tarbiyyar `ya`ya a musulunci

179
1 ABUBUWAN DA KE CIKIN LITTAFIN Muqaddima 3 Ma’anar tarbiyya 6 Hukuncin tarbiyya 9 Manufar tarbiyya a Musulunci 14 Himmar Magabata wajen tarbiyyar `ya`ya 16 Vangarorin tarbiyya 23 Wuraren da a ke samun tarbiyya 26 Hanyoyin koyar da tarbiyya 34 Haxarin sakaci game da tarbiyyar `ya`ya 42 Yadda a ke yin tarbiyyar `ya`ya 51 Qalubalen da ke fuskantar tarbiyya 152 Kammalawa 175 Daga cikin littafan da aka yi amfani da su 176 FA’IDODIN DA KE QASAR LAYI (HASHIYA) Siffofin mace ta qwarai da hanyoyin faranta wa miji rai 18 Hukuncin auren mace fiye da huxu 20 Faxakarwa game da littafin Tarbiyyatul Awlād na Ulwān 23 Falalar masallaci 30 Huxubar Juma’a ko idi cikin harshen Hausa 31 Fa’idodin auren wuri 48 Matsayin auren dole 49 Ladubban da suka shafi jariri/jaririya 53 Daidaituwar Allah a kan Al’arshi 59 Sharuxxan kalmar shahada da abubuwan da ke warware ta 62 Wajibcin riqo da Alqur’ani da Sunnah 65 Siffofin Ahlus-Sunnah da asasin da’awarsu 67 Matsayin Manzon Allah (SAW) 69 Alamomin son Allah (Maxaukaki) da ManzonSa (SAW) 70 Hukuncin zagin Manzon Allah (SAW) 71

Upload: tarbiyyarmusulunci

Post on 26-Jun-2015

946 views

Category:

Documents


21 download

DESCRIPTION

This book describes the Islamic manner of upbringing based on the teachings of the Qur'an and Sunnah in the light of the salaf saaliheen

TRANSCRIPT

Page 1: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

1

ABUBUWAN DA KE CIKIN LITTAFIN

Muqaddima 3

Ma’anar tarbiyya 6

Hukuncin tarbiyya 9

Manufar tarbiyya a Musulunci 14

Himmar Magabata wajen tarbiyyar `ya`ya 16

Vangarorin tarbiyya 23

Wuraren da a ke samun tarbiyya 26

Hanyoyin koyar da tarbiyya 34

Haxarin sakaci game da tarbiyyar `ya`ya 42

Yadda a ke yin tarbiyyar `ya`ya 51

Qalubalen da ke fuskantar tarbiyya 152

Kammalawa 175

Daga cikin littafan da aka yi amfani da su 176

FA’IDODIN DA KE QASAR LAYI (HASHIYA)

Siffofin mace ta qwarai da hanyoyin faranta wa miji rai 18

Hukuncin auren mace fiye da huxu 20

Faxakarwa game da littafin Tarbiyyatul Awlād na Ulwān 23

Falalar masallaci 30

Huxubar Juma’a ko idi cikin harshen Hausa 31

Fa’idodin auren wuri 48

Matsayin auren dole 49

Ladubban da suka shafi jariri/jaririya 53

Daidaituwar Allah a kan Al’arshi 59

Sharuxxan kalmar shahada da abubuwan da ke warware ta 62

Wajibcin riqo da Alqur’ani da Sunnah 65

Siffofin Ahlus-Sunnah da asasin da’awarsu 67

Matsayin Manzon Allah (SAW) 69

Alamomin son Allah (Maxaukaki) da ManzonSa (SAW) 70

Hukuncin zagin Manzon Allah (SAW) 71

Page 2: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

2

Aqidar Ahlus-Sunnah game da Sahabbai 72

Ma’anar Ahlul-Baiti da matsayinsu a wajen Ahlus-Sunnah 73

Hanyoyin neman na kai 74

Hukunce-hukuncen addu’a 78

Haxarin zunubi ga rayuwar Musulmi 80

Ma’anar bidi’a, da illolinta, da siffofin `yan bidi’a 82

Bidi’o’in da a ke yi a cikin watannin shekara 86

Hukuncin rawa ko kixa a wurin zikiri 89

Rigakafin Shan Inna (Polio) 90

Falalar zikiri da ladubbansa 94

Muhimmancin ilmi a rayuwar Musulmi 97

Wajibcin dogaro da kai, da haramcin maula da barace-barace 100

Hukunce-hukuncen jinin al’ada 108

Kyawawan xabi’u 111

Munanan xabi’u 112

Shan taba sigari 115

Amsa sallamar kirista ko bayahude 118

Falalar Salati ga Manzon Allah (SAW) 121

`Yan’uwantakar Musulunci da hanyoyin tabbatar da ita 126

Ladubban savani 127

Haxarin sanya tufafi ya wuce idon qafa a haqqin maza 138

Sharuxxan hijabin mace Musulma 141

Savanin malamai game da niqabi 142

Fa’idodin sanya hijabi 145

Muhimmancin lokaci a rayuwar Musulmi 147

Haxarin finafinai 148

Matsayin da’awa da yadda a ke gudanar da ita 150

Matsalar talauci da hanyoyin magance ta 153

Munanan aqidun da ke karen-tsaye ga tarbiyya 154

Haqqoqin ma’aura da hanyoyin warware savani a tsakaninsu 164

Matsayin mace da gudummuwar ta a Musulunci 168

Hanyoyin kyautata mu’amala da `ya`ya 172

Matsalar maraici 173

Page 3: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

3

MUQADDIMA

Godiya ta tabbata ga Allah; muna gode maSa, muna neman

taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman

tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu.

Wanda Allah Ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda Ya

vatar babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu

wanda a ke bauta wa bisa cancanta sai Allah, Shi kaxai, ba

Shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa Muhammad

bawanSa ne kuma ManzonSa.

‚Ya ku waxanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa, a

kan haqqin binSa da taqawa, kuma kada ku mutu face kuna

masu sallamawa (Musulmi)‛1

‚Ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da taqawa, Wanda Ya

halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi,

ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa

da mata. Kuma ku bi Allah da taqawa, Wanda kuke roqon

juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta. Lalle ne Allah Ya

kasance, a kanku, Mai tsaro ne.‛2

‚Ya ku waxanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa,

kuma ku faxi magana madaidaiciya. Ya kyautata muku

ayyukanku, kuma Ya gafarta zunubanku. Kuma wanda ya yi

xa'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, ya rabanta, babban

rabo mai girma.‛3

Bayan haka: Lallai, mafi kyawun magana, (shi ne) littafin

Allah, kuma mafi kyawun shiriya, (ita ce) shiriyar

Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).

Kuma mafi munin al'amura, (su ne) abubuwan da aka qago 1 Aal Imrān, 3:102

2 Nisā, 4:1

3 Ahzāb, 33:70-71

Page 4: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

4

(a cikin addini). Domin dukkan qagaggun abubuwa

(waxanda ba su da asali a cikin Alqur'ani da Sunnah) bidi'a

ce, kuma dukkan bidi'a vata ce, kuma dukkan vata

(makomarta) cikin wuta.

Bayan haka:

Daga lokacin da littafi na, Ni’imar Haihuwa da Haqqoqin `Ya`ya a Musulunci, ya fito, mutane sun nuna matuqar

buqatar hanzarta fitar da littafin da na rubuta a kan tarbiyyar

`ya`ya, wanda na yi ishara zuwa gare shi a cikin wancan

littafi, don ya zamanto cikamaki gare shi. Kasancewar,

mutane sun nuna gamsuwarsu da wancan, da kuma

matsuwarsu ga wannan, na ga dacewar in sake yin bitar

littafin, duk da irin yawan ayyukan da ke gabana, domin a

fitar da shi ga `yan’uwa Musulmi, musamman waxanda

suka ba al’amarin tarbiyya muhimmanci.

Na yi amfani da tsarin rubutu a qasar layin da ke qarshen

shafi, wato, hashiya, domin qara fito da waxansu mas’aloli,

da kuma bayyana waxansu fa’idodin da suka shafi vangarori

na musamman a cikin littafin. Ina ba mai karatu shawarar

bin hashiyar littafin a lokacin da ya ke karantawa,

kasancewar za ta taimaka masa wajen kyautata fahimtar

saqon da ke ciki.

Ina roqon Allah (Mai girma da xaukaka) Ya karvi wannan

xan aiki a matsayin ibada, Ya ba ni ladan da Ya tanadar wa

waxanda ke qoqarin karatu da karantar da addininSa, kuma

Ya yi sakamakon alhairi ga waxanda suka taimaka, ta

kowace hanya, wajen tabbatar littafin. Ina roqon Allah Ya

yafe mani kurakuran da ke ciki.

Page 5: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

5

Haka kuma, ina roqon waxanda suka ga kuskure a cikin

littafin, su faxakar da ni, domin a qara kyautata shi idan za a

sake bugawa nan gaba.

Ahmad Bello Dogarawa, Abū Abdir-Rahmān

Al-Muharram, 1430

[email protected]

Page 6: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

6

MA’ANAR TARBIYYA

Kalmar ‘tarbiyya ( )’, kalma ce ta larabci, da bahaushe ya

hausantar, ta yadda da zarar an ambace ta, duk wanda ke jin

Hausa sosai, zai fahimci abin da a ke nufi. Kalmar na da

ma’ana ta harshe, da ma’ana ta Shari’ah.

A harshen larabci, mafi yawan malamai sun ce asalin kalmar

‘tarbiyya’ daga ‘ ’ ne, wato qaruwa da daxuwa, kamar

yadda ma’anar ta zo a cikin Alqur’ani [Hajj, 22:5; Baqarah, 2:276; Rūm, 30:39; Hāqqah, 69:10]; ko kuma daga fi’ilin

‘ ’, wato, ya qara, ya daxa, ko kuma ya rena, kamar yadda

ta zo a cikin Alqur’ani [Isrā, 17:24; Shu’arā, 26:18]. A bisa

waxannan bayanai, kalmar ‘tarbiyya’ na nufin reno, da

kulawa, da ladabtarwa, da karantarwa, da kyautatawa, da

xaukar matakin gina qaramin yaro, kaxan-kaxan, har ya

zama cikakken mutum, a vangaren hankali da tunani, kuma

ya zamanto kammalalle, a wajen mu’amala da wayewa.

A shari’ance, ‘tarbiyya’ na nufin: tattali, da kintsa mutum

domin ya samu cikakkiyar rayuwar da ke qunshe da

walwala; ya zamanto mai qaqqarfar jiki; mai cikakken

hankali; mai cikakken tsarin gudanarwa; mai tausasawa a

cikin mu’amalarsa; qwararre a cikin ayyukansa; kuma mai

jawo amfani ga waninsa. Tarbiyya a musulunci ta qunshi

kyautata al’amarin musulmi, da inganta yanayinsa don ya

zamanto cikakke, a vangaren lafiyarsa, da hankalinsa, da

aqidarsa, da ruhinsa, da xabi’unsa, da mu’amalarsa, da

wayewarsa, ta hanya mafi dacewa, kuma a bisa karantarwar

addinin Musulunci.4

4 Sālih ibn Aliyyu Abu ‘Arrād, At-Tarbiyyatul Islāmiyyah: Al-

Musxalah wal Mafhum, (1426), shafi na 36-37,

http://saaid.net/Doat/arrad/17.htm

Page 7: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

7

Bincike ya nuna cewa kalmar ‘tarbiyya’, a yadda a ke

amfani da ita yanzu, ba ta shahara a wajen magabata ba.

