fahimta kafin karatu da lokacinsa da kuma bayan kammala shi. Ɗan koyon da aka koya wa iya amfani da fahimta, zai iya hasashen makomar labari, ya kuma auna fahimtarsa game da labarin, yayin da yake cikin karatu, tare da bayyana ra’ayinsa bayan ya kammala karatun labarin.

Manyan Hanyoyin Koyarwa Na Tsarin Koyar Da Karatu Akwai hanyoyin koyarwa da dama da ake amfani da su wajen Ayyukan Binciken Karatu Na RARA.

• Koyo a tare• Gwajin Yau da Kullum• In Yi, Mu yi, Ku Yi• Kunnenka Nawa• Harshen Baka: Fahimtar Furta Sauti Da Sanin Kalmomi• Rarrafe na Koya Karatu

Koyo A TareKamar yadda sunan ya nuna, tare ake koyo da koyarwa. Koyo a tare na ba da dama ga masu koyo su yi aiki tare da ‘yan ajinsu kullum, ko kuma na ɗan lokaci, a ajin koyar da karatu. Yana daga cikin tsarin ‘In Yi, Mu Yi, Ku Yi, ko dai kafin a fara wani aiki, ko kuma bayan an kammala shi. Koyo a tare

Jagoran Malamai - Aji 2vii

yana ƙarfafa koyo, yayin da yake ƙara samar da damar koyon amfani da sababbin bayanai tare da wasu. Yana kuma taimakawa wajen rage matsalolin da ke tattare da aji mai ɗalibai da yawa.

Gwajin Yau Da KullumAyyukan gwaji na yau da kullum a kan cusa su ne a cikin darussan koyarwa na kowace rana.Darussan Jumma’a su ake keɓewa a matsayin darussan bita da na gwajin ƙwarewar masu koyonkaratu. Mafi yawancin ayyukan ranar Juma’a na “Ku Yi” ne, inda ake sa ran masu koyo su yi aikin da kansu, da yake sun share mako suna koyon irin waɗannan ayyuka. Wannan yakan ba da dama ga malamai su kimanta da rubuta ƙwazon masu koyo a lokacin da suke kammala ayyukan da aka ba su.

In Yi, Mu Yi, Ku YiHanyar koyon karatu ta daki-daki, ita ce aka fi sani da sunan “In Yi, Mu Yi, Ku Yi”. Da farko, masu koyo za su ga malami/ma yana aikinsa shi kaɗai. Sannan, sai masu koyo su yi aikin tare da malami/ma da sauran ‘yan aji. Da ƙarshe, kowane mai koyo zai gwada yin aikin shi kaɗai. Wannan hanyar ce aka fifita a yawancin ayyukan koyo, kamar yadda aka nuna a sashen ‘Hanyar Koyarwa’ na wannan Jagoran Malamai. Hanyar tana taimakon koyon karatu, domin tana ƙara ƙarfafa gwiwar ɗan koyo, yayin da yake fama da sabon aiki.

Kunnenka NawaKoyarwa ta hanyar tsarin kunnen ka nawa ta ƙunshi ayyukan da ke buƙatar masu koyo su yi amfani da hanyoyi biyu ko fiye na ji a jiki, don fahimtar sabon bayani. Ta ƙunshi yi wa masu koyo jagora don amfani da ganinsu da jinsu da kuma gaɓɓan jiki. Ana amfani da waɗannan hanyoyi a duk tsawon darasi. An jima ana amfani da hanyar koyarwar da ta haɗa ji da gani da motsi da taɓi, ga waɗanda aka haifa da ƙarancin fahimta. Yanzu an gano cewa kowane ɗan koyo na iya samun amfanin koyarwa ta wannan hanya.

Harshen Baka: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti Da Sanin Kalmomi Iya karanta kalmomi yakan zo cikin sauƙi idan an sami ingantaccen horon iya magana. Bunƙasa fahimtar ƙwayoyin sauti da kalmomi shi ke samar da tushe ga koyon karatu. Fahimtar ƙwayoyin sauti na nufin samun fahimtar dangantakar da ke akwai tsakanin sautukan harshe, da rassa, kamar gaɓoɓin kalma da raujin sautuka cikin kalma. Haka kuma masu koyo na bukatar su sami damar koyo da amfani da kalmomi. Samuwar kalmomi na taimaka wa masu koyo lokacin da suka fara karatu.

Fahimtar Tsarin RubutuGanin harshe a rubuce na taimaka wa ɗalibai wajen fahimtar yadda rubutu yake, da kuma muhimmancinsa. Dole ne masu koyo su sami damar amfani da littattafai da ire-iren hanyoyin rubutu, domin su saba da amfani da bayanai ta kafofi daban-daban. Wannan hanyar koyo za ta taimaka wa masu koyon karatu su gane cewa rubutu wakilin magana ne, kuma yana tattare da ma’ana.

Rarrafen KaratuWannan hanya kai tsaye take tallafa wa bayanin fara aiki daga sananne zuwa ga baƙon aiki. Ta hanyar farawa da rarrafen, masu koyo za su tinkari sabon aiki da ma’aunin fahimtar da suke da ita. A koyarwa, maimakon jin amsar tambaya kai tsaye, ana tallafa wa ɗalibai su samo amsar da ta yi daidai. Ya kamata a tallafa wa masu koyo da hanyar ta rarrafe, ta hanyar yi musu gyara. Misali, ɗan koyon karatu ya yi kuskuren karanta kalmar “yaro”, ya ambaci “yawo”, sai a ce masa, “ka samo sautin farko daidai”. Ko kuma, ɗan koyon da ya nuna jan biro, ya kira shi “baƙin biro”, sai a ce da shi, “haka ne, biro ne. To sai dai baƙi ne, ba ja ba”. Hanyar Koyarwa Ta RARA, tsari ne na jaddadawa da faɗaɗa muhimman rassan da ke dunƙule a cikin Manhajar Hausa ta Hukumar Bincike Da Bunƙasa Ilmi (NERDC ). Haka kuma tsarin ya tsamo jigogin rayuwa ta yau da kullum na manhajar, da suka haɗa da bayanin iyali da ciniki da kiwon lafiya da motsa jiki da sufuri da noma da ire-iren ayyukan jama’a, waɗanda a kansu ne aka gina darussan da ke ciki.

Jagoran Malamai - Aji 2 viii

GwajiMuhimmancin gwajin bi-da-gyara - A cikin kowane aji za a sami ɗalibai da ke da buƙatu da ƙwarewa da suka sha bamban da juna. Abu ne mai muhimmanci malamai su samar da hanyoyin inganta koyarwarsu domin dukkan ɗalibansu su kai ga samun nasara. Gwajin bi-da-gyara zai fayyace wa malamai muhimman bayanai dangane da abin da ɗalibai suka koyo, sannan hanyar za ta iya bai wa ɗalibai shawarar gyara aikinsu nan take.

Gwajin bi-da-gyara na iya kasancewa da ɗaiɗaikun ɗalibai, ko ɗan rukuninsu, ko kuma da dukkan ɗaliban aji. Ana ba da shawarar yadda gwajin zai kasance a ko’ina cikin Jagoran Malamai, domin tallafawa wajen binciko fahimtar ɗalibai yau da kullum, domin bunƙasa ci gabansu.

Mene ne gwajin bi-da-gyara? Gwajin bi-da-gyara hanya ce mai sauƙi da malamai kan iya binciko fahimtar ɗalibansu. Gwajin bi da gyara a kan iya ɗaukar salo iri-iri wadda malamai za su iya amfani da su. A cikin wannan jagora, za a sami misalai ƙarara kan yadda za a gudanar da gwaje-gwajen gano fahimta.

Hanyar gwajin bi-da-gyara da aka fi sani ita ce yin tambaya. Malamai na iya amfani da yin tambayoyi domin gano bayanin fahimtar ɗalibai. Kowane darasi da ke cikin jagoran malamai na ƙunshe da rubutattun tambayoyi da ke maida hankali kan muhimman bayanan da labari ya ƙunsa. Malamai na iya amfani da yin tambaya su binciko fahimtar ɗalibai. Ta hakan, gwajin zai ba da hasken yadda za a tinkari matakin koyarwa na gaba.

Wata sananniyar hanyar gwajin bi-da-gyara na faruwa ne lokacin da ɗalibai ke karatu a bayyane: ko a matakin baƙi, ko na gaɓa, ko na kalma, ko na jimla. Malamai na iya binciko fahimtar darasi a lokacin da ɗalibai suka maida hankali ga yin ayyukan da aka ba su a lokuta daban-daban cikin koyar da darasi. Misali, a lokacin da aka nemi dukkan aji su maimaita karanta wata gaɓar kalma, ko kalma, ko jimla, malami na iya tono zurfin fahimtar ɗalibi. Ta hakan, sai malamai su iya tantance ko lokacin wucewa gaba ya yi, ko kuma sai an maimaita koyarwar.

Gwajin bi-da-gyara a matsayin tsarin koyarwa na yau da kullum - Akwai hanyoyin gwajin bi-da-gyara da dama a cikin tsarin darasinka dake cikin jagoran malamai. Kowane darasi an raba shi gida biyar: Fahimtar Ƙwayoyin Sautuka, Tsarin Baƙaƙe, Gwanewa, Kalmomi da Fahimta. Sannan kuma kowane reshe daga cikin waɗannan yana da jerin ayyuka uku: ‘In Yi, Mu Yi, Ku yi’: da farko malami zai yi dukkan abin da yake son a kwaikwaya. A aikin ƙarshe na ‘Mu Yi, ana sakin ragamar koyarwar ne a hankali, don mai da koyo a hannun ɗalibi. A aikin ‘Ku Yi’ kuwa, ɗalibi zai sami damar nuna ƙwarewarsa a fannin da aka koya masa. A cikin ayyukan biyu na ƙarshe a cikin darasi ne malami ke da tarin damar binciko fahimtar ɗalibansa.

Misali, a sashen darasin da ke koyar da Fahimtar Kwayoyin Sauti, za a nemi ɗalibai su ‘Tafa Kalma’. Malami zai nemi dukkan ɗalibai su furta kalma, su kuma tafa ta. Ta hakan, malami zai sami damar duddubawa ya ga ɗaliban da ba sa aikin furuci da tafawa tare da sauran ɗalibai. Ka ga malami na da ƙarin samun damar binciko fahimta, ta hanyar tambayar ɗalibai su nuna ƙwarewarsu wajen tafa gaɓoɓin kalma su kaɗai.

Jagoran Malamai yana ba da damar ƙara horuwa a dukkan sassan a lokacin darasi na biyu cikin mako. Ana son malamai su karkato darasin na biyu a cikin mako zuwa samun ƙwarewar ɗalibai a kan sassan nan biyar da ke cikin kowane darasi: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti, Tsarin Baƙaƙe, Iya Karatu, Kalmomi, da Fahimta.

Jagoran Malamai - Aji 2ix

Gano abin da ɗalibai suka sani tun farko

Gano fahimta - wucewa zuwa

wani bayani, ko a maimaita

koyarwa

Koyar da bayani

Binciko fahimtar bayani

Koyar da bayani na gaba, ko a maimaita koyarwa

Gwajin Jagoranci Koyarwa:

Da’ira Auna FahimtaDa’irar tana farawa da auna abin da ɗalibai suka sani ko fahimta a baya. A kowane mataki na batun da aka koyar, ya kamata malami ya auna fahimtar ɗalibai, don gano ko sun fahimci abin da aka koya musu. Idan ba su fahimta ba sai a sake bitar batun, sannan a sake auna fahimtarsu a kan wannan batu.

Jagoran Malamai - Aji 2 x

Ƙa’idojin Amfani Da Allo1. Da zarar malamai sun shiga aji, su tabbatar an kawar da duk wani abu da

bashi da alaƙa da darasin da zasu gabatar.

2. A raba allon gida biyu don jin daɗi gabatar da rubuta bayanai/kayan aiki.

3. Malamai zasu fara rubutu a allo daga hagu zuwa dama

4. Malami/ma ya/ta tsaya gefe idan yana rubutu a allo. Kada malami/ma ya/ta riƙa magana da allo, ya/ta juyawa aji baya.

5. Malami/ma zai/zata yiwa aji bayani yana kallon ɗalibai, sannan ya koma gefe ya yi rubutu a allo.

6. Rubutu a allo ya kasance mai kyau kuma mai karantuwa (ba a jirikce ba).

7. Kada bayanai/kayan aiki su yi yawa a allo

8. A riƙa goge allo da dasta, kodayaushe.

9. Malamai su riƙa duba bayanan da suka rubuta/kaya aiki, idan sun ga wani kuskure su gyara

10. Malamai na iya sanya ɗalibai yin wani aiki a kan allo

Jagoran Malamai - Aji 2xi

Dabarun Iya RubutuKula da sigar baƙi: Yana da muhimmanci ɗalibai su naƙalci yanayin kowane baƙi. Idan har basu naƙalce su ba kuwa, kada ka damu da su san girma ,karkace ko rarraba su wajen rubutu. Amma da zarar ɗalibai sun naƙalci yanayin baƙi, to sai a jawo hankalinsu wajen yanda ake ƙawata su da rubuta su dalla-dalla, musamma dangantakar harafi da layukan takarda.

Lura da yadda aka rubuta baƙi :A yayin kowane rubutu, baƙaƙe na kasancewa ne a ƙasan layi a tsakanin layuka biyu. Manya baƙaƙe ana rubuta su ta hanyar cika tsakanin layukan da su. Su kuwa ƙananan baƙaƙe wasu kan sami layin da zai cika daga sama (b, d, h i), wasu kuma wutsiyarsu daga ƙasa kan ketara har layin da ke ƙasa (g, j, y), amman mafi yawansu na tsayawa a tsaka-tsakin layukan nan biyu. Da zarar ka gabatar da sabon baƙi, to sai ka danganta shi da bayanan da muka yi a baya dangane da layukan nan biyu, ko da yake ba dole ba ne ɗalibai su kiyaye da wananna ƙai’dar, har sai sun gama naƙaltar yanayinsu. A wannan lokacin sai ka jawo hankalinsu a kan wannan ƙai’dar.

