8 % 1 & % = 3 = -2 ( % 7 9 / % 7 , -6 = % 6 ( % 7 % 1 % 6 -2 7 - islamic … · 2017-11-16 ·...

105

Upload: others

Post on 05-Feb-2020

28 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

1

TAMBAYOYIN DA SU KA SHIRYAR DA SAMARIN SHI’AH

ZUWA GA GASKIYA

MARUBUCI

SULAIMAN SALEH AL-KHARASHI

FASSARA

UMAR MANSUR

[email protected]

1438 - 2017

www.islamic-invitation.com

2

SHIMFIDA

Godiya ta tabbata ga Allah da ya fada a cikin littafinsa mai tsarki:

“﴾ هليبس نع مكب قرفتف لبسلا اوعبتت وال هوعبتاف اميقتسم يطارص اذ هـ نأو ﴿

“Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kadaku bi wasu hanyõyi” (al-An’am :156)

Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzonsa cikamakin annabawawanda yace “hakika Yahudu sun kasu zuwa ga kungiyoyi saba’in da biyu,al’umma ta za ta kasu kashi saba’in da uku, dukkaninsu suna cikin wuta saiguda daya! Sai aka tambaye shi: waccece guda dayar? Sai yace “abinda nake kai ni da sahabbai na”.1

Bayan haka, hakika Allah da nufinsa ya kaddara rabuwar kan al’ummarmusulmi zuwa kungiyoyi mabanbanta,sashensu na gaba da sashe, sunamasu sabawa abinda Allah ya umurce su da yi yayin sabani wato maidaal’amari ga Allah ta’ala, Allah yana cewa

رخ اآل مويلا و هللا ب نونمؤت متنك نإ لوسرلا و هللا ىلإ هودرف ءيش يف متعزانت نإ﴾ ال يوأت نسحأو ريخ كلذ

Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah daManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wannan

ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara” (An-Nisa: 59).

Don haka ne ya zamto wajibi ga kowanne mai kaunar al’ummarsa da songanin haduwarta da dunkulewarta wuri guda yayi kokari matuka wajenganin ya hada ta akan gaskiya, ya dage wurin ganin ya maidata kan asalinmatsotsarta kamar yadda ya ke a zamanin Manzon Allah (s.a.w), wato tabangarorin (Akida, Sharia, da Sanin ya kamata), domin aiki da fadin Allahta’ala:

1 Sahihin Imam Tirmidhi na Albani (2129)

3

“﴾ اوقرفت وال اعيمج هللا لبحب اومصتعا ﴿

“Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba”

(Al-Imran: 103)

Daga cikin abinda zai taimaka wurin ganin hakan ya tabbata akwai haskakahanya ga kungiyoyin da suka kaucewa kiran Alkur’ani da Sunnah da fadakarda su kan wannan bata da su ke ciki, abinda ya makantar da su dagakaucewa hanyar gaskiya da siradin shiriya.

Ta dalilin haka ne na yi tunanin tsara wadannan tambayoyi masu dauke dayanayi na kalubale wa-la’alla ko za su haskaka wa samari daga cikin yanShi’ah ‘yan Sha biyu hanya su dawo kan gaskiya, domin matukar dai suncire son ransu sun dubi abinda ke kunshe a karkashin wadannan tambayoyikuma su ka yi kasa a gwiwar tabukawa wurin iya amsa su to hakan na nufinwajabcin karbar gaskiyar da ke ciki, da komawa zuwa ga Alkur’ani da Sunnamatukar dai an cire son zuciya.

Ya burge ni matuka rubutun da wani da’uwa2 da ya yi bayan ya shiryu ya barshi’anci, inda a ciki ya ke bayanin halin da ya tsinci kansa da matakan da yabi daga bata zuwa ga shiriya a cikin littafinsa mai suna “Na ribaci Sahabbaiba tare da na yi asarar Ahlul-Baiti ba”3.

Babu shakka wannan littafi da ya wallafa ya yi bankaye kwarai, dominyadda abin yak e shine mu Ahlus Sunnah daman mu ba mu da wani abindamuwa na hadawa tsakanin Shabbai da Iyalan Gidan Manzon Allah (s.a.w),wannan shine ma asali wurinmu, domin dukkaninsu jagorori ne na shiriyada Allah ya yabe su, sabanin yan Shi’a da ke rarrabewa tsakaninsu.

Wannan ya tunatar da ni wani littafi da wani Banasare da ya musulunta yawallafa ya sanya masa suna “Na ribaci Muhammad..kuma ban rasa Isa ba”tsira da amincin Allah yabbata garesu.

Abinda ya kamata a sani anan shine na zakulo galibin wadannan tambayoyi

2 Sunanshi Abu Khalifa Al-Khutaibi, mutumin kasar Bahrain, ya ziyarce ni har gidana da ke Riyadh.3 Sunan littafin a larabce : تيبلا لآ رسخأ ملو ةباحصلا تحبر

4

ne a shafukan tattaunawa da muhawara tsakanin ma’abota fahimta daban-daban a yanar gizo, musamman kuma shafin nan na “Al Difa’u anis Sunnah”,sai na kara wasu tambayoyin da na zakulo daga littafan da su ke kunshe datattaunawa da Shi’a, sai na tsara su na fitar da su a wannan littafi nawa,don haka falala dukkaninta a wurin Allah madaukakin sarki ta ke.

Daga karshe fatana Allah ya datar da samarin Shi’a ga fahimtar gaskiya, yasanya wannan littafin a mazaunin mabudin gaskiya gare su, kamar yaddana ke amfani da wannan dama wurin tunatar da su cewa karbar gaskiyasanda ta zo wa dan-adam ya fi dogewa akan karya, kuma karbar da dayadaga cikin yan Shi’a zai yi ga gaskiya da taimakonta da yada Sunnah zai iyasamun lada sama da na dubban matasan Sunnah da suke kara zube batare da su na yin hibbasa irin wannan ba, irin samarin da su ka nitse cikinbiyewa soye-soyen zukatansu, da fadawa cikin shubuhohi.

Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabinsa tare da Sahabbansa daIyalan gidansa tsarkaka.

Marubuci/ Abu Mus’ab

[email protected]

5

TAMBAYOYI

1- Yan Shi’a su na kudurce cewa Sayyidina Aliyu (r.a) Imam nema’asumi da ba ya laifi, sai kuma gashi da li’itirafinsu ya aurawaUmar (r.a) ‘yarsa mai suna Ummu Khulsuum (‘yar uwar Hassan daHussaini)!

To anan wurin dayan biyu ne:

Na farko: ko dai su ce Aliyu (r.a) ba ma’asumi ba ne, don haka ne yadau ‘yarsa ya baiwa Kafiri!4 Wannan kuma ya warware abinda kerubuce a littattafan kungiyarsu ta Shi’anci, kuma duba da wannanzancen za a gina cewa sauran limaman ma ba ma’asumai ba neKenan.

Na biyu: ko kuma su ce a’a Umar (r.a) musulmi ne ba kafiri ba! Donhaka ne Aliyu (r.a) ya amince ya aura masa ‘yarsa.

Kowanne daya daga cikin wadannan amsoshin suka zaba to akwaitufka da warwara a ciki.

2- Shi’a suna kudurce cewa Abubakar (r.a) da Umar (r.a) kafirai ne! saigashi kuma Aliyu (r.a) ya yarda da khilafancinsu, ya yi mu sumubaya’a ya zauna karkashinsu, wanda hakan na nufin shi Aliyu (r.a)ba ma’asumi ba ne Kenan, domin babu yadda za a yi ma’asumi yayimubaya’a ga kafirai azzalumai da tabbatar da su akan wannan batana su. Abu na biyu da za a iya fadi shine cewa aikinsu daidai ne shi yasanya ya yi tafiya da su, ma’ana su khalifofi ne muminai masugaskiya da rikon amana Kenan shi ya sa ya yi aiki kafada-da-kafadada su. idan Shi’a kuma suka fadi haka sun sabawa tushen akidarsu takafirta wadancan khalifofi su da la’antarsu da suke yi, don hakahanyoyi biyu ne babu ta uku: ko dai mu yi koyi da hanyar da Abul

4 Domin a akidarsu Umar da galibin sahabbai kafirai ne! wal iyazu billah!

6

Hasan (Aliyu r.a) ya bi, ko mu bi hanyar wadanda suka saba masamasu kiran kansu da cewa su ne mabiyansa.

3- Aliyu (r.a) ya auri mata da yawa bayan rasuwar Fatima (r.a), yasamu ‘ya’ya da su, daga cikin ‘ya’yan akwai Abbas dan Aliyu, daAbdullahi dan Aliyu, da Jafar dan Aliyu, da Usman dan Aliyu.Mahaifiyar wadannan ita ce “Uwar Maza, ‘yar Hizam dan Daarim.

Hakanan daga cikin ‘ya’yansa akwai Ubaidullahi dan Aliyu dan AbiTalib, da Abubakar dan Aliyu. Mahaifiyarsu ita ce “Laila ‘yar Mas’ud al-Dharimiyya”5.

Bugu da kari akwai “Yahya dan Aliyu, Muhammad karami dan Aliyu,da Aunu dan Aliyu. Mahaifiyarsu itace “Asma’u ‘yar Uwais”6

Haka nan akwai Rukayya ‘yar Aliyu, da Umar dan Aliyu , wanda ya rasuyana da shekaru 35 a rayuwarsa. Mahifiyarsu ita ce “Ummu Habib ‘yarRabi’ata”7.

Sannan akwai Ummul-hasan ‘yar Aliyu, da Ramla babba ‘yar Aliyu binAbi Talib. Mahaifiyarsu it ace “Ummu Mas’ud ‘yar Urwa dan Mas’udAttaqafi”.8

Tambaya a nan ita ce ta ya mutum zai sanya wa ‘ya’yansa sunayenmakiyansa? ‘ka’ka sayyidina Aliyu zai aiwatar da danyen aiki irinwannan ? shin kun san da cewa Aliyu (r.a) shi ne farkon bakuraishenda ya sanya wa ‘ya’yansa sunan Abubakar da Umar da Usman kuwa?!

4- Ma’aboci littafin (Nahjul Balaga) wanda ya ke littafi ne abin dogarowajen Shi’a kwarai ya ruwaito a cikin littafinsa abin da ke nuna cewa

5 Duba Al-Irshad (167)6 Al-Irshad (167)7 Al-Irshad (167)8 Kashful Ghumma (2/66)

7

sayyidina Aliyu (r.a) ya nemi a hutar da shi daga batun khilafa, haryana cewa “ku kyale ni ku nemi wani na”9, wanda wannan na nunabacin mazhabar Shi’a domin ta ya ne zai nemi a kyale shi daga batunkhilafa alhali kuma umurni ne na tilas daga Allah kamar yadda ku keriyawa?

5- Shi’a suna riya cewa Nana Fatima (r.a) wadda tsoka ce daga jikinManzon Allah (s.a.w) an wulakanta ta a zamanin Abubakr (r.a) har maan karya kwankwasonta, haka nan an kona gidanta da zubar daabinda ke cikinta na ‘da har su ke cewa sunanshi Muhsin!

To tambaya a nan ita ce: ina mijinta Aliyu (r.a) ya ke duk wannan abinya faru? Ko ragon namiji ba zai yadda da haka ba ballantana Aliyuuban Jarumai. To menene ya faru yayi shiru bai karbar mata hakkintaba matukar dai ba tatsuniyar gizo da koki ba ce?

6- Tarihi ya tabbatar da cewa da dama daga cikin jagororin sahabbaisun yi surukuta da adadi mai yawan gaske na iyalan gidan AnnabiMuhammad (s.a.w), ta hanyar basu aure da aura daga cikinsu. Gamisalai:

- Manzon Allah (s.a.w) ya auri Aisha ‘yar Abubakr (r.a), da Hafsah‘yar Umar (r.a).

- Manzon Allah (s.a.w) ya aurawa Usman (khalifa na uku r.a)‘ya’yansa mata guda biyu (wato Rukayya sannan Ummu Khulthum),don haka ne ake masa lakabi da “Zun Nuraini” – ma’ana ma’abocinhaskaka biyu”.

- Hakanan ‘dan cikin Usman wato Aban dan Usman bin Affan shi maya auri Ummu Khulthoum ‘yar Abdullahi dan Jafar dan Abi Talib.

- Hakanan jikan Usman mai suna Marwan dan Aban dan Usman ya

9 Nahjul Balaga (136)

8

auri Ummul Kasim ‘yar Alhasan dan Alhasan dan Aliyu bin AbiTalib (r.a).

- Haka Zaidu dan Amru dan Usman bin Affan ya auri Fatima ‘yarHussaini dan Aliyu bin Abi Talib (r.a).

Za mu dakata da wadannan misalan da mu ka kawo na auratayyatsakanin gidajen khalifofin nan guda hudu, amma ba don haka baakwai dimbin misalai na auratayya tsakanin iyalan Manzon Allah(s.a.w) da gidajen sauran sahabbai.

Ta wani bangaren kuma za mu ga yadda iyalan gidan Annabi(s.a.w) ke radawa ‘ya’yansu sunayen sahabbansa, kamar yadda yake sananne kuma tabbatacce a wurin malaman tarihi AhlusSunnansu da Shi’arsu.

Mun ga yadda Aliyu (r.a) ya sanyawa ‘dansa da matarsa Laila bintMas’ud ta Haifa masa suna Abubakar , kuma shi Aliyu ne mutumna farko da ya fara radawa dansa suna Abubakar a cikin BanuHashim dangin Manzon Allah (s.a.w).10

Haka nan Alhasan dan Aliyu (r.a) ya sanya wa ‘ya’yansa sunaAbubakar da Abdurrahman da Talha da Ubaidullahi.11

Hakanan Alhasan dan Alhassan dan Aliyu dan Abi Talib

Da Musal Kaazim shi ma ya sanya wa diyarshi suna Aisha.

Daga cikin Ahul baiti kuma akwai wanda ake wa alkunya daAbubakr doriya ga sunanshi, kamar Zainul Abidin dan Ali, da Aliyudan Musa Ar-Ridha.12

Daga cikin wadanda suka sanyawa ‘ya’yansu suna Umar daga cikinAhlul baiti akwai Aliyu (r.a) wanda ya sanyawa danshi suna Umarbabba, wanda mahaifiyarsa it ace Ummu habib ‘yar Rabee’ah,

10 Duba Makatilut Talibiyyina na Abul Faraj Al Asfahani Al Shi’ee (91). Al-Irshad na Mufid (64)11 At-Tanbih wal Ishraaf na Mas’udi (263)12 Makatilut Talibiyyina (561-562)

9

wanda aka kashe tare da dan’uwansa sayyidina Hussaini (r.a) aIraqi.

Sai Umar karami wanda Shahba ‘yar kabilar Taglab ta haifa, wandaya rayu har bayan mutuwan ‘yan’uwanshi kuma ya gade su.

Haka Alhassan dan Aliyu ya sanya wa ‘ya’yanshi suna Abubakar daUmar.

Haka nan Aliyu dan Hussaini dan Aliyu shi ma ya aikata hakan.

Haka batun yake game da Aliyu Zainul Abidin.

Haka nan Musa Al-Kazim.

Haka nan Alhussaini dan Zaidu dan Aliyu.

Haka nan Ishak dan Alhassan dan Aliyu dan Hussaini.

Haka nan Alhassan dan Aliyu dan Alhassan dan Hussaini danAlhassan, da dai sauransu. Dukkaninsu sun sanya wa ‘ya’yansusuna Umar.

Suna da yawa matuka saidai za mu takaita da wadannan da mukaambata don su zama manuniya.

Sa’annan daga cikin wadanda su ka sanya wa ‘ya’yansu mata sunaAisha akwai:

- Musal khazim

- Aliyu Al-Hadi.

7- “Al-khulaini” ya ambata a cikin littafin “Al-Khafi” cewa limamai sunsan sanda za su mutu, kuma suna da zabin ranar da za su mutun”13.Sai kuma ga Al-Majlisi ya ambaci wani hadisi a cikin littafinsa“Biharul Anwaar” cewa: ‘babu wani daga cikin limamai face ya mutu

13 Usulul Khafi (1/258)

10

ne ta hanyar kisar gilla ko guba”14 ! to matukar dai Imam ya san gaibukamar yadda Al-Khulaini da Al-Aamili suka ambata to ai ya kamata nea ce ya san duk irin abinci da abin shan da ake kawo masa, idanakwai guba a ciki zai sani kuma zai nisance shi, idan kuwa ya saniamma bai nisance shi ba to ya kashe kanshi da gangan Kenan, alhaliManzon Allah (s.a.w) yace duk wanda ya kashe kanshi yana wuta, toyanzu ‘yan shi’a sun lamince hakan ga limamansu?

8- Mu na sane da cewa Alhassan (r.a) ya janyewa Mu’awiya (r.a) dagashugabanci, bayan ya yi sulhu da shi, a lokacin fa yana da karfin dazai iya jan-daaga da dogewa akan shugabancin da ya ke a hannunsa,duba da irin karfin da ya ke da shi na soji, amma ya hakura ya sauka.Ta gefe daya kuma mun ga yadda dan’uwansa Hussaini (r.a) ya yitawaye ga Yazidu dan Mu’awiya tare da wasu daga cikin iyalansa, alokacin da yana da damar sasantawa da Yazidu, kuma bas hi dakarfin fito-na-fito da shi. To ana wajen dole ne yan shi’a su yadda dacewa daya daga cikinsu daidai yayi daya kuma kuskure yayi, dominidan abinda Alhassan yayi na hakuri duk da yana da karfin da zai iyashiga yaki da Mu’awiya daidai ne, to tirjiyar da Hussaini yayi Kenanduk da ba shi da karfi kuskure ne. idan kuma kujerar nakin daHussaini ya hau duk da ba shi da karfi ce daidai, to sallamawar daAlhassan yayi duk da yana da karfi kuskure ne Kenan.

A nan ne ake yenta, domin ko dai ‘Yan Shi’a su ce dukkaninsu daidaisu ka yi, to a nan sun yi tufka da warwara, domin fari da baki bas utaba zama abu guda ba, kuma karara hakan zai rushe Akidarsu da suke tafiya akai. ko kuma su ce abinda Alhassan ya yi ne ba daidai ba,to a nan ma sun rushe akidarsu ta cewa limami ba ya kuskure. Idankuma su ka ce Hussaini ne yayi kuskure to shi ma sun rushe akidarsu,kuma da zarar tushen akida ta girgiza to duk wani reshe zai yi yaushi.Sai su zabi wanda ya fi mu su sauki!

14 Biharul Anwaar (43/364)

11

Wadansu daga cikin yan shi’a masu wayau sun so su kaucewawannan matsin ta yadda suka yi kokarin banbacewa tsakanin Imamada Jagoranci, su ka ce ai Alhassan ya janye ne daga jagoranci naduniya ba Imama ta addini ba. Wannan abin dariya ne matuka waiyaro ya tsinci hakori, domin idan jagorancin da khalifofi su ka yi ba shine irin wanda imamai ke yi ba to na menene Yan Shi’a ke rigima dasahabban har da kafirta su saboda sun kwacewa Ahlul Baiti shi?!

9- Al-Khulaini ya ambata a cikin littafinsa Al-khafi cewa: “ wasu dagacikin abokanan karatunmu sun bamu labari daga Ahmad danMuhammad daga Abdullahi dan Hajjal daga Ahmad dan Umar Al-Halabi daga Abu Basir yace: na shiga wajen Abu Abdillahi (alaihissalam) sai na ce masa, Allah gafarta Malam! Ina da tambaya maimuhimanci amma ga wani can zai iya jin maganarmu, sai AbuAbdillahi ya ja labule ya fito yace masa tambayi abinda kake sontambaya akai. Sai Abu Abdillah yayi shiru kadan, can sai yace: Anbamu Mus’hafu Fatima (alaihas salam), ko kun san menene Mus’hafuFatima? Sai nace masa menene Mus’hafu Fatima kuma? Sai yace: aiwani mus’hafi ne da ke dauke da kwatankwacin wannan Alkur’aninnaku sau uku! wallahi babu ko harafi daya na Akur’aninku a cikinshi!Sai na kada baki na ce: “tabbas wannan wani babban ilimi ne”, saiyace “tabbas ilimi ne amma na musamman !”.15

Abin tambaya a nan shine shin Manzon Allah (s.a.w) ya san dawannan mus’hafin na Fatima? Idan bai san da shi ba to ‘ka’ka Ahlulbaiti su ka san da shi bayan shudewarsa alhali shi ne Manzon Allah(s.a.w)? idan kuma ya san da shi to ta ya aka yi ya boye shi gaal’umma alhali Allah na fadin cewa :

﴾ـ هتلا سر تغلب امف لعفت مل نإو كبر نم كيلإ لزنأ ام غلب لوسرلا اهيأ اي ﴿

15 Usulul Khafi (1/239)

12

Yã kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka dagaUbangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da

manzancinSa ba ke nan.” (Al-Mai’da: 67)

10- A juzu’in farko na littafin Al-khafi na Kulaini akwai sunayenmutanen da su ka ruwaitowa shi’a hadisan Manzon Allah (s.a.w),suka koro ruwayoyin maganganun Ahlul Baiti, daga cikinsu akwaiwadannan sunayen;

Mufaddal dan Umar, Ahmad dan Umar Al-Halabi, Umar dan Abaan,Umar dan Uzainah, Umar dan Abdul’aziz, Ibrahim dan Umar, Umar danHanzala, Musa dan Umar, Abbas dan Umar, a kowanne daya dagacikin sunayen nan akwai Umar a ciki ! to ta ya suka sanyawa kansuwannan suna?

11- Allah ta’ala yana cewa:

* نوعجار هيلإ ـا نإو هلل انإ اولا ق ةبيصم مهتباصأ اذإ نيذلا * نيرباصلا رشبو ﴿ـ

.﴾ نودتهملا مه كئ ـ لوأو ةمحرو مهبر نم تاولص مهيلع كئ ـ لوأ

Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri Waɗanda suke idan wata masĩfa tasãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa

gare Shi, muke kõmãwa."(Al-Baqara: 155 – 157)

A wani wajen yana cewa :

﴾ـ سأبلا نيحو ءارضلا و ءاسأبلا يف نيرباصلا ﴿ـو

“da mãsu haƙuri a cikin tsanani da cũta da lõkacin yãƙi” (Al-Baqara: 177)

Aliyu (r.a) ya fadi bayan rasuwar ”:Ya zo a cikin “Nahjul Balaga” cewaManzon Allah s.a.w cewa: ya Manzon Allah ! ba don ka hana kokawada Shewa ba kuma ka bada umurnin yin hakuri, da mun karar da

13

hawayen idanuwanmu akanka”16

ce:”wanda ya buga hannuwansa kan A wani wajen yace : Aliyu (r.a) yabaci”17. cinyarsa saboda wata musiba da ta fada masa, to aikinsa ya

Hakanan Hussaini ya gayawa ‘yar’uwarsa Zainab a Karbala kamaryadda mai littafin “Muntahal Aamaal ya ruwaito cewa18 :” ya ‘yar’uwata ina hadaki da Allah ki kiyaye wannan amana da zan fada miki: idanan kashe ni kada ki yaga riga, kada ki keta fuskarki da kumbarki, kadaki yi na-bani-na-lalace akaina”.

Abu Jafar Al-Kummi ya ruwaito cewa Amirul Muminina (alaihis salam)ya fadi cewa: “kada ku sanya bakin kaya, domin shi din tufafinFir’auna ne”19.

Ya zo a cikin tafsirin Al-Safi a karkashin tafsirin ayar:

﴾ـ فورعم يف كنيصعي الو ﴿

“kuma bã su sãɓa maka ga wani abu da aka sani na sharĩ´a,”

(Al-Mumtahana: 12)

ya fadi cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya yi wa mata mubaya’a akancewa ba za su sanya bakin kaya ba, ba za su keta riguna ba, kuma baza su kiran “bone da lalacewa” ba.

Ya zo a cikin “furu’ul khafi” na Al-Khulaini cewa Manzon Allah (s.a.w)ya yiwa Fatima wasici da cewa : “idan na mutu kada ki yakushi fuska,kada ki fisgi gashi akaina, kada ki kira na bani na lalace, kada ki yibikin shelanta mutuwa ta”20

16 Nahjul Balaga (576)17 Wasa’ilus shi’a (3/270)18 (1/248)19 Man la Yahduruhul Faqih (1/232).20 (5/527)

14

Shi ma shehin shi’a mai suna Muhammad dan Hussain Babawaihi Al-Qummi da su ke wa lakabi da (Al-Saduq) yana cewa : daga kalamaimasu fasaha da Manzon Allah (s.a.w) da ya yi fice da su akwaifadainsa: “bikin shelanta mutuwa yana daga cikin ayyukan Jahiliyya”21.

Haka nan malamansu kamar Al-Majlisi da An-Nuri da Al-Burujardi sunruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w) yana cewa “sautu iri biyula’anannu ne Allah na fushi da su: kokawa lokacin faruwar musiba, dawaka yayin kida, ma’ana koken mutuwa da kada-kade da wake-wake”22.

Abin tambaya anan bayan mun ji dukkanin wadannan ruwayoyinshine: da wani dalili ne Shi’a su ke saba ma wannan gaskiyar da ta zomusu ta hanyar sanya bakaken kaya da jiwa jiki ciwo da koke-kokebayan haka? Kuma a nan wa za mu gasgata? Manzon Allah (s.a.w) daAhlul baiti za mu gasgata ko kuwa masu rawunnansu da shehunansuda su ke daure mu su gindi kan wadannan ayyukan da su ke yi nasabawa a’imma?

12- Idan jiwa kai ciwo da koke-koke da dukan kirji da ‘yan Shi’asuke yi yana da lada me ya sanya malamansu ba sa yi saidai jahilancikinsu?