Kalma ce da aka fara amfani da ita daga baya. Wannan yasa,

magabata ba su yi amfani da kalmar ba, a cikin rubuce-

rubucensu. A magana mafi qarfi, an fara amfani da kalmar

‘tarbiyya’ ce a cikin qarni na ashirin.5

Kafin wannan lokaci, malamai sun yi amfani da kalmomi

mabambanta, waxanda ke xaukar ma’ana kusan iri xaya da

ma’anar kalmar tarbiyya a yanzu. Daga cikin kalmomin da

aka yi amfani da su, a wancan lokaci, akwai:6

1. At-Tanshi’ah ( ): reno da kulawa ta musamman.7

2. Al-Islāh ( ): canzawa zuwa ga mafifici, da kulawa ta

musamman, da karkata zuwa ga abin da ya fi kyau.

3. At-Ta’adīb ( ): yin ado da siffofi masu kyau, kuma

da koyar da xabi’u da halayen girma, da nisantar

munanan abubuwa.

4. At-Tahzīb ( ): tsaftace zuciyar mutum, da tsarkake

ta, da daidaita ta a kan tarbiyya, a bisa ayyuka masu

daraja, da kyawawan maganganu.8

5. At-Taxhīr ( ): tsarkake rai daga dauxa da abubuwan

qasqanci.

6. At-Tazkiyyah ( ): tsaftace zuciya da tsarkake ta daga

munanan xabi’u da miyagun halaye.

5 Muhammad Munīr Marsī, At-Tarbiyyatul Islāmiyyah: Usuluhā wa

Taxawwuruhā fil Bilādil ‘Arabiyyah, (‘Aalamul Kutub, Al-Qāhirah,

1421), shafi na 48 6 Sālih ibn Aliyyu Abu ‘Arrād, At-Tarbiyyatul Islāmiyyah: Al-

Musxalah wal Mafhum, shafi na 4-18 7 Ibn Khaldun ya yi amfani da wannan Isxilāhi a cikin littafinsa

Muqaddimah 8 Ibn Maskawih ya yi amfani da kalmar a littafinsa Tahzībul Akhlāq wa

Taxhīrul A’arāq, da Al-Jāhiz, a cikin Tahzībul Akhlāq

Page 8: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

8

7. At-Ta’alīm ( ): ilmantarwa da zaburarwa zuwa ga

neman ilmi.

8. As-Siyāsah ( ): jagoranci da zurfafa tunani, kafin a

zartar da abin da za a yi.9

9. An-Nushu wal Irshād ( ): shiryarwa zuwa ga

abu mai kyau, ta hanyar lalama da tausasawa.10

10. Al-Akhlāq ( ): gyara xabi’u, da miqar da

karkatattun halaye.11

Kowane xaya daga cikin waxannan kalmomin da suka

shahara a cikin littafan magabata, ya qunshi sashen

ma’anonin da kalmar ‘tarbiyya’ ta qunsa a yau. Ke nan, a

yadda a ke amfani da ita a yanzu, kalmar ‘tarbiyya’ ta

qunshi dukkan ma’anonin da waxancan kalmomi suka

qunsa.

Tarbiyyar Musulunci na da abubuwan da ta kevanta da su,

kuma babu wani tsarin tarbiyya a duniya da ya qunshi irin

abubuwan da tarbiyyar Musulunci ta qunsa. Wannna yasa,

duk da cewa al’ummomin duniya na qoqarin canza tsarin da

su ke bi wajen tarbiyyar mutanensu a halin yanzu, al’ummar

musulmai ba ta buqatar sauyi a cikin nata tsarin.

Tsarin tarbiyyar Musulunci ya kevanta da waxannan

abubuwa:

1. Tsari ne daga Allah da aka gina a bisa asasin Musulunci.

Allah (Maxaukaki) Shi ne da kanSa Ya tarbiyyantar da

malamin farko ga wannan al’umma, wato, Manzon Allah

9 Ibn Al-Jazzār Al-Qairawāni ya yi amfani da wannan isxilahi a littafin

da ya rubuta a kan tarbiyya, Siyāsatu-s-Sibyān wa Tadbīruhum 10

Ibnul Jauzī ya sanya wa littafinsa suna Laftatul Kabad ila Nasīhatil Walad, shi kuma Al-Hārith Al-Mahāsabī ya sanya wa littafinsa suna

Risālatul Mustarshidīn 11

Abu Bakr Al-Aajurri ya sanya wa littafinsa suna Akhlāqul Ulamā

Page 9: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

9

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), wanda shi

kuma ya tarbiyyantar da al’ummarsa a bisa shiriya da

karantarwar da Allah (Maxaukaki) Ya yi masa.

2. Gamammen tsari ne, da ya dace da dukkan xan Adam,

ba tare da kevantuwa ga wani gari ko wata al’umma ko

jinsi ba.

3. Tsari ne da ke lazimta wa kowane mutum neman

ilminsa, kuma ya ke lazimta wa kowane malami xaukar

xawainiyar karantar da shi.

4. Tsari ne da ya ba da cikakkiyar kulawa ga dukkan

vangarorin al’umma, da dukkan fannonin ilmi mai

amfani, kuma da dukkan matakan rayuwa.

5. Tsari ne da ke karantar da tsakaitawa, ba tare da

zurfafawa ko taqaitawa ba.

6. Tsari ne mai xorewa, ba tare da yankewa ba.

7. Tsari ne da ya qulla alaqa mai qarfin gaske a tsakanin

tarbiyya da ilmi; ilmi da aiki; rayuwar mutum xaya da

rayuwar al’umma gaba xaya.

8. Tsarin tarbiyya ne da ya kula da al’amuran duniya da

lahira baki xaya.

9. Tsari ne da ya dace da yanayi, da kuma xabi’un da aka

halicci xan Adam a kansu.

10. Tsari ne da ke bi sannu-sannu wajen kai wa ga manufa.

HUKUNCIN TARBIYYA

Tarbiyyar `ya`ya a kan imani da ibada; da xabi’u da

mu’amala; da kula da lafiyar jiki da hankali da tunani; da

tsarin zamantakewa, wajibi ne da Allah Ya xora a kan iyaye

da dangi, da malamai, da shugabanni, da sauran jama’a.

Tarbiyya ba ta samuwa a cikin al’umma, sai kowane xaya

daga waxannan vangarori ya ba da gudummuwarsa, kuma

ya sauke wajibinsa game da tarbiyya.

Page 10: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

10

Iyaye su ne a kan gaba wajen wannan al’amari muhimmi,

kasancewar su ne suka haifi `ya`ya, kuma suka fi zama tare

da su. Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ba iyaye amanar

`ya`yansu, don su kula da su, su tsare su daga faxawa cikin

haxari, kuma su yi masu kyakkyawar tarbiyya. Allah (Mai

girma da xaukaka) Ya ce: ‚Ya ku waxanda suka yi imani!

Ku kare wa kanku da iyalinku wata wuta (da) makamashinta mutane da duwatsu ne…‛

12 Aliyyu ibn Abi Xālib (Allah Ya

yarda da shi) ya fassara wannan ayar da cewa: ‘Ku ladabtar

da su, wato, ku yi masu tarbiyya, kuma ku ilmantar da su’. Haka kuma, Qatādah (Allah Ya jiqansa) ya fassara da cewa:

‘Ku umurce su da yin xa’a ga Allah, kuma ku hana su savon

Allah’.13

Haka nan, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) ya ce: ‚Dukkanku masu kiwo ne, kuma za a

tambayi kowa game da kiwonsa: shugaba mai kiwo ne a kan

mutanensa, kuma za a tambaye shi game da kiwonsa.

Mutum (magidanci) mai kiwo ne ga iyalinsa (matansa, da

`ya`yansa, da sauran waxanda ke qarqashinsa), kuma za a

tambaye shi game da kiwonsa. Mace mai kiwo ce ga gidan

mijinta da `ya`yansa, kuma za a tambaye ta game da su.

Bawa makiyayi ne ga dukiyar mai gidansa, kuma za a

tambaye shi game da kiwonsa. Kowannenku makiyayi ne,

kuma za a tambaye shi game da kiwonsa.‛14

`Yan’uwa da dangi na da babban nauyi wajen tabbatar da

tarbiyyar qannensu da danginsu da `ya`yan `yan’uwansu,

kasancewar su ne mafi kusa da su bayan iyayen da suka

haife su. Kasancewar qanne da `ya`yan `yan’uwa na

dangantuwa zuwa gare su, rashin ba da gudummuwarsu

12

Tahrīm, 66:6 13

Ibn Kathīr, Tafsīrul Qur’ānil Azhīm, (Maktabah Anas ibn Mālik,

Makka), 4/362 14

Bukhari da Muslim

Page 11: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

11

wajen cinma manufar tarbiyya, da tabbatar da ita gare su, na

iya jawo matsala, musamman idan yara suka aikata wani

mummunar abu. Duk wani aikin assha, da danginsu ko

`ya`yan `yan’uwansu za su aikata, zai shafi mutuncinsu, da

matsayinsu a cikin al’umma. Wannan yasa, Musulunci ya

wajabta wa dangin mutumin da ya yi kisan kai bisa kuskure,

yin haxaka da karo-karo wajen biyan kuxin diyya, idan

wanda ya yi kisan ba shi da dukiyar da zai biya da kansa.15

Ke nan, haxari ne babba ga `yan’uwa, su yi sakaci wajen

tarbiyyar `yan’uwa da danginsu na jini.