Yanayin zama, Aje takarda, da Riƙon fensiri

Za a fara da nunawa ɗalibai yadda za su riƙe fenciri daidai. Ana son su sanya fensirin tsakanin yatsu uku (babban yatsa, manuniya, da kuma na tsakiya). Babban yatsa shi ne gefe, manuniya na sama, shi kuma na tsakiya yana daga ƙasa ya tare fensir. A ɗan karkata fencirin kaɗan. A duk lokacin koyon rubutu, musamman a darussan farko-farko, ana iya koyawa ɗalibai waƙa kamar haka: Babban ɗan yatsa gefe,Manuniya ko na sama,Ɗan tsakiya kuma na ta ƙasa.

Bayan gama rera waƙar sai a sanya su riƙe tare da ɗaga fensirinsu sama don ka/ki kewaya ganin yanda suka riƙe. A tabbatar ɗalibai su ya bada yar tazara tsakanin yanda suke zaune da tebirinsu, yadda zasu iya aza damtsensu a kan tebir cikin jin daɗi da natsuwa.Badaman ɗalibai su aje takardarsu a kusurwa daga dama. Bahagun ɗalibai kuma su aje takardunsu a kusurwa daga hagu.

Jagoran Malamai - Aji 2 xii

Aikin Malami/Malama:A nan malami/malama zai/za ta yi aiki shi/ita kaɗai yayin da ɗalibai ke koyon aikin ta hanyar kallo da sauraron aikin da malami/malama yake/take yi.

Aikin Malami/Malama da Ɗalibai:A nan malami/malama zai/za ta yi aiki sa’annan ɗalibai su gwada yin aikin da malamin/malamar ya/ta gama aikatawa.

Aikin Ɗalibai:A nan ɗalibai kaɗai za su gwada yin aiki, yayin da malami/malama ke jagorantarsu.

Alamar akwati: An danganta sashen ‘Sunayen Haruffa da Sautukansu’ da wannan alamar ta akwati. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar akwati da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar da’ira: An danganta sashen ‘Gano Gaɓar Kalma’ da wannan alamar ta da’ira. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar da’ira da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar dala: An danganta sashen ‘Kalmomin da za a karanta’ da wannan alamar ta dala. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar dala da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar tauraro: An danganta sashen ‘Karatun Jimla’ da wannan alamar ta tauraro. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar tauraro da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar agogo: Wannan alamar na nuna wa malami/malama lokacin da zai/za ta ɗauka domin karantar da sashe.

Alamomi

1

ZANGO NA 1Mako 1 - 8

Darasi 1 - 16

Jagoran Malamai - Aji 2

Jagoran Malamai - Aji 2 2

Manufar Malamai Manufar Ɗalibai

Zango na 1

Jigo na 1: Iyali

• Ƙarshen wannan sashe, ya kamata malamai su san muhimman bayanan koyar da karatu a azuzuwan farko:

• Furta sauti da saurare• Ƙa’idojin haruffa• Ganewa da iya karatun jimla• Kalmomi da fahimta da iya amsa

tambayoyi

A wannan sashe za a gabatar da iyalan gidansu Nana ga ɗalibai.

Malamai su taimaka wa ɗalibai su ƙara kusantar gidajensu da mutanen da ke gidajensu ta hanyar karanta labarin gidansu Nana.

Ayyukan mako 1-4

A ƙarshen kowane darasi na 1, ana son malamai su iya gano ƙwazon ɗalibai wajen iya karanta haruffa da gaɓoɓin kalma da kalmomi dake ƙunshe da haruffan koyo kamar haka:• Mako na ɗaya: ‘N’, ‘n’, ‘A’, ’a’• Mako na biyu: ‘K’, ‘k’, ‘A’, ‘a’• Mako na uku: ‘M’, ‘m’, ‘A’ ‘a’• Mako na huɗu: ‘S’, ‘s’, ‘A’, ‘a’

A ƙarshen kowane darasi na 1, ana son ɗalibai su iya gano ƙwazonsu wajen iya karanta haruffa da gaɓoɓin kalma da kalmomi dake ƙunshe da haruffan koyo kamar haka:• Mako na ɗaya: ‘N’, ‘n’, ‘A’, ’a’• Mako na biyu: ‘K’, ‘k’, ‘A’, ‘a’• Mako na uku: ‘M’, ‘m’, ‘A,’ ‘a’• Mako na huɗu: ‘S’, ‘s’, ‘A’, ‘a’

A ƙarshen kowane darasi na 2, ana son malamai su iya gano ƙwazon ɗalibai, wajen iya karanta labari da kuma fahimtar abin da ya ƙunsa,a:• Mako na ɗaya: hanyar saurare.

• Mako na biyu: yi musu tambaya ɗaya wadda amsar ke cikin hoton labarin.

• Mako na uku: yi musu tambaya ɗaya wadda amsar ke cikin labarin karatu a bayyane

• Mako na huɗu: hanyar yin tambayoyi biyu da amsoshinsu ke cikin Littafin Karatu A Bayyane.

A ƙarshen kowane darasi na 2, ana son ɗalibai su iya gano ƙwazonsu wajen iya karanta labari da kuma fahimtar abin da ya ƙunsa,a:• Mako na ɗaya: hanyar saurare.

• Mako na biyu: yi musu tambaya ɗaya wadda amsar ke cikin hoton labarin.

• Mako na uku: yi musu tambaya ɗaya wadda amsar ke cikin labarin karatu a bayyane

• Mako na huɗu: hanyar yin tambayoyi biyu da amsoshinsu ke cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Shawara akan auna/gwajin fahimta

A ƙarshen wannan sashe, malamai su maimaita baƙaƙen ‘N’ ‘K’ ‘M’ ‘S’ da wasalin ‘A’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon ɗaliban da suka karanta:1. Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da

haruffan koyo

2. Jimloli dake cikin labarai da amsa tambayoyi

Malamai su tisa aiki inda ya dace.

A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san matakin nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya furta haruffa da sanin kalmomi da Jimloli da kuma gane inda suke da rauni daga malami/malama.

A ba ɗalibai keɓaɓɓen aikin gida ko ayyukan bita.

Manufar Malamai Da Ɗalibai

Jagoran Malamai - Aji 23

Manufar Malamai Manufar Ɗalibai

Zango na 2

Jigo na 2: Yanayin muhalli

• Ƙarshen wannan sashe, ya kamata malamai su san muhimmancin bayanan koyar da karatu a azuzuwan farko:

• Furta sauti da sauraren fitar sauti a baka.

• Ƙa’idojin haruffa da dangantakarsu da sauti.

• Ganewa da iya karanta jimla da labari sosai.

• Kalmomi da fahimta da iya amsa tambayoyi

A wannan sashe za a gabatar wa ɗalibai ayyuka da suka danganci ciki da zagayen gidansu Nana.

Ana son malamai su taimaka wa ɗalibai wajen kamanta aikace-aikacen da suke yi a gidanjensu, da waɗanda ake yi a gidansu Nana.

Ayyukan mako 1-4

A ƙarshen kowane darasi na 1, ana son malamai su iya gano ƙwazon ɗalibai wajen iya karanta haruffa da gaɓoɓin kalma da kalmomi dake ƙunshe da haruffan koyo kamar haka:

• Mako na ɗaya: ‘Ts’, ‘ts’, ‘I’, ’i’• Mako na biyu: ‘R’, ‘r’, ‘I’, ‘i’• Mako na uku: ‘D’, ‘d’, ‘I’ ‘i’• Mako na huɗu: ‘T’, ‘s’, ‘I’, ‘i’

(ɗalibai su iya rubuta su dai dai)

A ƙarshen kowane darasi na 1, ana son ɗalibai su iya ganewa da karanta haruffa, gaɓoɓin kalma da kalmomin dake ƙunshe da haruffan koyo kamar haka:

• Mako na ɗaya: ‘Ts’, ‘ts’, ‘I’, ’i’• Mako na biyu: ‘R’, ‘r’, ‘I’, ‘i’• Mako na uku: ‘D’, ‘d’, ‘I’ ‘i’• Mako na huɗu: ‘T’, ‘s’, ‘I’, ‘i’

(ɗalibai su gwada rubuta haruffan dai dai)

A ƙarshen darasin mako na 1-4, malami/ma ya/ta iya gane ƙwazon ɗalibai wajen:• iya karanta labari da kuma fahimtar abinda

labarin ya ƙunsa ta hanyar saurarensu lokacin da suke karatu,

• yi masu tambayoyi biyu da amsarsu ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin Littafin Karatun A Bayyane.

A ƙarshen darasin mako na 1-4, ɗalibai su:• iya yin hasashen abinda zai faru dangane

da labarin da za a karanta,• su kuma iya karanta labarin da ke kunshe

da baƙin kalmomi• da kuma kalmomin da suka koya, • tare da amsa tambayoyi biyu da amsarsu

ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin Littafin Karatun A Bayyane.

Auna fahimta

A ƙarshen wannan sashe malamai su maimaita tagwan baƙi ‘Ts’ da baƙaƙen ‘R’ ‘D’ ‘T’ da kuma wasalin ‘I’ sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta bayanin ƙwazon ɗalibai wajen:1. Karanta kalmomi da gaɓoɓi da

kalmomin dake ƙunshe a ayyukan koyo

2. Iya karanta jimloli dake cikin labari da kuma amsar da ta dace da tambayoyi.

3. Malamai su tisa aiki inda ya dace.

A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san matakin nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya furta keɓaɓɓun haruffa da sanin kalmomi da jimloli ta hanyar samun bayannin ƙwarewarsu da rauninsu daga malamai.

Ana son a ba ɗalibai shiryayyen aikin gida ko na koyo a gida.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

4

Kafin Darasi

Waƙar Gaisuwa

Idan muka tashi da safeSai mu gai da iyayenmu x 2

Mamata ina kwanaGaisuwa ce da safe

Ina wuni BabanaGaisuwa ce da ranaMamata sai da safeGaisuwa ce da dare.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [Nana]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [Nafisa, nama, noma].

Aikin Malami:

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

5

1. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [N n].

2. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [N], sautinsa /n/.”

3. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na biyu (2) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

4. Maimaita mataki na uku (3) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

5. Koya wa ɗalibai furta sautin [N] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[N] na da sautin /n/ kamar a cikin kalmar noma.” Ka/ki kwatanta yadda ake noma kana/kina furta sautin ‘n’ ‘n’ ‘noma.

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

6. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

7. Maimaita mataki na shida (6) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

8. Maimaita mataki na farko zuwa na huɗu(1-4) da ɗaya harafin [A a].

9. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

10. Maimaita mataki na shida da na bakwai (6-7).

11. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [N, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 6

Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [na].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [an, nan].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalma [Nana] a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita aikin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita aikin tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [na, ana].

Jagoran Malamai - Aji 27

Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Karatun Jimla Minti-3

1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na gida].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [gida].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya banbanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Nana na nan. Nana na gida. Nana na wasan gala-gala.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2 8

Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 2 a cikin Littafin Karatu A Bayanne.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙabila, rana]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Nn, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsunsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa, ko a bayan wani ɗalibi/ɗaliba da suke tare.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 29

Zango Na: 1 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Matashiya a kan Darasi Na 2

Rubuta waƙar kan babbar takarda na taimaka wa

ɗalibai wajen rera waƙar. Ana iya amfani da bayan

kalandu, da manyan kwalaye wajen rubuta

waƙar.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 3 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [zaune, tebur].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [2] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti.Aiki: Bambanta Sautuka.Manufa: Yi gwajin gano ko ɗalibai na iya bambantawa tsakanin sautin farko da na

ƙarshe.Tsari: Faɗi kalmomi biyu. Nemi ɗalibai su gaya maka/maki sautukan farko da na

ƙarshe na kalmomin ɗaya ne.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darussan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Wane bangare na darasi ɗalibai suka fi fahimta? Me ya sa ka/ki ke ganin ka/kin shirya wa wannan darasi? Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin ya kamata a canza

cikin waɗannan abubuwa?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

10

Kafin Darasi

Waƙar Haruffa

a, b, c, d, e, f, g, h!i, j, k, l, m, n, o, r!

s, t, u, w, y, z!

An taso daga makaranta‘Ya’yan kaji na wasa

Tare da ‘ya’yan HausawaKomai girman ɗan bokoBai wuce abachada ba!

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [kaka]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [kaza, kakaki, kare].

in Malami:

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

11

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [N, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [K k].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [K], sautinsa /k/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na hudu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [K] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[K] na da sautin /k/ kamar a cikin kalmar kama.” Ka/ki yi amfani da

Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6

hannunka/ki na dama kana/kina kama na hagu kana/kina furta sautin ‘k’ ‘k’ ‘kama’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruf-fan [K, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

12

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ka].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [na].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [kaka] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [kana, naka].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

13

Karatun Jimla Minti-3

1. Rubuta jimlar a kan allo [Kaka na masa].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [masa].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Kaka na gida. Kaka na masa. Nana na kallo.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2 14

Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 4 a cikin Littafin Karatu A Bayanne.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [Ƙofa, bishiya]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayanne.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Kk, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsunsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 215

Zango Na: 1 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

Matashiya a kan Darasi Na 2

Lura da fahimtar ɗalibai: Zaɓi biyar da za ka lura da aikinsu tun da farko. Idan 4 ko 5 na iya tafa kalmomi

daidai, to ka ci gaba. Idan 3 ko 4 ne kawai ke iyawa, to a

maimaita aikin.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 5 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [marainiya, ladabi].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [4] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Fahimtar Ƙwayoyin Sauti.Aiki: Ɗaga Hannu Taɓo Tauraro.Manufa: Yi gwajin fahimtar ɗalibai wajen sauraron sautukan kalamomi.Tsari: Nemi ɗalibai su tashi tsaye. Malami/Malama zai/zata faɗi kalma. Su kuma

ɗalibai za su yi kamar suna kan cafko tauraro daga sama, a kowane sauti ko gaɓa a sheɗara ko jimla.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Ko ɗalibai sun ji daɗin waƙar da kuma motsa jikin da ake yi a cikinta? Saboda me?

Ko ka/kin shirya wa aiwatar da waƙa kafin shiga aji? Idan i/a’a me ya sa?

Bayan waiwaye me ka/ki ke tunanin zaka/ki canza don koyar da waƙa sosai.