13- Idan ‘yan shi’a suna riya cewa adadin sahabban da su ka halarci”Ghadir”23 dubbai ne kuma sun ji wasicin da Manzon Allah (s.a.w) yayina kalifiancin Aliyu (r.a) bayanshi kai tsaye, to don menene ba a samuko da daya daga cikinsu ba ya fusata tare da kokarin ganin sai an bi

21 Man La Yahduruhul Faqih (4/271).22 Biharul Anwaar (82/103)23 Ma’anar “Ghadir” shine kwazazzabo, wannan wani kwazazzabo ne mai suna “Khum”, yana da nisankilomita 160 daga Makkah zuwa Madina, yana kusa da Al-Juhfa, a wajen ne Manzon Allah (s.a.w) ya fadihadisin “ اله" وم يلعف اله وم تنك نم “ ma’ana wanda na ke masoyinshi to Aliyu ma masoyinshi ne”, wannanlafazin ne Yan Shi’a su ka rika su ka ce ai Manzon Allah (s.a.w) na ishara ne da cewa Aliyu ne mai mayegurbinshi bayan rasuwarshi.

15

ma Aliyu hakkinsa ta hanyar nuna inkari ga Abubakar (r.a) kai tsaye?Gashi kuwa ko da irinsu Ammar dan Yasir da Al-Mikdad dan Amru daSalmanul Farisi wadanda su ka shahara da goyon bayan Aliyu babuwanda yayi haka cikinsu. To me hakan ke nufi Kenan?

14- Me ya sanya Aliyu (r.a) bai yi magana ba yayin da Manzon Allah(s.a.w) ya nemi rubuta musu littafin da ba za su bace ba bayanshi harabada, alhali shine jarumin da ba ya shakkar kowa sai Allah tunda daisun ce Umar ne ya hana a rubuta wasiyyar a rubuce?

15- Ashe ba yan Shi’a ba ne ke cewa galibin ruwayoyin da ke cikinlittafin “Al-Khafi” masu rauni ne ba? shin ba su ke cewa ba su da waniingantaccen littafi sai Al-Kur’ani ba? To da wane dalili ne su ke riyacewa galibin fassarar da Allah ya yi ga Al-Kur’ani yana cikin wannanlittafin (Al-Khafi) wanda galibin ruwayoyin da ke cikinsa masu raunine?

16- Bauta ga Allah a ke yin ta shi kadai, kamar yadda ya fadi cewa :

﴾ دبعاف هللا لب ﴿

ôaha! Ka bauta wa Allah kaɗai,(Az-Zumar: 66)

Idan haka ne da wane dalili ne ‘yan Shi’a ke sanyawa ‘ya’yansu suna“Abdul Hussain” wato “Bawan Hussain” da “Abdu Ali” da Abdul Zahra”da “Abdul Imam”. Kuma don me su limaman ba su taba sanyawa‘ya’yansu suna Abdu Ali da Abdul Zahra ba? Kuma dai babu yadda zaa yi ma’anar Abdul Hussain ta zamto mai hidimar hussaini a larabce,bayan kuwa shi Hussaini ya riga yayi shahada ya riga mu gidan

16

gaskiya. Shin hankali zai dauki cewa kawai mutum da ya zo yagabatar wa da Hussaini abinci da abinsha ya zuba masa ruwanalwala shikenan ya zamto mai hidima ga Hussaini?

17- Idan Aliyu (r.a) ya san cewa shi khalifa ne na Manzon Allah(s.a.w) da nassi24, don menene ya yi wa Abubakar da Umar da Usman(r.a) mubaya’a?

Idan kun ce yana da raunin da ba zai iya ja da su ba ne, to mai raunibai kamata ya rike jagorancin koli na al’umma ba, domin ba zai iyadaukar nauye-nauyenta ba.

Idan kuma ku ka ce zai iya saidai bai nema ba ne, to wannan ha’incine Kenan. Shi kuma maha’inci ba a amanna da jagorancinsa. Kumababu yadda za ayi sayyidina Ali (r.a) ya zama haka.

Menene amsarku in dai da gaske ku ke?

18- Bayan darewar sayyidina Aliyu (r.a) kan karagar khilafa ba muga ya sabawa Abubakar da Umar (r.a) ba kan harkokin tafiyar damulkinshi, ba mu ga ya kawo mu su wani Alkur’anin ba sabaninwanda su ke kai, bai musanta wani abu ba na tsarin mulki da suka tafisuka bari, saidai ma abinda aka ruwaito daga gare shi yana cewa“mafificin wannan al’umma bayan annabinta shine Abubakar da Umar,bai halasta mutu’a ba, bai dawo da gonar Fadak ba, bai wajabta hajjinTamattu’i ba ga mutane, bai wajabta cewa “hayya ala khairil amal” baa sallah, kamar yadda bai soke fadin “Assalatu Khairun Minan Naum”ba daga cikin kiran sallah.

lallai da ace yana kallonsu a matsayin kafirai da suka kwaci mulki daya bayyana hakan, tunda karfin mulki ya dawo hannunshi, sai gahakan ba ta faru ba, saidai ma muka ga kishiyar hakan, ta yadda ya ke

24 Nassi shi ne aya ko hadisi

17

yabansu yana jinjina wa irin ayyukan da suka gabatar.

Dayan biyu ne, Ko dai ku tsaya inda ya tsaya,ko kuma ku ce ya ha’incial’umma ne shi ya sanya bai fallasa su ba, kowanne ku ka dauka anan ya warware akidarku.

19- Yan shi’a suna riya cewa khalifofin nan shiryayyu kafirai ne, toabin tambaya a nan shine: ta ya Allah ya musu fatahi suka budegaruruwa da musulunci a zamaninsu, musulunci ya daukaka ya yikwarjini a duniya duk a lokacinsu?

Shin wannan bai ci karo da sunnar Allah a ban kasa ba ta tabar dakafirai da munafukai da lalata aikinsu da rashin sanya masa albarka?

Ta dayan bangaren kuma za mu ga yadda musulunci yayi raunimatuka a zamanin jagorancin sayyidina Aliyu (r.a), domin an samufadace-fadace da zubda-jini tsakanin al’ummar musulmai har ta kaiga kafirai na shinshinar kasashen musulmai da ganin damarsu, toidan haka ne ina rahamar da ku ke cewa tana sauka lokacinjagorancin Ma’asumai matukar dai kuna da hankali?

20- Yan Shi’a suna kudurce cewa Mu’awiya (r.a) kafiri ne! sai kumaga shi Hassan (r.a) ya sauka ya mika masa jagorantar al’umma, to kodai ku ce Hassan ya sauka ya mikawa kafiri jagorantar daularmusulunci, wanda hakan ya sabawa maganarku ta cewa Ma’asumi ne,ko kuma kuce a’a Mu’awiya musulmi ne! sai ku zabi daya.

21- Shin Manzon Allah (s.a.w) ya yi sujjada akan “turbayar Hussaini”wadda yan Shi’a ke yi n sujjada akanta ko bai yi ba? idan sun ce eh yayi to wannan tsantsar karya ce, idan kuma bai yi ba to kun fi ManzonAllah sanin gaskiya ne da ku ke yi? Ko da ya ke a cikin ruwayoyinsusuna riya cewa wai Jibrilu ya zo wa da Manzon Allah (s.a.w) da

18

kwano dauke da kasar Karbalaa ciki. Abin dariya.

22- Yan Shi’a na kudurce cewa sahabban Manzon Allah (s.a.w) sunyi ridda bayan mutuwarshi! Abin tambaya a nan shine: shin kafinriddar ta su, su din sun a bin tafarkin Shi’a ne masu limamai sha biyu,ta yadda bayan rasuwarsa sai su ka zama Ahlus Sunnah ne? Ko kuwakafin rasuwarsa su Ahlus Sunnah ne sai su ka koma Shi’ah ‘yan shabiyu bayan rasuwarsa? Ya abin ya ke?

23- Sanannen abu ne cewa Alhassan (r.a) ‘da ne ga Aliyu daFatima (r.a), kuma yana cikin wadanda Manzon Allah (s.a.w) yalullube cikin mayafi, kuma ma’asmu ne a wajen ‘yan Shi’a, kamar daidan uwansa Hussaini (r.a), to da wane dalili ne yan Shi’a su ke nunamasa wariya ta hanyar nesanta zuriyarsa daga Imama da takaiceimama akan jikokin Hussaini alhali ciki daya su ka fito, mahaifinsudaya, mahaifiyarsu daya, dukkaninsu jagorori ne shiryayyu? bugu dakari kuma Alhassan yana gaba da Hussaini a shekaru. To donmenene wannan wariyar ta babu gaira babu dalili haka?

24- Me ya sa sayyidina Aliyu (r.a) bai jagoranci mutane ko dasallah guda ba yayin rashin lafiyar Manzon Allah (s.a.w) matukar daishine mamayinsa bayan rasuwarsa? Ashe karamin limanci (na sallah)ba ya nuni ga babba (na jagorancin al’umma)?

25- Kuna riya cewa dalilin buyar limaminku na sha biyu cikin ramishine tsoron zalunci da azzalumai, to da wane dalili ne ya zarce dabuyar bayan gushewar wannan zaluncin kasantuwar an samutsayuwar daulolin shi’anci da dama bayan haka, kamar daularUbaidiyya da Buwaihiyya da Safawiyya ga uwa-uba kuma daular Iran ayau?

19

Me ya hana shi bayyana a yau tunda dai Iran za ta iya bashi kariya dakarfin da take dashi?

26- Manzon Allah (s.a.w) ya abokanci Abubakar (r.a) a yayinhijirarshi , a yayin da ya kwantar da Aliyu (r.a) a kan shimfidarsa,abinda kan iya jayo halakarsa a hannun Kuraishawa, to matukar daiAliyu (r.a) shine khalifa kuma Iman bayan rasuwar Manzon Allah(s.a.w) shin zai bijirar da shi ga yanayin da za a iya halaka shi a ciki,kuma a lokaci guda ya baiwa Abubakar (r.a) damar rayuwa wanda koda ya mutu babu damuwa tunda ba shi ba ne imam bayansa? Asheana bijirar da Yarima mai jiran gado ga halaka dama?

Idan kun ce Aliyu (r.a) ya san gaibu don haka ya san ba za a kashe shiba, to menene amfanin kwanciyar Kenan tun asali?

27- Mun san cewa Takiyya ana yin ta ne saboda tsoro, shi kumatsoro kala biyu ne: tsoron mutuwa, da tsoron fadawa cikin wahala tazagi da azabtarwa da keta haddi.

Shi tsoron halaka ba zai yiwu Limamai su yi shi ba, sabili da dalilaibiyu: na farko saboda su limamai suna mutuwa ne kan zabinsu kamaryadda ku ke riyawa. Na biyu saboda su limamai sun san abinda yawuce da wanda zai zo, da hanyar da za su mutu, kamar yadda ya ke awajenku. Kenan ba su da matsala da mutuwa kafin zuwanta, donhaka ba su da bukatar su bayyana munafinci ta hanyar nuna Takiyyaa rayuwarsu.

Shi kuwa dayan bangaren na nuna tsoro sakamakon cutarwa daazaba da zagi da keta mutunci da za su iya samun mutum, to babushakka jure irin wannan cutarwa shine aikin malamai da jagororinaddini, wanda Ahlul Baiti su ne su ka fi cancanta da wannan siffar tajajircewa sama da wasunsu domin tabbatar da wannan addini nakakansu (s.a.w). to da wane dalili za su yi takiyya Kenan?

20

28- A ra’ayin yan Shi’a dalilin da ke wajabta sanya limamima’asumi shine domin tsayu wajen kauda sharri da zalunci a birni dakauye, da kafa adalci da tabbatar da sanin ya-kamata a tsakaninal’umma.

Abin tambaya anan shine: shin Kenan kuna nufin a cikin kowane birnida kauye da Allah ya halitta akwai Imam mai hana zalunci da tsaidaadalci tsakanin mutane? Idan kun ce eh akwai sai muce wannandanne gaskiya ne kiri-kiri! Ku na nufin har kasashen kafirai akwaiMa’asumai Kenan ? hakanan a Sham wajen Mu’awiya ma akwaikenan?

Idan kuma ku ka ce eh shi Imam din guda daya ne amma yana damataimaka da ke wakiltar shi a sauran wurare sai mu ce muku:wadannan wakilan a dukkanin garuruwan duniya akwai su ko kuwa awasu kebantattun garuruwa ne?

Idan ku ka ce eh a dukkanin birane da kauyuka ne sai mu ce mukuwannan zancen kawai ne a wajen dukkanin mai hankali!

Idan ku ka ce a ‘a yana da mataimaka ne a wadansu daga cikin biraneda kauyuka kadai sai mu ce muku yo ai dukkanin birane da kauyukasuna bukatar ma’asumi da zai tsaida adalci ya kawar da zalunci, dawane dalili za a baiwa wasu birane da kauyuka fifiko a kan wasu?

29- Al-Khulaini ya kulla babi mai zaman kansa a cikin littafinsa “Al-khafi” da matashiya kamar haka: “Mata ba sa gadon komi daga Aqaar(gidaje da filaye da kango)” a ciki ya ruwaito ruwaya daga AbuAbdillahi cewa “Mata bas a gadon komi na Aqaar (gidaje da filaye dakango)”

At-Tusi ya rawaito a cikin littafinsa “At-Tahzeeb” 25 daga Maysir cewa“na tambayi Abu Abdillahi game da mata me za a basu na gado? Sai

25 Furu’ul Khafi (7/127)

21

yace: za a basu hasafin duk bulo da turbaya da katakon da aka yiamfani da ita wurin gini, amma ba a basu kasa ko kango ko gini dasunan gado.

Muhammad dan Muslim ya ruwaito daga Abu Abdillahi cewa “mataba sa gadon komi na abinda ya shafi kasa da gini’.

An karbo daga Abdulmalik dan A’ayun cewa “Mata ba su da gadongini ko gona ko wani abu na daban”.

Idan mun lura da kyau za mu ga ba a keba Fatima (r.a) ko waninta baa cikin wadannan ruwayoyin da mu ka ambata.

Duba da wadannan ruwayoyi na Shi’a za mu ga Kenan babu hakkinFatima (r.a) a cikin gadon da Manzon Allah (s.a.w) ya bari.

Bugu-da-kari za mu ga cewa a wajen ‘yan Shi’a dukkanin gadon dawani Imam ya mutu ya bari to hakkin Imam din bayansa ne!

Muhammad dan Yahya ya ruwaito daga Ahmad dan Muhammad, yadaga shi zuwa ga Amru dan Shamr, daga Jabir, daga Abu Abdillahiyace :” Allah ya halicci Adamu, sai ya yanka masa kasa yankawa,dukkanin abinda Adam ya rasu ya bari to na Manzon Allah ne (s.a.w)ne, haka nan dukkanin abinda Manzon Allah (s.a.w) ya bari to nalimamai ne daga cikin iyalan Muhammad”26. Kuma limamin farkobayan Annabi Muhammad (s.a.w) a akidar Shi’a shine sayyidina Aliyu(r.a), Kenan shi ke da hakkin tambayar gadon gonar Fadak ba NanaFatima (r.a) ba, sai gashi ba mu ga ya yi hakan ba, har an ruwaitodaga wajenshi ma yana cewa “da na so da na kama hanya ta tamallakar matatar zuma, da mabakacin alkama, da masakar riga,amma ba zai yiwu in biye wa son zuciya ta ba, ta yadda zan tsundumawajen tattara nau’ukan abinci, alhali za ta yiwu a can wajajen Yamanda Yamama a samu wanda rabon da ya koshi da abinci har yamanta.27

26 Usulul Khafi (1/476)27 Nahjul Balaga (1/211)

22

30- Me ya sa Abubakar (r.a) ya yaki masu ridda har yana cewa: daace za su hana ni igiyar akalar rakumi da su ka saba baiwa ManzonAllah (s.a.w) da sai na yake su? Sai gashi Shi’a su na cewa sayyidinaAliyu (r.a) ya ki fito da Mus’hafin da ya gada ne daga Manzon Allah(s.a.w) saboda tsoron riddar mutane! Wannan Magana akwai rudania cikinta, domin me zai hana shi hakan bayan ya zamto Khalifa,musammankuma ga karfafa ta musamman da ya samu dagaUbangiji kamar yadda ya shahara a cikin ruwayoyin yan Shi’a. To anan Kenan ya yadda ya bar mutane cikin bata saboda tsoron riddarsu?Ya abin yake ne? ku bayyana mana.

31- Ahlus Sunnah da ‘yan shi’a da dukkanin kungiyoyinsu sun haduakan cewa sayyidina Aliyu (r.a) jarumi ne kwarai, ba ya tsoron zarginmai zargi ko fusatar mai fusata sai tsoron Allah kadai, kuma dawannan shaja’a ya taso bai taba rasa ta ba kwata-kwata, har zuwalokacin da Ibnu Muljam ya kashe shi. Kuma mun sani cewa yan Shi’asuna bayyana Aliyu (r.a) a matsayin wanda manzon Allah (s.a.w) ya yiwa wasiyyar khilafa bayansa, to a nan wurin jarumtarsa ce ya rasahar ya yi wa Abubakar Mubaya’a Kenan? Bayansa kuma ya yiwa Umarda Usman (r.a). me ya hana shi hawa minbarin Manzon Allah (s.a.w)ko da sau daya ne a lokacin jagorancin wadannan bayin Allah yabayyana cewa shine Khalifa an dai zalunce shi ne kawai tunda daiJarumi ne?

Me ya sa bai nemi hakkinsa ba lokacin jagorancinsu duk da yana damuridai da magoya baya da yawa?

32- Hadisin mayafi ya shafi mutane hudu ne daga iyalan Aliyu (r.a),to da wane dalili ne yan Shi’a ke shigar da wasunsu na daban cikinfalalar hadisin ya kebe ne tare da tsarkake wadannan mutane hudunkadai?

23

33- Shi’a sun ruwaito daga Imam Ja’afar As-Sadik – wanda su keriya cewa shi ne wanda ya assasa mazhabar Ja’afariyya – yana fadiyana mai alfahari da cewa: “Abubakar (r.a) so biyu ya haife ni”28,saboda yana dangantuwa zuwa ga Abubakar ta hanyoyi biyu:

Na farko: ta hanyar mahaifiyarsa Fatima ‘yar Kasim dan Abubakar.

Na biyu: ta hanyar kakarsa ta wajen uwa Asma’u ‘yar Abdurrahmandan Abubakar wato mahaifiyar Fatima ‘yar Alkasim dan Muhammaddan Abubakar .

Amma saboda rashin basira sai ga Shi’a sun ruwaito ruwayoyin karyaa cikin littafansu inda Jafar As-Sadik ke zargin kakansa Abubakar(r.a)!

Abin tambaya shine: ta ya Jafar zai yi alfahari da kakansa, a lokaciguda kuma yana kushe shi da sukarsa? Idan gamagarin mutum ne yayi haka za a iya bashi uzuri da jahicinsa, amma babu yadda za a yimalami kuma masani irin Jafar As-sadik ya yi wannan tufka dawarwarar.

34- A zamanin Umar (r.a) an ‘yanta masallacin Al-Aqsa, haka nan azamanin Jagoran musulmi Sunni Salahud Dinil Ayyubi ma haka.

Me yan Shi’a su ka taba yi a tarihinsu na bajinta?

Muna kalubalantar yan Shi’a da su kawo mana taku daya na kasa dasu ka taba ‘yantawa ko budewa ko wani mashahurin yaki da sukagwabza da kafirai a cikinshi da su ka yi.

35- Yan Shi’a suna babatun cewa Umar (r.a) yana gaba da Aliyu(r.a), sai gashi Umar (r.a) ya wakilta Aliyu a garin Madina bayan ya fita

28 Kashful Ghumma na Al-Irbili (2/374)

24

karbo makullan Baitul Maqdis, duk da yake da ace wani abu ya samuUmar a wannan tafiyar har ya rasu to Aliyu ne zai maye shi amatsayin Khalifa tun da shi aka nada a matsayin na’ibi.

To a kan wace kiyayya ku ke Magana ya k u yan Shi’a?!

36- Yan Shi’a suna riya cewa idan Mahadinsu ya bayyana zai yihukunci ne da irin hukuncin iyalan Dawuda, ma’ana ba zai tambayidalilan kowa daga cikin masu kawo gara gabanshi ba! To ina shari’arMuhammad (s.a.w) Kenan da ta shafe shari’o’in da su ka gabace tawadda ke wajabta tambayar dalilai daga masu ‘kara ya ku yan Shi’a ?

37- Me ya sa Mahadin Shi’a zai yi zaman lafiya da Yahudu daNasara idan ya bayyana amma ya yaki Larabawa da Qurayshawakamar yadda ku ke riyawa a takardunku? Ashe Manzon Allah (s.a.w)da sauran limamanku ba larabawa ba ne daga kabilar Quraish?

38- ‘yan Shi’a suna riya cewa su limamai daga kwankwaso akedaukar cikinsu, a haife su ta cinyar dama!29 Shin da su da ManzonAllah (s.a.w) wanene ya fi daraja da falala? Ga shi dai Manzon Allah(s.a.w) mahaifiyarsa a cikinta ta dauke shi, ta haife shi ta mahaifa.

39- Shi’a sun ruwaito daga Abu Abdillahi yana cewa: “Ma’abocinwannan al’amari namu (Mahadi) wani irin mutum ne wanda babu maikiranshi da sunanshi sai kafiri!”30.

Sai gashi sun ruwaito daga Abu Muhammad Alhassan Al-Askari yafadawa mahaifiyar Mahadi cewa : za ki haifi wani ‘da, sunansa

29 Ithbatul Wasiyyah na Al-Mas’udi (196)30 Al-Anwarun Nu’umaniyya (2/52)

25

Muhammad, shine zai dora daga inda na tsaya”31

Ashe wannan ba tufka da warwara ba ne? wani lokacin su ce wandaya kira shi da sunanshi kafiri ne, wani lokacin kuma sai ga AlhassanAl-Askari ya kira shi da sunanshi Muhammad?

40- Al-Khulaini ya ruwaito a cikin Al-Khafi daga Ahmad danMuhammad wanda ya ruwaito cewa Abu Abdillahi ya ce : “Anharamta sanya bakin abu, saidai a Huffi da Rawani da Mayafi”32.

Wata ruwayar daga Abu Abdillahi daga Manzon Allah (s.a.w) yanacewa : “Manzon Allah (s.a.w) yana kin sanya bakin abu, sai a huffi damayafi da rawani”33

Al-Hurrul Amili ya ruwaito a cikin littafinshi “Al-Wasa’il” daga Sadukdaga Muhammad dan Sulaiman zuwa ga Abu Abdillahi cewa antambaye shi: za a iya sallah a cikin bakar hula? Sai ya ce kada ka yisallah da ita, domin ita din kayan ‘yan wuta ce”!34

Haka an ruwaito daga Abu Abdillahi yana cewa : “kada ku sanyabakaken kaya, domin su tufafin Fir’auna ne”. haka nan an samo dagaHuzaifa dan Mansur yace: Na kasance zaune wurin Abu Abdillahi a“Haira”, sai wani ga dan aike daga khalifa Abul Abbas ya zo yacekhalifa na kiransa, sai ya sa aka zo masa da wani tufafin tanfol maimaganin ruwan sama ya sanya.

Akwai ruwayoyin da suke nuna cewa bakaken kaya kayan abokananadawarsu ne na Banul Abbas.

An ruwaito daga Saduk yace : an ruwaito cewa Jibrila ya zo wurinManzon Allah (s.a.w) yana sanye da bakar abaya, sai Manzon Allah(s.a.w) yace: ya Jibril wannan wane irin kaya ne haka?! Sai yace :

31 Al-Anwarun Nu’umaniyya (2/55)32 Al-Wasa’il (3/278)33 Al-Khafi (2/205)34 Al-Wasa’il (3/281)

26

kayan ‘ya’yan amminka ne Abbas! Sai Manzon Allah (s.a.w) ya fita yaje wurin Abbas yace masa “ya Ammina! Bone ya tabbata gawadannan ‘yaya namu! Sai yace ya Manzon Allah ya zanyi in gogehakan? Sai Manzon Allah (s.a.w) yace : ai alkalami ya riga ya bushe.Amma35 dai zahirin ‘yan wutan da ake nufi a nan su ne wadanda za sushiga su dawwama cikinta ranar tashin alkiyama, su ne Fir’auna dawadanda suka bi hanyarsa, da masu kama da shi daga cikin batattunkungiyoyi, kamar khalifofin Abbasiyya, da wadansu daga cikin kafiranwannan al’umma da wadanda su ka rigaye ta, wadanda su ka rikibakaken kaya a matsayin tufafin sanyawarsu36.

Haka nan ya ruwaito daga Saduk da sanadinshi zuwa Ismail danMuslim, zuwa ga Abu Ja’afar As-Sadik yana cewa: Allah ya yi wahayiga daya daga cikin annabawanshi cewa: ka gayawa muminai kada susanya tufafin makiya na, kada su ci daga abincin makiya na, kada subi hanyoyin makiya na, idan ku ka aikata haka sai ku zama makiya nakamar yadda su ke makiya na.

Ya kawo a cikin littafin “Uyunul Alkhbaar” daga Aliyu (r.a) cewaManzon Allah (s.a.w) yace : “tufafin makiya su ne bakake, abincinsusu ne giya…. Har zuwa inda yace : dabi’un makiya su ne zakkewaabubuwan zargi, da majalisun shan giya da shagala, da majalisunzagin limamai da sauran mutan kwarai, da majalisar aikata laifuka dazalunci da barna.37

Bayan wadannan tarin maganganun da su ka ruwaito daga limamaina zargin bakaken tufafi, da nuna cewa wadannan tufafi ne irin namakiya Shi’a, to da wane dalili ne a yau ‘yan Shi’a ke sanya bakakentufafi da girmama su ?