Dangane da malamai, Allah (Mai girma da xaukaka) Ya

siffanta su da Rabbaniyyun, wato, malamai na Allah,

waxanda ke yi wa mutane tarbiyya a kan ilmi.16

An ruwaito daga Aliyu ibn Abi Xālib (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‚Su

ne waxanda ke qosar da mutane hikimomi, kuma su ke yi wa mutane tarbiyya a kansu.‛ Haka nan, Mujāhid (Allah Ya

ji qan shi) ya ce: Rabbaniyawa su ne waxanda ke koya wa

mutane qananan ilmi, kafin manya.‛17

Gudummuwar malamai a fagen tarbiyyar al’umma na

qunshe cikin qoqarin yaxa sahihin ilmi; da karantar da

al’umma, da shiryar da ita, da yin mata saiti; da yaqar

bidi’a; da tsaftace ilmi daga hadisai masu rauni, da hadisan

qarya, da ra’ayoyin da babu dalili a kansu; da tarbiyyantar

da al’umma a kan tataccen ilmi; da qalubalantar `yan bidi’a

15

Ana biyan diyya idan an yi kisan ganganci, kuma waliyyan wanda

aka kashe suka ce za su karvi diyya, maimakon a kashe mutumin da ya

kashe masu xan’uwa. Haka kuma, waliyyan mamacin na iya yafe

diyyar gaba xaya, ba tare da la’akari da ko kisan ganganci ne ko na

kuskure ba. Sai dai kuma ko da an yafe diyya, dole ne wanda ya yi

kisan ya `yanta bawa ko ya yi azumin wata biyu, a matsayin kaffara. 16

Aāl Imrān, 3:79; Mā’idah, 5:44 17

Ahmad ibn Abdil-Halīm ibn Taimiyyah, Majmu’ul Fatāwā,

(Maktabah Ibn Taymiyah), 1/62

Page 12: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

12

da kuma bidi’o’insu, ta hanyar bayani da rubutu bisa hujjoji;

da kare martabar Alqur’ani da Sunnah, ta hanyar mayar da

martani ga vatattun mutane, da zindiqai, da munafukai, da

sauransu.18

Shugabanni su ne ke xaukar dukkan matakan da suka dace

don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da bin

doka da oda a tsakanin mutane.19

Haka nan, wajibi ne su

tabbatar da tsaro ga dukiya da rayuka da mutunci da hankali

da addinin jama’a. Waxannan abubuwan ba za su tabbata ba

har sai shugabanni sun yi umurni da kyakkyawa, da hani da

mummuna, kuma sun ba da goyon baya, da qarfafa gwiwa

wajen tarbiyyar mutane. Allah (Mai girma da xaukaka) Ya

ce: ‚Waxanda su ke idan muka ba su iko (mulki) a cikin

qasa, sai su tsai da salla, kuma su bayar da zakka, kuma su

yi umurni da abin da aka sani, kuma su hana daga abin da ba

a sani ba…‛20

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce: ‚…shugaba mai kiwo ne a kan

mutanensa, kuma za a tambaye shi game da kiwonsa…‛.21

Haka kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce: ‚Babu wani bawa da Allah zai ba

shi shugabancin mutane, sannan, ya mutu, yana mai

ha’intarsu, face Allah Ya haramta aljanna gare shi.‛22

Sauran mutanen gari na da rawar da za su taka wajen

tabbatar da tarbiyyar al’ummarsu. Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya wajabta wa muminai

canza duk wani mummunan aiki da suka ga ana aikatawa,

18

www.islamweb.net, Daurul Ulamā fit Tarbiyyatil Islāmiyyah, 98319 19

Wani daga cikin magabata yana cewa:

‚Lallai Allah Yana gusar da varna ta hanyar mulki, irin gusarwar da ba

Ya yi da Alqur’ani‛ 20

Hajj, 22:41 21

Bukhari da Muslim 22

Bukhari da Muslim

Page 13: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

13

gwargwadon ikonsu.23

Haka kuma, Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tabbatar da cewa

addinin Musulunci ya qunshi nasiha ga kowane musulmi.24

Wannan ke nuna cewa kowane mutum a cikin al’ummarsa,

yana da haqqin taimakawa wajen tabbatar da daidaituwar

al’amura.

Sakaci da rashin tsayuwa da al’amarin tarbiyya, ta hanyar

umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, na haifar da

matsaloli ga al’umma baki xaya, waxanda suka haxa da:

Bijirowa ga fushin Allah da azabarSa a duniya. Allah

(Mai tsarki da xaukaka) Ya ce: ‚Kuma ku ji tsoron fitina

wadda ba ta samun waxanda suka yi zalunci daga gare

ku, a keve, kuma ku sani, lalle ne Allah Mai tsananin

uquba ne.‛25

Dangane da fassarar wannan aya, Ibn Kathīr ya ciro magana daga Ibn Abbās (Allah Ya yarda

da shi) ya ce: ‚Allah Ya umurci muminai da su yi inkarin

dukkan mummuna, ko kuma Ya lulluve su da azaba.‛26

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Idan mutane suka qi hana azzalumi aikata

zalunci, ba wuya Allah Ya lulluve su da uquba.‛27

Haka

kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce: ‚Babu mutanen da wani daga cikinsu zai

aikata savo, amma su qyale shi, alhali suna da ikon

hanawa, face Allah Ya jarabe su, kafin su mutu.‛28

Qasqanci da wulaqanci za su lulluve su, kuma varna da

gurvacewar al’amura za su bayyana a cikin al’umma.

23

Muslim 24

Muslim 25

Anfāl, 8:25 26

Ibn Kathīr, Tafsīrul Qur’ānil Azhīm, 2/185 27

Abu Dāwud, da Tirmidhi da Ibn Mājah 28

Abu Dāwud da Ibn Mājah

Page 14: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

14

Rashin amsa addu’a, kamar yadda Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Ku yi

umurni da kyakkyawa, kuma ku yi hani da mummuna,

tun gabanin ku yi addu’a, amma a qi amsa maku.‛29

MUNAFAR TARBIYYA A MUSULUNCI

Tarbiyyar `ya`ya, ta hanyar koya masu kyawawan halaye da

xabi’u nagari, da karantar da su ilmin addini da ilmin sana’a

yadda ya dace, don su zamanto masu kishin zuci da dogaro

da kai, abu ne da Musulunci ya ba muhimmanci sosai. Da

kyakkyawar tarbiyya ce a ke samar da matasa na gari,

waxanda za su zama tubalan gina qaqqarfar al’umma, masu

kishin Musulunci, masu tsoron Allah, waxanda al’umma za

ta yi alfahari da su, kuma waxanda za su tabbatar da

dokokin Allah a kan qasa.

Haka kuma, da kyakkyawar tarbiyya ce a ke samar da xa na

qwarai, da zai zamanto sanyin ido ( ) ga iyayensa, a nan

duniya, kuma ya yi masu addu’a, idan suka riga shi mutuwa.

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ce: ‚Kuma waxanda su ke

cewa, ‚Ya Ubangijinmu! Ka ba mu sanyin idanu daga

matanmu da zuriyarmu, kuma Ka sanya mu shugabanni ga

masu taqawa.‛30

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce: ‚Idan xan Adam ya mutu, duk

ayyukansa sun yanke, ban da abubuwa guda uku: sadaka

mai gudana; da ilmin da ya bari ana amfani da shi; da xa na

qwarai, da zai yi masa addu’a.‛31

29

Ahmad da Ibn Mājah 30

Furqān, 25:74 31

Bukhari da Muslim

Page 15: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

15

Tarbiyyar `ya`ya a Musulunci na da manufofi guda shida:

1. Qoqarin tabbatar da manufar halittar xan Adam. Allah

(Mai tsarki da xaukaka) Ya bayyana cewa Ya halicci

mutane da aljannu ne don su bauta maSa: ‚Kuma Ban

halitta aljannu da mutane ba sai domin su bauta Mini.‛32

Tarbiyya a Musulunci ta qunshi xaukar matakan da suka

dace wajen kyautata al’amarin `ya`ya, da inganta

yanayinsu, a vangaren lafiya, da hankali, da aqida, da

ruhi, da xabi’u, da mu’amala, da wayewa, domin su

zamanto bayin Allah (Mai tsarki da xaukaka) tsantsa,

waxanda za su bi dokokinSa, kuma su tabbatar da

tsarinSa a bayan qasa.

2. Kai wa ga manyan xabi’un girma da halayen qwarai,

waxanda za su taimaka wajen ciyar da al’umma gaba, da

yin mata jagoranci wajen tabbatar da manufar rayuwa.

3. Tattali da qintsi ga rayuwar duniya da lahira, da bin

hanyoyin da suka dace domin samun daddaxar rayuwa a

nan duniya, da babban rabo a lahira.

4. Koyar da hanyoyin dogaro da kai, da kishin addini, da

qoqarin jawo amfani ga al’umma da tunquxe cuta gare

ta, da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da

tabbatar da tsaro da kariya ga addini da rayuwa da

dukiya da mutunci da hankali.

5. Gina mafi alhairin al’umma mumina wadda za ta kawo

amfani da jawo ci gaba ga kowa, kuma ta tunkuxe varna

da aibu daga kowa.

32

Zāriyāt, 51:56

Page 16: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

16

6. Tabbatar da tsarin gudanarwa da wayewa mafi havaka,

da zaburar da mutane a kan tattalin arziqi mafi bunqasa,

da ilmantar da al’umma tsarin ci gaba da kawo zaman

lafiya da walwala da kwanciyar hankali, da koyar da

shugabanci da jagorancin da ke cike da adalci.

HIMMAR MAGABATA WAJEN TARBIYYAR `YA`YA

Magabata, a cikin al’ummar Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) da waxanda suka gabace ta, sun

ba al’amarin tarbiyyar `ya`yansu matuqar muhimmanci, ba

kawai qananan yara ba, har ma waxanda suka manyanta

daga cikin `ya`yansu. Magabata ba su gushe ba suna

qoqarin tarbiyyantar da su a kan aqida da ibada, da

kyawawan xabi’u da mu’amala, da kyautata alaqa da Allah

(Mai tsarki da xaukaka).

Allah (Mai tsarki da xaukaka) Ya ba mu labarin Annabi Ibrāhīm da `ya`yansa (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare su), da irin matakan da ya xauka wajen ganin ya

tarbiyyantar da su, duk da cewa Allah (Mai tsarki da xaukaka) ya zave su da Annabta.

33 Annabi Ibrāhīm (amincin

Allah ya tabbata a gare shi) ya roqi Allah (Mai tsarki da

xaukaka) Ya azurta shi da salihan `ya`ya;34

Ya nisantar da

shi tare da su daga bautar gumaka;35

kuma Ya sanya shi da zuriyyarsa masu tsai da salla.

36 Haka kuma, Ibrāhīm

(amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roqi Allah (Mai

girma da xaukaka) Ya sanya zuriyyarsa daga cikin masu yin

jagoranci a cikin imani da taqawa da haquri da da’awa;37

33

Maryam, 19:54; Sāffāt, 37:112 34

Sāffāt, 37:100 35

Ibrāhīm, 14:35 36

Ibrāhīm, 14:40 37

Baqarah, 2:124

Page 17: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

17

kuma Ya sanya su masu sallamawa ga Allah (Mai girma da xaukaka).

38 Bayan wannan, Annabi Ibrāhīm (amincin Allah

ya tabbata a gare shi) ya yi wa `ya`yansa wasiyyar su

tabbata a kan addini har zuwa mutuwa.39

Domin ya qara tabbatar da tarbiyyar `ya`yan shi a aikace, Annabi Ibrāhīm ya kasance yana bin diddigin al’amuransu,

hatta bayan sun girma. Misali, Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ba da labarin ziyarar ba zato, wadda Annabi Ibrāhīm ya yi wa xansa Annabi

Ismā’īl (amincin Allah ya tabbata a gare shi) har sau biyu,

domin ya gane wa idonsa halin da xansa ke ciki tare da iyalinsa. A karon farko da Ibrāhīm (amincin Allah ya

tabbata a gare shi) ya kai ziyarar, ya bar wa xansa Ismā’īl

(amincin Allah ya tabbata a gare shi) saqon cewa ya saki

matarsa, kasancewar bai dace ta ci gaba da zama matarsa ba. A karo na biyu kuwa, Ibrāhīm (amincin Allah ya tabbata a

gare shi) ya bar wa xansa wasiyyar cewa ya riqe matar da ya

auro bayan ya saki waccan ta farko, kuma ya kula da ita

sosai.40

Ke nan, a ziyararsa ta farko, Ibrāhīm (amincin Allah ya

tabbata a gare shi) ya fahimci cewa matar da Ismā’īl

(amincin Allah ya tabbata a gare shi) ke aure ba ta dace da

shi ba, kasancewar ba ta da godiya, da sanin ya kamata,

kuma ba ta da rufin asiri a cikin zamantakewarta da mijinta.