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

16

Kafin Darasi

Waƙar Gaisuwa

Idan muka tashi da safeSai mu gai da iyayenmu x 2

Mamata ina kwanaGaisuwa ce da safe

Ina wuni BabanaGaisuwa ce da ranaMamata sai da safeGaisuwa ce da dare.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [masa]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [mama, masara, makaranta].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

17

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [K, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka dan-ganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [M, m].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [M], sautinsa /m/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [M] ta hanyar motsin jikin da aka dan-ganta da furta sautin harafin. “[M] na da sautin /m/ kamar a cikin kukan Saniya.” Ka/ki rinƙa ɗagawa

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

da miƙa wuyanka/ki gaba kana/kina furta sautin ‘m’ ‘m’ ‘mmoow’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A, a].

10. Koyawa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruf-fan [M, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

18

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ma].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [am, na].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [mama]

a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [amma, nama].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

19

Karatun Jimla Minti-3

1. Rubuta jimlar a kan allo [Mama na cin nama].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [cin].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Mama na gida.Mama na cin nama.Nana na masa.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2 20

Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 6 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [kogi, tsoro]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da kake/kike karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Mm, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 221

Zango Na: 1 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

Matashiya a kan Darasi Na 2

A kwaɗaita wa ɗalibai son gano keɓaɓɓun kalmomin darasin ‘Tafa Kalma’ da ke

haɗe da hoto a cikin littafin.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 7 a Littafin Karatu a Bayyane. Kalmomin da ta a koyar su ne [gwala-gwalai, mamaki].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [6] a cikin Littafin Karatu a Bayyane.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 6 a Littafin Karatu A Bayyane.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na bukatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me yasa ka/ki ke ganin yawancin ɗalibai sun tafa kalmomin daidai?

Me ka/ki ke ganin ya sa ka/kin ci nasarar koyar da wannan sashe na darasin?

Bayan waiwaye me ka/ki ke tunanin zaka/ki canza don koyar da tafa gaɓar kalma.

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

22

Kafin Darasi

Waƙar Haruffa

a, b, c, d, e, f, g, h!i, j, k, l, m, n, o, r!

s, t, u, w, y, z!

An taso daga makaranta‘Ya’yan kaji na wasa

Tare da ‘ya’yan HausawaKomai girman ɗan bokoBai wuce abachada ba!

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗalibai ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [saƙa]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [sanda, saniya, sarauniya].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

23

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [M, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [S s].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [S], sautinsa /s/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [S] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[S] na da sautin /s/ kamar a cikin kalmar saƙa.” Ka/ki riƙa lanƙwasa

Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6

hannuwa kamar kana/kina saƙa kana/kina furta sautin ‘s’ ‘s’ ‘saƙa’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [S, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

24

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [sa].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ma, na].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [kasa] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [sama, nasa].Karatun Jumla

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

25

Karatun Jimla Minti-3

1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na saƙa].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [saƙa].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Nana na saƙa. Nana ta saƙa hula. Hula na saman tebur.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2 26

Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 8 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [kwaɗayi, gunaguni]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

a

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kake karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sababbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ss, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutawa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 227

Zango Na: 1 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

Matashiya a kan Darasi Na 2

Yi amfani da azancin maganar hannu, kamar

ɗaga yatsa wajen ba ɗalibai dama don su ba da amsa

tare da kuma yi musu gyara a inda suka yi kuskure.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 9 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [faɗi, juya].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [8] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Tsarin Baƙaƙe.Aiki: Tono Kalma.Manufa: Zai jaddada sanin baƙaƙe a rubutu.Tsari: A ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen bin ba’asin ɗaiɗaikun baƙaƙe da kalmomi da

aka gabatar musu da su a cikin darasi, waɗanda suke cikin Littafin Ɗalibai.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na bukatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Wane taimako ne jami’an taimakawa malamai ya baka/ki a cikin darussan da suka gabata?

A wane ɓangare na darasi ne ka/ki ke buƙatar taimakon jami’an taimakawa malamai?

Ko kana da jami’an da ke taimaka maka/ki a makaranta? A waɗanne abubuwa ne ka/ki ke so jami’an su tattauna a lokacin taro malamai na gaba.

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

28

Kafin Darasi

Waƙar Tsafta

Tsafta TsaftaTsafta Tsafta Tsafta

TsaftaWanke hannu yara shi ne tsafta

TsaftaWanke baki yara shi ne tsafta

TsaftaWanka, wanki yara shi ne tsafta

TsaftaTsafta Tsafta

Tsafta Tsafta TsaftaTsafta.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [rana]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [rigima, rijiya, riga].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

29

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [S, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [R, r].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [R], sautinsa /r/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [R] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[R] na da sautin /r/ kamar a cikin

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

kalmar rawa.” Ka/ki ɗan yi ‘yar rawa kana/kina furta sautin ‘r’ ‘r’ ‘rawa’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [R, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

30

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ra].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ri].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [rina] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [rana, rini].

Jagoran Malamai - Aji 231

Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana

na rina riga].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [riga].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Rana ta fito. Nana na rina riga. Amina na rina riga.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 32

Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Rr, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutawa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 10 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [girmama, yafe]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

33

Matashiya a kan Darasi Na 2

Manufar ita ce a samu ɗalibai su iya karanta

kalmomi 9 cikin 10 babu kuskure. Idan ɗalibai sun kasa samun maki 90% a

karatun, to a sa su, su yi ta maimaita jimlar don samun

ƙwarewa.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 11 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [rassa, tsallake].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [10] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Gwanewa.Aiki: Tusa Karatu.Manufa: Tusa karatun labari sau da dama, domin ɗalibai su haɓaka gwanewarsu ta

hanyar ƙara ganin kalmomi da kuma aiki da su.Tsari: Sa su su tusa karatu sau da dama, sannan a dubi halin fahimtarsu.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Ko sun gane/ba su gane sunayen haruffa da sautin su ba?

Waɗanne ɓangarori ne suke baka/ki matsala wajen koyar da sunayen haruffa da sautinsu?

Me za ka/ki canza a cikin darasin bayan waiwaye?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafin su.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

34

Kafin Darasi

Waƙar Haruffa

a, b, c, d, e, f, g, h!i, j, k, l, m, n, o, r!

s, t, u, w, y, z!

An taso daga makaranta‘Ya’yan kaji na wasa

Tare da ‘ya’yan HausawaKomai girman ɗan bokoBai wuce abachada ba!

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [daka]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [Ladi, dila, dillali].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

35

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [R, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [D, d].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [D], sautinsa /d/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [D] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[D] na da sautin /d/ kamar a cikin kalmar daka.” Ka/ki riƙa ɗaga hannuwanka/ki sama kana/kina

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

sako su kamar mai daka, kana/kina furta sautin ‘d’ ‘d’ ‘daka’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i” ‘i” ‘ido’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [D, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

36

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [di].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [da, mi].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar

[damina] a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [dami, daka].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

37

1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana

na gyara dami].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [gyara].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Kaka na daka dawa. Nana na gyara dami. Sai ga mage.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 38

Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Dd, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 12 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [reshe, danƙo]. Faɗi kalmomin, kuma ka koyar da su ta hanyar amfani da sassan jikinka, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin

Jagoran Malamai - Aji 239

Zango Na: 1 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

Matashiya a kan Darasi Na 2

Karatun Amsa Amo: Nemi ɗalibai su karanta kalma ko jimla bayan ka/kin karanta

don gano ƙwarewarsu.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 13 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [dabara, ankara].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [12] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Gwanewa.Aiki: Karatun Tare.Manufa: Yi amfani da tusa karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba su

ƙwarin gwiwa. Tsari: Haɗa ɗalibai, sannan ka tsamo labarin da za su yi aiki a kai.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Ko kana ganin motsin sautuka sun yi sauƙi/tsauri ga ɗalibai?

Saboda me ka/ki ke ganin koyar da motsin sautuka ya yi sauƙi/tsauri?

Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin zaku tattauna da abokan aikin ka/ki a wurin taron malamai?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafin su.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

40

Kafin Darasi

Waƙar Gaisuwa

Idan muka tashi da safeSai mu gaida iyayen mu x 2

Mamata ina kwanaGaisuwa ce da safe

Ina wuni BabanaGaisuwa ce da ranaMamata sai da safeGaisuwa ce da dare.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [dafi]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [takalmi, titi, turmi].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

41

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [D, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [T t].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [T], sautinsa /t/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [T] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[T] na da sautin /t/ kamar a cikin kalmar tafi.” Ka/ki riƙa tafa

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

hannuwanka/ki kana/kina furta sautin ‘t’ ‘t’ ‘tafi’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [T, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

42

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ti].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ta].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [mata] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [titi, tasa].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

43

1. Rubuta jimlar a kan allo [tana

riƙe da tasa].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [riƙe].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin yara daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Kaka na kan tabarma. Nana na kan turmi. Tana riƙe da tasa.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 44

Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Tt, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 14 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [muhalli, mamaki]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Jagoran Malamai - Aji 245

Zango Na: 1 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

Matashiya a kan Darasi Na 2

Faɗaɗa kalmomi yana da alaƙa da ƙwarewa wajen

karatu. A koyar da ma’anar kalmomi, da jimlolinsu, da

labarin da suka ƙunsa.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 15 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [dabbobi, halaka].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [14] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Karatun Tare.

Manufa: Yi amfani da tusa karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba su ƙwarin gwiwa.

Tsari: Nemi ɗalibi ɗaya ya karanta labarin sau uku - shi kuma. Ɗaya zai yi bayani a kan abu guda da ya karanta sosai, da kuma ɗaya wanda zai gyara a gaba.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Ko kana ganin ɗaliban ka/ki suna iya/ ba su iya rubuta haruffa daidai? Me ya sa?

Wace matsala ka/ki ke fuskanta wurin koyar da rubutu?

Bayan waiwaye wace dabara zaka/ki canza wajen koyar da rubutu?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

46

Kafin Darasi

Waƙar Tsafta

Tsafta TsaftaTsafta Tsafta Tsafta

TsaftaWanke hannu yara shi ne tsafta

TsaftaWanke baki yara shi ne tsafta

TsaftaWanka, wanki yara shi ne tsafta

TsaftaTsafta Tsafta

Tsafta Tsafta TsaftaTsafta.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [tsafta]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [motsi, hatsi, tsintsiya].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

47

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [T, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ts ts].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ts], sautinsa /ts/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ts] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ts] na da sautin /ts/ kamar a cikin kalmar tsalle.” Ka/ki riƙa yin tsalle a

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

hankali kana/kina furta sautin ‘ts’ ‘ts’ ‘tsalle’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ts, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

48

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [tsa].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [tsi, ni].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar

[tsakani] a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [tsinka, tsanani].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

49

1. Rubuta jimlar a kan allo [Abba

na da tsananin tsafta].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [tsafta].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/

ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Abba na da tsintsiya. Abba na shara. Abba na da tsananin tsafta.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 50

Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ts, ts, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsunsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutawa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 16 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [samaniya, tashi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sababbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Jagoran Malamai - Aji 251

Zango Na: 1 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

Matashiya a kan Darasi Na 2

Yi amfani da ‘yar takarda mai ɗauke da keɓaɓɓun

kalmomi uku da aka koya, don tantance azancin

kowane ɗalabi/ɗalaba na tsamo kalmomin a lokacin da suke karatu da kansu.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 17 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [hikima, sulhi].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [16] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Tusa Karatu.

Manufa: Tusa karatun labari sau da dama, domin ɗalibai su haɓaka gwanewarsu ta hanyar daɗa ganin kalmomi da kuma aiki da su.

Tsari: Faɗa wa ɗalibai cewa suna karanta labarin ne don su ƙara goguwa wajen karatu, da sanin kalmomi, da muhallinsu, da kuma karanta kalma ba da garaje ba.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Wane taimako ne jami’in/ar taimakawa malamai ya/ta baka a cikin darussan da suka gabata?

A wane ɓangare na darasi ne ka/ki ke buƙatar taimakon jami’ian taimakawa malamai?

Ko kana da jami’in/ar da ke taimaka maka/ki a makaranta? A waɗanne abubuwa ne ka/ki ke so jami’ian su tattauna a lokacin taron malamai na gaba.

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2 52

Aikin Malami/Malama:A nan malami/malama zai/za ta yi aiki shi/ita kaɗai yayin da ɗalibai ke koyon aikin ta hanyar kallo da sauraron aikin da malami/malama yake/take yi.

Aikin Malami/Malama da Ɗalibai:A nan malami/malama zai/za ta yi aiki sa’annan ɗalibai su gwada yin aikin da malamin/malamar ya/ta gama aikatawa.

Aikin Ɗalibai:A nan ɗalibai kaɗai za su gwada yin aiki, yayin da malami/malama ke jagorantarsu.

Alamar akwati: An danganta sashen ‘Sunayen Haruffa da Sautukansu’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalin su ga alamar akwati da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar da’ira: An danganta sashen ‘Gano Gaɓar Kalma’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar da’ira da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar dala: An danganta sashen ‘Kalmomin da za a karanta’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar dala da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar tauraro: An danganta sashen ‘Karatun Jimla’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar tauraro da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar agogo: Wannan alamar na nuna wa malami/malama lokacin da zai/za ta ɗauka domin karantar da sashe.

Alamomi

Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

Jagoran Malamai - Aji 2

ZANGO NA 2Mako 1 - 8

Darasi 1 - 16

53

Jagoran Malamai - Aji 2 54

Manufar Malamai Manufar Ɗalibai

Zango na 2/ kashi na3

Jigo na filin wasa

Ƙarshen wannan sashe, ya kamata malamai su lura, tare da yin amfani da rubutaccen bayanin gano fahimtar ɗalibai, da kuma iyawarsu wajen:

• Tafa adadin gaɓoɓin kalma a kalmomi• faɗin sunan harafi da furta sautinsa• karanta kalmomi da jimlolin koyo• karanta labari da amsa tambayoyi• Rubuta harrufan koyo da kuma • Sauraren labari tare da amsa a ƙalla

tambayoyi uku, waɗanda amsoshinsu ke cikin labarin.

A wannan sashe an wayar da kanmu game da wasanni da holewa dake gudana a filin wasanni na makaranta da na unguwa.

Malamai su taimaka wa ɗalibai wajen kamantawa da kuma bambanta wasannin da suke yi a filin wasa da kuma waɗanda su Nana ke yi.