41- Idan mutum na son shiga Shi’anci, to wane daga cikin

35 Daga nan zuwa kasa maganar Al-Hurrul Amili ce da sharhinsa36 Al-Faqih (2/252)37 Uyunul Akhbar (1/26)

27

mazhabobin shi’a zai shiga ? Imamiyya ko Isma’iliyya ko Nusairiyyako Zaidiyya ko Duruz? Kowanne a cikin wadannan yana riya cewa shine ne ke kan hanyar Ahlul baiti, kuma dukkaninsu sun yi Imani daImama kuma suna gaba da sahabbai38, bugu da kari sun yi amannada limancin Aliyu (r.a) da cewa ita din rukuni ce, kuma shi ne khalifana farko kai tsaye.

42- Shin an saukarwa Manzon Allah (s.a.w) da wadansu takardunbanda Alkur’ani mai girma? Ta yadda Aliyu (r.a) ya kebanta da su?Idan kun ce a’a, to me za ku ce gameda wadannan ruwayoyin naku?Ga su kamar haka:

A- “Al-Jami’a”: An ruwaito daga Abu Basir ya ruwaito daga AbuAbdillahi yace : ni ne Muhammad, kuma a tattare da mu akwai“Jami’ah”! sai nace : Allah gafatta Malam! menene “Jami’ah” kuma?Sai yace: ai wani littafi ne mai tsayin zira’i saba’in da awon zira’inManzon Allah (s.a.w), shi yayi shiftar rubutun ciki, shi kuma Aliyuna rubutawa, a cikinta akwai dukkanin halal da haram, ta kunshidukkanin abinda mutane ke bukata!…39

Ku taya ni duba inda yace “ta kunshi dukkanin ababen da mutane kebukata”. to da wane dalili ne aka boye ta aka hana mu amfana daabinda ke cikinta?! ashe wannan ba boye ilimi ba ne?

B- “Littafin Namus”: An ruwaito daga Ridha (r.a) cewa daga cikinalamomin Imam shine “za a samu wani littafi a wurinsa wadda kedauke da sunayen yan Shi’ansu daga nan har ranar tashinAlkiyama!”40.

Wannan kam wane irin littafi ne da zai dauke sunan dukkanin wanidan Shi’a da aka yi har zuwa ranar Alkiyama?! Da ace a yau za adau sunayen mutanen Iran kadai a rubuce su a wannan littafi da

38 Zaidiyya ta fi sauran sassauci a wannan babin39 Al-Khafi (1/239)40 Biharul Anwar (25/117)

28

mun samu akalla mujalladi dari alal akalla!

C- “Littafin Abeeta”: an ruwaito daga Amirul Muminina Aliyu yanacewa : “Na rantse da Allah akwai dimbin takardu a waje na da kedauke da labaran Manzon Allah (s.a.w) da na iyalan gidansa! dagaciki akwai littafin da ake kira “Abeeta”, su ne mafi tsanani akanlarabawa, littafin ya ambaci kabilu sittin na larabawa da ba su dawani rabo a cikin addinin nan kwata-kwata”41

Tsokacin da za mu yi a nan shine lallai ne hankali ba zai daukiwannan littafi ba, domin idan dukkanin kabilun nan na larabawa basu da rabo a musulunci to wanene musulmi Kenan? Sannan kuduba ku ga yadda aka kebance larabawa kadai da wannanmummunan hukunci, ba abinda hakan ke nunawa face kabilancikawai.

D- Littafin “Zu’abatus saif”: an ruwaito daga Abu Basir daga AbuAbdillahi yana cewa a kan tsinin takobin Manzon Allah (s.a.w)akwai wani dan kankanin littafi, a cikinshi akwai haruffan dakowanne daya daga cikinsu jagora ne zuwa ga bude harafi dubu!Abu Basir yace: Abu Abdillahi yace: har maganar nan da akeharuffa biyu ne kadai suka fito daga cikinsu!

Tambayarmu a nan itace: ina sauran haruffan su ke?

Ashe bai dace su fito fili ba ko Shi’ar Ahlul Baiti za su amfana dasu?

Ko kuwa dai za su cigaba da fakewa ne su ma har sai Mahadinsuna kogo ya fito sai su fito tare?

Ina amfaninsu idan ba za su fito ba alhali ga al’umma na ta halakada jahilci ?

E- “Littafin Aliyu”: wannan shi ma wani littafin ne da suka ce yanamakale a saman takobin Manzon Allah (s.a.w)!

41 Biharul Anwaar (26/37)

29

An ruwaito daga Abu Abdillahi (r.a.) yana cewa : an gano wanilittafi a saman takobin Manzon Allah (s.a.w) sai ga shi an rubuta ajikinsa cewa: “Da sunan Allah mai Rahama mai Jinkai, mafi barnadaga cikin mutane shine wanda ya kashe wanda bai tsokane shiba, da wanda ya doki wanda bai doke shi ba, shi kuma wanda yajibinci wadanda ba iyayen gidansa ba to ya kafurta da abinda Allahya saukar ga Muhammadu (s.a.w), wanda ya kirkiri bidi’a ko yabaiwa dan bidi’a mafaka to Allah ba zai karbi aikin farillarsa danafilarsa ba ranar Alkiyama”42

F- “littafin Al-Jafr (Rami)” shi ma iri biyu ne, akwai fari akwai ja: Anruwaito daga Abul ala yace: na ji baban Abdillahi (r.a.) yana cewa:“ina da farin rami”. Sai na ce masa: menene a cikinshi? Sai yace :Zaburar Dawuda da Attaurar Musa da Injilar Isa, da littattafanIbrahim (a.s) da halal da haram! Sai nace: to menene a cikin janramin? Sai yace: Makami! Ba a bude shi sai idan za a zubar da jini!Sai Abdullahi dan Abul Ya’fur yace masa: tsaya tukuna! shin‘ya’yan Alhassan sun san da wannan? Yace: eh wallahi kamaryadda su ka san hasken rana da duhun dare, sai dai son kai dadanne gaskiya ne kawai da ke damunsu shi ya sa su ke boyegaskiya, amma da sun neme ta da sun same ta.43

Haba yan Shi’a! idan akwai duka wadannan ababe da ake fada acikin wannan littafi, Zabura, Lingila, Attaura da littattafan Ibrahimda dukkanin halal da haram to don menene ake boye shi ba za afito da shi ba al’umma ta amfana?

G- “Mus’hafu Fatima”: An ruwaito daga Aliyu dan Sa’eed daga AbuAbdillahi (r.a.) yana cewa : Akwai Mus’hafin Fatima tattare da mu,babu aya daya daga cikinshi a cikin Alkura’ani, Manzon Allah dakanshi ya yi wa Aliyu (r.a.) shifta ya rubuta shi.44

An ruwaito daga Muhammad dan Muslim daga daya daga cikinsu

42 Biharul Anwaar (27/65)43 Usulul Khafi (1/54)44 Biharul Anwaar (26/41)

30

(r.a.) yana cewa : Fatima ta bar wani littafi shi ba Alkur’ani ba ne,amma dai littafi ne mai dauke da maganar Allah da aka saukarmata, Manzon Allah (s.a.w) ne ya yi shiftarsa Aliyu (r.a.) yarubuta.45

Daga Aliyu dan Abu Hamza daga Baban Abdillah (r.a.) yana cewa:“Muna da littafin Fatima da aka bamu, babu harafi daya naAkur’ani a ciki, Manzon Allah (s.a.w) ne ya yi shiftarsa ga Aliyu (r.a.)ya rubuta.46

To matukar dai wannan littafin Manzon Allah (s.a.w) ne ya yi shiftarsa,Aliyu (r.a) ya rubuta don menene ake boye shi, a fito dashi fili kowa yaamfana mana, alhali gashi nan Allah ya wajabta ma Manzonsa bayyanar dailimi da barin boye shi, Allah ta’ala yana cewa :

﴾ هتلا سر تغلب امف لعفت مل نإو كبر نم كيلإ لزنأ ام غلب لوسرلا اهيأ ﴿

Yã kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka dagaUbangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinSa ba

ke nan. (Al-Ma’ida: 67)

Haba dai! Ta ya Manzon Allah (s.a.w) zai boyewa al’ummarsawannan ilimi mai matukar muhimmanci haka? hakanan ba girmanAliyu (r.a) ba ne da shi da limaman da su ka zo bayanshi su boyewannan ilimi musamman ga Shi’arsu, matukar dai akwai shi.

H- “Attaura da Linjila da Zabura”: daga Abu Abdillahi (r.a) cewa yakasance yana karanta Zabura da Attaura da Linjila da yarenSiryaniyya.47

A nan sai mu ce me Amirul Muminina da limaman da su ka zodaga bayansa za su yi da Attaura da Zabura da Linjila da har su ke

45 Biharul Anwaar (26/41)46 Biharul Anwaar (26/48)47 Usulul Khafi (1/227)

31

karanta su a tsakaninsu a cikin sirri, alhali wasu nassoshin naShi’a sun nuna cewa Aliyu (r.a) ne kawai ya karade Alkur’ani maigirma da wadansu ilimomin ma, to me zai yi da Zabura da Attaurada Injila kuma bayan Alkur’ani ya riga ya shafe su bakidaya?

Mu abinda mu ka sani kawai shine musulunci littafi daya gare shiwato Alkur’ani mai girma, shi kuwa yawaitar littafai a wajenYahudu da Nasara kadai mu ka sanshi ba ya daga cikin tsarinaddinin musulunci.

43- Me ya sanya Manzon Allah (s.a.w) bai doki fuskarshi da jikinshiba yayin da danshi Ibrahim ya rasu? Shi ma Aliyu (r.a) me ya sanyabai yi haka yayin rasuwar matarshi Fatima (r.a)?

44- Da yawa daga cikin malaman Shi’a ba su san harshen larabciba, musamman na Iran, to ‘ka’ka su ke kwakulowa tare da fahimtarhukunce-hukunce daga cikin Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah(s.a.w) duk da yake sananne ne cewa larabci ginshiki ne na malanta aaddinin musulunci?

45- Yan Shi’a su na kudurce cewa galibin sahabbai munafukai neda kafirai sai fa ‘yan kadan! To idan haka ne me ya sanya suwadannan masu yawan da su ka yi ridda ba su gama da wadannankalilan din ba da ke tare da Manzon Allah (s.a.w)? idan kun ce saibayan ya rasu ne su ka yi ridda ta yadda mutum bakwai ne kadai suka yi ragowa a musulunci! To me ya sa su wadannan da su ka yiriddan ba su ga bayan yan kadan din da su ragu a cikin musulunci bata yadda za su ga bayan addinin kwata-kwata a koma bautar gumakagaba daya kamar yadda yanayin yake a zamanin iyayensu dakakanninsu?

32

46- Shehin Shi’a Abu Ja’afar Muhammad dan Hassan Al-Tusi ababban littafinsa “Tahzibul Ahkaam48” yana fadi cewa: Godiya tatabata ga Allah majibincin gaskiya, salatinsa ya tabbata akanzababbun halittarsa Muhammad (s.a.w). bayan haka akwai wanidan’uwa da ya ja hankali na kan wadansu hadisai na malamanmuAllah gafarta musu, wadanda ke dauke da sabani da tufka dawarwara ta yadda ba za ka ga wata magana ba face da ka gusa gabakadan za ka ga kishiyarta ko mai warware ta, haka nan ba ka ganinwani hadisi sai ka ga kishiyarsa kusa da shi, har masu sabani da musuka yi riko da wannan dalili a matsayin babban makamin sukarakidar da mu ke kai…”

Sayyid Daldar Ali Al-Lakahnawi Al-Shi’ee ya fada a cikin “Asasul-Usuul49” cewa : hadisan da aka ruwaito daga limamai suna tsananincin karo da juna, ba za ka samu wani hadisi ba face ka ci karo da maiwarware shi, har wannan ya zamto dalilin fitar wasu daga cikin masu‘yar karamar fahimta daga Shi’armu….”

Babban malaminsu Hussein Al-Kurki yana cewa a cikin littafinsa“Hidayatul Abraar”50 yana cewa : saboda wancan dalili ne na yawaitartufka da warwara a cikin ruwayoyi da maganganun da ke cikinlittafanmu ya wallafa littafin “Tahzibul Ahkaam” kamar yadda yabayyana a matashiyarsa bayan labarin da ya samu na ficewar adadimai yawa na yan Shi’a daga cikin mazhabar”

Abin da zan yi tsokaci da shi a nan shine kun ga dai jagororin Shi’a dakansu sun tabbatar da tufka-da-warwarar da ke cikin mazhabarsu,gashi kuma Allah na fadi game da karya cewa :

ـ﴾ اريثك اف ال تخا هيف اودجول هللا ريغ دنع نم ناك ولو ﴿

“kuma dã yã kasance daga wurin wanin Allah haƙĩƙa, dã sun sãmu, acikinsa, sãɓã wa jũna mai yawa?” (An-nisa: 82)

48 (1/45)49 Shafi (51)50 Shafi (164)

33

47- Shi’a suna kudurce cewa Aliyu dan Abu Talib (r.a) yana da fifikoakan dansa Hussaini, to idan dai da gaske ku ke me ya sa ba kwakokawa game da kisan da aka yi masa duk sanda ranar ta zagayokamar yadda ku ke yi ga Hussaini (r.a)?

Sannan ashe ba Manzon Allah (s.a.w) ne sama da su biyun duka ba?To me ya sa ba kwa sharara kuka saboda mutuwarsa da rashinsasama da nasu?

48- Idan Imamar Aliyu (r.a) da ‘ya’yansa biyu rukuni ce daga cikinrukunnan addinin musulunci ta yadda Imani ba ya cika sai da ita,kuma wanda bai yi Imani da ita ba sai ya shiga wuta ko da kuwa yashaida da babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ya yi salla yabada zakka ya je hajji ya yi azumi kamar yadda Shia ke riyawa, to meya sanya babu ko da ishara guda ga wannan muhimmin rukunin acikin Alkur’ani mai girma? Duk da gashi Alkur’ani ya bayyana wadansurukunnan da wajibban da ba su kai girmanshi da muhimmancinshi ba.Za mu ga yadda Alkur’ani ya ke bayanin sallah, da zakkah da hajji daazumi har da wasu baubuwan ma da mustahabbai ne ba wajibai bakamar hukunce-hukuncen farauta misali, amma kuma babu bayaninImama a ciki ko ta kusa ko ta nesa. Ya aka yi?

49- Da ace al’ummar sahabbai al’umma ce mara tsari mai cike dahasada da keta ga junanta da neman mulki da khilafa ta kowacehanya kamar yadda yan Shi’a ke so su nuna, da ace haka ne damusulunci bai kai inda ya kai ba ta hanyar tasiri da bude garuruwa dayaduwa cikin dan kankanin lokaci, kuma duk a lokacin sahabbaihakan ta faru, Allah kara yarda da su.

50- Da wane dalili ne da dama daga cikin ‘yan Shi’a ke wofintar da

34

sallar Juma’a wadda Alkur’ani ya wajabta halattar ta a fili a cikin ayarSuratul Jumu’a mai cewa :

مكلذ عيبلا اورذو هللا ركذ ىلإ اوعساف ةعمجلا موي نم ةالصلل يدون اذإ اونمآ نيذلا اهيأ اي ﴿

﴾ـ نوملعت متنك نإ مكل ريخ

“Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni ! Idan anyi kirã zuwã ga salla a rãnarJumu´a, sai ku yi aiki zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki.

Wancan ɗinku ne mafi alheri a gare ku idan kun kasance kunã sani.” (Al-Jumu’a:62)

Idan su ka ce ba ma yinta ne saboda muna son fitowar Mahadi51! Saimu ce yanzu wannan ya isa ya zama dalilin barin ibada mai matukarmuhimmanci irin wannan ta yadda dubban daruruwan yan Shi’a kemutuwa ba tareda sallatar wannan babbar ibada ba? Me za sufadawa Ubangijinsu?

51- Yan Shi’a na kudurce cewa Abubakar da Umar (r.a) sun shafewadansu daga cikin ayoyin Alkur’ani mai girma!

Sun ruwaito cewa an tambayi Abu Ja’afar cewa me ya sa aka sanyawaai Allah ne ya rada masa, ga yadda : Aliyu suna Amirul Munina? Sai yace

:ayar ta ke a cikin Alkur’ani

تسلأ مهسفنأ ىلع مهدهشأو مهتيرذ مهروهظ نم مدآ ينب نم كبر ذخأ ذإو )!( نينمؤملا ريمأ ايلع نأو يلوسر ادمحم نأو مكبرب

Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya karɓi (alkawari) daga ɗiyan Ãdam, )daga bãyayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rãyukansu,(Ya ce): "Shin, bã Nĩ ne Ubangijinku kuma Muhammadu manzona ne Aliyu

51 Domin su na ganin cewa ayyukan ibada sun fadi har sai mahadi ya bayyana, wasunsu kuma na ganinyawan zakkewa ayyukan sabo ne zai gaugauta fitar mahadin don ya zo ya kawo gyara, kamar yaddaruwayoyi da dama su ka zo da hakan daga littattafansu.

35

52(!!kuma Amirul Muminina?

Al-Kulaini yana cewa a karkashin tafisirin ayar:

﴾ هب اونمآ نيذلا ف ﴿

(To, waɗanda suka yi ĩmãni da shi)

Yace: ma’ana Imam Kenan!,

﴾ نوحلفملا مه كئ ـ لوأ هعم لزنأ يذلا رونلا اوعبتاو هورصنو هورزعو ﴿

kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka taimake shi, kuma suka bi haske wandaaka saukar tãre da shi, waɗannan ne mãsu cin nasara." (Al-Aaraf:157)

yace: ma’ana: wadanda su ka nesanci bautar Jibtu da Dagutu Kenan,su kuwa Jibtu da Dagutu su ne wane da wane.53”

Al-majlisi yace: abin da ya ke nufi da wane da wane su ne Abubakarda Umar!54

Da wannan ne yan Shi’a ke kallonsu a matsayin Shaidanun mutane,Allah kiyaye!

Ya zo a cikin tafisirinsu ga ayar:

﴾ ناطيشلا تاوطخ اوعبتت ال ﴿

“kada ku bi hanyõyin Shaiɗan”(An-Nur: 21)

Sai su ka ce: “wallahi hanyoyin shaidan din da ake nufi su ne khilafarwane da wane!”55

52 Usulul Khafi (1/412)53 Usulul khafi (1/429)54 Biharul Anwaar (23/306)55 Tafsirin Ayyashi (1/214)

36

Sun ruwaito cewa Abu Abdillahi yace:

{ اميظع ازوف زاف دقف هدعب نم ةمئ األ ةي ال وو يلع ةي وال يف هلوسرو هللا عطي نمو }

Ma’ana: “wanda ya yi wa Allah da manzonsa “da’a game da wilayar Aliyu dawilayar a’imma da su ka zo bayansa to hakika ya rabauta da rabo maigirma!!”

Su ka ce: Baban Abdallah yace haka ayar ta sauka!56

Daga Abu Abdillahi yace: haka Jibrila ya saukarwa Manzon Allah(s.a.w) da wannan aya:

{ ايغب يلع يف هللا لزنأ امب اورفكي نأ مهسفنأ هب اورتشا امسئب }

Ma’ana: “tir da abin da su ka siya ga kawunansu da kafircewa da abindaAllah ya saukar na wilayar Aliyu bisa zalunci!!”57.

Daga Jabir yace : Jibril ya saukarwa Muhammad da wannan aya haka:

{ هلثم نم ةروسب اوتأف يلع يف اندبع ىلع انلزن امم بير يف متنك نإو }

“idan kun kasance cikin kokonto daga abinda mu ka saukar gabawanmu game da Aliyu to ku zo da surah kwatankwacinsa”58

Daga Abu Abdillahi yace: haka Jibrila ya saukarwa Manzon Allah(s.a.w) da wannan aya:

{ انيبم ارون يلع يف انلزن امب اونمآ بتكلا اوتوأ نيذلا اهيأ اي }

Ma’ana: “ya ku wadanda aka saukarwa littafi, ku yi Imani da abinda mu “ka saukarwa Aliyu na haske bayyananne”59.

Daga Muhammad dan Sinan daga Rida (a.s) yana cewa:

56 Usulul Khafi (1/414)57 Usulul Khafi (1/417)58 Sharhu Usulil Khafi (7/66)59 Sharhu Usulil Khafi (7/55)

37

ي} لع ةي وال نم دمحم اي هيلإ مهوعدت ام يلع ةي ال وب نيكرشملا ىلع ربك }

Ma’ana: “Abinda ka ke kiran mushirikai akanshi ya kai Muhammad na batunwilayar Akiyu ya girmama gare su”

.Yace haka aka saukar da ita.60

Daga Baban Abdallah yace :

{ عفاد هل سيل يلع ةي ال وب نيرفاكلل عقاو باذعب لئاس لأس }

“Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa gawadanda su ka kafircewa wilayar Aliyu babu mai tunkude ta”Yace: wallahi haka jibrila ya sauka da ita61.

An ruwaito daga Abu Abdillahi yana cewa: haka Jibrila ya saukar dawannan aya:

نيذلا ىلع انلزنأف مهل ليق يذلا ريغ ال وق مهقح دمحم لآ اوملظ نيذلا لدبف }.{ نوقسفي اوناك امب ءامسلا نم ازجر مهقح دمحم لآ اوملظ

Sai waɗanda suka dannewa iyalan Muhammad hakkinsu suka sakemagana watar wannan da aka ce musu, saboda haka muka saukar a kanwaɗanda suka suka dannewa iyalan Muhammad hakkinsu da azãba

daga sama sabõda abin da suka kasance suna yi na fãsiƙanci.62

An ruwaito daga Abu Jaafar yana cewa: Jibril haka ya sauka dawannan aya:

إال اقيرط مهيدهيل وال مهل رفغيل هللا نكي مل مهقح دمحم لآ اوملظ نيذلا نإ }{ منهج قيرط

:sannan yace

60 Sharhu Usulil Khafi (301/5)61 Usulul Khafi (1/422)62 Uuslul Khafi (1/423)

38

مكل اريخ اونمآف يلع ةي وال يف مكبر نم قحلا ب لوسرلا مكءاج دق سانلا اهيأ اي }ةي ال وب اورفكت نإو

.63{ ضر األ يف امو تاوامسلا يف ام هلل نإف يلع

Yan Shi’a na ganin cewa wadannan ayoyin suna nuna imamar Aliyu(r.a) a fili, saidai Abubakar da Umar ne suka canza su kamar yadda suke riyawa.

A nan wajen za mu iya mika tambayoyi guda biyu ga yan Shi’a:

Na farko: idan Abubakar da Umar sun canza akalar wadannan ayoyinme ya sanya Aliyu bai bayyana hakan ba bayan ya zamto khalifanmusulmai bayansu da gyara ayoyin kamar yadda suke?

Idan mun duba za mu ga bai aiwatar da hakan ba, Alkur’ani mai girmaya ci gaba da wanzuwa kamar yadda ya ke a lokacin kalifofi shiryayyuda su ka gabace shi, da lokacin Manzon Allah (s.a.w), domin Allah neya dau nauyin kare shi Alkur’ani kamar yadda yace:

﴾ـ نوظفاحل هل انإو ركذلا انلزن نحن انإ ﴿

Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur´ãni), kuma lalle Mũ, haƙĩƙa,Mãsu kiyayewane gare shi.(Al-Hijr: 9)

Saidai Shi’a na da mantuwa.

Na biyu: wasu daga cikin ayoyin da Shi’a su ka malkwada su domintabbatar da wilayar Aliyu (r.a) suna nuna mana rashin yiwuwar hakana fili!!

Ku duba wannan ayar da ke Magana kan Yahudawa amma su ka juyata kan musulmi:

63 Usulul Khafi (1/424)

39

لآ اوملظ نيذلا ىلع انلزنأف مهل ليق يذلا ريغ ال وق مهقح دمحم لآ اوملظ نيذلا لدبف }.{ نوقسفي اوناك امب ءامسلا نم ازجر مهقح دمحم

A fassarar yan Shi’a suna ganin wannan aya tana Magana ne akanwani abu da zai zo nan gama, wanda Aliyu ya rigaya ya san da hakan.

To a nan wajen da wane dalili ne Aliyu (r.a) da sauran Ahlul Baiti za sunemi a basu hakkinsu matukar dai sun riga sun san cewa za a kwacemusu kuma ba zai taba dawowa wurinsu ba?

Kuma da yaushe ne azabar da Allah ya yi alkawarin saukarta ta saukadin akan wadanda su ka cuci iyalan Annabi game da batun khilafakamar yadda ayar ta nuna?

Kowa ya san hakan bai faru ba, illa iyaka kokari ne na yan Shi’a nacanza Nassi da malkwada shi ta hanyar rashin basira.

52- Shi’a sun ruwaito daga Abul Hasan yana sharin wannan ayar :

﴾ مههاوفأب هللا رون اوؤفطيل نوديري ﴿

Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunansu.(As-Saf: 61)

sai ya ke cewa: ai suna burin bishe hasken Allah ne game da wilayarAmirul Muminina Aliyu.

﴾ هرون متم هللا و ﴿

"alhãli kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne,"

Yace: sai Allah ya kammala Imamarsa, haske a nan wurin shineimama, kamar yadda Allah yace :

40

﴾ـ انلزنأ يذلا رونلا و هلوسرو هللا ب اونمآف ﴿

Sabõda haka ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa da hasken nan daMuka saukar.(At-tagabun: 8)

yace: ma’anar haske a nan shine limamai daga cikin zuriyar ManzonAllah (s.a.w)64.