Babu shakka, aibi ne babba a samu mace tana da irin

waxannan halaye, musamman saboda mummunar tasirinsu a

kan tarbiyyar `ya`ya. Lokacin da ya koma a karo na biyu, Ibrāhīm (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya fahimci

38

Baqarah, 2:128 39

Baqarah, 2:132 40

Bukhari

Page 18: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

18

cewa xansa ya dace da mace ta qwarai ( ),41

wadda

za ta iya faranta ran mijinta,42

kuma ta taimaka masa wajen

tarbiyyar `ya`ya.

Haka kuma, Allah (Maxaukaki) Ya ba mu labarin addu’ar

da Annabi Zakariya (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya

yi dangane da samun zuriyya mai kyau,43

wadda za ta yi aiki tuquru domin yardar da Allah;

44 da himmar Annabi Ismā’īl

(amincin Allah ya tabbata a gare shi) wajen umurtar iyalinsa

da salla da zakka da tsare haqqoqin Allah (Maxaukaki);45

da dogon wa’azi da gargaxin da Luqmān

46 ya yi wa xansa a

41

Mace ta qwarai ita ce wadda idan mjinta ya kalle ta, zai yi farin ciki;

idan ya umurce ta, za ta yi biyayya; idan ba ya nan, za ta kiyaye

mutuncinta da dukiyarsa; kuma idan ya yi rantsuwa a kanta, za ta

kuvutar da shi. 42

Faranta wa miji rai ya qunshi abubuwa kamar haka: (1) kyakkyawar

tarba a duk lokacin da miji ya shigo gida (2) lazimtar qamshi mai daxi

da gyara jiki da cava ado (3) daxaxa murya da tsara magana (4)

qwarewa wajen kwanciyar aure da gaggauta ba da kai idan aka fahimci

miji yana da buqatar jima’i (5) wadatar zuci, da yin haquri da kaxan, da

rashin nuna kwaxayin abin duniya (6) godiya da yabawa ga miji a kan

xan abin da ya samu (7) kasancewa tare da miji, musamman a lokacin

tsanani, da taimaka wa miji da kuxi ko kaya, idan da buqatar yin haka

(8) qoqarin zarce sauran mata wajen ilmi da iya abinci da tsafta da

aikin gida da sauransu (9) biyayya a cikin duk abin da bai sava wa

Shari’a ba (10) sanya miji ya huce idan ya yi fushi, ta hanyar ba da

haquri da rarrashi da rashin yin jayayya (11) tsare mutuncin miji da

kulawa da `ya`yansa da gidansa da dukiyarsa, musamman idan ba ya

nan (12) girmama `yan’uwansa da taimaka masu (13) qarfafa masa

gwiwa a cikin biyayya ga Allah (14) tattali, da yin tsuwurwurin

dukiyarsa. 43

Aal Imrān, 3:38 44

Maryam, 19:6 45

Maryam, 19:54-55 46

Luqmān ba Annabi ba ne, kasancewar babu wani dalili a cikin

Alqur’ani ko hadisin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) da ya tabbatar da annabtarsa. Aqidar Ahlus-Sunnah ta ginu a

kan cewa ba a iya tabbatar da annabta ga wani mutum sai ta hanyar

Page 19: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

19

kan kaxaita Allah (Mai girma da xaukaka) da bauta, da

wajibcin barin shirka, da muhimmancin taqawa da

muraqaba (kiyaye Allah), da wajibcin tsai da salla da yin

umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, da haramcin

wulaqanta mutane ko yin taqama da alfahari gare su, da

sauransu.47

Bayan wannan, ya tabbata cewa Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) da sahabbansa (Allah

Ya yarda da su) sun kasance masu matuqar damuwa da

kulawa game da tarbiyyar `ya`yansu, manya da qanana.

Misali, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tafi wajen `yarsa Fāximah (Allah Ya yarda da

ita) domin ya sanar da ita cewa zikirorin kwanciyar barci ya

fi muhimmanci a kan kuyangar da ta ke nema a wajensa.48

Kuma ya tabbata cewa yana zuwa gidan Aliyyu ibn Abi Xālib (Allah Ya yarda da shi), ya tashe su daga barci domin

su yi qiyamullaili, wato, sallar dare.49

Haka kuma, yana zuwa ya umurci `ya`yansa su fita sallar īdi.

50

A vangaren sahhabai (Allah Ya yarda da su), ya tabbata

cewa Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ya yi amfani da

sanda wajen ladabtar da `yarsa A’isha (Allah Ya yarda da

ita), matar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) kuma uwar muminai, a lokacin da ta zaunar da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

nassi qarara. A magana mafi qarfi, Luqmān xaya daga cikin bayin

Allah ne, waxanda Allah (Maxaukaki) ya yi wa baiwar ilmi, da hikima,

da fasaha, da himmar tarbiyyar `ya`ya. Duba tafsirin Al-Qurxubi, da Ibn Kathīr, da As-Sa’adiy, a qarqashin Luqmān, 31:13, 16-19, don

qarin bayani. 47

Luqmān, 31:13, 16-19 48

Bukhari 49

Bukhari 50

Ahmad

Page 20: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

20

a wajen da babu ruwa, saboda ba ta ga abin wuyanta ba.51

Haka kuma, Umar (Allah Ya yarda da shi) ya shiga wajen

`yarsa Hafsah (Allah Ya yarda da ita), matar Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), domin ya

faxakar da ita cewa kada kishinta52

ga A’isha ya hana ta

51

Muslim 52

Kishi a tsakanin mata yana tasowa ne daga lokacin da namiji ke da

mace fiye da xaya a qarqashinsa. Auren mace fiye da xaya har zuwa

huxu, abu ne da aka shar’anta bisa nassin Alqur’ani da Sunnah da

haxuwar malamai (Ijma’i). Haka nan, auren mace fiye da xaya ya

tabbata a cikin tarihin Annabawa da Manzanni da sahabban Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), kuma ya dace da

xabi’ar xan Adam.

Nassin Alqur’ani da Sunnah, da Ijma’i, da Qiyasi duk sun taqaita

wa kowane musulmi auren mata huxu kawai, ba tare da wuce haka ba.

Haka nan, fatawoyi da tarihi da ayyukan sahabbai (Allah Ya yarda da

su) da tabi’ai da waxanda suka bi hanyarsu, da fahimtar dukkan

malaman tafsiri da malaman hadisi da malaman fiqihu da malaman

usuli sun tabbatar da cewa haramun ne ga kowane musulmi ya tara

mace fiye da huxu a qarqashinsa a lokaci xaya, in ban da qwarqwara, a

lokacin jihadin da aka yi a tsakanin musulmi da kafirai a bisa tsarin da

Alqur’ani da Sunnah da Ijma’i suka tabbatar.

Auren mace fiye da xaya na da dalilai masu yawa. Daga ciki, akwai:

(1) matsalar jinin al’ada ko jinin haihuwa da ke sabbaba wa waxansu

majaze takura (2) mata sun fi maza yawa a duniya (3) kowace macen

da ta balaga tana shirye da yin aure da zarar ta samu miji, savanin

maza, kasancewar namiji sai ya yi shiri da tanadi na musamman (4)

larurar rashin haihuwa (5) yawan tafiye-tafiye.

Sharuxxan auren mace fiye da xaya su ne: ikon yin adalci a tsakanin

mata; da amintuwa daga faxawa cikin fitinar addini a sanadiyyar qara

aure; da ikon biya masu buqatar sha’awa; da ikon ciyarwa. Wanda bai

cika waxannan sharuxxa ba, bai dace ya auri mace fiye da xaya ba.

Kishi a tsakanin mata wani abu ne na xabi’a. A mafi yawan lokaci,

mata na yin kishi ne a tsakaninsu saboda rashin tabbas game da

makomarsu idan miji ya qaro aure; da tsoron juya masu baya ko

wulaqanci daga miji; da tsoron rashin adalci a tsakaninsu da amarya; da

rashin jin daxin yawaita ambaton kishiya a gabansu; da karkatar

`yan’uwan miji da abokansa ga wata daga cikin matan.

Page 21: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

21

Ko da ya ke kishi xabi’a ce ta mata, kuma wani abu da ba za a iya

raba mata da shi ba, akwai abubuwan da ba su halatta mace ta aikata ba

saboda kishi: (1) cutar da miji ko hana shi yin sukuni, ko kuma cutar da

`ya`yansa, a matsayin martani a kan sabon auren da ya yi (2) cin

mutunci da yin vatanci ga kishiya (3) cutar da kishiya ta hanyar sihiri

ko tsafi (4) neman a saki kishiya (5) ruxar kishiya ta hanyar nuna mata

kamar miji na fifita ta a kan abokiyar zamanta ko kuma yana bata wani

abu a voye.

Yana daga varnar da aka shigar a cikin mas’alar auren mace fiye da

xaya, da’awar da waxansu ke yi cewa ya halatta mutum ya ajiye mace

fiye da huxu a qarqashinsa a lokaci xaya, a matsayin matan aure.

Asalin wannan da’awar a Nijeriya, ta samo asali ne daga `yan qala-

qato, waxanda babu ruwansu da hadisan Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi). Daga baya, sai aka samu labarin

mutumin da ya ajiye matan aure fiye da tamanin a lokaci xaya. Da aka

ce masa ya zavi guda huxu daga cikinsu, ya saki sauran, sai ya ce ‘an

takura shi ne saboda ba shi da gata, domin kuwa waxansu shaihunnan

xariqa da sarakunan gargajiya na da mata barkatai a qarqashinsu’. Ana

cikin wannan kace-nace, kwatsam sai ga wani matashin xalibin ilmi a

garin Bidda, jihar Neja, da ke da’awar Sunnah-Salafiyyah yana iqirarin

cewa babu ijma’i a kan haramcin zaman aure tare da mace fiye da guda

huxu a lokaci xaya, yana mai kafa hujja da bayanan da ya gani a cikin littafin Nailul Awxār da tafsirin Fat-hul Qadīr na Imam ash-Shaukāni,

da kuma bayanan da Jamāluddīn Al-Qāsimi ya yi a cikin tafsirinsa,

Mahāsinut Ta’awīl, cewa babu ijma’i a kan wannan mas’alar.

Duk da cewa an shirya taron qara wa juna ilmi na kwana biyu, kuma

aka gayyaci mutane daga wurare dabam daban na wannan qasa domin

su gabatar da maqala/qasidu a cikin harshen Hausa da Turanci da

Nufanci dangane da wannan mas’ala, wannan xalibi ya qi zuwa, duk da

an ba mu labarin cewa kafin ranar taron, ya yi alqawarin zai halarta.