Ayyukan mako 1-4

A ƙarshen darasi na 1, ana son malamai su iya gano ƙwazon ɗalibai wajen iya karanta haruffa da gaɓoɓin kalma da kalmomin dake ƙunshe da haruffan koyo kamar haka:

• Mako na ɗaya: ‘B’, ‘b’, ‘A’, ’a’• Mako na biyu: ‘W’, ‘w’, ‘A’, ‘a’• Mako na uku: ‘G’, ‘g’, ‘I’ ‘i’• Mako na huɗu: ‘Y’, ‘y’, ‘I’, ‘i’

A ƙarshen darasi na 1, ana son ɗalibai su iya gano ƙwazonsu wajen iya karanta haruffa da gaɓoɓin kalma da kalmomi dake ƙunshe da haruffan koyo kuma su rubuta dai-dai kamar haka:

• Mako na ɗaya: ‘B’, ‘b’, ‘A’, ’a’

• Mako na biyu: ‘W’, ‘w’, ‘A’, ‘a’

• Mako na uku: ‘G’, ‘g’, ‘I’ ‘i’

• Mako na huɗu: ‘Y’, ‘y’, ‘I’, ‘i’

A ƙarshen darasi na 2, ana son malami ya iya gano ƙwazon ɗalibai, wajen iya karanta labari da kuma fahimtar abin da ya ƙunsa, a:

• Mako na ɗaya: Hanyar sauraren karatunsu.• Mako na biyu: Yi musu tambayoyi uku

waɗanda amsoshinsu ke cikin hoton labarin karatu a bayyane.

• Mako na uku: Yi musu tambaya ɗaya wadda amsar ke cikin labarin karatu a bayyane

• Mako na huɗu: Hanyar yin tambayoyi uku da amsoshinsu ke cikin Littafin Karatu A Bayyane.

A ƙarshen darasi na 2, ana son ɗalibai su iya gano ƙwazon su wajen iya karanta labari da kuma fahimtar abin da ya ƙunsa, a:

• Mako na ɗaya: Kalmomi da kuma kalmomin da suka koya.

• Mako na biyu: Yi musu tambaya uku wadda amsoshinsu ke cikin abubuwan dake cikin karatu a bayyane.

• Mako na uku: Yi musu tambaya uku wadda amsoshinsu ke cikin labarin karatu a bayyane

• Mako na huɗu: hanyar yin tambayoyi a ƙalla uku da amsoshinsu ke cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Shawara a kan auna/gwajin fahimta

A ƙarshen wannan sashe, malamai ysu maimaita baƙaƙen ‘B’ ‘W’ ‘G’ ‘Y’ da wasalin ‘A’, sannan su binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta ƙwazon kowane ɗaliban suka karanta:1. Gaɓoɓi da kalmomi ƙunshe da haruffan

koyo2. Jimloli dake cikin labarai da amsa

tambayoyin da suka dace.

Malamai su tisa aiki inda ya dace.

A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san matakin nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya furta haruffa da sanin kalmomi da Jimloli da kuma gane inda suke da ƙwarewa da kuma rauni daga malami/malama.

Ana son a ba ɗalibai shiryayyen aikin gida ko na koyo a gida.

Manufar Malamai Da Ɗalibai

Jagoran Malamai - Aji 255

Manufar Malamai Manufar Ɗalibai

Zango na 2

kashi na 4: Aji

Ƙarshen wannan sashe, ya kamata malamai su san ɗalibai da ke da matsala wajen karatu da rubutu, sannan ya shirya musu aikin da za su yi a waɗannan sassa:• Fahimtar ƙwayoyin sauti–bambance

sautin haruffa.• Karatu – iya karanta gaɓar kalma da

kalmomin koyo.• Ganewa a karantu – iya karatu dai-dai

wadaida, tare da fitar da ma’ana.• Ƙwarewa da fahimta - iya amsa

tambayoyin dake cikin labarin.

A wannan sashe za a gabatar wa ɗalibai ayyuka da Nana da Abba ke yi a makaranta.

Ana son malamai su taimaka wa ɗalibai wajen kamanta abubuwa ta hanyar yin bayanin wasu ayyukan da ke faruwa a makarantarsu.

Ayyukan mako 1-4

A ƙarshen darasi na 1, ana son malamai su iya gano ƙwazon ɗalibai wajen iya karanta haruffa da gaɓoɓin kalma da kalmomi dake ƙunshe da haruffan koyo kamar haka:• Mako na ɗaya: ‘L’, ‘l’, ‘U’, ’u’• Mako na biyu: ‘C’, ‘c’, ‘I’, ‘i’• Mako na uku: ‘Sh’, ‘sh’, ‘I’, ‘i’• Mako na huɗu: ‘H’, ‘h’, ‘U’, ‘u’

(ɗalibai su iya rubuta su dai dai)

A ƙarshen darasi na 1, ana son ɗalibai su iya ganewa da karanta da kuma rubuwa dai-dai na haruffa, gaɓoɓin kalma da kalmomin dake ƙunshe da haruffan koyo kamar haka:• Mako na ɗaya: ‘L’, ‘l’, ‘U’, ’u’• Mako na biyu: ‘C’, ‘c’, ‘I’, ‘i’• Mako na uku: ‘Sh’, ‘sh’, ‘I’, ‘i’• Mako na huɗu: ‘H’, ‘h’, ‘U’, ‘u’

(ɗalibai su gwada rubuta haruffan dai dai)

A ƙarshen darasin mako na 1-4, malami/ma ya/ta iya gane ƙwazon yara wajen:• iya karanta labari da kuma fahimtar abinda

labarin ya ƙunsa ta hanyar saurarensu lokacin da suke karatu,

• yi masu tambayoyi biyu da amsarsu ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin littafin Karatun A Bayyane.

A ƙarshen darasin mako na 1-4, ɗalibai su:• iya yin hasashen abinda zai faru dangane

da labarin da za a karanta,• su kuma iya karanta labarin da ke kunshe

da baƙin kalmomi• da kuma kalmomin da suka koya, • tare da amsa tambayoyi biyu da amsarsu

ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin littafin Karatun A Bayyane.

Auna fahimta

A ƙarshen wannan sashe malamai su maimaita baƙaƙen ‘L’ da baƙaƙen ‘C’ ‘Sh’ ‘H’ da wasulan ‘U’ ‘I’ sannan ya binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar rubuta bayanin ƙwazon kowane ɗalibai wajen:1. Karanta kalmomi da gaɓoɓi da kalmomin

dake ƙunshe a harrufan koyo

2. Iya karanta jimloli dake cikin labari da kuma amsar da ta dace da tambayoyi.

3. Malamai su tisa aiki inda ya dace.

A ƙarshen wannan sashe, ana son ɗalibai su san matakin nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya furta keɓaɓɓun haruffa da sanin kalmomi da jimloli ta hanyar samun bayannin ƙwarewarsu da rauninsu daga malamai.

Ana son a ba ɗalibai shiryayyen aikin gida ko na koyo a gida.

Jagoran Malamai - Aji 2 56

Kafin Darasi

Waƙar Gaisuwa

Idan muka tashi da safeSai mu gaida iyayenmu x 2

Mamata ina kwanaGaisuwa ce da safe

Ina wuni BabanaGaisuwa ce da ranaMamata sai da safeGaisuwa ce da dare

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [baba]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [babba, bishiya, dabara].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Jagoran Malamai - Aji 257

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ts, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [B b].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [B], sautinsa /b/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [B] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[B] na da sautin /b/ kamar a cikin kukan babur.” Ka/ki nuna alamar kana/kina kan babur kana/kina

Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6

murɗa hannun babur ɗin kana/kina furta sautin ‘b’ ‘b’ ‘boom-boom’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [B, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

58

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ba].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [bab, ni].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [baba] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [babba, babana].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

59

1. Rubuta jimlar a kan allo [Baba da Abba na wasa].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [wasa].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo. Abba a babban fili. Baba da Abba na wasa. Nana da Amina na wasa. Kowa na wasa a fili.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 60

Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 19 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [hantsi, birni]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su mai da hankali kan gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Bb, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 261

Zango Na: 2 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Matashiya a kan Darasi Na 2

Ba su dama su furta kalmomi, tare da jinsu a cikin waƙa yana haɓaka

fahimtarsu ta sauraro da gina kalmomi.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 20 a Litaffin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [abokinsa, buhuna].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [19] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Koyon Sabuwar Kalma.Manufa: Ba ɗalibai damar su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen

makaranta.Tsari: Keɓe minti ɗaya ko biyu a mako domin samun jin bayanin yadda ɗalibai suka

tsinci kalma, da kuma ma’anarta. Nemi ɗalibai su fito su rubuta kalmominsu a jikin allo.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me ka fahimci yawancin ɗalibai sun fi so ?

Me ka fi jin daɗin koyarwa a cikin darasinka ?

Bayan waiwaye waɗanne sassa ne ka/ki ke jin kana iya koyarwa yau ?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

62

Kafin Darasi

Waƙar Kirge

Ɗaya mafarin ƙirgeBiyu idanun dabba

Uku duwatsun murhuHuɗu ƙafafun tebur

Biyar na yatsun hannu.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [wake]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [wanka, rawa, taimakawa].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

63

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [B, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [W w].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [W], sautinsa /w/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [W] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[W] na da sautin /w/ kamar a cikin kalmar wanka.” Ka/ki kwatanta

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

watsa ruwa da cuɗawa kana/kina furta sautin ‘w’ ‘w’ ‘wanka.’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [W, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

64

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [wa].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [sa, san].

Kalmomin da za a karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [wasa] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [wata, wanka].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

65

1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana ta

yi wanka].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [yi].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo. Jiya an ga watan sallah. Nana ta yi wanka. Nana da Amina na rawa. Ana wasan sallah.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 66

Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 21 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [fushi, dace]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ww, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 267

Zango Na: 2 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

Matashiya a kan Darasi Na 2

A sa ɗalibai su yi hasashen ma’anar kalmomi, sannan

a saurari bayaninsu don tabbatar da hasashensu.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 22 a cikin Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [wahala, wurare].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [21] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Kalmomi.Aiki: Koyon Sabuwar Kalma.Manufa: Ba ɗalibai damar su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen

makaranta.Tsari: Samar da waje, ko allon manna sabbin kalmomi.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me ka gano ɗaliban ka sun fi ƙwarewa a wajen koyon sunayen haruffa da sautukansu?

A ina kake da matsala a wajen koyar da sunayen haruffa da sautukansu?

Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin ya kamata ka/ki canza wajen koyar da sunaye haruffa da sautukansu?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

68

Kafin Darasi

Waƙar Haruffa

a, b, c, d, e, f, g, h!i, j, k, l, m, n, o, r!

s, t, u, w, y, z!

An taso daga makaranta‘Ya’yan kaji na wasa

Tare da ‘ya’yan HausawaKomai girman ɗan bokoBai wuce abachada ba!

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [gari]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ganga, gatari, gajimarai].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

69

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [W, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [G g].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [G], sautinsa /g/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [G] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[G] na da sautin /g/ kamar a cikin kalmar gudu.” ka/ki kwatanta yin

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

gudu kaɗan kaɗan kana/kina furta sautin ‘g’ ‘g’ ‘gudu’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar(2- 5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [G, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

70

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [gi].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [gan, dan].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar

[Ringimi] a kan allo

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [gasa, ganga].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

71

1. Rubuta jimlar a kan allo [Ana

gasar kokawa a Ringimi].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [kokawa].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo. Ana gasar kokawa a Ringimi. Ana buga ganga. A gidan su Ali akwai ganga. Abba na gasar kokawa.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 72

Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 23 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gada, kwale-kwale]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Gg, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 273

Zango Na: 2 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

Matashiya a kan Darasi Na 2

Sanya ɗalibai su ba da labari abin da suka karanta

yana bai wa malamai damar gano fahimtarsu.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 24 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [giwa, teku].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [23] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Kalmomi.

Aiki: Kwaikwayon Bayanin Kalma.

Manufa: Don a ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen fahimtar sabbin kalmomi.

Tsari: Malami/ma zai/zata rubuta kalma a kan takarda.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan Ƙara Ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me za ka/ki iya cewa game da ɗaliban ka/ki wajen koyon motsin jikin da aka danganta da suna da sautin harafi?

Wace matsala ce ka/ki ka fuskanta wajen motsin jikin da aka danganta da suna da sautin harafi

Wace buƙata ce zaka/ki zo da ita wajen taron malamai a kan darasi don tattaunawa?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau ga iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

74

Kafin Darasi

Waƙar Kirge

Daya mafarin ƙirgeBiyu idanun dabba

Uku duwatsun murhuHuɗu ƙafafun tebur

Biyar na yatsun hannu.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [yau]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [rairayi, tsautsayi, matambayi].

Amon sautin gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

75

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [G, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Y y].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Y], sautinsa /y/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Y] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Y] na da sautin /y/ kamar a cikin kalmar yanka.” Ka/ki yi amfani da hannunka/ki a matsayin wuƙa

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

kana/kina yanka ɗayan hannun kana/kina furta sautin ‘y’ ‘y’ ‘yanka’

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido.’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Y, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

76

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [yi].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ya, wa].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [yayi] a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [iya, yawa].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

77

1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana

ta iya kwalliya].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [kwalliya].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo. Yau ma ana bikin sallah. Abba na yawon sallah. Nana ta iya kwalliya. Amina ma ta iya kwalliya. Sun sanya kayan yayi.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 25 a cikin Littafin Karatun A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [take, sauƙi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Yy, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

78

Jagoran Malamai - Aji 2

Matashiya a kan Darasi Na 2

Tsaro irin tambayoyin da za a yi wa ɗalibai tun farko zai taimaka wa malamai wajen

auna fahimtarsu.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 26 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [ainun, damu].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [25] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Kalmomi.

Aiki: Kwaikwayon Bayanin Kalma.

Manufa: Don a ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen fahimtar sabbin kalmomi.

Tsari: Ɗalibi zai fito gaban aji, ya kwaikwayi ma’anar kalmar.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Wane taimako ne jami’in/ar taimakawa malamai ya/ta baka a cikin darussan da suka gabata?

A wane ɓangare na darasi ne ka/ki ke buƙatar taimakon jami’an taimakawa malamai?

Ko kana da jami’in/ar da ke taimaka maka/ki a makaranta? A waɗanne abubuwa ne ka/ki ke so jami’an su tattauna a lokacin taron malamai na gaba.