Abin tambaya a nan shine: shin Allah ya cika haskenshi ne damusulunci ko kuwa da zuwan limamai da wadanda aka wa wasiyyadaga cikin Ahlul baiti?

53- A tarihance mutum biyu ne kadai daga cikin limaman da ku kefada su ka samu khilafa, wato Aliyu da Dansa Alhassan (r.a), to inacika hasken da Allah ya yiwa wannan al’ummar tunda dai saurantakwas din bas u samu ba?

54- Littattafan Shi’a sun ruwaito cewa wata mata ta tambayi JafarAs-Sadiq cewa shin ina iya kaunar Abubakar da Umar ? sai yace: eh kikaunace su! Sai tace to idan na hadu da ubangiji na in sanar da shicewa kai ne ka ce in kaunace su? Sai yace: eh.65

Hakanan sun ruwaito cewa wani mutum daga cikin daliban ImamBakir ya yi mamaki wata rana da jin Imam Bakir ya siffanta Abubakarda cewa Siddiq (mai gaskiya), sai mutumin yace: yanzu a bakinka zaa ji wannan yabon ga Abubakar? Yace: kwarai kuwa shine Siddiqkuma duk wanda bai kira shi da mai gaskiya ba to kada Allah yagasgata maganarshi a ranar lahira66

To menene ra’ayin Shi’a game da Abubakr (r.a)

64 Alkhafi (1/149)65 Raudatul Khafi (8/237)66 Kashful Ghumma (2/360)

41

55- Abul-faraj Al-Asfahani ya ambata a cikin littafinshi “MakatilutTalibiyyeen67”, da Irbili a cikin “Jala’ul Gumma68”, da Majlisi a cikin“Jala’ul Uyuun”69, cewa Abubakar dan Aliyu dan Abu Talib yana dagacikin wadanda aka kashe a Karbala tare da dan’uwanshi Hussaini(r.a), kamar yadda aka kashe ‘daya daga cikin ‘ya’yan Hussaini maisuna “Abubakar”! to da wane dalili yan Shi’a ke boye hakan su kebada kulawa akan Hussaini kadai?

Ba wani dalili ba ne face saboda sunansu Abubakar ne kawai.Wannan kuma shine abinda ‘ya Shi’a ba sa son mabiyansu su sani,domin zai fallasa karerayinsu matuka, na cewa akwai jikakkiyatsakanin Ahlul Baiti da sahabbai musamman manyansu irinsuAbubakar da Umar da sauransu, domin kuwa da ace Abubakar kafirine wanda yayi fashin khilafa kamar yadda su ke riyawa da ba mu gaAhlul baiti su na rada wa ‘ya’yansu wannan sunan ba. Babu abinda yarage sai dai mu ce tsananin kauna ce da zumunci da ke tsakaninsu yasanya su ke sanya sunansu.

Sannan da wane dalili ne yan Shi’a ba sa koyi da imamansu wajensanyawa ‘ya’yansu suna Abubakar da Umar da sauransu matukar daida gaske su mabiyansu ne?

56- Imani da kasantuwar Manzon Allah (s.a.w) cikamakinannabawa da Manzanni shine mafi girman abu da wanda yayi shikuma yayi ayyuka na gari zai shiga aljanna ya kubuta daga wuta amusulunce, kuma ita Imama ma dai babu yadda za a yi matukarta tawuce hakan , Kenan Imani da Allah din da Manzonsa ya wadatar dagabarinta, domin idan mutum zai shiga aljanna ba tare da ita ba, to itadin ba dole bace akanshi Kenan, idan kuma an ce ba za a shigaaljanna ba sai da ita to wannan ya sabawa Nassin Alkur’ani mai girma,domin Allah ta’ala ya wajabta samun aljanna ga wanda ya yi Imani da

67 (88, 142)68 (2/66)69 (582)

42

shi yayi da’a gare shi da Manzonsa, amma babu inda ya alakantashiga aljanna da Imani da wilaya ko biyayya ga Imam.

Allah ta’ala yana cewa:

نيقيدصلا و نييبنلا نم مهيلع هللا معنأ نيذلا عم كئ ـ لوأف لوسرلا و هللا عطي نمو ﴿

﴾ اقيفر كئ ـ لوأ نسحو نيحلا صلا و ءادهشلا و

“Kuma waɗannan da suka yi ɗã´a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan sunãtãre da waɗanda Allah Ya yi ni´ima a kansu, daga annabãwa da mãsuyawan gaskatãwa, da masu shahãda da sãlihai. Kuma waɗannan sun

kyautatu ga zama abõkan tafiya.” (An-nisa: 69)

A wani wajen yana cewa:

نيدلا خ راهن األ اهتحت نم يرجت تانج هلخدي هلوسرو هللا عطي نمو ﴿

﴾ـ ميظعلا زوفلا كلذو اهيف

“Kuma wanda ya yi ɗã´a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi agidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya

bãya, ( Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi.” (An-Nisa: 13)

Tabbas da ace Imama tana da alaka da batun Imani ko kafirci ko aceita din rukuni ce mai girma daga cikin rukunnen addini ta yadda addiniba ya yiwuwa sai da ita to da Allah ya ambace ta filla-filla a cikinlittafinsa, kuma ba zai yiwu ace a tumuemusa ta a dunkule karkashinayoyin da suke maganar wajabcin biyayya ga Allah da Manzonsa ba,lallai ne za a yi bayaninta filla-filla, domin da haka na yiwuwa da saiAllah ya wadatu da ambatar ‘da’a ga Manzonsa kadai domin ai takunshi da’a ga Allah din, amma bai yi haka ba sai ya daidaitabangarorin domin nuna muhimmancinsu, don haka ne ya alakanta

43

tsira a ranar tashin kiyama da da’a ga su biyun duka.

57- Babu shakka a zamanin Manzon Allah (s.a.w) an samumutanen da su ka ganshi sau daya kadai a rayuwarsu su ka komagarinsu, ba tare da sun ji an ambaci wani abu wai shi Imamar Aliyu(r.a) ko ta ‘ya’yansa da jikokinsa ba, musamman kuma gashi Shi’a suna riya cewa umurni da imama ya faru tun farkon fara da’awa, to irinwadannan mutanen imaninsu ya inganta ko kuwa tauyayye ne?

Idan kun ce eh tauyayye ne, sai mu ce to ai Manzon Allah shi ne yakamata ace ya sanarda su kafin tafiyarsu, sai kuma ga shi bai yihakan ba! Me hakan ke nufi Kenan?

58- Ya zo a cikin littafin Nahjul Balaga cewa:

“ Aliyu (r.a) ya aiwaka Mua’awiya sako da cewa: ya kamata ka kwanada sanin cewa wadanda su ka mini mubaya’a su ne dai wadanda suka yi wa Abubakar da Umar da Usman mubaya’a, na kusa ba shi dazabi, na nesa ma ba zai hau kujerar na ki ba, domin tsarin shawara neda ke hannun Muhajirai da Ansar, idan su ka hadu kan wani mutum suka sanya shi Jagora to shi Kenan ta zauna har a wurin Allah, idanwani bayan haka ya ki amincewa sai a maida shi kan gaskiya, idan yatirje yana soke-soke ko shigo da wadansu sabbin lamurra sai su yakeshi har sai ya dawo kan hanyar muminai. Ina tabbatar maka ya kaiMu’awiya da za ka kaucewa son zuciyarka ka yi amfani da hankalinkada ka tabbatar da cewa ni dinnan na barranta daga zubar da jininUsman, kuma za ka san da cewa na yi nisa da hakan, saidai fa idanlaifi kake son dora mini to shikenan ba zan iya hana ka ba! Sai anjima”70.

A cikin nan akwai dalilai ga abubuwa kamar haka:

70 Safwatu Shuruhi Nahjil Balaga (593).

44

1- Muhajirai da Ansar su ne ke zaben imam (jagora), ba shi da wataalaka da rukunin Shi’a a wajen Shi’a.

2- Aliyu (r.a) an zabe shi ne ta irin hanyar da aka zabi Abubakar daUmar da Usman (r.a).

3- Cewa Shura (shawari) yana hannun Muhajirai da Ansar ne, wannanyana nuna falalarsu a wajen Allah ta’ala, ba kamar yadda yan Shi’ake riyawa ba.

4- Cewa abinda Muhajirai da Ansar suka yadda tareda amanna dashina mubaya’a ga wani jagora yardajjen abu ne har wajen Allah ta’ala,babu wani abu wai shi kwatar Imama kamar yadda su ke fadi, idanba haka ba to ta ya Allah zai yarda da hakan?

5- Yan Shi’a suna la’antar Mua’wiya (r.a), saidai ba mu ga sayyidinaAli yana la’antarsa ba a cikin wasikun da ya ke aika masa da su.

59- Yan Shi’a ba su isa su yi inkarin cewa sayyidina Abubakar daUmar da Usman sun yi wa Manzon Allah (s.a.w) mubaya’a akarkashin bishiyar “hudaibiyya” ba, kuma gashi Allah ya bayyanacewa ya yarda da su duk da ya san abubuwan da ke cikin zukatansu,to da wane dalili ne yan Shi’a su ke tawaye ga zancen Allah nakasanutuwarsa ya yarda tare da aminta da su? Allah sawaka.

60- A daidai lokacin da mu ke ganin Yan Shi’a na neman lada tahanyar zagin manyan sahabban Manzon Allah (s.a.w) kamarAbubakar da Umar da Usman, a daidai lokacin kuma ba mu tabaganin wani daga cikin Ahlus Sunnah na zagin daya daga cikin Ahlulbaiti ba, sabanin haka ma kusantar Allah su ke yi ta hanyar kaunarsu.Wannan maganar babu wani dan Shi’a da ya isa ya ja da ita ko dakuwa ta hanyar kage ne.

45

61- So da dama za ka ji yan Shi’a na fadar cewa sayyidina Husaini(r.a) ya rasu ne ta hanyar kishirwa da ya yi fama da ita a fagen fama!da haka ne ma za ka ga suna rubuta wannan ibarar a wajajenfamfunan shan ruwa cewa “sha ruwa amma ka tuna da kishirwarHussain”!

Tambayar mu gare su a nan wurin itace: tun da dai suna riya cewaImam Hussaini ya san gaibu, ashe bai sanda cewa ruwanshi zai kareba ne yayin yakin ta yadda zai yi guzurin ishasshen ruwa da zai isheshi har zuwa gama yakin ba?

Sannan ashe rike isasshen guzurin ruwa a lokacin yaki ba ya cikin rikoda sabubba da Allah ya yi umurni da a yi tanadi wa makiya akarkashin fadinsa:

﴾ مكودعو هللا ودع هب نوبهرت ليخلا طابر نمو ةوق نم متعطتسا ام مهل اودعأو ﴿

.[60: لا فن [األ

“Kuma ku yi tattali, dõminsu, abin da kuka sãmi ĩkon yi na wani ƙarfi,kuma da ajiye dawaki, kunã tsoratarwa, game da shi, ga maƙiyin Allah

kuma maƙiyinku” (Al-Anfal: 60)

62- Hakika addinin musulunci ya cika da fadin Allah (s.a.w):

﴾ مكنيد مكل تلمكأ مويلا ﴿

“A yau Nã kammalã muku addininku,” (Al-Ma’ida:3)

Sai ga shi mazhabin Shi’a din kacokam dinshi ya bayyana ne bayanrasuwar Manzon Allah (s.a.w)!

63- Hakika Allah ya saukar da barrantar Aisha (r.a) a cikin littafinsa,

46

a cikin shahararriyar kissar nan ta kage, Allah ya tsarkake ta dagawannan sharri da kage, sai gashi wadansu daga cikin ‘yan Shi’a ba sukame kabinsu daga daina jingina mata wannan kagen ba, wanda acikin hakan akwai wani nau’i na suka ga Allah ta’ala da Manzonsa aciki.

Tir da mazhabin da ba shi da aiki sai suka ga matan fiyayyen halitta(s.a.w).

64- Matukar dai Aliyu (r.a) da ‘yayansa suna dauke da dukkaninmu’ujizozin da Shi’a su ke jinjina musu a jiya da yau, to me ya sanyaba su amfane su ba lokacin da su ke da rai?

Domin tarihi ya nuna cewa hatta natsuwa da kwanciyar hakalisayyidina Ali bai samu ba a lokacin khilafarshi, daga karshe kumawani dan ta’adda ya far mai ya masa kisan gilla, hakanan shi maAlhassan dole dai da karshe ya ydda kwallon mangwaro ya huta dakuda ta hanyar mikawa Mu’ayiwa shugabancin al’umma, haka shi maHusaini ya shiga cikin matsatsi matuka daga karshe ‘yan ta’adda suka kashe shi!

Idan bas u iya amfanar da kawunansu ba, to ina wadannan dabarunda mu’ujizozin da ‘yan Shi’a ke jingina musu Kenan?

65- Yan Shi’a suna riya cewa falalolin Aliyu suna da yawan gaske,hakanan nassoshin da ke Magana akan imamarshi, anan wajen saimu ce musu mun san da cewa dai babu yan shi’a cikin sahabbai,kuma su ma sun kafirta sahabban! To wanene ya nakalto musuwadannan nassoshin da su ke kafa hujja da su wajen tabbatar dawadannan ababen da su ke son tabbatarwa? Domin dai matukarabubuwan da su ke jinginawa Manzon Allah (s.a.w) ba a samo su tahanyar sahabbai ba, to kai tsaye ba shi da tushe ballantana makama,kuma sahabban da ‘yan Shi’a su ka aminta da su ba su kai adadin

47

cikin ‘yan yatsun hannu daya ba, ma’ana abinda su ka ruwaito dankadan ne, ba zai yiwu a wadatu da ruwayarsu ba, to ta ya hankali zaifahimci wannan tufka-da-warwara ta ‘yan Shi’a?

66- Yan Shi’a su na riya cewa manufar Abubakar da Umar daUsman ba komai ba ne face neman shugabanci da mulki da daukaka,don haka ne su ka zalunci wadanda su ka fisu cancanta dashugabanci! To a nan wajen sai mu ce musu mu dai ba mu ga wajenda wadannan bayin Allah su ka yaki wani mahaluki ko zubar da jininwani dan adam ba saboda neman kujerar mulki, amma mun ga indasu ka yaki kafirai da masu yin ridda, su ne suka karya mulkin Kisra daQaisar suka bude masarautar Parisa su ka shigar da musulunci ciki,su ka ‘daukaka musulunci suka ‘daga kan dukkanin wani musulmi suka kaskantar da kafirci da kafirai. Sannan ga Usman wanda ya ke baikai Abubakar da Umar falala ba amma da masu tada kayan baya suka nemi kashe shi bai yake su ba don kawai ya cigaba da zama akankaragar mulki, ma’ana ko jinin kuda bai zuba ba a lokacinsu tabangaren rigimar neman mulki ko tabbata a kan kujera.

Idan kuwa yan Shi’a su ka doge akan kakaba wa wadannan bayinAllah laifin aikata zalunci don fafutukar ganin sun samu kujerar ikoko dawwama akanta, to anan ya zama tilas su fadi haka game daAliyu (r.a) domin duk tafiyarsu daya ce.

67- Hakika kungiyar “Qadiyaniyya71” ta kafirta ne saboda ta jinginaannabta ga shugabanta, to menene bambancinta da Yan Sha biyumasu jinginawa limamansu dukkanin wata siffa ta annabta?

A cikin siffofin da su ke jinginawa limamansu babu ta yadda za a

71 Qadiyaniyya wata kungiya ce da Mirza Ahmad Gulam Al-Qadiyani ya kafa a kasar India a shekarar 1900.Ya fara a matsayin mai wa’azi, daga nan yace shi ne Mahadi, sannan yace shine Al-Masihu da aka ce zaidawo, sannan liyafa ta cigaba inda ya yi da’awar annabta. Ya rasu a shekarar 1908c.e. duba Mausu’atulAdyan , bugun An-Nadwa (2/93).

48

fahimci wani bambanci tsakaninsu da Manzanni ko kadan, kuma mawai Manzon Allah (s.a.w) ya zo ne don fayyace mana siffofin limamaiko kuwa ya zo ne don fayyace mana addinin musulunci da hukunce-hukuncenshi?

68- Ya aka yi aka bisne Manzon Allah (s.a.w) a dakin Nana Aishabayan gashi ku na tuhumarta da kafirci da munafinci? Ashe wannanba dalili ba ne da ke nuna yardarshi gareta ?

69- Bugu-da-kari me ya sanya aka bisne Manzon Allah (s.a.w)tsakanin Abubakar da Umar (r.a) bayan kuna yi musu kallon kafirai?Ashe Allah zai bar gangan jikin Annabinsa a tsakanin kafirai bayanrayuwarsa?

Kuma ma wace matsaya Aliyu ya dauka na hana hakan? Zai yiwu aceyana ganin za a tafka mummunan aiki kamar wannan ya kauda kai?

Karshe dai dole ku yadda cewa Abubakar da Umar (r.a) musulmai neda su ka samu daukaka ta makwaftaka da abota da Manzon Allah(s.a.w) a raye da mace, idan ba haka ba kuma sai dai ku ce Aliyu (r.a)ya yi kara tare da kauda kai ga munanan ayyuka musamman na barina bisne Manzon Allah (s.a.w) tare da kafirai! Duk wanda ku ka daukaa nan rusau ne ga akidarku.

70- Yan Shi’a su na ganin cewa ayoyi da dama sun tabbata a cikinAlkur’ani mai girma masu nuni da imamar Aliyu (r.a), sai dai sahabbaine su ka boye su!

To wannan tsabar zuki-ta-malle ne! Domin kuwa gashi mun samuhadisan da ke Magana kan falala da limancin Aliyu (r.a) kuma su daisahabban ne su ka ruwaito su, kamar hadisin da Manzon Allah (s.a.w)ya ce da shi: “kai a waje na kamar Haruna ne a wajen Musa” to me ya

49

sa sahabban ba su boye wadannan ba?

71- Halastaccen Khalifa bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w) shine Abubakar kamar yadda dalilai da dama su ka nuna, ga wasu dagaciki:

- Haduwar daukacin sahabbai akan yi masa biyayya akan abubuwanda yayi umurni akansu, da barin ababen da ya hana, ba tare dawani ya ja da baya ba, domin da ace ba su yadda da shi ba da basu bishi akan kuskure ba.

- Aliyu (r.a) bai taba saba mishi ba, hakanan bai taba fito-na-fito dashi ba, don haka a nan wajen dayan abubuwa uku ne: ko dai ku cebai yi haka ba ne saboda gudun fitina, ko saboda ragwanci, kosaboda ya san cewa Abubakar kan gaskiya ya ke.

A nan wajen ba zai yiwu mu ce ya bar hakan ba ne saboda gujewafitina, tunda gashi ya yaki Mu’awiya, kuma an kasha dimbinmutane a wannan yaki, haka nan ya yaki Dalha da Zubairu, daAisha (r.a), don haka tunda dai ya tabbatar shi ke da gaskiya sai beyi tararradi ba wajen yakarsu lai tsaye, ba tare da la’akari da fitinarda ke ciki ba.

Kuma ba za ta taba sabuwa ba a ce ajizanci da ragwanci ba ne,domin wadanda su ka yi yaki tare da shi su na nan a lokacin“Saqifa”, da ace sun tabbatar cewa danniya aka yi mishi da babuabinda zai hana su yi fito-na-fito da Abubakar domin ba ajizai bane, kuma ba ragwaye ba ne da ba su da shaja’a da karfin hali.

Kenan Magana ta karshe itace gaskiya, cewa ya bar fito-na-fito neda Abubakar saboda yarda da nutuswar zuciya da ya yi dajagorancin shi.

72- Yan Shi’a su na riya cewa Mu’awiya (r.a) Kafiri ne da ya yi ridda!

50

Idan hakan ya tabbata to lallai wannan babban suka ne ga Aliyu daAlhassan (r.a), domin abin nufin hakan shine cewa Masu ridda sun cinasara kan Aliyu da Alhassan, kuma Kenan Alhassan ya mikaragamar jagorancin al’ummar musulmi ga kafiri mai ridda wal iyazubillah! A lokaci guda kuma za mu ga cewa Khalid bin Walid ya yakimasu ridda har ma ya tarwatsa su a lokacin Abubakar (r.a), to a nanwanene jarumi Kenan? Sannan kuma a lokacin Abubakar da Umar daUsman (r.a) musulmai na da karfi matuka, rundunoninsu sun karyakafirai, arna na kwarjininsu kwarai, amma sai gashi a lokacin Aliyu (r.a)har masu ridda ma an kasa yakarsu da nasara akansu! Gashi kumaAllah yace:

﴾ـ نينمؤم متنك نإ نولع األ متنأو اونزحت وال اونهت وال ﴿

Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baƙin ciki, alhãli kuwa kũ ne mafiyaɗaukaka, idan kun kasance mãsu ĩmãni.(Al-imran: 139)

A wani wajen kuma yace :

ـ﴾ مكلا معأ مكرتي نلو مكعم هللا و نولعألا متنأو ملسلا ىلإ اوعدتو اونهت الف ﴿

“Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãlikuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa

muku ayyukanku ba.” (Muhammad: 35)

Haka nan za mu ga yadda Aliyu (r.a) ya bukaci Mua’wiya da tsagaitawuta tsakani, kowa ya tsaya kan matsayarsa, a lokacin da ya kasa cinnasara kansa, to da ace mai ridda ne zai bukaci tsakgaita wuta da shi?Ko kuwa hankulan yan Shi’a sun yi nisa ne?

73- Yan Shi’a ba su da wata hanyar tabbatar da Imani da adalcinAliyu (r.a) sai hanyar da Ahlus Sunnah ke bi na tabbatar da hakan!

51

Domin kuwa da ace Khawarijawa da masu kamanceceniya da su dake kafirta Aliyu (r.a) ko fasikantar da shi za su tirje akan kafircinsa dafasikancinsa kamar yadda yan Shi’a ke yi game da Abubakar da Umar(r.a), da babu wata hanya da yan Shi’a za su bi don tabbatar daimaninshi sai irin dai hanyar da Ahlus Sunnah su ka bi ta yin hakan,kuma ita hanyar dai za a bi tilas wajen tabbatar da imanin Abubakarda Umar (r.a)!

Idan su ka kafa hujja ne da ayyukan kirki da da ya yi bayan shigamusluncinsa, to da ire-irinsu dai za a kafa hujja game da Imani danagartar Abubakar da Umar da sauran sahabbai, har ma da irinsuMua’wiya da wasu daga cikin khalifofin Banu Umayya da Banul Abbasna sallolinsu da azuminsu da jihadi a kan kafirai.

Idan Yan Shi’a su ka jingina manafunci ga daya daga wadannan to suma Khawarijawa da irin dalilan dai za su yi amfani cikin sauki sujingina shi ga Aliyu (r.a) ridda da faskianci domin duk jirgi daya ne yakwaso sahabbai gabadaya!

Duk shubuhar da su ka kawo to za a iya basu sama da ita.

Idan su ka tirje wajen maimaita cewa su Abubakar da Umar (r.a)munafinci sukayi ta yadda suka bayyana sabanin abinda ke boye aransu, to Bakhawarije shi ma zai iya cewa shi ma Aliyu (r.a) haka ne!zai ce dama ai shi yana yiwa dan amminsa hasada ne na annabta,kuma akwai ta dama tsakanin ‘ya’yan wa da kani, ya shiga addininsane don bata shi, sai ya kasa hakan har sai lokacin khalifa na ukuUsman, a wannan lokacin ne ya tunzura mutane su yi wa khalifa boredon ya dare akan mulki, ya haifar da yaki da kashe-kashe cikinal’umma, kuma ya kauda kai ga munafukan da su k ace shi Allah ne,domin shi ma yana fito da sabanin abinda ke zuciyarsa ne fili tahanyar takiyya, don haka ne ma a cikin mabiyanshi ne aka samun yanBadini masu fito da munan akidunsu da suka gada daga wajenshi!Khawarijawa duk za su iya fadin haka.

Idan kuma yan Shi’a suna kokarin tabbatar da imaninshi da adalarshi

52

ne ta hanyar ayoyin Alkur’ani mai girma sai a ce musu ai ce musu shiAlkur’ani yana Magana ne a cikin rububi, kuma ko da ya kebe shi dawata falala a wani wuri to ya keba wasunsa ma da wasu falalolinsama da nashi.

Idan su k ace nassoshi ne su ka tabbatar da falalarsa da ingancinimaninsa da adalarsa sai a ce nasossoshin da su ka tabbatar dahakan ga Abubakar da Umar sun fi nashi yawa.

74- Yan Shi’a su na riya cewa Aliyu (r.a) shine ya fi cancantarkhilafa bayan Manzon Allah (s.a.w), saboda falalarsa.

A nan wajen sai mu ce mun ji, to ku taya mu gwadawa tsakaninfalalolin Hassan da Hussaini, da kuma na mutane irinsu Sa’ad bin AbiWakkas, Abdurrahman bin Auf, Abdullahi bin Umar da sauransahabbai daga cikin muhajirai da Ansar, wane ne ya fi falala? Shin zasu iya fifita Hassan da Husseini akan wadannan ta bangaren falala?

Shin suna da wani nassi da zai daure musu gindi kan hakan? Idan suna da shi to akan sahabban da muka amfata ya fi cancanta a samunassoshi daban daban sabode ficen da su ka yi a kan musulunci dada’awa da jihadi, har Mu’awiya ma sai ya shiga gabansu a wannanbabi domin hatta tirjewar da yayi na cewa sai an yi kisasi ga makasadan’uwansa Usman, yana da nassi dake goyon bayansa a cikinAlkur’ani mai girma a ayar:

ناك هنإ لتقلا يف فرسي فال اناطلس هيلول انلعج دقف امولظم لتق نمو ﴿

﴾ اروصنم

Kuma kada ku kashe rai wanda Allah Ya haramta fãce da haƙƙi, kumawanda aka kashe, yanã wanda aka zãlunta to, haƙĩƙa Mun sanya hujja

53

ga waliyyinsa, sai dai kada ya ƙetare haddi a cikin kashewar. Lalle shĩya kasance wanda ake taimako.(al-Isra: 33)

A nan za a iya ce musu ai wanda aka zalumta a nan shi ne Usman (r.a)ta hanyar kisar gilla da aka masa, gashi kuwa Allah ya taimakiwaliyyinsa wato Mu’awiya ya jibinci jinin nasa!