Alhamdu Lillah, ina daga cikin waxanda suka gabatar da maqala a

wajen taron. Haka kuma, Dokta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, da Shaikh Abdul-Wahhāb Abdullah Kano, da Mal. Aminu Gusau, da

Mal. Auwal Maiduguri, da wakilin kwamitin Shari’a na qasa, da

waxansu `yan’uwa daga wurare dabam daban sun gabatar da bayanai

gamsassu a wajen taron. A qarshe, mutanen Bidda da sauran musulmin

Nijeriya, waxanda suka samu labarin sakamakon taron, sun gamsu

cewa Alqur’ani da Sunnah, da Ijma’i, da Qiyasi, da fatawoyi da tarihi

da ayyukan sahabbai (Allah Ya yarda da su) da tabi’ai da waxanda

suka bi hanyarsu, da fahimtar dukkan malaman tafsiri da malaman

Page 22: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

22

kwanciyar hankali, ko ya kai ta ga aikata abin da bai dace

ba.53

Waxannan misalai na nuna irin muhimmancin da magabata

suka ba al’amarin tarbiyya, da irin matakan da suka xauka

wajen tarbiyyantar da `ya`yansu da matansu da sauran

waxanda ke qarqashinsu. Abin sha’awa shi ne, magabata ba

su taqaita tarbiyya a kan qananan yara ba, a’a, har manya

ana yin masu tarbiyya gwargwadon yadda kowannensu ke

buqata.

hadisi da malaman fiqihu da malaman usuli da malaman tarihi duk sun

tabbatar da haramcin ajiye matan aure fiye da huxu a lokaci xaya, kuma maganar da Shaukāni da Jamāluddīn Al-Qāsimi suka yi, babu

hujja a cikinta. Hasali ma, ra’ayin da suka danganta wa wasu daga cikin

malaman Shi’a, kuskure ne, kasancewar bai tabbata daga gare su ba.

Kasancewar an rushe dukkan rikice-rikice da hayaniyar da ya ke

taqama da su, sai kwatsam ya fasa wani sabon bom; ya ce wai Umar ibn Khaxxāb (Allah Ya yarda da shi) ya mutu ya bar matan aure fiye da

huxu a qarqashinsa! Gaskiya ne cewa Umar (Allah Ya yarda da shi) ya

auri mace fiye da huxu a cikin rayuwarsa, amma kuma, bai tava zama

tare da mace fiye da huxu ba a lokaci xaya. Sanannen abu ne cewa, a

cikin sahabbai, akwai waxanda suka auri mata da yawa a cikin

rayuwarsu, amma ba su tava zama da guda uku ba ma a lokaci xaya,

ballantana huxu ko fiye da huxu. 53

Bukhari

Page 23: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

23

VANGARORIN TARBIYYA54

54

Mafi yawan bayanan da ke qarqashin wannan sashe na ciro su ne daga littafan Abdullah Nāsih Ulwān, Tarbiyyatul Awlād fil Islām,

(Dārus-Salām lix-Xibā’ah wan-Nashr wat-Tauzi’ wat-Tarjamah, Al-

Qāhirah, 2005), shafi na 132-137; da Mas’uliyyatut Tarbiyyatil Jinsiyyah min Wijhati Nazaril Islam, (Dārus-Salām lix-Xibā’ah wan-

Nashr wat-Tauzi’ wat-Tarjamah, Al-Qāhirah, 2003).

Littafin Tarbiyyatul Awlād fil Islām na Abdullah Nāsih Ulwān na

daga cikin littafan tarbiyya waxanda suka shahara a cikin al’umma,

kuma ana yawan karantar da shi a masallatai da wuraren karatu. Nazari

cikin littafin yana nuna cewa, mawallafinsa, Allah Ya jiqansa, ya yi

kura-kurai masu yawan gaske, musamman a vangarorin tauhidi da

aqida da manhaj. Wannan yasa malamai suka yi rubuce-rubuce don

faxakarwa game da matsalolin da ke cikin littafin, kuma suka yi gyare-

gyaren da ya kamata, don nasiha ga al’ummar musulmai. Misali, Ihsān al-Utaibī, a cikin littafinsa, Kitāb Tarbiyyatil Awlād fil Islām fi Mīzānin Naqdil Ilmī, ya bayyana kura-kuran Abdullah Nāsih

Ulwān a vangarorin tauhidi da aqida, da manhajin Ahlus-Sunnah, da

tsarin da’awa, da mu’amala da `yan bidi’a, da amfani da hadisai masu rauni. Yana daga abin mamaki da ke cikin littafin Tarbiyyatul Awlād,

yawaita yabon waxanda suka shahara da mummunar aqida, da

kwarzanta malaman bidi’a, da kwaxaitar da mutane karanta littafan da

ke cike da kwamacala da ruxani da tsugarara, da kuzuzuta xariqun

sufaye, da rubuta karamomin bogi, da kuma kafa hujja da hadisan qarya ko masu tsananin rauni. Abin bai tsaya nan ba, Abdullah Nāsih

Ulwān, ya yawaita suka da zargi ga Ahlus-Sunnah, `yan Salafiyyah,

waxanda ke bin Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (tsira da aminci su

tabbata a gare shi) bisa fahimtar magabata na qwarai. Ban da wannan, a fakaice, Ulwān, ya yi qoqarin shayar da masu karanta littafin

Tarbiyyatul Awlād gurvatacciyar aqidarsa da karkataccen manhajinsa

da kuma nazariyyarsa mai rauni.

Ya kamata xaliban ilmi su fahimci matsalolin da ke cikin wannan

littafi, don su san irin mu’amalar da za su yi da shi. Haka kuma, kafin a

karantar da littafin a masallaci ko wuraren xaukar karatu, ya kamata a

yi wa mutane bayani game da kura-kuran da ke cikin littafin da kuma

hanyar da mawallafinsa ya bi wajen rubuta shi. Qin bayyana wa xalibai

varnar da ke cikin littafin, musamman wadda ke da alaqa da aqida da

manhaj, dai dai ya ke da ha’intarsu ko kuma cin amanarsu a cikin

harkar ilmi. Allah Ya shiryar da mu.

Page 24: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

24

Tsarin tarbiyya a Musulunci, gamammen tsari ne da ya kula

da kowane vangare na addini da rayuwa, ta yadda za a

samar da mutum mai zurfin fahimtar addini, da cikakken

hankali, da qoshin lafiya, da kyakkyawar xabi’a, da

wayewa, da dogaro da kai, da kishin al’umma, da sanin

haqqin kowa. Tarbiyyar `ya`ya na da vangarori guda

bakwai: vangaren imani, da xabi’u, da kula da jiki, da

hankali, da tunani, da mu’amala da zamantakewa, da kiyaye

bambancin jinsi.

A vangaren imani, wajibi ne a tarbiyyantar da `ya`ya a kan

aqida sahihiya, da ilmantar da su hukunce-hukuncen halal

da haram, da koya masu bautar Allah (Maxaukaki), da nuna

masu girman Allah da matsayi da martabar Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da cusa masu

son Allah (Mai girma da xaukaka) da son Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da sanar da su

haqqoqin Allah (Mai girma da xaukaka) da haqqoqin

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi),

da saba masu karatun Alqur’ani da qoqarin hardace shi.

A vangaren xabi’u da halaye, iyaye na buqatar xora `ya`yansu a kan makārimul akhlaq, wato, kyawawan xabi’u,

ta yadda za su taso a kan xabi’u na qwarai da halaye

managarta; da bayyana masu haxarin munanan xabi’u,

waxanda yara ke saurin xauka a wajen wasa tare da

sa’o’insu, kamar qarya da sata da zage-zage da cuxanya a

tsakanin maza da mata. Wannan zai samu ne idan iyaye suka

ba da kulawa ta musamman ga irin wasan da `ya`yansu ke

yi, da waxanda `ya`yansu ke yin wasa da su, da irin

maganganun da su ke yi a wajen wasa, da lokacin fitarsu da

kuma lokacin dawowarsu.

A vangaren tarbiyyar gangar jiki, `ya`ya na buqatar kulawa

ta musamman game da abincinsu da lafiyarsu, da koya masu

Page 25: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

25

tsafta da tsarki, da nisantar da su daga dukkan abubuwa

masu cutarwa, da hana su yin wasa da abin da zai haifar

masu da matsala, da tarbiyyantar da su a kan lura da jikinsu

da tufafinsu. Haka kuma, a wannan vangare, akwai buqatar

iyaye su sanya ido a kan `ya`yansu domin tabbatar da cewa

ba su auka cikin munanan xabi’un da yara ke koyo daga

abokai/qawaye, musamman, a lokacin da suka fara girma.

Irin waxannan munanan xabi’un sun haxa da: shan taba

sigari; da qoqarin fitar da maniyyi a asirce, ta hanyar wasa

da al’aura ko kallon finafinan batsa ko aikawa da hotunan

tsiraici ta hanyar wayar tafi da gidanka; da shan abubuwan

da ke sanya maye; da zina; da luwaxi. A wannan vangare,

wajibi ne iyaye su mayar da himma wajen ganin `ya`yansu

sun taso a cikin qoshin lafiya.

Tarbiyyar `ya`ya a vangaren hankali, ta qunshi karantar da

su ilmin addini da rayuwa, da ba su nagartaccen ilmi, da

ladabtar da su a kan ayyuka da xabi’u masu kyau, da

faxakar da su al’amuran rayuwa, da saitin tunaninsu, da

tabbatar da lafiyar qwaqwalwarsu, da horar da su a kan

sana’a.

A vangaren tunani, tarbiyyar `ya`ya ta qunshi koyar da su

xabi’ar jarumta da sadaukantaka; da jin girma da martabar

addini a cikin zukatansu; da qimanta wayewa da ci gaban

Musulunci; da nisantar da su daga xabi’ar sangarci da

ragwantaka, da tsoro ko firgici mara dalili, da jin kasawa da

naqasu da kuma tawayar zuciya.

A vangaren zamantakewa da mu’amala da jama’a, `ya`ya na

buqatar tarbiyya a kan kyakkyawar mu’amala da halin

girma da karamci, da muhimmancin taqawa, da

`yan’uwantaka, da tausayi, da jin qai, da rangwame, da

yafewa, da jarumta; da sanar da su haqqoqin iyaye da

`ya`ya, miji da mata, `yan’uwa da dangi, maqwabta,

Page 26: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

26

shugabanni da waxanda a ke shugabanta, dukkan musulmi

da waxanda ba musulmi ba, da haqqoqin dabbobi da

tsuntsaye da sauran halittar Allah (Maxaukaki); da

tarbiyyantar da su a kan ladubban Musulunci, kamar

ladubban cin abinci, da yin sallama, da neman izni kafin a

shiga gida, da ladubban zaman majalisi, da magana, da taya

murna ko yin jaje, da ladubban gaishe da mara lafiya.

A vangaren bambancin jinsi, wajibin iyaye ne su

tarbiyyantar da `ya`yansu a kan sanin bambancin da ke

tsakanin namiji da mace, da abubuwan da suka yi tarayya,

da irin mu’amalar da mace za ta iya yi da namiji, da

abubuwan da ba za su yi ba a tsakaninsu. Haka kuma, a

wannan vangare, `ya`ya na da buqatar sanin hukunce-

hukuncen kallon muharramai, da wadda a ke nemanta da

aure, da hukunce-hukuncen kallo a tsakanin ma’aura, da

hukuncin kallo a tsakanin namiji da matar da ya halatta ya

aura (ajanabiyyah) ko a tsakanin namiji da namiji, ko mace

da mace, ko kafiri da musulma. Bayan wannan, vangaren

tarbiyyar jinsi na wajabta karantar da `ya`ya hukunce-

hukuncen balaga, da alamomin balaga, da yadda matasa za

su yi mu’amala da tashen balaga.