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Zango Na: 2 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

79

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

80

Kafin Darasi

Waƙar Gaɓar Kalma

A, i, o, u, e!A, i, o, u, e!

Ba bi, bo, bu, be!Ba, bi, bo, bu, be!Ca, ci, co, cu, ce!Ca, ci, co, cu, ce!

Da, di, do, du, deeeee!!!

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [lada]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [langa, lauje, ludayi].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

81

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Y, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [L l].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [L], sautinsa /l/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita matakin na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [L] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[L] na da sautin /l/ kamar a cikin kalmar leƙa.” Ka/ki kwatanta leƙa

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

wani abu kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘leƙa’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [U u].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [U] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[U] na da sautin /u/ kamar a cikin kalmar ungo.” Ka/ki riƙa miƙa hannu zuwa ga ɗalibai kamar za a basu wani abu kana/kina furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo.’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [L, U], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

82

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [lu].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa

na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [lun, bu].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [lungu]

a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa

na biyar (1-5) da sauran kalmomin [ulu, lambu].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

83

1. Rubuta jimlar a kan allo [Amina a lungu cikin lambu].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [cikin].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo. Amina a lungu cikin lambu. Tana wasa da ulu. Ga Nana da littafin karatu. Sai suka zauna tare.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 84

Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 27 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [zaƙi, gudawa]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ll, Uu].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta harafin a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta harafin a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 285

Zango Na: 2 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

Matashiya a kan Darasi Na 2

Yi amfani da azancin tambaya cikin labari, don

gano fahimtar ɗalibai wajen ba da amsa.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 28 a Litaffin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [likita, girma].

3. Ka/ki tunafar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [27] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Kalmomi.Aiki: Kwaikwayon Bayanin Kalma.Manufa: Don a ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen fahimtar sabbin kalmomi.Tsari: Ɗalibi/Ɗalibar da ya/ta gano kalmar da aka kwaikwaya shi zai/ita zata

kwaikwayi kalmar gaba.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me ka/kika fahimci na faruwa da ɗalibai a lokacin karatun labari a bayyane?

Me ya kamata ka/ki yi don inganta karatun labari a bayyane?

Bayan waiwaye me ya kamata ka/ki yi don inganta koyar da karatun labari a bayyane?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

86

Kafin Darasi

Waƙar Gaisuwa

Idan muka tashi da safeSai mu gai da iyayen mu x 2

Mamata ina kwanaGaisuwa ce da safe

Ina wuni BabanaGaisuwa ce da ranaMamata sai da safeGaisuwa ce da dare.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin

1. Furta wannan kalma [ci]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ciki, ciniki, masallaci].

Amon sautin gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

87

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [L, U]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [C c].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [C], sautinsa /c/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [C] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[C] na da sautin /c/ kamar a cikin kalmar ci.” Ka/ki ɗauki hannunka/ki kana/kina sakawa a baki alamar cin

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

abinci kana/kina furta sautin ‘c’ ‘c’ ‘ ci’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [C, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

88

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ci].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [ki, kin].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [cinnaka] a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [cikin, abinci].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

89

1. Rubuta jimlar a kan allo [Cinnaka

ya ciji Amina].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [ciji].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Nana da Amina cikin aji. Amina na cin abinci a aji. Cinnaka ya ciji Amina. Amina ta ji ciwo.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 90

Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 29 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [kiyaye, haɗama]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Cc, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa akan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 291

Zango Na: 2 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

Matashiya a kan Darasi Na 2

Koyar da sabbin kalmomi uku, don kafa tushen sani

da fahimtar labari, tun kafin ɗalibai su saurari

‘Labarin Karatu a Bayyane.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 30 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [fari, matashi].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [29] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Fahimta.

Aiki: Sake ba da labari.

Manufa: Don gano fahimtar ɗalibai.

Tsari: Nemi ɗalibai su sake ba da labarin da basu jima da saurara ba, ko kuma karantawa ba, kamar dai yadda ainihin marubucinsa ya zubo shi.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me yasa ka/ki ke ganin ɗaliban ka/ki sun taka rawar gani a wannan darasin?

Ko ka/ki kan yaba wa ɗaliban ka/ki lokacin da suka taka rawar gani? Ta wace hanya?

Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin zaka/ki iya yi don ƙara yaba wa ɗaliban ka/ki?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

92

Kafin Darasi

Waƙar Haruffa

a, b, c, d, e, f, g, h!i, j, k, l, m, n, o, r!

s, t, u, w, y, z!

An taso daga makaranta‘Ya’yan kaji na wasa

Tare da ‘ya’yan HausawaKomai girman ɗan bokoBai wuce abachada ba!

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [hutu]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [huhu, hukuma, mahukumta].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

93

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [C, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [H h].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [H], sautinsa /h/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [H] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[H] na da sautin /h/ kamar a cikin Kalmar hamma.” ka/ki kwatanta yin

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

hamma kana/kina furta sautin ‘h’ ‘h’ ‘hamma’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [U u].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [U] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[U] na da sautin /u/ kamar a cikin kalmar ungo.” Ka/ki riƙa miƙa hannu zuwa ga ɗalibai kamar za a basu wani abu kana/kina furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo.’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [H, U], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

94

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [hu].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [la, tu].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [hutu] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [hutawa, hula].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

95

1. Rubuta jimlar a kan allo [Ali ya

cire hular Abba].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [cire].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo. Lokacin tara ya yi. Abba da Ali suna hutawa.

Abba ya sa farar hula. Ali ya cire hular Abba.

Abba ya ture hannun Ali.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 96

Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Hh, Uu].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 31 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [rumfa, sha’awar]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu..

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane. Aikin

Jagoran Malamai - Aji 297

Zango Na: 2 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

Matashiya a kan Darasi Na 2

A tabbatar ɗalibai sun koyi rubuta baƙi daga hagu zuwa

dama, sannan daga sama zuwa ƙasa, ta hanyar zagayen duba

aiki a cikin aji.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 32 a Litaffin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [salaf, tabɗi].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [31] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Fahimta.Aiki: Mu Tambayi Juna.Manufa: Sanin labari ciki da waje.Tsari: Nemi ɗalibai su yi tambaya ɗaya, wadda amsarta na cikin labari.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Wace matsala ka/ki ke fuskanta wajen koyar da gano gaɓar kalma, kalmomin da za a karanta, da karatun jimla?

Wane taimako ka/ki ke buƙata don inganta darasin ka/ki wajen koyar da ɗalibai?

Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin ya kamata masu kula da wannan shiri su yi don kawo canje-canje wajen gabatar da darasi?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

98

Kafin Darasi

Waƙar Tsafta

Tsafta TsaftaTsafta Tsafta Tsafta

TsaftaWanke hannu yara shi ne tsafta

TsaftaWanke baki yara shi ne tsafta

TsaftaWanka, wanki yara shi ne tsafta

TsaftaTsafta Tsafta

Tsafta Tsafta TsaftaTsafta.

1. Rubuta wannan waƙa a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [shiru]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [shayi, shinkafa, shiririta].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

99

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [H, U]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Sh sh].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Sh], sautinsa /sh/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita matakin na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Sh] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Sh] na da sautin /sh/ kamar a cikin kalmar shiru.” Ka/ki aza yatsan

Sunayen Haruffa dDa Sautukansu Minti-6

ka/ki a kan bakinka/ki kana/kina furta sautin ‘sh’ ‘sh’ ‘shiru’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [I i].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [I] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[I] na da sautin /i/ kamar a cikin kalmar ido.” Ka/ki nuna idon ka/ki da yatsa kana/kina furta sautin ‘i’ ‘i’ ‘ido’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Sh, I], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

A Picture of Abba with a plate of rice and A’isha with cup of tea inside the classroom. Include children in the background making noise.

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

100

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [shi].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓoɓin kalma [sha, ru].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [shayi]

a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [shiru, tashi].

Jagoran Malamai - Aji 2

Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

101

1. Rubuta jimlar a kan allo [Amina

ta zo da shayi].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [zo].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umarci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Amina ta zo da shayi. Abba ya zo da shinkafa. Abba ya zubar da shinkafa. Yara sun tashi suna surutu.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 102

Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Sh sh, Ii].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa, ko a bayan wani ɗalibi da suke tare.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 33 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ɗanɗano, ƙauri]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Jagoran Malamai - Aji 2103

Zango Na: 2 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

Matashiya a kan Darasi Na 2

Yin amfani da allon koyon rubutu na ɗalibai don ba

da damar auna ƙwarewa a rubutu nan take. A lokacin

da suka ɗaga allunansu don nuna yadda suke zana baƙi,

za a gani nan take.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 34 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [gutsuro, tsohuwa].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [33] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Fahimta.Aiki: Mu Tambayi Juna.Manufa: Sanin labari ciki da waje.Tsari: Nemi ɗalibai su yi tambaya ɗaya, wadda amsarta na cikin labari.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me ka/ki ke ganin shi ne aikin jami’in/ar taimakawa malamai?

Me ka/ki ka ƙaru da shi tun fara wannan shiri zuwa yau?

Bayan waiwaye waɗanne abubuwa ne ka/ki ke buƙatar karin taimako a kan su?

Aikin Gida

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

Jagoran Malamai - Aji 2 104

Aikin Malami/Malama:A nan malami/malama zai/za ta yi aiki shi/ita kaɗai yayin da ɗalibai ke koyon aikin ta hanyar kallo da sauraron aikin da malami/malama yake/take yi.

Aikin Malami/Malama da Ɗalibai:A nan malami/malama zai/za ta yi aiki sa’annan ɗalibai su gwada yin aikin da malamin/malamar ya/ta gama aikatawa.

Aikin Ɗalibai:A nan ɗalibai kaɗai za su gwada yin aiki, yayin da malami/malama ke jagorantarsu.

Alamar akwati: An danganta sashen ‘Sunayen Haruffa da Sautukansu’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalin su ga alamar akwati da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar da’ira: An danganta sashen ‘Gano Gaɓar Kalma’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar da’ira da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar dala: An danganta sashen ‘Kalmomin da za a karanta’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar dala da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar tauraro: An danganta sashen ‘Karatun Jimla’ da wannan alamar. A nan malami/malama zai/za ta jagoranci ɗalibai zuwa ga sashen ta hanyar jan hankalinsu ga alamar tauraro da ke cikin Littafin Ɗalibai.

Alamar agogo: Wannan alamar na nuna wa malami/malama lokacin da zai/za ta ɗauka domin karantar da sashe.

Alamomi

ZANGO NA 3Mako 1 - 9

Darasi 1 - 18

Jagoran Malamai - Aji 2105

Jagoran Malamai - Aji 2 106

Manufar Malamai Manufar Ɗalibai

Zango na uku

Jigo na 5Kasuwa

A ƙarshen wannan sashe, malamai su iya gano ɗaliban da ke da matsala wajen karatu da rubutu don shirya masu aikin taimako a waɗannna sassa:

• Fahimtar kwayoyin sauti – bambance sautin haruffa.

• Karatu - iya karanta gaɓar kalma da kuma kalmomin da aka keɓe.

• Gwanewa a karatu- iya karatu da kyau ta yadda zai fitar da ma’ana.

Kwarewa da fahimta – iya fahimtar labari da kuma iya tambayoyin da ke biye da labarin.

A wannan kashi, za a gabatar da abubuwan muhimmai da ke da dangantaka da kasuwanci a kasuwa.

Malami /ma ya/ta taimakawa ɗalibai fito da gudummuwar da suke bayarwa ga iyayensu wajen samar da kayan anfanin gona da ake sayar wa a kasuwar garinsu.

Ayyukan mako 1-4

A ƙarshen darussian mako na 1-4, malamai su iya gane ƙwazon ɗalibai wajen gane haruffan da karanta su,da kuma iya karanta gaɓoɓi da kalmomi masu ɗauke da haruffan nan.‘Kuma su iya rubuta su dai dai.

• Mako na ɗaya; ‘F’ ‘f’ ‘A’ ‘a’• Mako na biyu; ‘Ɗ’ ’ɗ ‘ ‘A’ ‘a’• Mako na uku; ‘J’ ’j’ ‘E’ ‘e’• Mako na huɗu ‘Z’ ’z’ ‘O’ ‘o’

A ƙarshen darussan mako na 1-4, ɗalibai su iya gane haruffa, karanta su da kuma iya karanta gaɓoɓi da kalmomi masu ɗauke da haruffan nan da ke rubuce a ƙasa. Ɗalibai su kuma gwada rubuta haruffan dai dai.

• Mako na ɗaya; ‘F’ ‘f’ ‘A’ ‘a’

• Mako na biyu; ‘Ɗ’ ’ɗ ‘ ‘A’ ‘a’

• Mako na uku; ‘J’ ’j’ ‘E’ ‘e’

• Mako na huɗu; ‘Z’ ’z’ ‘O’ ‘o’

A ƙarshen darasin mako na 1-4, malamai su iya gane ƙwazon ɗalibai wajen

• iya karanta labari da kuma fahimtar abinda labarin ya ƙunsa ta hanyar saurarensu lokacin da suke karatu,

• yi masu tambayoyi biyu da amsarsu ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

A ƙarshen darasin mako na 1-4, ɗalibai su

• iya yin hasashen abinda zai faru dangane da labarin da za a karanta,

• su kuma iya karanta labarin da ke kunshe da baƙin kalmomi

• da kuma kalmomin da suka koya, • tare da amsa tambayoyi biyu da amsarsu

ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Auna Fahimta A ƙarshen wannan kashi malami/ma ya/ta maimaita baƙaƙen ‘F’ ‘Ɗ’‘J’ ‘Z’ da wasullan ‘A’ ‘E’ ‘O’ sannan ya/ta binciki fahimtar ɗalibai ta hanyar:1. Aje bayanin ƙwazon kowane ɗalibi/ba

wajen karanta gaɓoɓi da kalmomin da ke ɗauke da haruffan da aka yi.

2. Aje bayanan ƙwazon kowane ɗalibi na iya karatun jimloli a cikin labari da amsa tambayoyi dai dai.

Malamai su tisa aiki, inda ya dace.

A ƙarshen wannan kashi, ɗalibai su san matakin nasarar da suka samu wajen ƙwarewa da iya furta keɓaɓɓun haruffa da sanin kalmomi da jimloli ta hanyar bada ƙwarin gwiwa a inda suka yi dai dai da kuma nuna kasawarsu inda ba su yi dai dai ba daga malami/ma.