75- Yan Shi’a su na riya cewa Abubakar da Umar (r.a) sun yibabakere ta hanyar kwacen khilafa daga wajen Aliyu (r.a) da daisauransu…

A nan wajen sai mu ce musu idan haka ne me ya sanya Umar (r.a) yasanya shi cikin mutane shida da ya tanada na kwamitin Shurawadanda a cikinsu ne za a cire Khalifa bayansa? Kuma fa ko da baisanya shi ba babu wanda zai damu ballantana yace uffan..

Wannan ke nuna cewa matsayin da yake akai shine daidai damukaminsa domin kuwa ba su tauye shi ba kamar yadda ba su dagashi sama da matakinshi ba, lallai babu komai a tsakaninsu sai zamanlafiya da kwanciyar hankali da girmama juna.

Abinda ke kara tabbatar da hakan shine a lokacin da aka nada shikhalifa sai dukkanin sahabbai Muhajirawa da Ansawa su ka masamubaya’a, idan da ace suna da ta cewa akanshi ko akwai jikakkiyatsakaninsu da ba suyi haka ba.

76- Hakika mun gani yadda mutanen Madina (Ansar) su ka cijegame da khilafa, suna ganin a baiwa daya daga cikinsu wato Sa’addan Ubada (r.a), shi kuma Aliyu (r.a) ya yi zamanshi a cikin gidanshiba ya tare da wadancan ba ya tare da wadannan, to ya a ka yiAnsarawa su ka dawo daga ra’ayinsu su ka yi mubaya’a ga Abubakar?

- Ko dai ya zamto an nuna musu karfin tuwo ne!

54

- Ko ya zamto cancantar Abubakar (r.a) su ka gani su ka mika wuya

- Ko ya zamto babu wani dalilin janyewar ta su.

Idan ‘yan Shi’a su ka ce Ansar sun masa mubaya’a ne da karfi, tosai mu ce wannan karya ne! domin babu wani abinda ya tabbatana nuna cewa an yi ko da cece-kuce a wurin mika jagoracinballantana amfani da karfi, kuma dai kowa ya san irin jarumtar dasu ke da ita wadda su ka nuna ta a lokacin rayuwar Manzon Allah(s.a.w), sun yaki Rumawa da Parisawa da mushirikai da ke saurankauyuka masu kokarin ganin bayan addinin musulunci. Don hakatabbas sun hakura ne saboda ganin cancantarsa ba don an fikarfinsu ba.

Kuma ba zai yiwu ace haka nan kawai su yi amfani da son zuciyadon a baiwa nasu saboda neman girma ko dukiya ba, saidaitabbas sun sallama ma hakan ne don ganin cancantar Abubakar(r.a), wanda hakan ya sanya su janyewa daga karshe, amma badon tsoronsa ba ko wani abu na daban.

To tunda dai neman gaskiya ne ya sanya su sakankancewa tare damikawa Abubakar igiyar jagorancin al’umma, to hakika da ace sunga cancantar Aliyu (r.a) sama da shi da sun masa hakan, don hakasallamawa Abubakar (r.a) da su ka yi ba don komi ba ne sai doncancantarshi da su ka gani gabadayansu. Wannan ko shakka babu.

77- Tunda har Abubakar da Umar (r.a.) su ka ci nasara wajennesanta Aliyu (r.a) da khilafa kamar yadda yan Shi’a ke riyawa, towace riba su ka samu akan hakan? Kuma me ya sa Abubakar daUmar (r.a) ba su gadar da ‘ya’yansu kan kujerar da su ka bari kamaryadda Aliyu (r.a) yayi matukar dai son kai ne abin?

78- Tarihi ya nuna mana cewa mahaifiyar Muhammad danAbdullahi dan Amru dan Usman dan Affan (r.a) itace Fatima ‘yar

55

Hussaini dan Aliyu dan Abu Talib , kenan kakarsa itace SayyidaFatima (r.a), haka nan kakansa shine Usman bin Affan (r.a).

To a nan tunda dai Shi’a suna la’antar Banu Umayya sun yadda dacewa daga cikin jikokin Fatima (r.a) akwai la’ananne Kenan, tunda shiwannan Muhammad din jikanta ne!

79- Sanannen abu ne sananne cewa yan Shi’a sun jinginawalimamansu siffofin Takiyya da tabbatar da cewa su ma’asumai ne basa laifi, alhali wadannan siffofi ne masu cin karo da juna da ba sahaduwa wuri daya, domin ina amfanin rashin laifin nasu matukar idansun firta magana ba a san da gaske su ke ba ko takiyya ce, tunda daitara cikin goman addininsu takiyya ce kamar yadda ku ke ambata atakardunku?

Tunda ya ke kun tabbatar da cewa takiyya na daidai da sallah, kumawanda ya bar takiyya kamar wanda ya bar sallah ne, kuma ita ce tarangoman addininku, Kenan limamanku sun aikata dukkanin taran nan,to me ya rage na kasantuwarsu ma’asumai a nan?

80- Tufka da warwarar ‘yan Shi’a na bayyana a fili wajen kafa hujjarda su ke yi da hadisin “Thaqalain (nauyaya guda biyu)”72, domin kuwasuna kafirta dukkanin wanda ya soki karamin mai nauyin, wato AhlulBaiti, sai kuma gashi a lokaci guda su na sukar mafi nauyinabubuwan guda biyu wato Alkur’ani mai girma, har su na cewa mawanda ya yi haka ijtihadi yayi, ba za a kafirta shi ba. Wannan wane irintufka-da-warwara ne.

81- ‘yan Shi’a na riya cewa daukacin sahabbai sun yi ridda, sai yankalilan da ba su wuce kwaya bakwai ba!

72 Wato hadisin da Manzon Allah (s.a.w) yake cewa : hakika na bar muku nauyaya a bayana, littafin Allahda iyalaina” Tirmizhi ya ruwaito (5/328-329).

56

Tambaya a nan” ina sauran Ahlul baitin kamar ‘ya’yan Jafar da naAliyu (r.a), shin su ma sun yi ridda ne tare da masu ridda?

82- Ya zo a cikin hadisin Mahadi cewa “da ace yini daya ne zaisaura na duniya, da Allah ya tsawaita shi har sai ya aiko wani mutumdaga cikin iyalaina, sunanshi ya dace da suna na, sunan mahaifinshiya dace da sunan mahaifi na”73.

Kenan Mahadin da ake Magana sunanshi zai zamto Muhammad danAbdullahi, amma abin mamaki shi ne na ‘yan Shi’a sunanshiMuhammad dan Alhassan, wannan wane irin rudu ne haka su kefama da shi.

Wani daga cikin malaman ‘yan Shi’a ya so warware wannansarkakiyar ta wata hanya ta ban dariya inda yace: da yake ManzonAllah (s.a.w) na da jikoki biyu, wato Alhasan baban Muhammad, daHusaini baban Abdullahi, shi kuma Mahadi daga cikin ‘ya’yan Husainibaban Abdullahi ya fito, to tunda alkunyar Husaini itace babanAbdullahi, sai Manzon Allah (r.a) ya maye sunan mahaifin Mahadin dalazafin alkunyar kakanshii, don a samu dacewa a sunan mahaifinshida na Manzon Allah (s.a.w)!!74. wannan abin dariya har ina.

83- Tufka-da-warwarar da ke cikin rayuwar Mahadin Shi’a:

- Wacece mahaifiyarsa:

Shin wata kuyanga ce mai suna Narjas? Ko kuyanga ce mai sunaSuqail? Ko kuyanga ce mai suna Mulaikah? Ko kuyanga ce maisuna Khamat? Ko kuyanga ce mai suna Hakima? Ko kuyanga cemai suna Raihana? Ko Sosan? Ko ‘ya ce mai suna Maryam?

- Yaushe aka haife shi?

73 Abu Dawud (1/106) Sahihul Jami (5180)74 Kashful Gumma (3/228)

57

Shin an haife shi ne bayan rasuwar mahaifinshi da watanni takwas?Ko kuwa an haife shi ne kafin rasuwar mahaifinshi a shekara ta252? Ko 255? Ko 256? Ko 257? Ko 258? Ko 8 ga watan Zhul Iqda,ko 8 ga Sha’aban, ko 15 ga sha’aban? Ko 15 ga Ramadan?

- Ta ya mahaifiyarsa ta dau cikinsa?

Shin a cikinta ta dauke shi kamar sauran mata? Ko a kugunta tadauke shi sabanin sauran mata?

- Ta ya mahaifiyarshi ta haife shi?

Shin ta gabanta ta haife shi kamar sauran mata, ko kuwa tacinyarta ne?

- Ya tashinsa fa?

An ruwaito daga Abul Hasan yace: mu limamai a rana daya mu kesamun karfin jikin da sai waninmu ya yi sati ya ke samu!

Daga Abul Hasan yace: idan wata ya zagayo wa yaronmu ya kanzama kamar wanda ya shekara!

Daga Abul Hasan yace: Mu limamai danmu kan tashi a rana dayairin tashin da ‘ya’yan wasunmu ke yi a shekara guda!75

- A ina ya ke zaune?

Wasu su ka ce a “Taibah”, wasu su ka ce a tsaunin “Radwah” da keRauha’u, wasu su ka ce a Makkah daidai “Zi-Tuwa”, wasu su ka cea “Samirra”76

- Zai dawo yana saurayi ne ko yana dattijo?

An ruwaito daga Al-Mufaddal yace: na tambayi As-Sadik nace yasayyidi shin (Mahadi) zai dawo saurayi ne ko tsoho? Sai yace :subhanallah! Wa ke da ilimin hakan? Zai dawo ne ta yadda ya ga

75 Al-Ghaibah na Tusi (1/159-160)76 Bihrul Anwaar (102)

58

dama cikin kamannin da ya so77.

A wata ruwayar yace “zai dawo ne yana saurayi dan shekara 32”78.

A wata ruwayar yace: zai dawo yana dan shekaru 51”79.

A wata ruwayar zai dawo yana saurayi dan 30”80

- Shekaru nawa zai yi akan mulki?

Muhammad Al-Sadr yace: maganganu sun yawaita masu cin karoda juna akan wannan, har hakan ya jefa da dama daga cikinmarubuta da mawallafa cikin dimuwa”81

A wani kaulin aka ce : “jagorancin da Mahadinmu zai yi ya kaishekaru 19”, a wata ruwayar shekaru 7, ta yadda Allah zai tsawaitamasa rana da yini, har shekara guda ta zamto kamar shekarugoma, ta yadda shekaru bakwai din da zai yi za ta yi daidai dashekaru 70 dinku”82.

Wata ruwayar kuma tace “ zai zauna shekaru 309 kamar yaddamutanen “Ahlul Khahfi” su ka zauna a cikin kogonsu.

- Shekaru nawa zai yi a boye?

Sun ruwaito daga Aliyu (r.a) yana cewa: “Mahadi zai boye kuma zaishiga dimuwa, ta yadda wasu za su ‘bata ta dalilinshi, wasu kumasu shiriya. Lokacin da aka tambaye shi dimuwar kwana nawa zai yi?Sai yace : kwana shida, ko watanni shida, ko shekaru shida”83.

Daga Abu Abdillahi yace: zangon da ke tsakanin fitar mahadi dakisan Muhammad Nafsul Zakiyya kwanaki 15 ne kadai! Ma’ana

77 Biharul Anwaar (53/7)78 Tarikhu Ma Ba’adal Zuhuur (360)79 Tarikhu Ma Ba’adal Zuhuur (361)80 Kitabul Ghaiba (420)81 Tarikhu Ma Ba’adal Zuhuur (433)82 Tarikhu Ma Ba’adal Zuhuur (436)83 Al-khafi (1/338)

59

shekara ta 140 kenan bayan hijira zai fita! Muhammad Al-Sadryace: wannan ingantaccen labari ne, wanda tarihi zai iya tabbatargasgata tsarin da na ke tafiya a kanshi a cikin wannan littafi nawako kishiyar hakan, domin Al-Mufid ya ruwaito hakan daga Sa’alabadan Maimun daga Shu’aibu Al-Haddad daga Saleh dan MuyattamAl-Jammaal, kuma dukkaninsu aminai ne masana.84

To me ya hana shi fitowa kamar yadda wadancan ruwayoyin su kalamunce, alhali ga wata ruwayar ma ta zo cewa Abu Abdillahi yace :“ya Thabitu! Lallai ne Allah ya tsaida lokacin wannan abu dashekara saba’in, amma lokacin da aka kashe Hussaini sai fushinAllah ya karu ya kaishi zuwa shekaru 140! Yayin da mu ka fadamuku haka sai ku ka fallasa abin ku ka yada shi, daga nan sai Allahya dage lokacin fitarshi”85

Sai wata ruwayar ta zo kuma tana karyata dukkanin abinda AbuAbdillahi ya fada a ruwayoyin baya, inda aka ruwaito daga wajenshiyana cewa: “masu sanyawa (Mahdi) lokaci sun yi kuskure! MuAhlul Baiti ba ma sanya lokaci”86.

A wata ruwayar yace: “ba ma kayyade lokacin abinda ya gabata,haka nan da abinda zai zo”87. Wannan kwamacala da yawa ta ke!

84- Shi’a sun ruwaito daga Aliyu (r.a) cewa lokacin da ya fito gabandalibansa a fusace yana nishi sama-sama, ya fada musu cewa: “ya zaku yi idan zamani ya zo muku da za a yi watsi da haddi a cikinshi, afifita dukiya a kan komi, a riki makiya Allah a matsayin masoya, a rikimasoyan Allah a matsayin makiya? Sai su ka ce: ya Amirul mumininaya za mu yi idan mu ka tsinci kanmu a wannan lokacin? Yace: kuzamto kamar sahabban Isa (a.s), an yanka su da zarto, an gicciye su

84 Tarikhu Ma Ba’adal Zuhuur (185)85 Usulul Khafi (1/368)86 Usulul Khafi (1/368)87 Usulul Khafi (11/368)

60

akan itace, amma su ka jure, ku sani cewa mutuwa akan da’arUbangiji ya fi mutuwa akan sabawa Ubangiji”88

To a nan ina batun takiyyar da ‘yan Shi’a ke cewa a yi idan wuya ta kaiwuya?

85- Menene ya tilasta Abubakar (r.a) kan ya yi hijira tare da ManzonAllah (s.a.w)?

Idan munafiki ne kamar yadda yan Shi’a ke riyawa to da wani dalili nezai guji kafirai yan uwansa na Makkah alhali ba tilasta shi a ka yi ba,kuma dai su ne ke da karfi a Makkah? Idan saboda neman dukiya neya ke nuna munafincin to miye abin sa rai na dukiya a tattare daManzon Allah (s.a.w) a wancan lokacin da har zai sa ido akai tundadai Manzon Allah (s.a.w) bai mallaki komi ba?

86- Hakika Allah ta’ala ya yabi sahabbai a wajaje da dama a cikinAlkur’ani mai girma kamar fadinsa:

مه نيذلا و ةا ـ كزلا نوتؤيو نوقتي نيذلل اهبتكأسف ءيش لك تعسو يتمحرو ﴿يذلا يم األ يبنلا لوسرلا نوعبتي نيذلا * نونمؤي انتايآب

مهرمأي ليجن واإل ةاروتلا يف مهدنع ابوتكم هنودجيعضيو ثئآبخلا مهيل ع مرحيو تابيطلا مهل لحيو ركنملا نع مهاهنيو فورعملا بهورزعو هب اونمآ نيذلا ف مهيلع تناك يتلا ل ال غ واأل مهرصإ مهنع﴾ نوحلفملا مه كئ ـ لوأ هعم لزنأ يذلا رونلا اوعبتاو هورصنو

"kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa´an nan zã Ni rubũta ta gawaɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke,game da ãyõyinMu mũminai ne." "Waɗanda suke sunã bin Manzo, Annabi,Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.yanã umurnin su da alheri kuma yana hana su daga barin abin da bã a so;

88 Nahjus Sa’ada (2/639)

61

kuma yanã halatta musu abũbuwa mãsu daɗi, kuma yana haramtarwarmũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da

ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, waɗanda suka yi ĩmãnida shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka taimake shi, kuma suka bi haske

wanda aka saukar tãre da shi, waɗannan ne mãsu cin nasara."( al-Araf: 156-157)

Da fadinsa:

مهنم اونسحأ نيذلل حرقلا مهباصأ ام دعب نم لوسرلا و هلل اوباجتسا نيذلا ﴿ميظع رجأ اوقتاو .

. اولا قو اناميإ مهدازف مهوشخاف مكل اوعمج دق سانلا نإ سانلا مهل لا ق نيذلا﴾ ليكولا معنو هللا انبسح

Waɗanda suka karɓa kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki yasãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata yi dagagare su, kuma suka yi taƙawa. Waɗanda mutãne suka ce musu: "Lalle ne,

mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai(wannan magana) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: "Mai isarmu Allah ne

kuma mãdalla da wakili Shĩ."(al-imran: 172-173) "

Da fadarsa:

يف ام تقفنأ ول مهبولق نيب فلأو {62} نينمؤملا بو هرصنب كديأ يذلا وه ﴿

زيزع هنإ مهنيب فلأ هللا نك ـ لو مهبولق نيب تفلأ ام اعيمج ضر األ

﴾ـ ميكح

Shĩ ne wanda Ya ƙarfafa ka da taimakonSa, kuma da mũminai."Kuma Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu. Dã kã ciyar da abin da yakecikin ƙasa, gabã ɗaya, dã ba ka sanya sõyayya a tsakãnin zukãtansu ba,kuma amma Allah Yã sanya sõyayya a tsakãninsu. Lalle Shi ne Mabuwãyi,

62

Mai hikima."(Al-Anfal: 62-63)

Da fadarsa:

﴾ نينمؤملا نم كعبتا نمو هللا كبسح يبنلا اهيأ اي ﴿

Ya kai Annabi! Ma´ishinka Allah ne, kai da wanda ya biye maka dagamũminai.

..(Al-anfal: 64)

Da fadarsa:

نونمؤتو ركنملا نع نوهنتو فورعملا ب نورمأت سانلل تجرخأ ةمأ ريخ متنك ﴿

﴾ هللا ب

"Kun kasance mafi alherin al´umma wadda aka fitar ga mutãne kunaumurni da alheri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã

ĩmãni da Allah.(Al-Imran: 110)"

Da sauran ayoyi sanannu.

Bugu-da-kari Sanannen abu ne cewa yan Shi’a na tabbatar da imaninsahabbai a lokacin rayuwar Manzon Allah (s.a.w), sai dai su na riyacewa sun yi ridda bayan rasuwarsa! Wannan abin mamaki har ina!Wane irin hadin baki ne haka mai kama da majigi ace gaba dayansusun yi ridda a lokaci guda?! Wane dalili ne ya kawo haka?

Saidai fa idan kuna ganin cewa sun yi ridda ne dalilin yin mubaya’a gaAbubakar (r.a),! to a nan sai mu ce muku menene ya kai su gahaduwa gabadayansu akan mubaya’a ga Abubakar din? Shin sabodayana da karfi ne ta yadda su na tsoron shi? Lallai ba shi da wannan

63

karfin, domin ko a cikin Quraishawa shi yana bangaren Banu Tamimne, ita kuwa kabila ce mara rinjaye da yawa, masu yawa da rinjaye dakarfi a cikin Quraishawa su ne Banu Hashim da Banu Abdid Dar daBanu Makhzhoum.

To idan har ba zai iya tilasta Shabban Manzon Allah (s.a.w) akanmasa mubaya’a ba saboda ba shi da karfin yin hakan, to da wanedalili ne sahabbai za su rasayar da imaninsu da jihadinsu dawahalhalun da su ka shiga akan biyan bukatar Abubakar (r.a) kadai?Hankali zai dau wannan?

87- Idan dai sahabbai sun yi ridda bayan mutuwar Manzon Allah(s.a.w) da gaske, to da wane dalili ne su ka yaki wadanda su ka yiridda daga cikin mabiyan Musalimah da Dhulaihah dan Khuwailid daAswad Al-Anasi da mabiyan Sajah da dai sauransu don kawai sudawo da su cikin musulunci? Don menene ba su taimake su ba koalal akalla su kau da kai daga barinsu matukar dai yan uwansu ne acikin ridda kamar yadda ku ke riyawa?

88- Rayuwa da addini da tarihi dukkaninsu sun nuna cewadukkanin annabi za ka samu cewa mafifitan al’ummarsa su nesahabbansa, domin kuwa da za ka tambayi ma’abota kowane addinigameda mafiya falala daga cikin mabiya addinin nasu za su ba kaamsa da cewa su ne sahabban annabinsu.

Da za a tambayi ma’abuta Attaura kan mafifita daga cikin addininsuza su ce su ne sahabban Annabi Musa (a.s). hakanan da za katambayi ma’abuta Linjila kan mafifita daga cikin addininsu za su cesu ne sahabban Annabi Isa (a.s). Hakanan dukkanin mabiya sauranannabawa. Dalili kuwa shine su sahabban kowane annabi su nemafiya kusa da wahayin da aka saukar a lokacinsa, su ne su ka fisauran ak’ummar tasu sanin rayuwar annabin da dabi’unshi dahukunce-hukuncen da aka saukar mishi. Don haka imaninsu ya dara

64

na sauran.

To ina kuma ga Annabi Muhammd (s.a.w) da aka turo shi ga mafialkhairin al’umma da mafificin sako da littafi da Sharia mai saukikuma aka rufe annabta da shi? Ta ya sahabban wannan annabi za suzama kafirai? Idan sun kafirta ta wace hanya hasken musuluncin daAllah ya yi alkawari zai cika zai samu? Tunda dai ta hanyarsu nekawai za mu iya sanin rayuwar Manzonmu da abinda ya ke dauke dashi? Wace irin kima ce da Manzon Allah (s.a.w) a wajenku bayan kunkori dukkanin abokanansa wadanda ta hanyarsu ne kadai za mu sanhakikaninshi? Ashe dukkanin kokarin da su ka yi na yada musuluncita hanyar kira da kafa hujja a magance, da amfani da takobi idan takama, har addinin ya ratsa sassan duniyar nan, ashe duk suna cikinridda su ka yi wannan kokarin?

89- Tarihi ya tabbatar mana da cewa Manzon Allah (s.a.w) bai tabaamfani da takiyya ba duk kuwa da irin matsanancin halin da ya tsincikanshi a ciki a lokuta da dama, sai gashi yan Shi’a na riya cewatakiyya ita ce taran na goman addini! Kuma wai har limamansu masun yi amfani da ita a lokuta da dama, to shin me ya hana su koyi dakakansu (s.a.w) wajen juriya da barinta?

90- Tarihi ya nuna mana cewa Aliyu (r.a) bai taba kafirtaabokanan husumarsa ba, hatta Khawarijawa da su ka yake shi su kamusguna masa tare da kafirta shi, bai taba kafirta su ba, to me yahana yan Shi’a koyi da shi a nan? Me ya sa su ke kafirta manyansahabban Annabi (s.a.w) da matayensa uwayen mumunai?

91- Ijma’i a wurin Shi’a bai zama hujja a karan-kanshi, har sai yara’bu da ra’ayin Liman Ma’asumi!89 To wannan wane irin rudani ne

89 Tahzibul wusul na Mahalli (70)

65

haka! Ai babu bukatar shi ma Kenan.

92- Sai gashi ‘yan Shi’a na kafirta Zaidiyya, bayan kuwa Zaidiyya suna kaunar Ahlul Baiti! Da wannan mu ka gane cewa abin lura a wurinyan Shi’a ba wai nuna kauna ga Ahlul Baiti ba ne, a’a nuna kiyayya nega sahabbai da kafirta su ba kamar yadda su ke riyawa ba.

93- Yan Shi’a su na riya cewa shi ne ya cancanci Khilafa bayanManzon Allah (s.a.w) saboda hadisin:

“ ىسوم نم نوراه ةلزنمب ينم تنأ »

Ma’ana “ kai a wuri na tamkar Haruna ne a wurin Musa (a.s).90

A nan wajen da mu ka duba sai mu ka ga ai Haruna bai gaji Musa (a.s)ba. Yusha’u dan Nun ne ya maye shi!

94- Yan Shi’a sun dora mabiyansu akan aikata sabo da munananayyuka saboda wai “son Ali lada ne, yana kankare dukkanin wani laifi”!saidai wannan wani ikrari ne kawai da Alkur’ani ya rigaya ya yi fatalida shi, ta yadda ya ke tsawatarwa kan aikata dukkanin wani laifi kowane iri ne, da kowane dalili, kamar yadda Allah yace :

هل دجي وال هب زجي اءوس لمعي نم باتكلا لهأ ينامأ وال مكينامأب سيل ﴿﴾ اريصن وال ايلو هللا نود نم

(Al´amari) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma ba gũrace- gũracen

90 Bukhari da Muslim su ka fitar

66

Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa dashi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi

mataimaki ba.”(An-Nisa: 123)

95- Yan Shi’a suna kudurce akidar “Bada’u”, wato Allah bai san abuba kafin faruwarsa, har sai ya faru tukun ya ke sani! Sai gashi dakansu su na jingina ilimin gaibu wajen limamansu, to shin limamaisun fi Allah Kenan ta yadda su su kan san abu gabanin faruwarshiamma shi ba ya iya sani? Duk yadda ‘yan Shi’a su ka so tawilinwannan mumunar akida ta su ba zai yiwu ba, domin maganganun dake cikin takardunsu akanta sun yi yawan da ba za su tunkudu ba koayi tawilinsu.