WURAREN DA A KE SAMUN TARBIYYA

Tarbiyya na da wuraren da a ke samunta. Malaman tarbiyya

sun ce an fi samun tarbiyya a wurare uku: (1) gida (2)

makaranta (3) masallaci. Ko da ya ke ana iya samun

tarbiyya a waxansu wuraren daban, wuraren nan guda uku

sun fi tasiri a kan tarbiyya, kuma sun fi ba da gagarumar

gudummuwa wajen tabbatar da tarbiyyar `ya`yan Musulmi.

Page 27: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

27

Gida

Gida ya qunshi wurin da aka haifi mutum kuma ya taso a

cikinsa har zuwa wani lokaci a rayuwarsa, ko da ba a gina

ba, da kuma sauran wuraren da ke maqwabtaka da gidan

iyaye. Musulunci yana xaukar gida a matsayin ginshiqin

farko a rayuwar kowace al’umma; kasancewar nan ne

cibiyar koyar da tarbiyya mafi girma, kuma nan ne wuri

mafi tasiri a cikin rayuwar kowane mutum.

Ana xaukar shekarun da yaro ke yi a cikin gidansu tun a

farkon rayuwarsa kafin ya fara mu’amala da sauran jama’ar

gari ko a tura shi makaranta, a matsayin shekaru mafi tasiri a

kan shi wajen tsara makomarsa, da kuma irin rawar da zai

taka a cikin al’umma. A waxannan shekaru, yaro na tare da

iyayensa, musamman mahaifiya, da sauran `yan’uwansa, a

mafi yawan lokaci, kuma yana dogaro da su wajen koyon

addini da xabi’u da al’adun da al’ummarsa ta ginu a kai.

Iyaye su ne mafi kusanci ga `ya`yansu, kuma su ne mafi

tasiri a cikin zukatansu. Tasirin iyaye a kan `ya`yan ya kan

ba su damar su canza su zuwa ga wani addini daban, savanin

tsarin da Allah (Mai girma da xaukaka) Ya halicce su a

kanta, kamar yadda Hadisi Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya tabbatar.55

A cikin gida ne yaro ke fara koyon mafi yawan abubuwan

da suka shafi rayuwarsa da sauran abubuwan da ke da tasiri

ga makomarsa. A bisa qiyasi, yara na yin kusan kashi biyu bisa uku (⅔) na rayuwarsu a tsakanin gidan iyayensu da

gidajen `yan’uwa da maqwabta, tun daga lokacin

haihuwarsu har zuwa shekara goma. Wannan yasa malaman

tarbiyya ke xaukar gida a matsayin wurin da ke hukunta irin

rawar da yaro zai taka, da gudummuwar da zai ba

55

Muslim

Page 28: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

28

al’ummarsa nan gaba. Haka kuma, suna xaukar gida a

matsayin ginshiqin dukkan tarbiyya, kasancewar, makaranta

da masallaci da sauran wuraren da a ke samun tarbiyya, na

qarasa abin da aka gina ne a gida.

Samun tarbiyya daga gida na dogara ne a kan asasin da aka

gina gida a kansa. Idan iyaye sun kula da haqqoqin

`ya`yansu, kuma suka tsayu wajen yin masu tarbiyya a

dukkan vangarorin da suka dace, `ya`yan za su taso cikin

tarbiyya ta qwarai. Uwa tana da matsayi mafi girma a

wannan fage. Shi yasa malaman tarbiyya ke cewa lallai ne a

samu uwa ta gari ga `ya`yan da za a haifa, kuma a yi tattalin

uwar domin ta iya xaukar wannan babban nauyi.

Makaranta

Makaranta ce wuri na biyu da a ke samun tarbiyya domin

gina al’ummar Musulmai mai qarfi da kishin zuci da sanin

ya kamata. Yara na daxewa a makaranta irin daxewar da ba

su yi a wani wuri in ban da gidajensu. A kusan kowace rana,

in ban da lokacin hutu, `ya`yan da ke zuwa makarantar

islamiyya da boko, suna yin awa shida ko fiye da haka a

makaranta.

Kasancewar nan ne yara ke zuwa domin koyon ilmi da

sauraren karatu daga malamai dabam daban, da gogayya da

`yan’uwansu xalibai waxanda suka fito daga wurare

mabambanta, makaranta tana da tasiri mai yawa a kan

aqidar yara da xabi’unsu da mu’amalarsu da tunaninsu da

wayewarsu. Idan iyaye suka zava wa `ya`yansu makaranta

ta qwarai, inda a ke koyar da ilmi da tarbiyya a haxe, za su

taso cikin kyakkyawar tarbiyyar da za ta qarfafi qoqarin da

iyaye ke yi a gida. Idan kuwa suka yi sakaci game da zaven

makarantar da ta dace, hakan zai haifar da mummunar tasiri

ga tarbiyyar `ya`yansu.

Page 29: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

29

Gudummuwar makaranta wajen tarbiyyar `ya`ya na da

fuskoki guda uku:

1. Gina al’umma a bisa tsarin daidaito da rashin fifiko a

cikin rayuwa, ta yadda za a daidaita matsayin xalibai, ba

tare da fifiko a tsakaninsu ba, sai ta hanyar ilmi ko

kyawun xabi’a. Hakan na taimakawa wajen zaburar da

yara a kan mayar da himma cikin karatu, da dagewa

wajen ganin sun zarce sa’o’insu ko abokan karatunsu,

tun da za su fahimci cewa nasabarsu ko matsayin

iyayensu ba su iya taimaka masu wajen samun ilmi ko

matsayin da ba su cancanta ba, a fagen ilmi.

2. Karantar da ilmi sahihi da gina kyawawan xabi’u ga

xalibai, matuqar an samu malamai amintattu kuma

qwararru, masu tsoron Allah, waxanda ke lazimtar

Shari’ar Allah (Maxaukaki) a cikin karantarwarsu, kuma

aka dace da abokan karatu na qwarai.

3. Tattalin yara a kan kyakkyawar wakilcin da za su yi wa

al’umma a kowane vangare na rayuwa bisa la’akari da

qoqari da qwazonsu, da fahimtarsu da qwarewarsu, da

jinsinsu da shekarunsu; da fahimtar da su qalubalen da

ke fuskantar al’ummarsu, da irin gudummuwar da za su

ba da wajen tunkararsa; da nusar da su zuwa ga wajibcin

da ke kansu na zama matasa masu tarbiyya, da iyaye

masu kulawa, da shugabanni masu adalci, da ma’aikata

qwararru, da dattijai masu kamun kai da tausayi idan sun

girma.

Tarbiyya ba ta samuwa daga makaranta yadda ya kamata har

sai idan iyaye sun nuna wa `ya`yansu muhimmancin ilmi da

qimar malaman da ke karantar da su, tare da bin diddigin

karatun da su ke koyo domin sanin halin da a ke ciki. Haka

Page 30: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

30

nan, kasancewar makaranta na tattara xalibai da malamai

waxanda suka fito daga wurare mabambanta, wajibi ne

iyaye su sanya ido a kan karatun `ya`yansu; su yi qoqarin

sanin malaman da ke koyar da `ya`yansu, da abokan

`ya`yansu a makaranta, don gudun kada a rusa tarbiyyar da

su ke ba su a gida.

Masallaci

Masallaci56

na daga cikin manya-manyan wuraren da a ke

samun tarbiyya, kasancewar shi ne matattarar Musulmi a

zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) da sahabbansa (Allah Ya yarda da su) da sauran

halifofi da sarakunan da suka biyo bayansu. A wancan

lokaci, a cikin masallaci ne a ke shawarwari game da

al’amuran siyasar al’umma, da tsarin gudanarwarsu da

tattalin arziqi, da tsaro, da jihadi, da sauran al’amuran yau

da kullum, xoriya a kan gyara aqida, da tsarkake rai, da yin

salla da zikiri da wa’azi da karantarwar da a ke gudanarwa a

cikinsa. Masallaci na ci gaba da ba da gagarumar

gudummuwa wajen tabbatar da tarbiyyar al’ummar

Musulmi har yanzu. Daga cikin ayyukan tarbiyya da a ke

gudanarwa a cikin masallaci, akwai:

56

Masallaci na da matsayi mai girma da falala mai yawa a Musulunci:

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ambaci masallaci a wurare goma sha

takwas a cikin Alqur’ani. Allah (Mai girma da xaukaka) Ya danganta

wa KanSa masallaci, dangantawar da ke nuna xaukaka da girman

masallaci a wajenSa [Baqarah, 2:114; Taubah, 9:18; Jinn, 72:18;

Muslim]; masallaci shi ne mafi soyuwar wurare ga Allah [Muslim]; son

masallaci da lazimtarsa na wajabta wa bawa shiga cikin inuwar Allah a

ranar da babu wata inuwa sai ta Shi [Bukhari da Muslim]; gwargwadon

tafiyar da aka yi zuwa masallaci a nan duniya, gwargwadon masaukin

da za a tanadar wa mutum a cikin aljanna [Bukhari da Muslm]; kuma

yin tattaki zuwa masallaci na kankare kurakurai kuma yana xaukaka

darajoji [Muslim].

Page 31: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

31

1. Sallar farilla cikin jam’i, da karatun Alqur’ani da

nau’o’in zikirin Allah (Maxaukaki).

2. Huxubobin Juma’a, waxanda a ke gabatarwa domin cin

ma manufar wa’azi da tunatarwa game da Allah (Mai

girma da xaukaka) da ranar lahira, da matakan gyaran

zukata, da kiran mutane zuwa ga alhairi, da umurni da

kyakkyawa da hani da mummuna; da ilmantar da

Musulmi game da haqiqanin addininsu da kyawawan

xabi’u a bisa karantarwar Alqur’ani da sahihiyar Sunnar

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi), kamar yadda magabata na qwarai suka fahimta; da

daidaita fahimtar mutane game da Musulunci, da mayar

da martani game da ruxanin da mavarnata ke kawowa;

da faxakar da al’umma game da abubuwan da ke faruwa

a yau da kullum, da yadda za a tunkare su; da faxakar da

mutane game da wata munasaba ko wani lokaci na

musamman, kamar azumin Ramadan da aikin Hajji; da

tabbatar da ma’anar `yan’uwantakar Musulunci a

tsakanin Musulmi; da rayar da ruhin jihadi a cikin

zukatan al’umma.57

57

Wannan na qara nuna muhimmancin gabatar da huxubar juma’a ko īdi cikin harshen da mafi yawan mutane ke fahimta. Babu yadda za a yi

jama’a su amfana daga huxubar da ba su fahimta, kasancewar an

gabatar da ita cikin harshen larabci. Ko da ya ke akwai savani a

tsakanin malamai dangane da halaccin yin huxuba cikin wani harshe

savanin larabci, magana mafi qarfi da dacewa da manufofin Shari’ar

Musulunci dangane da huxubobi, ita ce, babu wani sahihin dalilin da ya

hana a yi huxuba cikin harshen da mutane za su fahimta, tun daga farkonta har zuwa qarshe, kuma ba dole ne a yi huxubar juma’a ko īdi

cikin larabci ba. Wannan ita ce fatawar mafi yawan malamai da

kwamitotin fatawa a wannan zamani. Sun kafa hujja da faxin Allah

(Maxaukaki): ‚Ba mu aiko wani Manzo ba face (yana magana) da harshen mutanensa domin ya yi masu bayani.‛ [Ibrāhīm, 14:4]. Haka

kuma, sun dogara da umurnin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ba Zaid ibn Thābit (Allah Ya yarda da shi) ya

koyi harshen yahudu domin a kyautata mu’amala tare da su [Ahmad];

Page 32: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

32

3. Ayyukan da’awah, da faxakarwa da shiryarwa ga matasa

da dattawa, maza da mata.