Ana son a ba ɗalibai aikin gida ko na koyo a gida.

Manufar Malamai Da Ɗalibai

Jagoran Malamai - Aji 2107

Manufar Malamai Manufar Ɗalibai

Zango 3

Jigo na 6Safara

A ƙarshen wannan sashe, malamai su gano ɗaliban da ke da matsala wajen karatu da rubutu don shirya masu aikin taimako a waɗannna sassa:• Fahimtar kwayoyin sauti – bambance

sautin haruffa.• Karatu - iya karanta gaɓar kalma da kuma

kalmomin da aka keɓe.• Gwanewa a karatu- iya karatu da kyau ta

yadda zai fitar da ma’ana.

Kwarewa da fahimta – iya fahimtar labari da kuma iya amsa tambayoyin da ke biye da labarin.

A wannan sashe za a gabatar wa ɗalibai A wannan sashe, ɗalibai su gano hanyoyin daban daban na zuwa da dawowa kasuwa.

Malami /ma ya /ta taimakawa ɗalibai su dangantaka yanayi gidansu Nana

• Nana na zama da kakanninta yayin da Abba ke zaune da iyayensu. Ɗalibai su kawo matsayin su a kan wannan.

Ayyukan Mako na 1-5

A ƙarshen darussian mako na 1-4, malamai su iya gane ƙwazon yara wajen gane haruffan da karanta su da kuma iya karanta gaɓoɓi da kalmomi masu ɗauke da haruffan nan. Kuma su iya rubuta su dai dai:• Mako na ɗaya; ‘Ƙ’ ‘ƙ’ ‘U’ ‘u’• Mako na biyu; ‘Ƙw’ ‘ƙw’ ‘AI’ ‘ai• Mako na uku; ‘KW’ ‘kw’ ‘AI’ ‘ai’• Mako na huɗu ‘GW’ ‘gw’ ‘AU’ ‘au’ • Mako na biyar ‘ɓ’

A ƙarshen darussan mako na 1-4, ɗalibai su iya gane haruffa, karanta su da kuma iya karanta gaɓoɓi da kalmomi masu ɗauke da haruffan nan da ke rubuce a Kasa. Ɗalibai su kuma gwada rubuta haruffan dai dai:• Mako na ɗaya; ‘Ƙ’ ‘ƙ’ ‘U’ ‘u’• Mako na biyu; ‘Ƙw’ ‘ƙw’ ‘AI’ ‘ai’• Mako na uku; ‘KW’ ‘kw’ ‘AI’ ‘ai’• Mako na huɗu ‘GW’ ‘gw’ ‘AU’ ‘au’• Mako na Biyar ‘ɓ’

A ƙarshen darasin mako na 1-4, malamai/ su iya gane ƙwazon yara wajen:• iya karanta labari da kuma fahimtar abinda

labarin ya ƙunsa ta hanyar saurarensu lokacin da suke karatu,

• yi masu tambayoyi biyu da amsarsu ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

A ƙarshen darasin mako na 1-4, ɗalibai su:• iya yin hasashen abinda zai faru dangane

da labarin da za a karanta,• su kuma iya karanta labarin da ke kunshe

da baƙin kalmomi• da kuma kalmomin da suka koya, • tare da amsa tambayoyibiyu da amsarsu

ke cikin labarin da kuma tambaya ɗaya da amsarta bata cikin labaran da aka karanta daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Auna Fahinta

A ƙarshen wannan kashi malami ya maimaita bakaken‘Ƙ’ ‘ƘW’ ‘KW’ ‘GW’ da ‘ɓ’ da wasullan ‘U’ ‘AI’ ‘AU’sannan ya binciki fahimtar yara ta hanyar:1. Aje bayanin ƙwazon kowane yaro wajen

karanta gaɓoɓi da kalmomin da ke ɗauke da haruffan da aka yi.

2. Aje bayanan ƙwazon kowane ɗalibai na iya karatun jimloli a cikin labari da amsa tambayoyi dai dai.

Malamai tisa aiki, inda ya dace.

A ƙarshen wannan kashi, ɗalibai su san matakin nasarar da suka samu wajen ƙwarewa ga iya furta keɓaɓɓun haruffa da sanin kalmomi da jimloli ta hanyar bada ƙwarin gwiwa a inda suka yi dai dai da kuma nuna kasawarsu inda ba su yi dai dai ba daga malamai.

A ba ɗalibai shiryayyen aikin gida/aikin da zasu riƙa koyo a gida.

Jagoran Malamai - Aji 2 108

Kafin Darasi

Waƙar Motsa jiki

Yara mu tafa, muna ta tafawa Mu tashi, muna ta tasawa Mu juya, muna ta juyawa Mu duƙa, muna ta duƙawa

Mu zauna, muna ta zaunawa.

1. Rubuta waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [fara]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [fari, fartanya, fatimatu].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Jagoran Malamai - Aji 2109

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Sh, I]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [F, f].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [F], sautinsa /f/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [F] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[F] na da sautin /f/ kamar a cikin kalmar fere.” Ka/ki ɗaga yatsa ɗaya kana/kina mai kwatanta fere fensiri

Sunayen Haruffa da Sautukansu Minti-6

kana/kina furta sautin ‘f’ ‘f’ ‘fere’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A, a].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [F, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan. Ka/ki nemi ɗalibai su faɗi sunayen haruffan.

Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Jagoran Malamai - Aji 2 110

Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [fa].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ra, da].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [fara] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [dafa, fadama].

Jagoran Malamai - Aji 2111

Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

1. Rubuta jimlar a kan allo [Sun haɗu da fadawa].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [haɗu].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya banbanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Ana sayar da fara a kasuwa. Aimina ta sayi fara. Nana na dafa shinkafa. Za su kai wa kaka. Sun haɗu da fadawa.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 112

Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 36 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gangara, rafi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ff, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kai/ke ma kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2113

Zango Na: 3 Mako Na: 1 Darasi Na 1 da Na 2

Matashiya a kan Darasi Na 2

Yi amfani da duk damar da ka samu wajen ganin

ɗalibai sun nuna iyawarsu ta hanyar saka su rubuta haruffa ko kalmomin da

aka koyar da su.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 37 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za’a koyar su ne [nutse, lura].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [36] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Tsarin Baƙaƙe.Aiki: Ginin Gaɓoɓi.Manufa: Jaddada iya amfani da sauti.Tsari: Yi amfani da gaɓoɓin kalmar da aka koyar a cikin darasi (misali: ka, na). A

rubuta su a jikin allo. Nemi ɗalibai su ƙirƙiro sabbin gaɓoɓi, ta hanyar canza baƙaƙen farko (mislai: ta, ma).

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Waɗanne abubuwa ka/ki ke yi don ƙawata aji da rubuce-rubuce?

Me ya kamata ka/ki umurci ɗalibai su zo dasu don ƙawata aji?

Bayan waiwaye wace hanya za ka/ki mayar da ajin ka/ki abin sha’awa?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 114

Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

Kafin Darasi

Waƙar gaisuwa

Idan muka tashi da safeSai mu gai da iyayenmu x 2

Mamata ina kwanaGaisuwa ce da safe

Ina wuni BabanaGaisuwa ce da ranaMamata sai da safeGaisuwa ce da dare.

1. Rubuta waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [ɗa]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ɗaya, ƙafaɗa, mashinfiɗi].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2115

Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [F, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ɗ, ɗ].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ɗ], sautinsa /ɗ/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ɗ] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ɗ] na da sautin /ɗ/ kamar a cikin kalmar ɗanɗano.” Ka/ki kwatanta

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

ɗanɗana miya kana/kina furta sautin ‘ɗ’ ‘ɗ’ ‘ɗanɗano’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A, a].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ɗ, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 116

Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ɗa].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ɗi, gir].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [ɗari] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [faɗi, kafaɗa].

Jagoran Malamai - Aji 2117

Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

1. Rubuta jimlar a kan allo [Abba ya ɗauki dawa a kafaɗarsa].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [ɗauki].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Lokacin ɗari dawa kan nuna. Lokacin girbi ya yi. Kaka da Abba suna gona. Kaka da Abba suna girbin dawa. Abba ya ɗauki dawa a kafaɗarsa.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 118

Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 38 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gwada, daji]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ɗɗ, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2119

Zango Na: 3 Mako Na: 2 Darasi Na 3 da Na 4

Matashiya a kan Darasi Na 2

Katin I ko A’a - Yanki ’yan takardu ko kwalaye. Sai a rubuta l a gaba, sannan A’a a baya. Nemi ɗalibai

su ɗaga katin wajen ba da amsar tambaya.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 39 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [kunya, haƙuri]

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [38] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Tsarin Baƙaƙe.Aiki: GininKalmomi.Manufa: Jaddada sanin baƙaƙe a rubutu.Tsari: Ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen bin bahasin ɗaiɗaikun baƙaƙe da

kalmomin da aka gabatar musu a cikin darasi.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me ka/kika fahimci na faruwa da ɗalibai a lokacin karatun labari a bayyane?

Me ya kamata ka yi don inganta karatun labari a bayyane?

Bayan waiwaye me ya kamata ka yi don inganta koyar da karatun labari a bayyane?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 120

Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

Kafin Darasi

Waƙar Haruffa

a, b, c, d, e, f, g, h!i, j, k, l, m, n, o, r!

s, t, u, w, y, z!

An taso daga makaranta‘Ya’yan kaji na wasa

Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba!

1. Rubuta waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [jera]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [jaki, gajere, gajiyayyu].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2121

Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ɗ, A]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [J j].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [J], sautinsa /j/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [J] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[J] na da sautin /j/ kamar a cikin

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

kalmar ji.” Ka/ki riƙe kunne kana/kina furta sautin ‘j’ ‘j’ ‘ji’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [E, e]

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [E] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [E] na da sautin /e/ kamar a cikin kalmar eeh.” Ka/ki riƙa sunkuyar da kai sama da ƙasa alamar aminicewa kana/kina furta sautin ‘e’ ‘e’ ‘eeh’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [J, E], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 122

Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [je].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ji, ja].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [daji] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [je, kujera].

Jagoran Malamai - Aji 2123

Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

1. Rubuta jimlar a kan allo [Zai je kasuwa da dawa].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [zai].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jumlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Ga Kaka da jakinsa. Ya jera dawa a bayan jaki. Zai je kasuwa da dawa. Jaki ya bi ta daji a guje. Kaka yana bin jaki a baya. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da

yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 124

Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 40 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙirga, tunani]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Jj, Ee].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2125

Zango Na: 3 Mako Na: 3 Darasi Na 5 da Na 6

Matashiya a kan Darasi Na 2

Ana son malamai su mammanna hotuna ko

kalmomi, ko tsarin baƙaƙe, ko wata waƙa, ko kuma aikin ɗalibai a wurare

daban-daban a cikin aji.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 41 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [lura, hira].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [40] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Iya Karatu.Aiki: Maimaita Karatu.Manufa: Haɓaka ƙwarewar ɗalibai ta hanyar yawan ganin kalmomi da kuma aiki da su.Tsari: Faɗawa ɗalibai cewa, suna karanta labarin ne don su ƙara ƙwarewa wajen

iya karatu,da sanin kalmomi, da muhallinsu, da kuma karanta kalma ba da tangarɗa ba.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me yasa ka/ki ke ganin ɗaliban ka/ki sun taka rawar gani a wannan darasin?

Ko ka/ki kan yaba wa ɗaliban ka/ki lokacin da suka taka rawar gani? Ta wace hanya?

Bayan waiwaye me ka/ki ke ganin zaka iya yi don ƙara yaba wa ɗalibanka?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 126

Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

Kafin Darasi

Waƙar Gaɓar Kalma

A, i, o, u, e!A, i, o, u, e!

Ba bi, bo, bu, be!Ba, bi, bo, bu, be!Ca, ci, co, cu, ce!Ca, ci, co, cu, ce!

Da, di, do, du, deeeee!!!

1. Rubuta waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [zo]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [zane, zakara, zabarmawa].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2127

Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [J, E]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Z z].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Z], sautinsa /z/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Z] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Z] na da sautin /z/ kamar a cikin kalmar zane.” Ka/ki kwatanta yin zane. kana/kina furta sautin ‘z’ ‘z’ ‘zane’.

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [O o].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [O] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [O] na da sautin /o/ kamar a cikin kalmar oho.” Ka/ki riƙa buɗe hannayenka/ki kana/kina ɗaga kafaɗa nuna alamar rashin damuwa kana/kina furta sautin ‘o’ ‘o’ ‘oho’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Z, O], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 128

Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [zo].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [za, ne].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [zomo]

a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [zane, zakara].

Jagoran Malamai - Aji 2129

Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

1. Rubuta jimlar a kan allo [A gidan Kaka akwai dabbobi].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [akwai].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

A gidan Kaka akwai dabbobi. Nana na da zomo da zakara. Zomo na tono a gindin bishiya. Zakara na cin dawa. Nana ta kori zakara da gudu. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da

yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 130

Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 42 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙanwa, lambu]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatu A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Zz, Oo].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2131

Zango Na: 3 Mako Na: 4 Darasi Na 7 da Na 8

Matashiya a kan Darasi Na 2

Nemi ɗalibai su gwada rubuta kalmomin da

suka ga an mammanna a cikin aji, bayan sun gama

ayyukan da aka sa su a cikin aji.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 43 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [hira, wasa].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [42] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Iya Karatu.Aiki: Maimaita Karatu.Manufa: Haɓaka ƙwarewar ɗalibai ta hanyar yawan ganin kalmomi da kuma aiki da su.Tsari: Sa ɗalibai maimata karatu sau da dama, sannan a auna fahimtarsu.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Me yafi faranta maka/ki rai a wannan darasin na yau?

Wane ɓangare ne na darasin yau bai yi maka/ki daɗi ba?