96- Tarihi ya labarta mana yadda shi’a su ka wayi gari a matsayinmasu taimako da yin kafada-kafada da Yahudu da Nasara daMushirikai a wadansu manyan abubuwa da su ka faru a tarihi. Dagacikin akwai faduwar Bagadaza a hannun Magol, da faduwar Kudus ahannun Nasara, to shin ya kamata a ce musulmin kirki ya yi watsi daumurnin ubangijinsa na watsi da rikar Yahudu da Nasara a matsayinabokanan adawa da hada baki dasu wajen yin illa ga musulmai? Shinsayyidina Ali ko jikokinsa sun taba aikata hakan?

97- Muna ganin da yawa daga cikin yan Shi’a na sukar Alhassan(r.a) da shi da mabiyansa, duk da kasantuwarsa daya daga cikinlimamansu na Ahlul Baiti91. To me ya sa?

98- Wanda ya yi nazari game da Shi’a zai fahimci irin yawansabanin da ke tsakanin kungiyoyinsu daban-daban, da yawan kafirta

91 A’ayanush Shi’a (1/26)

67

junansu da ya zama musu ruwan dare, domin ko da a yau za mu gahaka. Misali na kusa-kusa shine yadda malaminsu mai suna AhmadAl-Ahsa’i ya kafa tashi kungiyar wadda aka fi sani da “Shaikhiyya”,bayan haka kuma dalibinsa mai suna “Khazim Al-Rashti” ya kafa tasakungiyar ya sanya mata suna “Al-Kashfiyya”, sa’annan wani dalibinshimai suna Muhammad Karim Khan ya ja tashi tawagar ya rada matasuna “Al-Kharimkhaniyya”,

Haka wata dalibarshi mace mai suna Qurratul Ain ta kafa tatakungiyar mai suna “Al-Qartiyya”, Mirza Ali Al-Shirazi ya kafa tashikungiyar da sunan “Al-Babiyya”, sai Mirza Hussain shi ma ya kirkiri “Al-Baha’iyya”!

Ku duba yadda dukkanin kungiyoyin nan su ka tofo a zamani daya amakusantan wurare. Allah ya yi gaskiya da ya ke cewa:

﴾ هليبس نع مكب قرفتف لبسلا اوعبتت وال ﴿

kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa”

"(al-An’am: 153-163)

"

99- Mun ga yadda Aliyu (r.a) ya bada kariya ga Usman (r.a) yayin dayan tawaye su ka zagaye gidanshi, ya yi kokarin tarwatsa su, har yatura yayansa Hassan da Hussaini, da dan da’uwansa Abdullahi danJa’afar, duk saboda bashi kariya, ba don shi Usman da kanshi yanemi mutane da su aje makamansu su koma gidajensu ba. Wannanna fito da kagen yan Shi’a fili na cewa akwai kiyayya tsakaninsu.

100- Sunnah da Shi’a sun hadu akan cewa Umar (r.a) ya kasanceyana shawartar Aliyu (r.a) a cikin al’amura da dama92! Da aceazzalumi ne kamar yadda Shi’a ke riyawa da bai shawarci kowa ba,

92 Nahjul Balaga (325)

68

domin azzalumi ba ya neman gaskiya balle ya nemi shawara.

101- Tarihi ya tabbatar da cewa Salmanul Farisi ya yi gwamna a “Al-Mada’in”, haka Ammar bin Yasir shi ma ya rike “Kufa” duk a zamaninUmar (r.a), wadannan biyun kuma su ne yan Shi’a ke riya cewa sunacikin tawagar Aliyu ne, to da ace Umar (r.a) a matsayin kafiri ya ke awajensu zasu amshi wannan nadin da ya musu? Ta ya za su farahaka bayan kuwa sun san da fadin Allah ta’ala:

﴾ـ رانلا مكسمتف اوملظ نيذلا ىلإ اونكرت وال ﴿ـ

Kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zãlunci har wuta ta shãfeku.”(Hud:113)

102- Yan Shi’a na riya cewa limamansu ma’asumai ne da ba sa laifi,haka nan Mahadinsu yana nan da rai, wadansu daga cikinmalamansu na ganawa da shi, aka ce su talatin ne, to idan hakabatun ya ke da wane dalili ne ake samun sabani a mazhabarsu, irinsabanin da babu shi a wata kungiya? Har ta kai ga ko wane bijiminmalami daga cikin malamansu yana da kebantacciyar mazhaba, to yaaka yi haka ta faru bayan kuma su na ganawa da matsotsa addininsuwato Mahadi?

Wani abin ban dariyar kuma shine sai ga malaminsu wato Majlisi yaruwaito cewa ba a ganin Mahadi, duk wanda yace ya ganshi to ya yikarya, a dayan bangaren kuma sai ga da dama daga cikin malamansuna riya cewa sun ganshi. Wannan wane irin wasa da hankali ne haka.

103- Abinda mu ke cewa Shi’a shine tunda dai kun riya cewa ba zaiyiwu wani zamani daga cikin zamunna ya kubuta daga Mahadi ba, toidan takiyya itace tara daga cikin goman addininku kamar yadda kuke fada, to don menene ba zai fito ya yi takiyya ba shi mahadin?

69

104- Yan Shi’a na riya cewa sanin limamai sharadi ne na Imani, tome za su fada game da wanda ya mutu kafin cikar limaman sha biyu?Wasu limaman naku ma sanda su ke da rai ba a san ko wanene zaimaye su ba. To ya za a ce wannan sharadin Imani ne?

105- Mai littafin “Nahjul Balaga” ya ruwaito cewa lokacin da Ansarsu ka yi ikirarin cewa su ne su ka fi cancanta da shugabanci, dalabarin ya kaiwa Aliyu (r.a) sai yace : shin ba ku ba su labari ba cewaManzon Allah (s.a.w) yayi wasiyya da a kyautatawa na kwaransu, akauda kai daga wanda ya munana daga cikinsu? Sai su ka ce me zamu fahimta a cikin wannan maganar? Sai yace: ma’ana da ace mulkina hannunsu ai ba za a yi wasici da a kyautata musu ba”93.

A nan sai mu ce wa yan Shi’a irin wannan wasicin da aka yi game daAnsarawa irin shi dai aka yi game da Ahlul Baiti a hadisin :

« يتيب لهأ يف هللا مكركذأ »

Ma’ana: “ina hada ku da Allah game da kula da iyalaina”,

Kenan da ace imama ta su ce su kadai da ba a yi wasici game da suba.

106- Da za a fadi maka cewa ga wani jagora mumini salihi bawanAllah amma kuma yana jibintar muminai da munafukai a lokaci guda,kuma yana gane munafukan idan sun yi Magana, sannan ace duk dahaka wannan jagoran bai riki na kirki ba sai ya zabo munafukai yacigaba da ciccida su gaba, da girmama su ta yadda ko me za a yi suya ke tunkudawa gaba, har ma ya aura daga gare su su ka aura masa‘ya’ya, shin irin wannan mutum ze za a ce game da yanayinshi? Dukabinda za ka iya fada ga mai wannan siffar shine irin kudurin Yan

93 Nahjul Balaga (97)

70

Shi’a gameda Manzon Allah (s.a.w)!

107- Malamin Shi’a mai suna “Alhur Al-Amili” ya ruwaito daga AbuJafar game da tafsirin ayar :

﴾ـ رفاوكلا مصعب اوكسمت الو ﴿

“Kuma kada ku riƙe auren mãtã kãfirai”(Al-mumtahana:10)

Yana cewa: duk wanda ke rike da mace kafira yana musulmi to lallaine ya tallata mata musulunci, idan ta karba sai ta cigaba da zama amatsayin matarshi, idan kuma ta kiya to tilas ya barranta daga gare ta,domin Allah ya hana shi cigaba da rike igiyar aurenta a wannanyanayin”94.

Da ace uwar muminai Aisha ba mumina ba ce kamar yadda Shi’a keriyawa ashe Manzon Allah (s.a.w) zai cigaba da rike ta karkashinsa?Saidai fa idan Manzon Allah (s.a.w) ne bai san da riddarta komunafincinta ba yayin da yan Shi’a su ka sani!

108- Kungiyar “Al-Khattabiyya” daga cikin kungiyoyin Shi’a ta tafiakan cewa Imam mai biyewa Jafar As-Sadik shine Ismail dansa, saimalaman Shi’a su ka maida masa martini da cewa shi Isma’il din maya rasu kafin rasuwar mahaifinsu Abu Jafar, shi kuwa mamaci ba yajagorantar mai rai…” 95.

A nan wajen sai mu fadawa Shi’a cewa ku ne fa ku ke kafa hujja dahadisin da Annabi ya fadawa Aliyu cewa “Kai a wajena kamar Haruna

94 Wasa’ilush Shi’a (20/542)95 Kamalud Deen Wa Tamamul Minna (105)

71

ne wajen Musa”, kuna kafa hujja da wannan hadisin, sai gashi shi maHaruna ya rasu kafin Musa din, a nan wajen amsarku itace amsar daku ka baiwa Khattabiyya cif-cif, baki shi ke yanka wuya!

109- Yan Shi’a na kokarin tabbatar da limancin limamansu da hadisin :

« شيرق نم مهلك ةفيلخ رشع ينثا ىلإ ازيزع رم األ لا زي «ال

Ma’ana “Al’amarin addinin nan ba zai gushe yana mai karfi ba har saian samu khalifofi goma sha biyu, dukkaninsu daga Quraishawa”96.

A cikin dukkanin ruwayoyin da hadisin ya zo da su za mu ga yanaMagana ne akan “khalifofi” ko ‘shuwagabanni” masu shuwagabantarmutane, kuma sanannen abu ne cewa babu wanda ya rikeshugabanci ko khilafa daga cikin Ahlul Baiti sai Aliyu da dansaHassan (r.a), Kenan hadisin ya yi gabas yan Shi’a sun yi yamma,domin ruwayoyin ma ko sunan mutum daya ba su ambata ba.

110- Yan Shi’a suna riya cewa sahabbai sun yi ridda sai yan kadan,to a nan wajen sai a ce musu dalilai biyu ke sanya mutum ridda, kodaiwata shubuha da ta makale masa, ko kuma wata sha’awar abinduniya da ta gallabe shi.

Idan batun shubuha ne to sanannen abu ne cewa shubuhohi a farkonmusulunci sun fi karfi, Kenan idan wadanda imaninsu yayi karfikwarai lokacin raunin muslmai ina ga kuma lokacin karfin musuluncida yaduwarshi?

Idan kuma sha’awar abin duniya ce ta sanya su to ya za ayi acewanda ya bar gidanshi wato Madina ya bar dukkanin dukiyar da yamallaka ba tare da wani ya tilasta shi ba sai don son Allah da

96 Bukhari da Muslim su ka ruwaito

72

Manzonsa, ya za ayi ace irin wannan mutumin kuma yana sha’awarwani abu bayan haka? Da sha’awa ce dalili da sun yi zamansu aMakkah Kenan tun asali akan kafircinsu, tunda acan ne gatansu daholewarsu su ke. Ko da ya ke yan Shi’a na cewa dalilin riddarsu shinebatun Imama da su ka kwacewa Aliyu, wato mafi girman rukuninmusulunci a wajen Shi’a. duk dai wannan kokari ne na kauce-kauceda sabewa.

111- Sanannen abu ne yadda yan Shi’a ke kudurce rashin adalcinsahabbai, saidai kuma mun ci karo da wasu ruwayoyi da ke nuni gaadalcin sahabban a cikin littafansu. Daga ciki akwai ruwayar da su karuwaito zuwa ga Manzon Allah (s.a.w) yana cewa :

«.. اهعمسي مل نم ىلإ اهغلب مث ، اهاعوف يتلا قم عمس ادبع هللا رضن »

Ma’ana: Allah haskaka fuskar bawan da ya ji Magana ta ya kiyaye taya isar da ita ga wanda ba ta iske shi ba…”97

Idan sahabbai ba adalai ba ne ta ya Manzon Allah (s.a.w) zai amintada su wajen isar da sakonsa?

112- An tambayi wani daga cikin Malaman Shi’a kamar haka: AsheManzon Allah bai kwadaitar da mu wajen zaben nagartacciyar maceba da surukuta da mutan kirki? Sai yace: eh ya kwadaitar kan hakan.Sai aka ce masa: to kana ganin zaka aminta ka yi siriki da dan zina?Yace: Allah fisshe ni! Aka ce masa: to ai ku kuna riya cewa wai Umar(r.a) da ne na zina da wata mata mai suna (Sahaak98) ta Haifa! Harma malaminku Ni’imatullahil Jaza’iri yana karyar cewa wai Umar ba

97 Al-Khisaal (149-150)98 Al-Kashkul na Al-Bahrani (3/212)

73

ya samun natsuwa sai ya taki mata99! Allah fisshe mu! , haka ku nariya cewa ‘diyarsa Hafsah munafika ce kamar babanta, ko ma kafira!Shin ka na ganin Manzon Allah zai yi surukuta da dan zina? Ko ka naganin zai zabi mutuniyar banza munafika a matsayin mata gareshi?Wallahi ba komai ku ke yi ba face kirkire-kirkire ga Manzon Allah dasahabbansa da lankaya musu abinda ku ba za ku lankaya ba gakawunanku.

113- Idan dukkanin sahabban nan yan Shi’a na cewa sun yi ridda,duk kuwa da yawansu da tasirinsu, to ta ya aka yi musulunci ya yadua lokacinsu ya zama hantsi leka gidan kowa? Ta ya akayi Parisa daRum suka fadi warwas aka bude Baitul Maqdis?

114- Malamin Shi’a mai suna Muhammad Khashif Al-Ghita yanafadi game da sayyidina Ali (r.a): cewa: “a lokacin da ya ga cewakhalifofin da su ka gabace shi guda biyu wato Abubakar da Umar sunkokarta kwarai wajen yada Kalmar tauhidi, da tura tawagar yaki zuwako ina, kuma ya ga ba su so kansu ba, ba su yi mulkin kama-karya ba,sai ya mika wuya ya yi musu mubaya’a”100

To matukar dai haka batun yake kamar yadda wannan malamin naShi’a ya fadi, don menene kuma su ke zarginsu da kafirci damunafunci? Menene na tufka-da-warwara kuma!

115- Yan Shi’a na kafa hujja akan riddar shabbai da hadisin daManzon Allah (s.a.w) ke cewa: “za a bijiro mini da wadansu mutane.Na sansu, sun sanni, sai a nesanta su da korama ta, sai in ce gaShabbai na can! Ga Sahabbai na can! Sai a ce: ina! Ai ba ka da labarin

99 Al-Anwarun Nu’umaniyya (1/63)100 Aslush Shi’a wa Usuluha (59)

74

ababen da su ka kirkiro bayanka.”101

A nan wajen sai mu ce ma yan Shi’a wannan hadisin gamammiyarMagana yayi, bai ware wasu ba a cikinsu, bai tsame irinsu Ammardan Yasir ba ko Al-Miqdad dan Al-Aswad ko Abu Zar ko SalmanulFarisi ba daga cikin mutanen da yan Shi’ake ganin su ba su yi ridda badaga cikin sahabbai, kai bai ma cire shi kanshi Aliyu dan Abi Talib ba!To da wane dalili ne za ku kebe wasu daga ciki ku shigar da wasu?Idan da abin haka yake ai da dukkanin wani mai dauke da kyashi gawani daga cikin sahabbai sai ya dora wannan hadisin a kansa, saiabin ya zama son zuciya Kenan.

116- Malik dan Ashtar daya daga cikin manyan almajiran Aliyu (r.a)wanda shi’a na girmama shi matuka yana cewa: “ya ku mutane!Hakika Allah ya aiko muku manzonsa yana mai bushara da gargadi,ya aiko masa da littafi, a cikinshi akwai halal da haram da farillai dasunnoni, sannan ya karbi ranshi a lokacin da ya riga ya saukenauyinshi, sannan aka shugabantar da Abubakar kan mutane, yayirayuwa irin tasa da aiki da sunnarsa, sannan Abubakar ya dora Umar,sai yayi aiki da irin waccan sunnar tasa”102.

A nan wajen za mu ga yadda Malik bin Al-Ashtar yake nuna yabonsada jinjinarsa a fili ga Abubakar da Umar da salon mulkinsu mai bankaye, amma sai gashi yan Shi’a na rufe ido a kan irin wannan dagangan, ba sa kawo shi kwata-kwata a wuraren taruwarsu inda babuabinda su ke yi sai jefa la’ana ga wadannan bayin Allah guda biyu,Allah shirye su. To da wane dalili?

117- Ibnu Hazmin yana cewa ga yan Shi’a: “me za ku fadi game daMubaya’a da Ali (r.a) yayi ga Abubakar (r.a) bayan watanni shida, ? kodai ya zamto jinkirin ne daidai, to mubaya’ar da yayi bayan jinkirin zai

101 Bukhari102 Malik bin Al-Ashatar, khutabuhu wa ara’uhu (89)

75

zamto kuskure ne Kenan, ko kuma rashin mubaya’ar itace daidai, tomubaya’ar da yayi ta zamto kure ce Kenan”103 sai ku zabi daya.

118- Idan aka cewa Shi’a: me ya sanya Aliyu (r.a) shiru game dabatun khilafa bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) bayan kuma kunfadi cewa akwai nassi akai? Idan an tambaye su su kan ce ai akwaiwasiyya ne da Manzon Allah (s.a.w) ya masa na cewa kada ya zaretakobinsa ko ya tada fitina a cikin wannan al’umma! Sai mu ce musu:idan haka ne da wane dalili ya zare takobi a rikicin “Jamal” da “Siffin”alhali fada ne tsakanin musulmai wanda dubban musulmai su ka rasarayukansu a cikinsa?

119- Yan Shi’a ba sa ambaton wani bambancin a zo a gani tsakaninlimamansu da Annabawa! Har malaminsu Al-Majlisi ya ruwaito cewalimamansu sun ce: “ba mu san wani dalilin da ya sa aka ki wasaftalimamanmu da annabci ba, sai don yin kara da nuna girmamawa gacikamakin annabawa kadai, mu a hankalce ba mu san wani bambancitsakanin Annabi da Liman ba”104.

Abin tambaya a nan shine shin menene muhimmancin akidar cikeannabta Kenan matukar dai dukkanin siffofi da mu’ujizozin daannabawa ke da su ba su kebanta da su ba ta yadda za su cigaba dakasantuwa tare da wadanda ba su ba har bayan shudewarsu , ma’analimamai sha biyu duk sun siffanta da su? To menene amfaninannabtar?

120- Yan Shi’a na ganin samun mukamin imamanci ya zama wajibine saboda dalilin “Lutufi”, wato tausayin da Allah ke ma bayinsa, donhaka ya turo musu annabawa da limamai!, amma abin mamaki sai ga

103 Al-Fisal fil Milali wal Ahwa’I Wan Nihal (4/235)104 Biharul Anwar (26/28)

76

limaminsu na sha biyu ya buya tun yana karamin yaro! To wanetausayi da jinkai musulmi su ka samu daga wanda ya buya tun yanayaro?!

121- Yan Shi’a na riya cewa jagororinsu ma’asumai ne, saidaidukkanin bayanan da aka samo suna nuna sabanin haka. Misali:

a- Alhassan (r.a) ya kasance yana adawa da matakin da mahaifinshiya dauka na yakar masu neman a bi musu Kadin jinin Usman (r.a)da aka zubar! To a nan dole daya daga cikinsu ya zamto kandaidai daya kan kuskure, kuma gashi dukkanin su biyun limamaine da ba sa aikata lefi a wajen yan Shia.

b- Hussaini ya sabawa dan’uwanshi Alhassan game da matsayar daya dauka na lalubo hanyoyin sasantawa da Mu’awiya, kuma gashidukkanin su biyun limamai ne da ba sa aikata zunubi a wajen yanShia.

c- Wadansu takardu na Shi’a sun ruwaito Aliyu (r.a) na cewa: kada kuboye maganar gaskiya, kada ku yi rowar shawari masu kyau gareni , domin zan iya kuskure a ko da yaushe”105.

122- Yan Shi’a sun yi ca kan malaman Saudiyya kan fatawar da suka bada ta halascin neman taimakon kafiri idan ta kama a lokacinfadansu da Saddam Hussein, sai ga shehinsu mai suna IbnulMutahhir Al-Hilli ya ruwaito a cikin littafinshi mai suna “MuntahalTalab fi Tahkikil Mazhab” ya Ambato Ijma’in Shi’a in bandamalaminsu Al-Tusi akan halascin neman taimakon kafiran amana kanyakar yan tawaye”

123- Yana daga cikin ka’i’dojin Shi’a cewa Imama tana tabbata ne

105 Al-Khafi (8/256)

77

ga wanda ya yi ikrarinta daga cikin Ahlul Baiti, kuma ya bayyanakaramomin da su ka nuna gaskiyar lamarinshi, sai gashi su din ba suyarda da limancin Zaidu dan Aliyu ba, duk da ya yi ikrarib hakan! Tadayan bangaren kuma sai gashi sun tabbatar da ita ga dan karaminyaro da bai taba ikrarinta ba wato Mahadinsu da su ke jira.

124- Lokacin da fadin Allah ta’ala ya sauka:

﴾ـ اهلهأ ىلإ تانام األ اودؤت نأ مكرمأي هللا نإ ﴿

Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsusũ. “(An-Nisa: 58)

Sai Manzon Allah (s.a.w) ya kira Banu Shaiba ya basu mabudin ka’aba,yace da su: “ya ku Banu Talha! ku karbe su ku adana su a wajenku harzuwa ranar tashin kiyama, babu mai kwace su daga hannunku saiazzalumi”106.

Idan mun lura za mu ga cewa Manzon Allah (s.a.w) ya fadi haka neakan wani karamin al’amari wato makullan ka’aba. To ya akayi in daimaganar Shi’a haka take bai ambaci irin wannan ba game da khilafarAliyu (r.a) duk kuwa da kasantuwar muhimmancinta ya fi na mukullai?

125- Yan Shi’a sun kirkiri wani hadisi mai cewa : “Allah ya la’anciwanda bai bi rundunar Usama yaki ba”107, suna so ne su kushe Umar(r.a) ta hanyar wannan hadisin.

To a nan wurin sais u zabi daya:

a- Ko dai su ce Aliyu yana cikin wannan rundunar, to wannan na nuna

106 Majma’ul Zawa’id naTabarani (3/285)107 Al-Muhazzab na Ibnul Barraj (1/13)

78

yardarshi da jagorancin Abubakar Kenan tunda har ya shigakarkashin rundunar da ya aika.

b- Ko kuma su ce bay a ciki, to irin abinda su ka fadama Umar shi maya hau kanshi Kenan.

126- Yan Shi’a na riya cewa Aliyu (r.a) na adane da wani kwafi naAlkur’ani mai dauke da surori a tsare kamar yadda su ka sauka! A nansai mu ce musu mun san Aliyu (r.a) ya yi shugabanci, ya akayi bai fitoda wannan Alkur’ani ba ya dora musulmai a kai? Tun da daiAlkur’anan da ke hannunmu na da bambanci da shi?

127- Yan Shi’a su na riya kaunar Ahlul Baiti da iyalan Manzon Allah(s.a.w), sai dai akwai tufka da warwara a cikin wannan kauna tasu afili, domin kuwa sun musanta nasabar wadansu daga cikin iyalanManzon Allah (s.a.w) zuwa gareshi, kamar Rukayya da UmmuKhulthum, ‘ya’yan Manzon Allah (s.a.w), su ka nesanta Abbas amminManzon Allah (s.a.w) da dukkanin ‘ya’yansa, hakanan su ka ki Zubairudan Safiyya Innar Manzon Allah (s.a.w), kamar yadda ba sa damuwada adadi mai yawa na ‘ya’ya da jikokin Fatima (r.a.) kamar Zaidu danAli da danshi Yahya, da Ibrahim da Jafar dan Musa Al-Khazim, hakanan su kushe Jafar dan Aliyu, dan’uwa ga limaminsu Alhasanul Askari.Haka dai su ke kudurce cewa hakika Alhassan dan Alhassan“Almusanna” da danshi Abdullahi “Almahd” da danshi Muhammad“Nafsuz zakiyya” gabadayansu sun yi ridda! Irin wannan kudurin su keda shi game da Ibrahim dan Abdullahi, da Zakariyya dan MuhammadAlbaqir, da Muhammad dan Abdullahi dan Hussaini da Hassan danMuhammad dan Alkassim dan Hussaini da Yahya dan Umar da daisauransu.To a nan ina batun kaunar Ahlul Baiti ya kwana?

Akwai maganar da wani daga cikinsu yayi mai karfafa wannan tufkada warwara tasu inda ya ke cewa: “daukacin ‘ya’yan Alhassan danAliyu suna da munanan ayyuka da su ka yi, kuma ba za a ce takiyya

79

ba ce”108 ku duba wannan danyen aiki.

128- Yan Shi’a suna kafirta daukacin Ahlul Baiti a karni na farko! Yazo a cikin da yawa daga cikin takardunsu cewa: daukacin al’umma tayi ridda banda mutane uku: Salman da Abu Zar da Al-Miqdad, wasukuma sun kara adadin zuwa mutane bakwai, amma daga cikinsubabu daya daga cikin Ahlul Baiti.109 A nan sun danganta ridda gadukkanin al’umma Kenan, Allah sawwaka.