4. Wa’azi da darussa dabam daban da muhadarori don

kyautata saqafar Musulmi da wayewarsu.

5. Taron tattaunawa a kan al’amuran da suka shafi

Musulmi, da taron qara wa juna ilmi ko taron bita.

6. Tsare-tsaren da ke taimakawa wajen tabbatar da

tarbiyyar `ya`yan Musulmi, kamar halqar karatun

Alqur’ani; da kwamitotin da ke taimaka wa Musulmi

gudanar da waxansu nau’o’in ibada yadda ya dace,

kamar kwamitin karva da rarraba Zakka, da kwamitin

sulhu, da kwamitin taimaka wa gajiyayyu, da kwamitin

taimaka wa matasan Musulmi wajen fannonin ilmi ko

samar da tallafin karatu ko sana’a ko aikin albashi.

7. Laburaren da zai qunshi littafai da na’urorin yaxa

da’awah irin na zamani.

Babu shakka, waxannan abubuwa da a ke gudanarwa a

masallaci na da tasiri mai yawa a kan tarbiyyar Musulmi a

vangaren aqida da gyaran zuciya, da ilmi da kyawawan

da kuma umurnin da ya ba sahabbai (Allah Ya yarda da su) cewa idan

sun tafi yaqi, kada su auka wa abokan gaba har sai sun kira su zuwa ga

addinin Allah [Bukhari da Muslim]. Malamai suka ce waxannan dalilai

na tabbatar da halaccin amfani da harshen da mutane ke fahimta domin isar da saqo gare su a cikin huxubar juma’a ko īdi. Amma Shaikh Ibn

Bāz na ganin zai fi kyau liman ya karanto ayoyin Alqur’ani da nassosin

hadisi cikin harshen larabci, ko da ya gabatar da huxubar cikin wani harshen daban [Duba littafin Taudīhul Ahkām, 3/581, da Fatāwā Islāmiyyah, 1/405-406; da The Friday Prayer na Jamāluddīn Zarābozo

domin qarin bayani].

Page 33: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

33

xabi’u da mu’amala ta qwarai. Wannan yasa, Ibn Taimiyyah

(Allah Ya jiqan shi) ya ce:

[Masallatai sun kasance matattarar al’umma, kuma wuraren

zaman shugabanni. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya assasa masallacinsa mai albarka a kan

taqawa, kuma ya kasance a cikinsa a ke salla, da karatun

Alqur’ani, da zikiri, da karantar da ilmi, da huxubobi. Kuma

a cikinsa a ke gudanar da tsarin shugabanci, da shirye-

shiryen yaqi, da zaven shugabanni, da bayar da sanarwa.

Haka kuma, a cikinsa Musulmi ke taruwa duk lokacin da

wani al’amarin da ya shafi addininsu da duniyarsu ya bijiro].

Wajibi ne iyaye su xauki matakan da suka dace domin ganin

sun alaqanta `ya`yansu da masallaci, kuma sun qaunatar

masu da zuwa masallaci a kan lokaci, da qoqarin zama a

cikinsa, da sauraron darussan da a ke gudanarwa, da yin

tarayya da sauran mutane a cikin ayyukan tsaftace masallaci,

da ba da gudummuwa domin havaka tsare-tsarensa. Daga

cikin hanyoyin da iyaye za su bi wajen cusa wa `ya`yansu

son masallaci, da fahimtar da su gagarumar gudummuwarsa

wajen tabbatar da tarbiyya, akwai:

1. Fahimtar da su girman masallaci da muhimmancinsa a

rayuwar Musulmi ta hanyar xora su a kan saurare da

kwaikwayon mai kiran salla duk lokacin da aka yi kira.

2. Zuwa masallaci tare da su da zarar sun xan yi wayo, da

shiryar da su cikin sauqi da tausasawa idan suka yi wasa

ko surutu a masallaci, maimakon a yi masu tsawa ko a

buge su ko a daina zuwa da su gaba xaya.

Page 34: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

34

3. Limamin masallaci da sauran masallata su yi

kyakkyawar mu’amala da yaran da ke zuwa masallaci, ta

hanyar jawo su a jika; da yin masu sallama; da yin

musafaha da su; da yabonsu a kan qoqarin zuwa

masallaci; da ba su kyauta wani lokaci; da kau da kai ga

kurakuran da ba su yi tsanani ba; da sakar masu fuska; da

yin masu murmushi; da tambayar labarinsu idan sun

kwana biyu ba su zo masallaci ba; da rashin kora su can

bayan sahu, matuqar sun zo masallaci da wuri.58

4. Saba masu da halartar halqar Alqur’ani da yin

musharaka cikin karatun Alqur’ani da sauran darussan

da a ke gudanar da su a keve.

5. Halartar darussa da muhadarorin da a ke gabatarwa a

masallaci tare da su.

HANYOYIN KOYAR DA TARBIYYA59

Amfani da hanyar da ta dace ko usulubin da ya fi cancanta

wajen tarbiyyantar da `ya`ya wajibi ne. Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) shi ne shugaban

masu tarbiyya kuma wanda ya fi kowa iya karantar da

tarbiyya, ta hanyar magana da aiki, da nuni da ishara, da

sauran hanyoyi da usulubai mafi dacewa. Bin diddigin

Sunnarsa na nuna cewa Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya yi amfani da hanyoyi guda

58

Yana daga kura-kuran da a ke yi a waxansu masallatai, tura yara can

baya, da kuma hana su shiga cikin sahu, ko da sahun farko ko sahu na

biyun bai cika ba, a lokacin da za a fara salla. 59

Mafi yawan bayanan da ke qarqashin wannan sashe na ciro ne daga littafin Muhammad Ad-Duwaysh, Al-Asālibut Tarbawiyyah inda Rasūlil Bashariyyah, www.quran.maktūb.com/vb/quran22761

Page 35: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

35

goma wajen tarbiyyantar da al’ummarsa, irin tarbiyyar da

duniya ba ta tava gani ba, kafin wancan lokaci da kuma

bayansa. Hanyoyin su ne:

1. Amfani da qissa, kasancewar mutane na son qissa, kuma

suna jawuwa zuwa gare ta, kamar yadda su ke saurin

koyon darasi da xaukar wa’azi daga gare ta. Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi amfani da irin wannan usulubi a lokacin da Khabbāb ibn

Al-Arat (Allah Ya yarda da shi) ya koka game da tsanani

da wahalar da su ke sha a hannun kafiran makka.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ba shi labarin waxansu mutane da suka rayu kafin

wannan lokaci; sun fuskanci nau’o’in azaba da kuma

kisar gilla, amma hakan bai sa sun bar addinin Allah

(Mai tsarki da xaukaka) ba.60

Bayan wannan, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya yi amfani da usulubin qissa a

wurare da dama domin isar da saqo na musamman.

Misali, ya ba da qissar mutane uku waxanda suka shiga

kogo, sai dutse ya toshe ramin kogon, har sai da suka

roqi Allah, ta hanyar yin tawassuli da kyawawan

ayyukansu, domin ya tarbiyyantar da al’ummarsa a kan

ikhlasi (yin kowane abu domin Allah);61

da qissar

mutumin da ya kashe mutane xari, sannan ya tuba, kuma

Allah Ya karvi tubarsa, domin ya nuna muhimmancin

tuba;62

da qissar makaho da kuturu da mai qwaiqwaido,

waxanda Allah Ya yi wa ni’ima bayan jarabawa, amma

biyu daga cikinsu suka butulce wa Allah, domin ya nuna

haxarin butulci ga Allah (Maxaukaki), da kuma amfanin

60

Bukhari 61

Bukhari da Muslim 62

Bukhari da Muslim

Page 36: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

36

gode wa Allah (Maxaukaki) a kan ni’imominSa;63

da qissar as-hābul ukhdūd, waxanda sarkinsu ya tirsasa su

shiga cikin wuta saboda sun yi imani da Allah

(Maxaukaki), domin ya karantar da muhimmancin

haquri a kan cutarwar da mumini zai fuskanta a dalilin

riqo da addini.64

2. Amfani da hanyar wa’azi, saboda tasirin wa’azi a cikin

zukata, tare da lura da yanayin mutane da kuma

buqatarsu ga irin wannan usulubi, ta yadda ba za a gundurar ko a gajiyar da su ba.

65 Al-Irbād ibn Sāriyah

(Allah Ya yarda da shi) ya ba da labarin wani wa’azin da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya yi a kan wajibcin biyayya ga shugaba da kuma

riqo da Sunnah, har idanuwa suka zubar da hawaye,

kuma zukata suka raurawa, kamar dai wa’azin mai ban

kwana da mutanensa.66

3. Usulubin kwaxaitarwa da tsoratarwa, bisa la’akari da

xabi’ar xan Adam ta fuskantowa da juyawa, da kuma

karsashi da gajiyawa, a lokaci zuwa lokaci. Misali,

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya yi amfani da hanyar tsoratarwa, a lokacin da ya

ce: ‚Da kun san abin da na sani, da kun yi dariya kaxan,

kuma kun yi kuka mai yawa‛;67

kuma ya yi amfani da

hanyar kwaxaitarwa, a cikin hadisin da ya ce: ‚Ba wani bawa da zai ce ‘Lā ilaha illallāh, sannan ya mutu a kan

haka, face ya shiga aljanna.‛ Abu Zarr (Allah Ya yarda

da shi) ya ce, ‘ko ya yi zina, ya yi sata’? Manzon Allah

63

Bukhari da Muslim 64

Muslim 65

Bukhari 66

Tirmidhi da Ibn Mājah 67

Bukhari da Muslim

Page 37: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

37

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚ko

ya yi zina, ya yi sata‛.68

4. Usulubin gamsar da tunani da hankalin mai saurare, ta

yadda mutum zai sallama wa abin da aka gamsar da shi a kai. Abu Umāmah (Allah Ya yarda da shi) ya ruwaito

cewa wani saurayi ya je wajen Annabi (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya ce, ‘Ka ba ni iznin yin

zina’, sai mutane suka daka ma shi tsawa, suka ce ‘mah, mah’69

. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce ya matso kusa da shi, sannan ya

ce masa: ‚Za ka so a yi zina da mahaifiyarka?‛ Ya ce,

‘wallahi, a’a’. Ya ce: ‚Haka nan sauran mutane ba za su

so a yi zina da uwayensu ba.‛ Ya ce: ‚Za ka so a yi da

`yarka?‛ Ya ce, ‘wallahi, a’a’. Ya ce: ‚Haka nan ma

sauran mutane ba su son a yi da `ya`yansu‛. Ya ce: ‚Za

ka so wa `yar’uwarka?‛ Ya ce, ‘wallahi a’a’. Ya ce:

‚Haka nan, mutane ba za su so wa `yan’uwansu ba‛. Ya

ce: ‚Za ka so a yi da guggonka?‛ Ya ce, ‘wallahi, a’a’.