Bayan waiwaye waɗanne ɓangarori ne ka/kika samu nasara a kan su cikin waɗanda ka/kika taɓa samun matsala da su?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 132

Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

Kafin Darasi

Waƙar Ƙirge

Ɗaya mafarin ƙirgeBiyu idanun dabba

Uku duwatsun murhuHuɗu ƙafafun tebur

Biyar na yatsun hannu

1. Rubuta waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [ƙura]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ƙurji, ƙuruciya, baƙunci].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2133

Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Z, O]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ƙ ƙ].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ƙ], sautinsa /ƙ/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ƙ] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ƙ] na da sautin /ƙ/ kamar a cikin kalmar ƙirge.” Ka/ki ɗaga hannunka/ki sama kana/kina

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

kwatanta yin ƙirge kana/kina furta sautin ‘ƙ’ ‘ƙ’ ‘ƙirge’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [U, u].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [U] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[U] na da sautin /u/ kamar a cikin kalmar ungo.” Ka/ki riƙa miƙa hannu zuwa ga ɗalibai kamar za a basu wani abu kana/kina furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo.’

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ƙ, U], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 134

Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ƙu].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa

na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [gu, ra].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [ƙura] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [tuƙa, ƙusa].

Jagoran Malamai - Aji 2135

Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

1. Rubuta jimlar a kan allo [motar Baba ta yi ƙura sosai].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [sosai].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa.

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya banbanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Baba da mama a mota. Suna dawowa daga kasuwa. Baba yana tuƙa mota. Motar Baba ta yi ƙura sosai. Ƙusa ta fasa tayar motar Baba. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da

yatsa a ƙasan kowace kalma

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 136

Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 44 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [ƙiba, attarugu]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ƙƙ, Uu].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2137

Zango Na: 3 Mako Na: 5 Darasi Na 9 da Na 10

Matashiya a kan Darasi Na 2

Samar da babbar takarda dake ɗauke da baƙin

kalmomi da ɗalibai za su ci karo da su a littattafansu.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 45 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [bayani, tsumbure].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [44] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Iya Karatu.Aiki: Karatun Tare.Manufa: Yi amfani da maimaita karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba

su ƙwarin gwiwa. Tsari: Haɗa ɗalibai, sannan ka tsamo labarin da za su yi aiki akai.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Wane cigaba ka/ki ke ganin ɗaliban ka/ki suke samu a cikin darussan ka/ki?

Ko akwai ɓangarorin darussan ka/ki da ba ka/ki ji daɗin fahimtar ɗaliban ka/ki a kan su ba?

Bayan waiwaye waɗanne ɓangarori ne ɗaliban ka/ki suka fi samun nasara a wannan shekara?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 138

Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

Kafin Darasi

Waƙar Haruffa

a, b, c, d, e, f, g, h!i, j, k, l, m, n, o, r!

s, t, u, w, y, z!

An taso daga makaranta‘Ya’yan kaji na wasa

Tare da ‘ya’yan Hausawa Komai girman ɗan boko Bai wuce abachada ba!

1. Rubuta wannan waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [ƙwai]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ƙwarewa, ƙwarai, maƙwabtaka].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2139

Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ƙ, U]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ƙw, ƙw].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ƙw], sautisa /ƙw/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ƙw] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ƙw] na da sautin /ƙw/ kamar a cikin kalmar ƙwaƙwa.” Ka/ki lanƙwasa hannunka/ki zuwa

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

hammata kana/kina karkaɗawa kana/kina furta sautin ‘ƙw’ ‘ƙw’ ‘ƙwaƙwaƙwa’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [Ai, ai].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ai] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [Ai] na da sautin /ai/ kamar a cikin kalmar aiki.” Ka/ki kwatanta yin wani aiki kana/kina furta sautin ‘ai’ ‘ai’ ‘aiki’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ƙw, Ai], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 140

Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ƙwai].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ƙwa, ai].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [ƙwai] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [ƙwarya, ƙwarai].

Jagoran Malamai - Aji 2141

Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

1. Rubuta jimlar a kan allo [Kaka ta ɗauki ƙwai a ƙwarya].

2. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar da aka ja wa layi a cikin jimlar [ɗauki].

3. Nuna, kuma ka/ki karanta baƙuwar kalmar tare da ɗalibai.

4. Umurci ɗalibai daban-daban su karanta baƙuwar kalmar.

5. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa

6. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

7. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

8. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

9. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Nana na tara ƙwai a ƙwarya. Kaka da maƙwabtanta za su

kasuwa. Kaka ta ɗauki ƙwai a ƙwarya. Maƙwabciyarta ta ɗauko

ƙwaƙwaƙwa. ƙwaryar Kaka tana da kyau ƙwarai. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da

yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5Karatun Jimla Minti-3

Jagoran Malamai - Aji 2 142

Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 46 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [gane, hali]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ƙw ƙw, AI ai].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2143

Zango Na: 3 Mako Na: 6 Darasi Na 11 da Na 12

Matashiya a kan Darasi Na 2

Manna sabuwar kalma a kowace rana, kuma a

nemi ɗalibai su gano/faɗi ma’anar kalmar.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 47 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [attajiri, kuka].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [46] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Iya Karatu.Aiki: Karatun Tare.Manufa: Yi amfani da maimaita karatu ta hanyar haɗa ɗalibai su yi karatu tare, don ba

su ƙwarin gwiwa. Tsari: Nemi ɗalibi ɗaya ya karanta labarin sau uku, shi kuma ɗaya ɗalibin yayi bayani

akan abu guda da aka karanta sosai, da kuma abu ɗaya wanda za a gyara a gaba.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Waɗanne irin abubuwa ne ka/kika samu gudumawa a kan su daga jami’an taimakawa malamai a wannan shekara?

Waɗanne ɓangarorin darasi ne shugaban makaranta ya taimaka maka/ki a kan su a wannan shekara?

Bayan waiwaye me ka inganta daga cikin taimakon horon da ka samu daga jami’an taimakawa malamai da kuma shugaban makaranta?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 144

Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

Kafin Darasi

Waƙar Ƙirge

Ɗaya mafarin ƙirgeBiyu idanun dabba

Uku duwatsun murhuHuɗu ƙafafun tebur

Biyar na yatsun hannu.

1. Rubuta wannan waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [akwai]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [kwaikwayo, bakwai, ƙwabbai].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2145

Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Ƙw, Ai]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Kw, kw].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Kw], sautinsa /kw/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [kw] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Kw] na da sautin /kw/ kamar a cikin kalmar kwalliya.” Ka/ki

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

kwatanta yin kwalliya kana/kina furta sautin ‘kw’ ‘kw’ ‘kwalliya’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [Ai, ai].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ai] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [Ai] na da sautin /ai/ kamar a cikin kalmar aiki.” Ka/ki kwatanta yin wani aiki kana/kina furta sautin ‘ai’ ‘ai’ ‘aiki’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Kw, Ai], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 146

Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [kwai].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [kwa, yo].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar

[kwakwa] a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [kwaikwayo, akwai].

Jagoran Malamai - Aji 2147

Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

1. Rubuta jimlar a kan allo [Nana na kwaikwayon kwalliyar Mama]

2. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa

3. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

4. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

5. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

6. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Jimla Minti-3

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin ta su fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Nana ta je garin Ringimi. Mama na kwalliya a cikin ɗaki. Nana na kwaikwayon kwalliyar

Mama. Sun yi kwalliya za su je kasuwa. Za su sayo kaji guda bakwai. Sun ga kwano cike da kwakwa. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da

yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2 148

Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 48 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [makirci, rarraba]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Kw kw, AI ai].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2149

Zango Na: 3 Mako Na: 7 Darasi Na 13 da Na 14

Matashiya a kan Darasi Na 2

Manna wannan tsarin ba da labarai, wanda zai taimaka

wa ɗalibai wajen gina labari, kamar haka:

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 49 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [rani, shanuwa].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [48] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Kalmomi.Aiki: Koyon Sabuwar Kalma.Manufa: Ba ɗalibai dama su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen

makaranta.Tsari: Keɓe ‘yan mintina a mako domin samun jin bayanin yadda ɗalibai suka tsinci

kalma, da kuma ma’anarta. Nemi ɗalibai su fito su rubuta kalmominsu a jikin allo.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

A farkon shekaran nan waɗanne matsaloli ne ka/kika samu wajen tsarin darasin ka/ki?

Me ka ke ganin ya sa ka/ki ke cigaba da samun waɗannan matsaloli?

Bayan waiwaye waɗanna shawarwari ne za ka/ki iya ba malamai a wajen taron malamai?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Taken Labari

Farkon Labari Tsakiyar Labari Ƙarshen Labari

Jagoran Malamai - Aji 2 150

Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

Kafin Darasi

Waƙar Gaɓar Kalma

A, i, o, u, e!A, i, o, u, e!

Ba bi, bo, bu, be!Ba, bi, bo, bu, be!Ca, ci, co, cu, ce!Ca, ci, co, cu, ce!

Da, di, do, du, deeeee!!!

1. Rubuta waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [gwauro]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [gwaza, gwaiba, gwauruwa].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2151

Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Kw, Ai]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Gw gw].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Gw], sautinsa /gw/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Gw] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Gw] na da sautin /gw/ kamar a cikin kalmar gwalo.” Ka/ki riƙa yin

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

gwalo kana/kina furta sautin ‘gw’ ‘gw’ ‘gwalo’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na bakwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [Au au].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [Au] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [Au] na da sautin /au/ kamar a cikin kalmar auna.” Ka/ki kwatanta auna hatsi kana/kina furta sautin ‘au’ ‘au’ ‘auna’.

11. Maimaita mataki na bakwai da na takwas (7-8).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Gw, Au], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 152

Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [gwau].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [gwai, za].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar

[gwauro] a kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-dabann.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [gwaza, gwaiba].

Jagoran Malamai - Aji 2153

Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

1. Rubuta jimlar a kan allo [Ya haɗu da gwauro a hanya].

2. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa

3. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

4. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

5. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

6. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Jimla Minti-3

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Kaka da jakinsa zai je kasuwa. Yana ɗauke da buhun gwaza. Ya haɗu da gwauro a hanya. Kaka ya dawo daga kasuwa. Ya sayo wa Nana kwandon

gwaiba. 5. Karanta labarin, kana/kina bi da

yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2 154

Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 50 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

3. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [tumu, damina]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

4. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin.

5. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

6. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

7. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun Labarai A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [GW gw, AU au].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2155

Zango Na: 3 Mako Na: 8 Darasi Na 15 da Na 16

Matashiya a kan Darasi Na 2

Ana son malamai su mammanna hotuna da

sabbin kalmomi, ko tsarin baƙaƙe, ko wata waƙa, ko

kuma aikin ɗalibai a wurare daban-daban a cikin aji.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 51 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [face, gudummawa].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [50] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Kalmomi.Aiki: Koyon Sabuwar Kalma.Manufa: Ba ɗalibai damar su faɗa wa abokansu sabbin kalmomin da suka koya a wajen

makaranta.Tsari: Samar da waje, ko allon manna sabbin kalmomi.

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

A farkon wannan shiri waɗanne ɓangarori ne ka/kika samu matsala da su a cikin darasin ka/ki?

Daga cikin waɗannan matsalolin da ka/kika rubuta a sama, yanzu waɗanne ka/kika samu ci gaba a kan su?

Bayan waiwaye wace shawara zaka/ki iya ba sabon malami/ma a wannan shirin?

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 156

Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18

Kafin Darasi

Waƙar Gaɓar Kalma

A, i, o, u, e!A, i, o, u, e!

Ba bi, bo, bu, be!Ba, bi, bo, bu, be!Ca, ci, co, cu, ce!Ca, ci, co, cu, ce!

Da, di, do, du, deeeee!!!

1. Rubuta waƙar a kan allo.

Waƙa Minti-3

1. Rera waƙar don ɗalibai su ji, tare da kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa, don taimaka wa ɗalibai sanin ma’anar kalmomin da ke cikin waƙar.

2. Sake rera waƙar tare da nuna kalmomin a kan allo.

3. Sake rera waƙar tare da ɗalibai.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su rera waƙar suna kwaikwayon abin da waƙar ke faɗa.

5. Nemi ɗalibi/ɗaliba ɗaya ko fiye don rera waƙar tare da nuna kalmomin.

1. Furta wannan kalma [ɓalle]. Idan akwai hoton kalmar, sai a taimaki ɗalibai su gano ta cikin hoton da ke littafinsu.

2. Maimaita furta kalmar tare da tafa kowace gaɓa.

3. Nuna yawan gaɓoɓin da ke cikin kalmar da yatsun hannu.

4. Ka/ki ce wa ɗalibai su furta kalmar tare da tafa kowace gaɓar kalma tare da kai/ke.

5. Maimaita mataki na ɗaya zuwa na huɗu (1-4) da sauran kalmomin [ɓera, ɓangare, ɓanɓarowa].

Amon Sautin Gaɓa Minti 2

Jagoran Malamai - Aji 2157

Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18

1. A tunawa ɗalibai haruffan da suka gabata [Gw, Au]. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan, da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

2. Rubuta babba da ƙaramin baƙi na sabon harafi [Ɓ ɓ].

3. Nuna harafin ka/ki faɗi sunansa da kuma sautinsa. “Wannan shi ne harafin [Ɓ], sautinsa /ɓ/.”

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar akwati. Maimaita mataki na uku (3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) da wasu rukunan ɗalibai daban-daban.

6. Koya wa ɗalibai furta sautin [Ɓ] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “[Ɓ] na da sautin /ɓ/ kamar a cikin kalmar ɓare.” Ka/ki riƙa yin kamar

Sunayen Haruffa Da Sautukansu Minti-6

kana/kina ɓare wani abu kana/kina furta sautin ‘ɓ’ ‘ɓ’ ‘ɓare’.

7. Dukkan ɗalibai su shiga cikin aikin motsin jikin furta sautin tare da Malami/Malama.

8. Maimaita mataki na batkwai (7) tare da wasu ɗalibai daban-daban.

9. Maimaita mataki na biyu zuwa na biyar (2-5) da ɗaya harafin [A a].

10. Koya wa ɗalibai furta sautin [A] ta hanyar motsin jikin da aka danganta da furta sautin harafin. “ [A] na da sautin /a/ kamar a cikin mamaki.” Ka/ki ɗaga hannuwanka/ki sama cikin mamaki kana/kina furta sautin ‘ah!’ ‘ah!’

11. Maimaita mataki na shida da na bakwai (6-7).

12. Yi ta aikin bambanta sunayen haruffan [Ɓ, A], da sautukansu, ko kuma motsin jikin da aka danganta da haruffan.

Jagoran Malamai - Aji 2 158

Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18

1. Rubuta gaɓar kalma a kan allo [ɓa].

2. Nuna kowane harafi da ke cikin gaɓar, kana/kina furta sautinsa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan gaɓar ka/ki bi ta daga hagu zuwa dama kana/kina furta sautinta da sauri.