129- Mun gani cewa Alhassan (r.a) duk da yawan da mabiyansa keda shi amma ya hakura ya mikawa Muawiya (r.a) jagoranci, ammakuma shi Hussaini (r.a) duk da karancin mabiyanshi bai yi mubaya’aga Yazidu dan Mu’awiya ba, har ta kai ga ya yi fito-na-fito da shi.Kuma daman da shi Hassan da Hussainin ma’asumai ne a wurin yanShi’a wadanda ba sa laifi! To matukar dai abinda Alhassan yayi nasallamawa Mu’awiya ragamar mulki daidai ne to Fito da na fito din daHussaini yayi kuskure ne Kenan, hakanan idan daidai Hussaini yayi toAlhassn kuskure yayi Kenan, domin babu yadda za ayi fari da baki suzamto abu daya! Tabbatar da kuskuren daya kuma rushe Ismar shi ce,sai su zo su mana bayani.

Domin ai su kan kafirta da yawa daga cikin Ahlul Baiti sabodazarginsu da fadawa cikin kuskure ko aikata ba daiai ba, kamar kafirtaAbbas ammin Manzon Allah (s.a.w) da su ka yi, kuma su ka riya cewawannan ayar ta sauka ne game da shi:

ـ﴾ـ ال يبس لضأو ىمعأ ةرخ اآل يف وهف ىمعأ هذ هـ يف ناك نمو ﴿

Kuma wanda ya kasance makãho a cikin wannan sabõda haka shi a Lãhira

108 Tanqihul Makaal (3/142)109 Kitab Salim bin Qais (62)

80

makãho ne kuma mafi ɓata ga hanya.”(Al-Isra:72)110

Haka nan su ka yi wa danshi wato Dan Abbas masanin tafsiri dafatawa daga cikin sahabbai, shi ma sun yi kokarin kafirta shi dakankanta sha’aninshi,.

Ya zo a acikin “Rijalul Kasshi”111 cewa: “ya Allah ka la’anci ‘ya’yanwane guda biyu, ka makantar da idanunsu, kamar yadda ka makantarda zukatansu”112

Malaminsu mai suna Hasan Al-mustafawi ya dan yi sharhi akanwannan Magana inda ya ke cewa wadanda ake nufi a cikin zancen sune Abbas dan Abdulmutallib da dansa Abdullahi dan Abbas113.

Har ‘yayan Manzon Allah (s.a.w) ketar yan Shi’a ta shafe su in bandaFatima, domin sun yi magagin kore cewa Manzon Allah (s.a.w) yanada ‘yaya mata banda Fatima!

To ina kaunar Ahlul Baitin da su ke tutiya da ita take?

130- Aliyu (r.a) ya yi tarayya da sauran musulmai wurin yakar masuridda bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w), har ya samu kuyanga maa yakin daga cikin kuyangun kabilar (banu Hanifa), wadda ta Haifamasa dansa mai suna (Muhammad dan Hanafiyya), wannan yanatabbatar mana da cewa Aliyu (r.a) ba ya ganin bacin khalifancinAbubakar (r.a) Kenan, domin ginin da aka gina akan lalataccen tusheshima lalatacce ne.

131- Maganganu irin wadanda aka rawaito daga Jafar Al-Sadik nacin karo da juna a cikin mas’aloli da dama, domin kuwa ba za ka ga

110 Rijalul Kasshi (53)111 Rijalul Kasshi (1/247)112 Rijalul Kasshi (53)113 Rijalul Kasshi (53)

81

wata mas’ala ta fikihu da aka ruwaito daga wajenshi ba face anruwaito kishiyarta daga wurinshi, wani lokacin ma har a kan nasabtazantuka uku ko sama da haka dashi.

Alal misali game da rijiyar da najasa ta fada cikinta, an ruwaito dagagare shi cewa ai ita kamar kogi ne da ba ya najastuwa, a wani kaulinkuma yace a yashe ta, a wani kaulin kuma akace yace a kwashe gugabakwai ko shida daga cikinta!

A yayin da aka tambayi wani malamin Shi’a kan mafita game dawadannan maganganu masu cin karo da juna sai yace : mai ijtihadiyayi ijtihadinsa wajen rinjayar da daya daga cikin wadannan, sauranmaganganun kuma ya dauke su a matsayin ya yi su ne domin takiyyakawai! sai aka ce da shi to idan wani mujtahidin ya rinjayar dasabanin abinda na farko ya rinjayar me zai fadi game da sauranmaganganun? Yace su ma zai ce takiyya ne kawai! Sai aka ce masaidan haka ne Kenan mazhabar jafar Assadik ta bata kuma ta bi rububi,domin babu wata mas’ala da za a danganta masa face an ce ya yi tane don takiyya, domin babu wani abu a fili da zai iya sanyawa atantance tsakanin abinda ya fadi a matsayin takiyya da wanda batakiyya ba.

132- Littafan hadisi abin dogaro wajen ‘Yan Shi’a su ne: “Al-Wasa’il”na Al-Hurrul Amili wanda ya rasu a shekarar 1104 bayan hijira , da“Biharul Anwaar” na Al-Majlisi da ya rasu 1111 Bh, da”MustadhrakulWasa’il” na Al-Tabrasi mai rasuwa shekara ta 1320bh, Kenandukkanin takardun na baya-bayan nan ne! to idan dai hadisan da kecikin wadannan takardu ta hanyar sanadi da ruwaya aka tattara suwane mai hankali ne zai yi amanna da wannan ruwayar da ba atattara ta ba sai bayan shekara dubu da doriya?!

133- Akwai tari mai yawa na hadisan da su ke cikin takardun yanShi’a wadanda su ka yi daidai da wadanda ke hannun Ahlus Sunnah

82

masu Magana akan tabbatar da akida da kore bidi’o’i a cikin addini,amma sai yan Shi’a su ka yi kokarin karkata alkibilar hadisan tahanyar nuna cewa ai an fade su ne ta dalilin takiyya, sun yi haka nekadai saboda kawai sun sabawa sauye-sauyen rayukansu.

134- Marubucin littafin “Nahjul Balaga” wanda yana daga cikinmanyan takardun da yan Shi’a ke ji da su, ya ruwaito ruwayoyi dadama na nuna yabo da jinjina ga Abubakar da Umar ta bangaren Aliyu(r.a), kamar maganarsa cewa: “ bawan Allah mutumin kirki ya tafi yabarmu, ya bar duniyar nan ya kubuta daga sharrinta, ya sauke nauyinda Allah ya dora masa na yin biyayya gare shi, kuma ya ji tsoronsamatukar jin tsoro”114.

Abin mamaki sai ka aga yan Shi’a sun karkatar da wannan yabo zuwaga cewa dalilin takiyya ya yi shi, har su na riya cewa ai ya fadi hakanne saboda karkato da zuciyar masu ganin ingancin khalifancinAbubakar da Umar zuwa gareshi, ma’ana dai ya so yaudarar sahabbaine a zancensa! To a nan wajen ya zama dole yan Shi’a su yarda dama’anar maganarsu, itace cewa Aliyu (r.a) ya munafinci sahabbaisaboda shi matsoraci ne, saidai wannan ya ci karo da abinda su keruwaitowa na cewa shi din jarumi ne!

135- Yan Shi’a na riya cewa limamansu ba sa kurskure, saidai akwairuwayoyi da dama wadanda su ka yi fatali da wannan zace-zace nasu,domin kuwa ruwayoyi da dama sun zo suna nuna yadda limamansuke kurakurai da mantuwa kamar dai sauran mutane, har saidababban malaminsu wato Al-Majlisi ya tabbatar da cewa “wannanmasa’alar tana da rudani da yawa, saboda hadisai da ayoyi da yawangaske da aka ruwaito na nuni da cewa rafkannuwa na riskarsu”115.

114 (350)115 Biharul Anwaar (25/351)

83

136- Limamin Shi’a na sha daya mai suna Alhassanul Askari ya rasuba tare da ya bar ‘da ba, amma saboda kada gidan sarautar Shi’a yagirgiza ya rushe sai wani mutum mai suna Usman dan Sa’id ya riyacewa ai Imam Al-askari yana da ‘da wanda ya buya yana da shekaruhudu, kuma shine magajinsa a harkar imamanci!

Wannan abin mamaki har ina! Su yan Shi’an da ke cewa ba sa karbarshaida sai ta ma’asumi, amma sai gashi takanas sun gina babbanrukunin addininsu (Imama) akan shaidar wani mutum wanda bama’asumi ba!

137- Yan Shi’a su na sukar Marwan dan Al-Hakam har su na jinginadukkanin wata mummunar sifa gare shi, saidai kuma a gefe guda suna ruwaitowa cewa Alhassan da Hussani su na yin sallah a bayanshi,wanda hakan ke nuna tufka da warwar da yan Shi’a ke fama da shi.116

Kuma abu mafi ban al’ajabi ma shine yadda Marwan ya auri Ramla‘yar Aliyu bin Abi Talib (r.a), kamar yadda masana su ka bayyana117,hakanan Zainab ‘yar Alhassan “Almuthanna” ta auri jikan Marwanmai suna “Walidu dan AbdulMalik”118, hakanan Walidu ya auri Nafisa‘yar Zaidu dan Alhassan dan Aliyu dan Abu Talib119.

138- Yan Shi’a a cikin kissoshin da su ke biyawa su na riya cewa“lokacin da aka haifi mahadinsu wanda ya buya daga baya sai wasutsuntsaye sun sauka daga sama su ka hau kansa, sannan su ka tashi,da aka fadawa mahaifinsa abinda ya faru sai yayi dariya yace: aiwadannan mala’iku ne daga sama su ka sauka su na tabarruki dawannan yaro, kuma su ne mabiyanshi idan ya fito”120.

116 Biharul Anwaar (10/139)117 Nasabu Quraish na Mus’ab Al-Zubaidi (45)118 Nasabu Quraish (52)119 Umdatut Talib fi Ansabi Aali Abi Talib na Ibnu Anaba (111)120 Raudatul wa’izin (260)

84

Abin tambaya a nan shine shin tsoron me ya ke ji na buya cikin kogodaruruwan shekaru bayan kuwa dukkanin mala’ikun nan mabiyansane da za su taimake shi?

139- Yan Shi’a sun sanya sharudda ga wanda zai zama Imami, dagaciki shine ya zamto shine babban ‘da a wurin mahaifinsa, sannan yazamto babu mai wanke shi idan ya rasu sai Imam irinsa. Haka nan yazamto garkuwar Manzon Allah (s.a.w) ta dace da shi, sa’annan yazamto mafi ilimi daga cikin mutane, kada janaba ta same shi a farkeko cikin mafarki, kuma ya zamto masanin gaibu ne….!

Saidai bayan sun shata wadannan sharudda sai su ka fada cikin watamatsalar da kwangaba-kwanbaya, domin kuwa an samu daga cikinlimamansu wadanda ba su ba ne manyan ‘ya’ya a wurin iyayensu,kamar Musal Kazim da Alhasanul Askari, wasu kuma ba limamai bane su ka musu wanka, kamar Ali Rida, ba dansa Muhammad Jawadba ne ya wanke shi, domin yana yaro bai kai shekaru takwas ba alokacin, haka nan Musal Kazim ba danshi Aliyu Rid aba ne ya wankeshi, domin ba ya nan ma a lokacin, haka nan Hussaini dan Ali badanshi Aliyu Zainul Abidin ba ne ya wanke shi, domin ya lazimcimakwancinsa a lokacin, kuma dogaran dan Ziyad sun hana shi.

Hakanan za mu ga cewa ba kowanne ba ne garkuwar Manzon Allah(s.a.w) zata yi masa, kamar Muhammad Al-Jawad wanda bai ketareshekaru takwas ba a duniya bayan rasuwar mahaifinshi, haka nandanshi Aliyu dan Muhammad shi ma sanda mahaifin ya rasu yanakarami.

Haka nan wasu daga cikinsu ba za ta yiwu ace sun fi kowa ilimi ba,kamar wanda ya gadi imama yana dan kankani. haka nan akwaiwadanda ruwayoyin Shi’a su ka tabbatar cewa su kan yi mafarki su yijanaba, kamar Aliyu (r.a) da ‘ya’yanshi Alhassan da Hussaini 121.

121 Uyunu Akhbarir Rida (2/60)

85

Game da sanin gaibu kuwa wannan wani sonrai ne irin na malamanyan Shi’a kawai, domin kuwa Allah ya rigaya ya yi watsi da karyar dukwani mai kiran sanin gaibu sabanin shi.

140- Yan Shi’a na riya cewa tilas ne samuwar Imam ta zamto tahanyar nassi ne na wahayi! Wannan ma wata ku zo mu jitan ce, dominkuwa idan dai haka lamarin ya ke me ya sanya sabani ya yawaitatsakanin kungiyoyinsu game da sha’anin imama kuma kowacce alokaci guda tana kafa hujja da nata nassoshin akan irin limancin da tayi Imani da shi, Kenan me zai sanya a fifita wata akan wata? Alalmisali za mu ga kungiyar “Khaisaniyya” su na ganin cewa limancibayan Aliyu (r.a) zai dawo ne wajen danshi “Muhammad danHanafiyya” ba waninsa ba! Haka dai sabanin nasu ya yi ta fadada.Kenan da ace nassi ne ke bayanin yadda imama ta ke da ba a samuwannan sabanin ba tsakaninsu.

141- Wani sashe na Yan Shi’a na kage ga Nana Aisha (r.a) ta hanyartuhumarta da abinda Allah ya riga ya wanke ta daga gare shi na zina!Idan haka ne sai mu ce musu me ya sanya Manzon Allah (s.a.w) baitsaida mata da haddi ba tunda shine ke fadi cewa : “wallahi da Fatimayar Muhammad za ta yi sata da na yanke hannunta”?122.Sannan me yahana Aliyu (r.a) tsaida mata haddi lokacin jagorancinsa?

142- Shi’a na riya cewa ilimi na taskace ne a wurin limamansu,kuma sun yi gadon fannonin ilimi da nau’ukan littattafai irin wadandababu wanda ya samu sai dai su Ahlul Baiti, su ke da “Sahifatul Jami’a”da “kitabu Aliy” da “Al-Abitah” da “Diwanush Shi’ah” da “Al-Jafr”, harsuna cewa akwai dukkanin abinda mutane ke bukata a cikinwadannan littattafan jeka-na-yi-kan!

122 Bukhari ya ruwaito

86

To idan haka ne sai mu ce menene fa’idar wadannan littattafan je-ka-na-yi-kan tunda dai babu wanda ya taba ganinsu ballantana yaamfana da su?

Sannan kuma miye amfaninsu mu a wajenmu a yau? Shin za sutaimake mu wajen warware mas’alolinmu na addini da rayuwa a yau?Idan za su taimaka to me ake jira ba a fito da su ba gashi yau kimaninkarni goma da doriya da boyuwar Mahadinsu, Kenan mutane sucigaba da zama cikin bata da halaka kenan? idan kuma ba su daamfani garemu to na menene kambama batunsu da basu kima samada tasu? Sannan da wane dalili ne yan Shi’a ke kauda kai daga littafinshiriya da Allah ya saukar wanda ke hannun mutane su na amfanadashi wato Alkur’ani, su ke fakewa da dogaro da littattafan dabatunsu ya yi kama da almara da tatsuniyoyi?

143- Yan Shi’a na yawan ambata a cikin littattafansu cewa zuwa daHussaini (r.a) ya yi zuwa wajen mutanen Khufa da yaudararsa da suka yi sannan da kashe shi da aka yi shine ummul-aba’isin riddar damutane su ka yi, in banda mutane uku kadai. To a nan wajen inaamfanin sanin gaibunsa Kenan? Domin ai da ya san abinda zai faruKenan ai da bai je ba Kenan.

144- Yan Shi’a na riya cewa sababin boyuwar limaminsu na sha biyushine tsoron kisa, to anan sai mu ce me ya sanya ba a kashe limamanda su ka gabace shi ba alhali suna rayuwa ne karkashin daular khilafakuma manya ne ba yara ba? A hankalce menene zai sa a bar manyasu sakata su wala a kashe dan kankanin yaro?

145- Yan Shi’a na ganin cewa suna dogaro ne da hadisan da su katabbata ta hanyar Ahlul Baiti123,! Saidai akwai dibi-dibi da yaudara a

123 Aslus Shi’a wa Usuluha na Muhamamd Hussain Alu Kashif (83)

87

cikin wannan maganar, domin a hakikanin zance fa kai tsaye za afahimci cewa su na kwatanta limamansu ne da Manzon Allah (s.a.w)ta yadda ba sa zance kan son zuciya, don haka ne ma maganganunManzon Allah (s.a.w) su ka yi karanci a cikin takardunsu, domin sunwadatu da maganganun limamansu ne kadai. Sannan maganar bogice cewa da su ke suna dogaro ne da abinda ya zo ta hanyar AhlulBaiti, domin sanannen abu ne cewa ba dukkanin Ahlul Baiti ne su ka yiImani da su ba, har zuriyar Alhassan ma ba sa damuwa da ita. Kawaiaddininsu sun tsuke shi ne kan abinda su ka nasabta ga limamansunnan sanannu kadai.

146- Sa’annan za a iya fada musu cewa: mu kaddara mun yarda damaganarku ta cewa dukkanin addininku daga limamanku na AhlulBaiti ku ke dauka, to shin akwai wanda ya riski Manzon Allah (s.a.w)da wayonsa cikinsu banda Aliyu bin Abi Talib? Amsa itace babu. Toshin Aliyu shi kadai zai iya nado dukkanin hadisan da su ka zo dagaManzon Allah (s.a.w) ga dukkanin al’ummar da ta zo bayansa? Ta yahaka za ta yiwu bayan gashi a wadansu lokuta Manzon Allah (s.a.w)kan aike shi ko ya tura shi wani gari ko ya sanya shi rikon kwarya awasu lokutan? Ma’ana akwai lokutan da za a yi wadansu abubuwanbai san an yi su ba saboda ba ya wajen. Ba komai zai iya ruwaitowaba Kenan.

Sannan ta wace hanya sayyidina Ali zai iya rawaito abinda ke shigatsakanin Manzon Allah (s.a.w) da iyalansa a kebe a cikin gidansa?

Don haka shi kadai ba zai iya dakko kano ba gammo ba!

147- Kuma a fili ya ke cewa galibin musulman da ke waste a saurankasashen duniya koyarwar Manzon Allah (s.a.w) ba ya zo musu ba neta hanyar Aliyu bin Abi Talib ko Ahlul Baiti ba! Manzon Allah (s.a.w)Sa’ad dan Zurara ya aika Madina domin kiransu zuwa musulunci dakoya musu Alkur’ani da fahimtar da su hukunce-hukuncen adddininsu,

88

haka nan ya tura Ala Al-Hadhrami Bahrain domin sauke wancan nauyi,kamar yadda ya tura Abu Musal Al-Asha’ari zuwa Yaman, da Itab danUsaidu zuwa Makka, duk dai saboda isar da sakon musulunci, kumadukkanin wadannan ba Ahlul Baiti ba ne! To ina karyar yan Shi’a tacewa babu mai isar da sakon Annabi (s.a.w) sai Aliyu ko iyalangidansa?!

148- Yan Shi’a su na yin ikirarin cewa sanin halal da haram dahukunce-hukuncen aikin Hajji bai je musu ba sai ta hanyar Abu JafarAl-Baqir, ma’ana dai babu abinda ya iske su a wannan babin ta hanyarAliyu (r.a)! suna fadi a cikin littafansu cewa: “yan Shi’a kafin bayyanarAbu Jafar ba su da ilimin sanin halal da haram da hukunce-hukuncenaikin hajji, har sai bayan bayyanar Abu Jafar wanda ya fayyace musuwadannan abubuwa, har mutane suka zamto suna bukatarshi bayangabanin haka suna daukar addini daga wadansu mutanen nadaban”124.

Idan haka ne ta ya Kenan Shi’a ke bautawa Allah kafin zuwan Baqir?!

149- Yan Shi’a na tafka kwangaba kwan baya ta yadda su ke riyacewa wanda ya ga mahadinsu mai jiran gado adali ne mai gaskiya.Malaminsu na cewa: “ Mutum ne mai babban matsayi wanda ya ga Al-Hujjah – wato Mahadinsu kenan – bayan bayyanarshi, wanda yaganshi muna masa shaida kan isarsa wata martaba ta koli taadala”125.

A nan sai mu ce musu me ya sa ba kwa fadin haka akan wanda ya gaManzon Allah (s.a.w)?

124 Usulul Khafi (2/20)125 Tankihul Maqaal (1/211)

89

150- Yan Shi’a su na yin tufka da warwara ta yadda su ke kin karbarruwayar dukkanin wanda ya musanta wilayar limamansu, da wannanne su ka ki karbar ruwayar sahabbai. Saidai a lokaci guda kuma munga yadda ba su dauki irin wannan matakin ba ga wasu daga cikinjagororinsu na Shi’a. malaminsu Al-Hur Al-Amily ya tabbatar da yaddaShi’a mai limamai sha biyu ke amfani da labaran kungiyoyi irinsu “Al-Fad’hiyya126” da “Al-Wakifiyya127” da “An-Nawusiyya128”, ko da ya kekowacce daga cikin wadannan su na inkarin wadansu daga cikinshuwagabannin Shi’a yan sha biyu, amma duk da haka malaman Shi’ana ambatar wadansu daga cikin malaman wadannan kungiyoyi amatsayin aminai da za a iya karbar ruwayarsu129, amma abin mamakikuma ba sa karbar ruwayar sahabban Manzon Allah (s.a.w)!

151- Da dama daga cikin malaman Shi’a na riya cewa littafin Al-khafina dauke da ingantattu da matsakaita da raunanan hadisai, duk dakuma sun tabbatar cewa wannan littafin sai da aka bijiro da shi galimaminsu Mahadi mai jiran gado, har ya ke cewa “ai wannan yawadaci yan Shi’armu”! abin tambaya a nan shine me ya sanya baigoge raunana da kirkirarrun hadisan da ke ciki ba?

152- Malamin yan Shi’a mai suna Al-Hamdani ya fadi a cikin littafin“Misbahul Faqih” cewa “abin lura wajen tabbatar da kulluwar ijma’inra’ayin malaman da su ka zo daga baya ba wai haduwa din ba ne,kawai ana samun ijam’i ne idan an samo wani ra’ayi na wani dagacikin limamai ko da kuwa a mafarki ne130”. ku duba yadda su ka yiwatsi da abinda aka sani a zahiri su ke laluben mafarke-mafarke daalmara don tabbatar da addini.

126 Su ne mabiyan Abdullahi dan Al-Aftah dan Jafar Al-Sadiq127 Su ne wadanda su ka cire hannunsu daga yadda da imamar duk wanda ya zo bayan Musal Kazim128 Su ne mabiyan wani mutum mai suna An-Nawus, masu cewa Jafar dan Muhammad bai mutu ba, kumashine Mahadi mai jiran gado.129 Misali z aka iya duba littafin “Rijalul Kasshi shafuka na (563, 565, 570, 612, 616, 597, 615)130 Misbahul Faqeeh (436)

90

153- Yan Shi’a na riya cewa daya daga cikin malamansu mai sunaIbnu Babawaihi Al-Qummy mawallafin daya daga cikin mafi girmanlittattafai hudu da su ke ji da su mai suna “Man La Yahduruhul Faqeeh”sun tabbatar da cewa wannan malamin na su ya kan ambaci ijma’i awata mas’ala a wani wuri, sannan ya ambaci ijma’i a kishiyarta a waniwurin131! Har wani malaminsu na cewa “idan haka dabi’ar mutum takena ambatar ijma’in karya ta ya za a dogara da shi wajen gina hukunce-hukuncen addini?132”

154- Daga cikin abubuwan ban al’ajabi na yan Shi’a shine idan akasamu maganganu guda biyu masu sabani da juna, daya an sanwanda ya fade ta, daya kuma ba a sani ba, to hujja a wajensu ita cemaganar da ba a san wanda ya fade ta ba! Domin a riyawarsuwannan zancen zai iya zama shine maganar imam ma’asumi, har saida ta kai malaminsu Al-Hur Al-Amili ya soke su kan wannan zanceinda yake cewa : “fadinsu cewa za a fifita ra’ayin da ba a sanmafadinshi ba wannan abin mamaki ne, domin ta ya za a yi su sanwanda ya fade sa ko ma’asumi ne ko ba ma’asumi ba ?133”.

155- Babban malamin Shi’a Al-majlisi yana cewa: “fuskantar kabariwajibi ne ko da kuwa ba fuskar alkibla ya ke ba134” . wannan fa awurin salla raka’a biyu da su ke yi ne idan sun ziyarci hubbarorinlimamansu.

Abin mamaki anan shine shi batun hani daga salla a makabartu yatabbata a cikin takardunsu, kamar yadda ya tabbata daga limamansu,saidai suna karkatar da hakan ta cewa ai duk takiyya ne kawai, kamar

131 Jami’ul Maqal Fi Ma Yata’allaku Bi Ahwalil Hadisi War Rijal na Al-Tareehi (15).132 Jami’ul Maqal (15).133 Muqtabasul Athar (3/63).134 Biharul Anwaar (101/369)

91

dai abinda su ka saba yi na karkatar da alakar dalilan da ba su daceda soye-soyen zukatansu ba.

156- Yan Shi’a na yawan kawo hadisin “Ghadeer” da hadisin “Inahada ku da Allah game da iyalaina”, saidai su na manta cewa su newadanda su ka fara keta umurnin wadannan hadisan, ta yadda su kakulla gaba da kaso mai tsoka na iyalan gidansa!

157- Za a iya fadawa Yan Shi’a cewa da ace sahabbai sun boyewani nassi da ke nuna cancantar Aliyu (r.a) ga Khilafa da sun boyehadisan da ke magana kan falalarshi, saidai ba su yi hakan ba, wandahakan ke nuna cewa tabbas da ace akwai irin wadancan nassoshinda ke nuna khilafarsa da sun kawo, musamman sabodamuhimmancinta, kuma da kowa ya sansu ta yadda ba za su boyu ba.