Gano Gaɓar Kalma Minti-6

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar da’ira. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran gaɓobin kalma [ɓul, ɓe].

Kalmomin da za a Karanta Minti-5

1. Rubuta wannan kalmar [ɓata] a

kan allo.

2. Nuna kowace gaɓa da ke cikin kalmar kana/kina karantawa a hankali.

3. Aza yatsa a ƙasan kalma ka/ki karanta ta daga hagu zuwa dama, cikin sauri.

4. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar dala. Maimaita mataki na biyu zuwa na uku (2-3) ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

5. Maimaita mataki na huɗu (4) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

6. Maimaita mataki na farko zuwa na biyar (1-5) da sauran kalmomin [ɓullowa, taɓarya].

Jagoran Malamai - Aji 2159

Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18

1. Rubuta jimlar a kan allo [Taɓaryar Kaka ta ɓata ].

2. Karanta jimlar kana/kina aza yatsa a ƙasan kowace kalma, yayin karantawa

3. Jagoranci ɗalibai zuwa ga sashe mai alamar tauraro a Littafin Ɗalibai.

4. Karanta jimlar tare da ɗalibai.

5. Maimaita karanta jimlar ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

6. Maimaita mataki na takwas (8) tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Jimla Minti-3

1. Faɗa wa ɗalibai cewa za ka/ki karanta musu labari, ka/ki ja hankalinsu zuwa ga hoton da ke cikin littafinsu.

2. Jagoranci ɗalibai su iya bambanta zanen hotuna, da kuma aikin da hotunan ke nunawa.

3. Kira wasu ɗaliban don su yi bayanin tasu fahimta.

4. Rubuta labarin a kan allo.

Taɓaryar Kaka ta ɓata Nana da Amina sun fita neman

taɓarya. Nana ta gano taɓarya a hanyar

kasuwa. Amma taɓaryar ta ɓaci a gefe

ɗaya. Kaka tayi murnar ganin

taɓaryarta.

5. Karanta labarin, kana/kina bi da yatsa a ƙasan kowace kalma.

6. Maimaita karanta labarin ta hanyar amfani da Littafin Ɗalibai.

7. Sake maimaita karatun tare da rukunin ɗalibai daban-daban.

Karatun Labari Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2 160

Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18

Karatun Labari A Bayyane Minti-5

1. Buɗa shafi na 52 a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

2. Karanta taken labari. Nuna hoto idan akwai shi. Tambayi ɗalibai su yi hasashen abin da zai iya faruwa a cikin labarin da za a karanta a yau.

2. Koyar da ma’anar sabbin kalmomi ta hanyar da ɗalibai za su fahimta [sharri, maƙoshi]. Faɗi kalmomin, kuma ka/ki koyar da su ta hanyar amfani da sassan jiki, ko kuma hotuna.

3. Nemi ɗalibai su gano kalmomin nan a lokacin da kake/kike karanta labarin. Sai ka/ki ce musu su ɗaga babban yatsa a duk lokacin da suka ji an faɗi sabbin kalmomin.

4. Karanta labari ta yadda zai burge ɗalibai.

5. Tambayi ɗalibai su koma kan hasashensu.

6. Yi wa ɗalibai tambayoyin da ke ƙarshen labarin da ka/kika karanta musu daga cikin Littafin Karatun A Bayyane.

1. Faɗa wa ɗalibai su lura da yadda kake/kike rubuta haruffa manya da ƙanana a kan allo [Ɓɓ, Aa].

2. Nemi ɗalibai su yi amfani da yatsarsu su tisa haruffan da ke cikin littafinsu, yayin da kake/kike tisawa a kan allo.

3. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a iska da yatsa.

4. Ka/ki sa ɗalibai su rubuta haruffan a cikin littattafansu.

5. Zagaya cikin aji domin duba duƙufarsu, da riƙon fensiri da inda suka fara rubutun, da kuma yadda suke rubutuwa.

Rubuta Haruffa Minti-5

Jagoran Malamai - Aji 2161

Zango Na: 3 Mako Na: 9 Darasi Na 17 da Na 18

Matashiya a kan Darasi Na 2

Ba su dama su furta kalmomi, tare da jinsu a cikin waƙa yana haɓaka

fahimtarsu ta sauraro da gina kalmomi.

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai cewa za a maimaita darasin da ya gabata.

2. A darasi na biyu, ka/ki maimaita dukkan darasin amma ka/ki yi amfani da labarin da ke shafi na 53 a Littafin Karatu A Bayyane. Kalmomin da za a koyar su ne [gallaza, fatake].

3. Ka/ki tunatar da ɗalibai inda aka kwana cikin labarin da ke shafi na [52] a cikin Littafin Karatu A Bayyane.

Reshen Darasi: Tsarin Baƙaƙe.Aiki: Ginin Kalmomi.Manufa: Jaddada iya amfani da sauti.Tsari: Yi amfani da gaɓoɓin kalmar da aka koyara cikin darasi (misali: ka, na). A

rubuta su a jikin allo. Nemi ɗalibai su ƙirƙiro sabbin gaɓoɓi, ta hanyar canza baƙaƙen farko (mislai: ta, ma).

Ana son Malamai su ƙara ba da damar ƙarin goguwa ga ɗalibai ta hanyar ganin yiwuwar shigo da ‘Ayyukan Ƙara Ƙwarewa’. Ayyukan ƙara ƙwarewa suna jaddada manyan rassan koyo da ake cin karo da su a tsarin darusan yau da kullum. Ana son malamai su yi amfani da waɗannan ayyukan, lokacin da suka fahimci ɗalibai na buƙatar ƙarin ayyuka, ko kuma a faɗaɗa fahimtar ɗaliban.

Na fahimci yawancin ɗalibai sun fi son:

Na fi jin daɗin koyar da waɗannan :

A kundin na ina iya koyar da waɗannan a sauran darussana na yau:

Aikin Gida

Waiwaye

Ayyukan ƙara ƙwarewa

Shawara

1. Ka/ki tuna wa ɗalibai su tafi da littafin karatunsu gida, don su karanta darasin yau tare da iyayensu ko ‘yan’uwa ko abokai.

2. Ka/ki tabbatar da ɗalibai sun gwada rubuta haruffa da kalmomin da aka koya a cikin darasin na yau a cikin littafinsu.

Jagoran Malamai - Aji 2 162

Kalmomin Aikin Koyar Da Karatu

Tsarin Baƙaƙen Hausa

Tsarin baƙaƙen Hausa na nunin yadda jaddawalin harruffan Hausa suke tare da yadda ake haɗa su don tayar da baƙaƙe, waɗanda da su ne ake tayar da kalma. Daga ƙarshe a haɗa kalmomin don tada jimla

Gwaji Gwaji hanya ce ta lura da kuma auna fahimtar ɗalibai.

Fahimta Fahimta ita ce fitar da ma’ana daga abinda aka rubuta ko aka koyar.

Bayani filla-filla Hanya ce ta koyarwa, inda ake tsefe abin da jigo ya ƙunsa dalla-dalla (don ƙarin fahimta).

Iya Karatu Iya karatu na nufin karanta rubutu daidai da yadda ƙa’idojin rubutu suka gindaya, a cikin harshen.

Tsarin Darasi Hanyar gabatar da darasi da ke ƙunshe da manufar aiki da kuma lokacin kammala shi.

Fahimtar Ƙwayoyin Sauti

Fahimtar ƙwayoyin sauti na nufin ƙwarewa wajen saurare, da rarrabewa da kuma sarrafa ɗaiɗaikun sautuka a cikin magana.

Baƙin Kalmomi Kalmomi ne sababbi da suka bijiro sakamakon gabatar da wani sabon darasi.

Tsarin Koyarwa Darasin da aka tsaro da ƙudurin ɗori a kan aikin da ya gabata, mai fitacciyar manufar koyar da wani aiki ga ɗalibai.

Kalmomi Kalmomi sune kalmomin da dole ɗalibai su san su kafin su fahimci abin da su ka gani a rubuce ko su ka ji a labari.

Rataye

Matakan Bunƙasa Koyon Karatu

Rarrafe Tashi Tattakawa Faɗi-tashi Tafiya Sassarfa

Mataki Ɗan Koyo

Rarrafe Yaro yana jin harshen uwa, amma sai da hotuna yake iya ganewa; zai nuna kamar ya iya karatu; yana jin tushen kalmomi.

Jagoran Malamai - Aji 2163

Harafi Motsi Bayanin Motsi

N Noma Malami/Malama ya/ta nuna yadda ake noma da fartanya, yana/tana furta sautin ‘n’ ‘n’ ‘noma’

A Ah! Malami/Malama ya/ta ɗaga hannunsa/ta sama cikin mamaki yana/tana furta sautin ah! ah!

K Kama Malami/Malama ya/ta ɗaga hannunsa/ta na hagu, ya/ta kama na dama, yana/tana furta sautin ‘k’ ‘k’ ‘kama’

M Moow Malami/Malama ya/ta rinƙa ɗagawa da miƙa wuyansa/ta gaba, yana/tana kwaikwayon kukan saniya wajen furta sautin ‘m’ ‘m’ ‘mmmooow’

S Saƙa Malami/Malama zai/zata yi kamar yana/tana saƙa da hannuwansa/ta, yayin da yake/take furta sautin ‘s’ ‘s’ ‘saƙa’

T Tafi Malami/Malama ya/ta dinga tafa hanuwansa/ta yana/tana furta sautin ‘t’ ‘t’ ‘tafi’

I Ido Malami/Malama ya/ta nuni idonsa/ta da yatsa, yana/tana furta sautin ‘I’ ‘I’ ‘Ido’

R Rawa Malami/Malama ya/ta kwatanta yin rawa yana/tana furta sautin ‘r’ ‘r’ ‘rawa’

D Daka Malami/Malama ya/ta rinƙa ɗaga hannuwansa/ta sama yana/tana sako su kamar mai daka, yayin da yake/take furta sautin ‘d’ ‘d’ ‘daka’

Ts Tsalle Malami/Malama zai/zata daka tsalle, kuma yana/tana furta sautin ‘ts’ ‘ts’ ‘tsalle’

B Boom Malami/Malama ya/ta nuna kamar yana/tana saman babur yana/tana murɗa hannun babur ɗin yana/tana furta sautin ‘b’ ‘b’ ‘boom- boom’

W Wanka Malami/Malama ya/ta kwaikwayi cuɗar jiki, kuma yana/tana furta sautin ‘w’ ‘w’ ‘wanka’

G Gudu Malami ya rinƙa sassarfa a cikin aji yana furta sautin ‘g’ ‘g’ ‘gudu’Y Yanka Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana yanka da hannu ɗaya, kuma

yana/tana furta sautin ‘y’ ‘y’ ‘yanka’L Leƙa Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana leƙen wani abu, kuma yana/

tana furta sautin ‘l’ ‘l’ ‘leƙa’U Ungo Malami/Malama ya/ta miƙa hannunsa/ta zuwa wani ɗalibi/ɗaliba,

kamar zai/zata ba shi/ta wani abu, yana/tana furta sautin ‘u’ ‘u’ ‘ungo’C Ci Malami/Malama zai/zata yi kamar yana/tana cin abinci da hannu,

kuma yana/tana furta sautin ‘c’ ‘c’ ‘ci’H Hamma Malami/Malama ya/ta yi hamma, yana/tana furta sautin ‘h’ h’ ‘hamma’Sh Shiru Malami/Malama ya/ta aza yatsansa/ta akan bakinsa/ta yana/tana furta

sautin ‘sh’ ‘sh’ ‘shiru’F Fere Malami/Malama ya/ta ɗaga yatsansa/ta ya/ta kwaikwayi fere fensiri,

kuma yana/tana furta sautin ‘f’ ‘f’ ‘fere’Ɗ Ɗanɗano Malami/Malama ya/ta kwaikwayi ɗanɗanar miya, yana/tana furta

sautin ‘ɗ’ ‘ɗ’ ‘ɗanɗano’.

Jagoran Malamai - Aji 2 172

Harafi Motsi Bayanin Motsi

J Ji Malami/Malama ya/ta riƙe kunnensa/ta kamar yana/tana gargaɗi, kuma yana/tana furta sautin ‘j’ ‘j’ ‘ji’

E Eeh! Malami/Malama ya/ta rinƙa ɗaga kai yana/tana noƙe shi nuna amincewa, kuma yana/tana furta sautin ‘e’ ‘e’ ‘eeh!’

Z Zane Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana zane, kuma yana/tana furta sautin ‘z’ ‘z’ ‘zane’

O Oho! Malami/Malama ya/ta buɗe hannayensa/ta, tare da ɗaga kafaɗunsa/ta, yana/tana yin ko oho, kuma yana/tana furta sautin ‘o’, ‘o’, ‘oho’

Ƙ Ƙirga Malami/Malama ya/ta nuna yana/tana ƙirga da yatsunsa/ta, kuma yana/tana furta sautin ‘ƙ’ ‘ƙ’ ‘ƙirga’

Ƙw Ƙwaƙwaƙwa Malami/Malama ya/ta kwaikwayi tafiyar agwagwa, yana/tana ɗaga hannayensa/ta yana/tana sakinsu, kuma yana/tana furta sautin ‘ƙw’ ‘ƙw’ ‘ƙwaƙwaƙwa’

Ai Aiki Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana wani aikin da ke son natsuwa, kuma yana/tana furta sautin ‘ai’, ‘ai’, ‘aiki’

Kw Kwalliya Malami/Malama ya/ta kwatanta shafa hoda, kuma yana/tana furta sautin ‘kw’ ‘kw’ ‘kwalliya’

Gw Gwalo Malami/Malama ya/ta zuro harshensa/ta yana/tana gwalo, kuma yana/tana furta sautin ‘gw’ ‘gw’ ‘gwalo’

Au Auna Malami/Malama ya/ta kwatanta auna hatsi da hannunsa/ta, kuma yana/tana furta sautin ‘au’, ‘au’, ‘auna’

Ɓ Ɓare Malami/Malama ya/ta yi kamar yana/tana ɓare wani abu, yana/tana furta sautin ‘ɓ’ ‘ɓ’ ‘ɓare’.