158- Yan Shi’a na ruwaitowa cewa Alhasanul Askari mahaifi gaMahadinsu ya yi umurni da boye labarin Mahadi, saidai fa gaamintattu kadai, amma a lokaci guda kuma suna tufka da warwarasuna riya cewa wanda ya mutu bai san Imam ba to wanin Allah ya kebautawa, kuma idan ya mutu a cikin wannan halin ya yi mutuwa irin tamunafikai da kafirai!135 Sannan wane irin tauye hakki ne wannan acemahaifinshi ya hana maboyansa na Shi’a labarinsa.

159- Yan Shi’a masu riya cewa Allah ya ja kwanan Mahadinsu zuwadaruruwan shekaru saboda bukatar bayi za mu iya cewa da su: daace Allah zai ja kwanan wani saboda bukatuwar bayi zuwa gare shida ya bar Manzon Allah (s.a.w) bai dauke shi ba.

135 Usulul Khafi (1/181)

92

160- Yan Shi’a ba sa karbar zancen Ja’afar dan’uwan AlhasanulAskari mahaifin limaminsu mai jiran gado, duk da dan’uwanshi baitaba haifar da na cikinshi ba, domin su a wajensu ba ma’asumi bane136. amma a lokaci guda kuma sun yarda da ikrarin da “Usman danSaid” yayi na cewa Alhassan yana da ‘da wanda ba ma’asumi ba!Wannan wane irin tufka da warwara ne.

161- Daga cikin shahararrun akidun Shi’a akwai akidar “Ad’-‘Deena”,abinda ta ke nufi shine wai Allah ya halicci yan Shi’a da turbaya tadaban, haka nan Sunnah ma ta daban, sai aka cakuda sashen wannanturbaya da sashe, don haka sabon da aka samu dan Shi’a na yi yasamo asali ne daga tasirin cakuduwar da yayi da turbayar AhlusSunnah, salahar da Ahlus Sunnah zai samu kuma ta samo asali nedaga tasirantuwarshi da turbayar dan Shi’a, idan kiyama ta zo sai atattara laifukan dan Shi’a a rafka su ga dan Sunnah, a tattara ladandan Sunnah a jefa su ga dan Shi’ah!

Saidai yan Shi’a sun manta cewa wannan akidar tasu ta sabawaabinda su ka kudurce a akidarsu ta babin “kaddara da aikin bayi”,domin abinda wannan akida ke nunawa shine shi bawa ba shi da zabia cikin aikinshi, domin “A’d-‘Deena” ce ke da tasiri akanshi Kenan! dukda yake a asalin mazahabarsu suna ganin dan adam ne kadai yamallaki aikinshi kamar dai mazhabar Mu’utazilawa! A nan ma antufka an warware.

162- Malaman Shi’a na ambatowa cewa sahabban Madina (Al-ansar)suna kaunar Aliyu (r.a) sosai, kuma suna da yawa matuka cikinrundunarsa a rigimar “Siffeen”, sai mu ce musu idan haka batun ya keme ya sanya ba su mika masa khilafa ba bayan rauswar ManzonAllah (s.a.w) sai su ka mikawa Abubakar? Ba za ka taba samun amsawai warkarwa ba.

136 Al-Ghaiba (106)

93

Hakika zurfin tunanin da Ansarawa da Muhajirai ke da shi ya ketanamu sosai, sun san ko menene khilafa sarai, kuma sunabambancewa tsakaninta da tsurar alaka ta zumunci mai kyau da ketsakanin mutum da mutum.

Shi ya sa za mu ga cewa takardun yan Shi’a da ke kawo wannanlabarin da yabon Al-Ansar saboda marawa Aliyu (r.a) baya da su ka yia yakin Siffeen, su takardun ne dai su ka zargi su Al-Ansar din daridda da munafinci game da abinda ya faru a Saqeefa!

Wannan wani ma’auni ne ja’iri da su ke auna sahabban Manzon Allah(s.a.w) da shi, idan sun goyi bayan Aliyu (r.a) a wadansu wajaje sai ayabe su tareda nuna fifkonsu a kan sauran mutane, idan kuma su kadau matsaya da ta sabawa matsayar da Aliyu (r.a) ya dauka sai anasabta su ga ridda da munafinci da kafirci!

Idan yan Shi’a su ka ce ai mun nasabta su ga ridda ne sabodamusanta hadisin dasu ka yi na mai dauke da wasiyyar khilafancinAliyu (r.a) da su ka yi, sai a ce musu ashe ba ku ke cewa wannanhadisin dimbin mutane sun ruwaito shi ba? To akan wane musantawakuma ku ke Magana? Domin idan nace Manzon Allah (s.a.w) yace“wanda na zamto masoyinshi to Aliyu ma masoyinshi ne”, a nan wanenassi ko hadisi na yi inkari? Gashi na kawo shi kowa ya ji, kumasahabbai su su ka ruwaito shi ba su boye shi ba.

Idan su ka ce ai ma’anar hadisin su ka musanta! Sai mu ce mukuwanene ya tilasta waninku bin irin fassarar da ku ku ka yi wa kanku?Shin wai kun fi sahabban da su ka rayu da Manzon Allah (s.a.w) ilimida hankali da fahimta da sanin yakamata ne? ko kuwa kun fisufahimtar larabci ne ta yadda ba sa gane maganganu sai ku ne keganewa?

163- Mutane kashi biyu ne: akwai masu ganin an canza alkur’ani maigirma tare da jirkita shi, kamar An-Nuri Al-tabrasi mai littafin Al-Mustadrak – daya daga cikin littafai guda takwas na hadisi mafiya

94

daraja wurin Shi’a – wanda ya wallafa littafi mai suna “Faslul KhidabFi Tahrifi Kitabi Rabbil Arbab”. Ya fada a cikin littafin cewa: “dagacikin ababen da ke nuna irin jirkitawar da aka wa tsarin fasaharharshe da aka yiwa Alkur’ani shine yadda za ka ga wani sashenshiyana dauke da salo na koli wajen fasaha yayinda wani sashen kare bazai ci ba137”!!

Haka nan shi ma Sayyid Adnan Al-Bahrani yana cewa : “Ruwayoyi sunzo masu yawan gaske ta yadda sun shahara sun yadu matuka wurinal’umma cewa Alkur’anin nan fa jirkitacce ne, kuma sanannen abu newajen sahabbai da tabi’ai, kuma an yi ijma’i kai, sannan yana cikinakidarsu da ba ta rawa138”

Haka nan Yusuf Al-Bahrani na cewa: “Abinda ke cikin wadannanruwayoyi gameda tabbatuwar jirkitar Alkur’ani a fili yake, domin idanza a iya sukar wadannan ruwayoyi to za a iya sukar dukkanin hukunce-hukuncen da addini ya zo da su, domin tushen ruwayoyin daya ne,hakanan maruwaitan da hanyoyin da ruwayoyin su ka zo duk daya ne.Ina rantsuwa da Allah maganar masu cewa ba a jinkirta Alkur’ani baba wani abu ake nufi da ita ba face laluben uzuri da bada kariya gaazzaluman shuwagabannin da ake tsammanin wai ba su ci amana bagame da khilafa, duk da kuwa sun yi ha’inci a mafi girmar amana takiyaye Alkur’ani wanda hakan ya fi hatsari matuka ga addini.139

Kashin farko Kenan da su ka yi ikrarin jirkita Alkur’ani a fili.

Kashi na biyu su ne sahabban Manzon Allah (s.a.w) wadanda laifinsua wajen Yan Shi’a shine sun mika ragamar khilafa ga Abubakar (r.a)maimakon Aliyu (r.a).

Malaman Shi’a na nemawa kashi na farko uzuri da kalamai irinsu(kuskure ne su ka yi), (ijtihadi su ka yi su ka kauce ba ma tare da su anan). Abin mamaki shine a yaushe ne mas’alar Alkur’ani ta zamto

137 (211)138 Masharikul Shumusid Durriyya (126)139 Ad-Durarun Najafiyya, Yusuf Bahrani (298)

95

batun ijtihadi? Kuma wane ijtihadi ne a cikin fadinshi cewa “ wanisashen Alkur’ani ko kare ba zai ci ba wajen fasaha!” wannan gangancine zalla.

Ga wani misali na yadda Malaman Shi’a yan sha biyu ke kallon masuriya jirkitar da Alkur’ani daga cikinsu:

Sayyid Ali Milani yana daga cikin manyan malaman Shi’a a yau, yanafadi a cikin littafinshi mai suna “Adamu Tahrifil Qur’an” yana mai badakariya ga Mirza Nuril Tabrasi cewa: “Mirza Nuri yana daga cikinmanya-manyan malaman hadisi, muna girmama shi, yana daga cikinjiga-jigan malamanmu, ba za mu iya sukarshi ba ko kadan, don baidace ba, kuma ba girmanmu ba ne, wannan babban malami ne140”. kuduba ku ga wannan kwangaba-kwanbaya.

164- Allah madaukakin sarki yace:

﴾ـ ءايلوأ هنود نم اوعبتت وال مكبر نم مكيلإ لزنأ ام اوعبتا ﴿

“Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kadaku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa”(Al-Aaraf:3)

Wannan nassi ne a fili da ke haramta bin wani sabanin Allah daManzonsa, kuma idan akwai fa’ida wajen turo Imam za ta zamto nedon aiwatar da umurnin da Allah ya aiko wa bayinsa, bawai aikinshishine ya zo wa da mutane abinda ba sa bukata na addini ba ko ya zomusu da sabanin abinda Manzon Allah (s.a.w) ya zo musu da shi,domin ga shi mun ga yadda Aliyu (r.a) a lokacin da aka kira shi zuwawarware sabani yayi kokarin hakan ta hanyar hukunta littafi AllahTsakani, har ya ke cewa matukar da Alkurani za a yi hukunci to

140 Thumma Absartul Hakika (294)

96

wannan shine daidai. To a nan wurin matukar dai abinda yayi nasanya Alkur’ani alkalin da zai yanke hukunci daidai ne, to wannanshine asali a wajenmu , idan kuma hukunta Alkur’anin da ya yi badaidai ba ne to mun yi amanna da cewa hakan ba zai taba yiwuwa badomin ba siffar shi ba ce. Domin da ace hukunci da Alkurani bagaskiya bane da Aliyu (r.a) ya ce musu da wane dalili ne za ku yihukunci da Alkurani bayan gani a tsakaninku nine mai isar daAdddinin da Muhammad (s.a.w) ya zo da shi? Amma bai fadi haka ba!

Idan su ka ce to ai bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w) ana bukatarImam din da zai isar da addini bayanshi!

Sai muce wannan ba haka ba ne, domin abin bukata daga wurinManzon Allah (s.a.w) dama shine isarwa , ko yana nan ko ba ya nan,abin bukata kadai shine isar maganganunshi zuwa ga dukkaninduniya ko da kuwa bayan rasuwarshi ne.

Idan su ka ce akwai bukatar samun Imam wanda zai shedi ayyukanda mutane ke yi sai mu ce wannan ma ba zai yiwu ba, domin duniyarnan da fadi ta ke, akwai wajajen da Imam bai isa ya san me ke faruwaa can ba, Kenan dole dai sai an bukaci wakili mai isarwa.

kuma ita isarwa da wakilci daga Manzon Allah (s.a.w) itace isarwa takololuwa mai share hawaye, ba isarwa daga wanda ke kasa da shi bawajen daraja141.

165- Ruwayoyi da dama wadanda su ka inganta a wajen yan Shi’asun zo suna masu tofin-ala-tsine ga manyan makaryata wadandaaddinin Shi’a ya ginu akan ruwayoyin da su ka samar, saidai manyanyan Shi’a sun kauda kai daga wannan badakalar, hujjarsu ita ce cewawai lallai ne karbar wannan sukar sokawa kai wuka ne, domin korewadannan akidun zai sanya akidar Shi’a sajewa da ta Sunnah, dominzai zamto babu wani bambancin azo-a-gani Kenan tsakanin yan Shi’a

141 Al-Fasl Fil Milali Wal Ahwa’I Wan Nihal (4/159)

97

da Sunnah, don haka ne su ka yi amfani da takiyya wajen bada kariyaga wadannan ruwayoyin da makaryatan su ka shuka musu.

Malaminsu mai suna Muhammad Ridha Al-Muzaffar wanda jigo ne naShi’anci a wannan zamanin ya yadda da cewa jigon ruwayoyinsu sunsamu suka daga manyan limamansu, kuma littattafan Shi’a sunruwaito haka, don haka ne ma ya kawo abinda ke nuna suka gawadansu manyan maruwaitansu. Ya fadi game da Hisham bin SalimAl-Jawaliki cewa : “ ya hadu da soke soke sosai, kamar dai yaddawadansu manya-manya daga cikin Mabiya Ahlul Baiti su ka gamu dairin wannan sukan, don haka ba akanshi aka fara ba, ko da yakeamsar wannan tufka da warwara a fili ta ke142” . sai yayi tsokaci akanwannan maganar da cewa: (ma’ana sun yi ne don takiyya143). A cangaba kadan yace: “ta ya za a soki irin wadannan jiga-jigan malaman?Ai mazhabar Ahlul Baiti ma bai yadu ba sai da kaifin hujjojinsu144!

Ku dubi yadda mutanen nan ke ake nuna ta’assubanci ga ra’ayoyinsua fili, sun rika tare da bada kariya ga mutanen da limamansu sunrigaya sun soke su a baro-baro, tareda kauda kai daga ruwayoyin dasu ka zo daga wajensu na sukarsu da tsoratarwa daga barinsu,wadanda da kansu littattafan Shi’an ke hakaitowa. Wannan ba komiba ne illa karyata Ahlul Baiti da gasgata abinda makaryata ke fadigame da su, ta hanyar riya cewa zargin da limamai su ka yi musu sunyi ne saboda takiyya kawai, Kenan ba sa bin Ahlul Baiti a cikinmaganganunsu da suka dace da abinda al’umma ta hadu akai, saidaisu bibiyi maganganun da makiyansu su ka shata su jingina musu,sannan su yasar da hakikanin maganganun a’imma din ta hanyarjingina musu takiyya.

166- Sanannen abu ne ta hanyar tawaturi cewa Abubakar da Umarda Usman (r.a) suna da daraja da kusanci na musamman da Manzon

142 Al-Imamus Sadik na Muhammad Hussain Al-Muzaffar (178)143 Al-Imamus Sadik (178)144 Al-Imamus Sadik (178)

98

Allah (s.a.w) bayan surukuta da ke tsakaninsu, kamar yadda ya nanuna musu matukar kauna, to ko dai ya zamto kan daidai su ke alokacin rayuwarsa da bayan rasuwarsa, ko kuma ya zamto kishiyarhaka.

Idan na farko ne, to abin nufi hakan ya boyu Kenan ga Manzon Allah(s.a.w), ko kuma ya sani amma yana yi musu ne kara da kauda-kai. Anan ko wane daya daga cikin biyun nan yan Shi’a su ka zaba baabinda zai nuna sai suka kai tsaye ga Manzon Allah (s.a.w), domin yinhakan kamar nunawa ne cewa bai san abinda ya ke ba!!

Idan na biyun su ka dauka cewa bai san hakikanin halinsu ba ne, to anan kamar ana so ace Allah ya tozarta al’ummar Annabi Muhammadne a fakaice! domin Allah dai shine ya dau alkawarin daukakawannan al’ummar da zabarta a matsayin mafififciya daga cikindukkanin al’ummu, amma kuma sai a samu cewa manyan abokananAnnabin wannan al’umma ba mutanen kirki ba ne, kuma duk da hakaAnnabin bai sani ba to idan dai abokanan annabi ba su zamto na kirkiba to su wanene za su zamto hakan Kenan?

Ta wannan babin ne malamai ke bayyana irin girman sukar da YanShi’a ke yiwa Manzon Allah (s.a.w) a fakaice.

Abu Zur’ah Ar-Razi yana cewa: “ ba komi –Yan Shi’a – ke nufi dawannan Magana ba face sukar Manzon Allah (s.a.w) a fakaice, dominidan abokananshi mutan kirki ne to kai tsaye mutane za su masahukunci da cewa shima na kirki ne, haka nan kishiyar haka, dominabokin barawo ai barawo ne”.

167- Yan Shi’a na cewa: Imama wajiba ce, domin shi Imam na’ibi nena Manzon Allah (s.a.w) ta bangaren kiyaye shari’ar musulunci, dakare addini daga kare-kare da ragi145”

Haka nan dai su na nuna cewa: dole ne a samu Imam wanda Allah ya

145 Ash-Shi’a Fit Tarikh (44)

99

turo ga mutan ban kasa, domin akwai bukatarshi din, kuma babu waniabu mara kyau tattare da zuwanshi, don haka tilas ne samunshi…146”

Sannan su na cewa ai ita imama ta zama tilas ne domin tattare dazuwanta akwai jinkan Allah ga bayinsa, domin matukar akwaishugaba kuma yana kokarinsa wajen hana azzalumi zalunci da sanyamutane aikata alheri, to mutane kan kusanci shiriya da nagarta , danesantar bata da barna, don haka Kenan ana bukatar Imam da zaitsayu da wannan aiki, wannan kuma shine dalilin tilascinsamuwarshi..147”

Amsar da za mu basu anan itace: kun ga dai gashi duk cikinlimamanku sha biyu banda Aliyu bin Abi Talib babu wanda ya rike irinwannan makamin na mulki da shugabanci da kuka siffata ballantanaya tsayu da wadancan ayyuka da ku ka ambata, to ta ya za kualakanta muhimmancin samuwarsu da wadancan ayyukan da asaliba su ma gudanar da su ba a rayuwa? Ma’ana jinkan da ku kemaganar dole ne samuwarsu saboda shi ba su aiwatar da shi baKenan. To wane irin limanci ne wannan.

168- Ya zo a cikin littafin “Nahjul Balaga” cewa Aliyu (r.a) ya kasanceyana ganawa da ubangijinsa da wannan addu’a: “ya Allah ka gafartamini gwargwadon yadda na dau alwashin wani aiki ban aiwatar ba,idan na dawo kan daidai ka gafarta mini, ya Allah ka gafarta minigwargwadon kusanta ta da harshe na da kirji na zuwa gare ka, Allahka gafarta mini kurakurai na na cikin maganganu na da mantuwargabbai na, da kurakuran harshe na148”.

A fili ya ke a nan yadda ya ke Kankan da kai wajen Allah don gafartamasa kurakuransa da sakacinsa, wannan ya sabawa kudurce-kudurcenku na cewa shi katangagge ne daga laifuka.

146 Manhajul Karama (72-73)147 A’ayanush-Shi’a (1/2)148 Nahjul Balaga , sharhin Ibnu Abil Hadid (6/176)

100

169- Yan Shi’a na riya cewa “babu wani Annabi face ya yi kira zuwaga imamar Aliyu149”, kuma wai Allah ya dau rantsuwar Annabawacewa su yi kira ga imamar Ali150”. Har wuce iyakarsu ma ya kai su gaikariri da daya daga cikin manyan malamansu mai suna “At-Tahrani”yana cewa an bijiro da imamar Aliyu ga daukacin annabawa, “abindaya karba shine daidai, abinda ya ki karba to batacce ne151”!

A nan sai mu cewa Yan Shi’a: hakika annabawa sunyi kira ne zuwa gakadaita Allah da bauta da yi masa ibada shi kadai ba wai zuwa gawilayar Ali ba, kamar yadda Alkur’ani ya fadi cewa:

﴾ هيلإ يحون الإ لوسر نم كلبق نم انلسرأ امو ﴿

“Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yinwahayi zuwa gare su.”(Al-Anbiya:25)

Idan ita wilayar Ali din a rubuce ta ke a dukkanin littattafan da su kagabata haka batun ya ke, to da wane dalili ne za a ce yan Shi’a nekadai su ka san da wannan labarin banda waninsu? Me ya sanyamabiya sauran addinai da su ka gabata kamar Yahudu da Nasara dasauransu ba su ga wannan wasiyyar da ake ikrari ba? Kuma gashidaga cikinsu wasu sun musulunta amma ba mu taba jin inda suambaci wani abu mai kama da wadannan ruwayoyi ba?! Kai me ya sama bai zo a cikin Alkur’ani ba wanda shi ne cikamakin dukkaninlittattafan da su ka gabace shi?

170- Shin limamai sun yi mutu’a? su wanene ‘ya’yansu na mutu’a?

171- Yan Shi’a na riya cewa limamai sun san abinda ya gabata da

149 Biharul Anwaar (11/60)150 Al-Ma’alimuz Zulfa (303)151 Wada’I’un Nubuwwa (155)

101

wanda zai zo nan gaba, kuma babu wani abu mai boyuwa gare su,kuma Aliyu (r.a) shine kofar ilimi, idan haka ne ta ya Aliyu ya jahilcihukuncin Maziyyi har ya tura a tambayar mishi hukuncinsa wajenManzon Allah (s.a.w)?

172- Babban laifin sahabbai a wajen yan Shi’a kamar yadda su kefadi shine yadda su ka karkatar da akalar wasicin da aka masa nakhilafa, da wannan ne su ka kore siffar adalci daga sahabbai! To idanhaka ne me ya sanya ba za su yi wa wasu daga kungiyoyin shi’a irinwannan hukuncin ba musamman kuma kasantuwar sun yi inkarinwadansu daga cikin limamansu? Misali kungiyoyin “Al-fadhiyya”, “Al-Wakifa” da sauransu kamar yadda ya gabata. Sabanin haka ma z akaiske malaman Shi’a yan sha biyu na kafa hujja da maganganunmalamai da maruwaitan wadannan kungiyoyi a cikin kaso mai tsokana littattafansu. Wane irin tufka-da-warwara ne wannan..?

173- Takardun yan Shi’a sun hadu akan cewa limamansu sunkasance su na yin aiki da takiyya, to sanannen abu ne cewa meaikata takiyya lallai ne wta rana zai yi karya, kuma karya haramun ce.

174- Khulaini ya ruwaito cewa daya daga cikin daliban Imam Ali yabashi shawarin cewa ya gyara barnar da khalifofin da su ka gabaceshi su ka yi (wato Abubakar da Umar da Usman (r.a), sai ya kiya yanamai kafa dalili da cewa yana tsoron yin hakan zai sa mabiyansa suwatse daga gefenshi152”. Kuma fa duk da ya ke daga cikin tuhumominda su ke yi mu su akwai canza Alkur’ani da Sunnah, ashe kauda kanAliyu gameda gyara wadannan manya-manyan kura-kuran ba zaikauda masa siffarsa ta Isma ba ?

152 Ar-Raudah na Al-Khulaini (29)

102

175- Umar (r.a) ya zabi mutane shida a matsayin majalisar dattawada za ta yi shawara ta fidda shugaba bayan rasuwarsa, sai mutaneuku daga cikinsu su ka janye, sannan shi ma Abdurrahman bin Auf yajanye, wadanda su ka ragu su ne Usman da Aliyu (r.a), to me ya saAliyu (r.a) tun farko bai sanar da su ba cewa shi fa shine aka wawasicci da khilafa? Shin akwai wanda sayyidina Ali tsoro ne bayanrasuwar Umar?

176- Abin mamaki za mu ga yadda yan Shi’a su ka zano sunayenlimamansu sha biyu tun daga rasuwar Manzon Allah (s.a.w) har zuwalimaminsu na sha biyu, amma kuma sai ga babban malaminsu nawannan zamani yana kore samuwar wannan sunayen, inda shi “Al-khu’i” ya ke cewa: “ruwayoyin da su ka zo mana ta hanyoyi birjik sundai kayyade yawan limamai da cewa su sha biyu ne, amma ba sufayyace sunayensu daya bayan daya ba153”

177- Sanannen abu ne cewa Yan Shi’a na kudurce riddar galibinsahabban Manzon Allah (s.a.w) bayan rasuwarshi, a gefe guda kumaza mu lura da yadda su ke kwangaba-kwanbaya wajen maida martiniga wadanda ke musu tambaya kamar haka: me ya sanya Aliyu (r.a)bai yi yekuwa cikin mutane da su mara masa baya su masa mubaya’aba bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w) matukar dai ya san cewa shiaka wa wasiyya ? amsar da su ke badawa itace wai bai yi haka ba nesaboda yana tsoron sahabbai za su iya ridda idan ya yi haka!!

Ya zo a cikin “Al-Khafi” daga Baqir cewa : “lokacin da mutane su ka yidanyen aikinsu na yin mubaya’a ga Abubakar babu abinda ya hanaAmirul Muminina (Ali) kira ga ayi masa mubaya’a sabanin Abubakarba sai don tsoron mutane za su iya yin ridda su koma bautar

153 Siratun Najah (2/452)

103

gumaka!154”

178- Yan Shi’a na riya cewa akwai hadisai da su ke dauke dabayanin limamansu! saidai mun samu dimbin ruwayoyi da ke fatali dawannan ikirari nasu daga cikin littattafansu, Ustaz Faisal Nur yatattara su a cikin littattafinsa mai suna “al-Imama Wan Nas”, maibukatar sanin hakika na iya komawa wannan littafin.

Daga karshe ina rokon Allah ya amfanar da samarin Shi’a dawadannan tambayoyi ya sanya su mabudin fahimtar alkhairi gare su,su karbi gaskiya ba tare da tsoron zargin mai zargi ba.

Sannan ina kira ga dukkanin wanda ke da wata tambaya maimuhimmanci da ya kamata in tambaya ban yi ba da ya aiko mini daita don sanya ta da riskar da ita cikin bugu na gaba.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (s.a.w).

154 Al-Khafi (8/295)