Ya ce: ‚Mutane ma ba za su so haka ga guggonninsu

ba.‛ Ya ce: ‚Za ka so a yi da innarka?‛ Ya ce, ‘wallahi,

a’a.’ Ya ce: ‚Haka nan ma sauran mutane ba za su so a yi zina da innoninsu ba…‛

70 Abu Umāmah (Allah Ya

yarda da shi) ya ba da labarin cewa a qarshen al’amari,

wannan saurayi ya nemi a yi masa addu’ar Allah

(Maxaukaki) Ya nisanta shi daga zina, kasancewar ya

gamsu da muninta, kuma ya fahimci illarta.

5. Amfani da hanyar tattaunawa da munaqasha, domin a

faxakar da mutane game da abin da ba su fahimta ba, ko

a shiryar da su zuwa ga abin da ya fi dacewa, kamar

68

Bukhari da Muslim 69

Kalma ce ta tsawatarwa da nuna tir ga wanda ya faxi wani

mummunan abu. 70

Ahmad

Page 38: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

38

yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi tare da mutanen madina, Al-Ansār, a

lokacin da suka nuna rashin jin daxinsu, saboda ya raba

ganimar da aka samu a yaqin Hunain, ba tare da ya ba su

komai ba. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya yi huxuba, kuma ya ce: ‚Ya ku

mutanen madina! Ashe ban same ku a kan vata ba,

amma Allah Ya shiryar da ku ta hanyata? Na same ku a

rarrabe, amma Allah Ya haxa ku wuri xaya ta hanyata?

Kuma na same ku cikin talauci, amma Allah Ya azurta

ku ta hanyata?...71

6. Hanyar zafafawa da yin uquba ko bayyana zargi ga

wanda ya yi abin da bai dace ba, matuqar yin hakan zai

fi kawo gyara. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya bayyana vacin rai, kuma ya zafafa

matuqar gaske, a lokacin da aka kawo qarar wani

sahabin da ke tsawaita wa mutanensa a cikin salla.72

Haka kuma, a lokacin da wani mutum ya yi tambaya

game da hukuncin tsintar raqumin da ya vace, Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Ina ruwanka da shi…!‛73

Bayan wannan, Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fisge

zinaren da ya gani a hannun wani, sannan ya ce:

‚Xayanku kan yi gangancin xaukar garwashin wuta, ya

sanya a hannunsa‛,74

kuma ya yi mummunar addu’a ga

mutumin da girman kai ya hana shi cin abinci da

hannunsa na dama.75

71

Bukhari da Muslim 72

Bukhari da Muslim 73

Bukhari da Muslim 74

Muslim 75

Muslim

Page 39: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

39

7. Qaurace wa wanda ya yi laifi, har sai ya tuba, kamar

yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi wa su Ka’ab ibn Mālik (Allah Ya yarda

da shi), a lokacin da ba su fita yaqin Tabuk tare da

Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ba.76

Sai dai kuma ba a kowane lokaci ba ne Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ke

amfani da wannan hanyar.

8. Amfani da usulubin da zai haxa kowa da kowa, ba tare

da an ayyana waxanda a ke nufi ba, illa iyaka, da zarar

mutanen da abin ya shafa suka ji, za su fahimci saqon;

ko kuma a faxi magana game da wani mutum a bayan

idonsa, don a sanar da shi daga baya. Misali, dangane da waxanda suka xora wa Barīrah (Allah Ya yarda da ita)

biyan kuxin fansa, bisa sharaxin cewa su ne ke da

walittarta, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce: ‚Mene ne ya sa mutane ke

sanya sharuxxan da ba su a cikin littafin Allah …‛77

Haka kuma, a lokacin da waxansu mutane uku suka

shiga gidansa domin sanin irin yadda ya ke ibada a cikin

gida, sannan, xayansu ya ce ba zai yi aure ba, na biyu ya

ce ba zai sake yin barcin dare ba, na ukun ya ce kullum

zai riqa yin azumi, Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Mene ne ya samu mutane,

suka ce kaza da kaza …‛78

Wani lokaci, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) na faxin magana domin a sanar da

wanda abin ya shafa. Misali, Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce wa matarsa

Hafsah bint Umar (Allah Ya yarda da ita): ‚Madalla da 76

Bukhari 77

Bukhari da Muslim 78

Bukhari

Page 40: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

40

Abdullah (ibn Umar), ina ma da yana yin sallar dare.‛79

A wani lokacin, yana faxin magana a cikin mutane

domin wanda a ke yi da shi ya fahimci saqon. Misali,

waxansu mutane guda biyu sun yi kace-nace a gaban

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi). Sai, a cikin fushi, xaya daga cikinsu ya zagi xayan. Sai Manzon Allāh (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce: ‚Na san kalmar da zai faxi, wannan fushin ya gushe. Da zai ce, ‘A’ūzu billah minash-shaixānir rajīm’, shi ke nan‛. Sai aka ce wa mutumin,

‘ka ji abin da Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce kuwa? Sai mutumin ya ce, ‘(na ji mana)

ai ni ba mahaukaci ba ne!80

9. Amfani da wata dama ko fursa, saboda la’akari da

munasabar lokacin ko yanayin ko kuma wurin. Irin

wannan hanya ta qunshi yin wa’azi a maqabarta; da yin

jim-kaxan bayan wani tashin hankali ya auku; da amfani

da lokacin farin ciki; da lokacin musiba; da lokacin

rashin lafiya; da lokacin mutuwa ; da lokacin aukuwar

wata aya, kamar girgizar qasa ko kisfewar rana; da

lokacin da wani abin tausayi ko abin jimami ya faru.

Abin da aka faxa wa mutane a irin wannan lokaci ya kan

yi tasiri sosai a zukatansu.

10. Usulubin qarfafa gwiwa, da yin yabo saboda qoqarin da

aka yi. A lokacin da Abu Hurairah (Allah Ya yarda da

shi) ya tambayi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) game da wanda zai fi rabauta da

cetonsa a ranar qiyama, Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Da ma na yi zaton

babu wanda zai riga ka yin wannan tambayar saboda

79

Bukhari 80

Bukhari da Muslim

Page 41: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

41

kwaxayin da ka ke da shi game da ruwayar hadisi.‛81

Haka kuma, a lokacin da Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya yi wa Ubayyu ibn Ka’ab

(Allah Ya yarda da shi) tambaya game da ayar da ta fi girma a cikin littafin Allah, Ubayyu ya ce, Āyatul Kursiyy, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce masa: ‚Madalla da yawan ilminka, yā Abā Munzir.‛

82

Iyaye na buqatar bin hanyoyin da suka fi dacewa wajen

tarbiyyar `ya`yansu, bisa la’akari da yanayi, lokaci, wuri,

shekaru, da jinsi. Rashin la’akari da waxannan abubuwa zai

haifar wa iyaye rashin fahimtar irin matakin da ya kamata su

xauka, a duk lokacin da `ya`yansu suka yi abin da bai dace

ba.

Bayan wannan, wanda zai yi tarbiyyar `ya`ya, yana buqatar

mallakar siffofi guda tara domin ya kai ga yin nasara:83

1. Gwargwadon ilmin addini, da ilmin abubuwan da ke

faruwa yau da kullum don tsai da wajibin koyar da

tarbiyya.

2. Riqon amana a cikin ibada da mu’amala, da qoqarin kula

da addini, da lazimtar Shari’ah a voye da bayyane, ta

yadda zai zamanto abin koyi ga wanda ya ke yi wa

tarbiyya.

3. Qarfi da ikon yin jagoranci ga waxanda a ke koya wa

tarbiyya.

81

Bukhari 82

Ahmad da Muslim 83

Duba littafin Kaifa Turabbi Waladaka na Lailā bint Abdir-Rahmān

Al-Jarībah

Page 42: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

42

4. Adalci a tsakanin waxanda za a yi wa tarbiyya, ba tare

da nuna bambanci ko fifiko ba, sai idan da larurar da za

ta halatta yin haka.

5. Kwaxayin shiryuwa da tarbiyyantuwar wanda a ke yi wa

tarbiyya, da zame masa jagora, kuma kyakkyawan abin

koyi, da yin masa addu’a, da bibiyar halin da ya ke ciki,

lokaci zuwa lokaci.

6. Himmar ganin an lazimta wa yaro abubuwan da za su

kiyaye masa addini da hankali da jiki da dukiya, da

nisantar da shi daga abubuwan da za su cutar da shi ta

kowane vangaren tarbiyya, bisa qa’idar ajiye kowane

abu a wurin da ya dace, ba tare da la’akari da jin daxin

yaron ko rashin jin daxinsa ba, a lokacin da a ke yin

masa tarbiyya.

7. Yi wa kai tarbiyya, da kuma qoqarin tabbatar da

kyakkyawar yanayi a wurin da za a gudanar da tarbiyya.

8. Amfani da hikima da kuma usulubin da ya dace wajen

yin tarbiyya.

9. Lazimtar gaskiya da kuma nisantar riya a cikin magana

da aiki.

HAXARIN SAKACI GAME DA TARBIYYAR `YA`YA84

`Ya`ya kyauta ce daga Allah (Mai tsarki da xaukaka),85

kuma ni’ima ce wadda ta dace da xabi’a, da yanayin xan

84

Mafi yawan bayanan da ke qarqashin wannan sashe na ciro su ne

daga littafi na Ni’imar Haihuwa da Haqqoqin `Ya`ya a Musulunci 85

Shūrah, 42: 49 – 50

Page 43: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

43

Adam. Wannan yasa xan Adam ke jin daxi, kuma ya ke yin

farin ciki, idan aka haifar masa `ya`ya. Haka kuma, yana

roqon Allah Ya azurta shi da `ya`ya, idan bai samu haihuwa

ba.86

Haihuwa arziqi ne,87

kuma tana daga cikin fa’idodin aure.

Su kuma `ya`ya, ado ne88

da aka qawata wa mutane

sha’awarsa.89

Fatan kowane mutum shi ne ya samu `ya`ya

nagari, masu albarka, masu biyayya, masu tausayi; waxanda

za su tsaya a makwafinsa, su cike gurbinsa, kuma su ci gaba

daga wajen da ya tsaya, idan Allah Ya xauki ransa.90

Burin

kowane uba nagari, shi ne, Allah Ya sa `ya`yansa su wakilce

shi a ko’ina, su zamanto sanyin ido a gare shi, su tausaya

masa, kuma su xauki nauyinsa idan ya tsufa, sannan su yi

masa addu’a idan ya mutu.91

`Ya`ya amana ce babba a wuyan iyaye, kuma wasiyya ce

daga Allah (Mai tsarki da xaukaka).92

Babu shakka, za a

tambayi kowane uba da uwa game da wannan amana da

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ba su, kuma za a tambaye

su game da wannan wasiyya.93

Haka kuma, `ya`ya da dukiya jarabawa ce daga Allah. Babu

mai cin wannan jarabawa sai wanda ya tsayu da haqqoqin

da ke rataye da ita, kamar yadda Musulunci ya shar’anta.

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ce: ‚Kuma ku sani cewa

abin sani kawai, dukiyoyinku da `ya`yanku, wata fitina

86

Aal Imrān, 3:38 87

Nahl, 16:72 88

Kahf, 18:46 89

Aal Imrān, 3:14 90

Maryam, 19:5 – 6 91

Furqān, 25:74 92

Nisā, 4:11 93

Muslim

Page 44: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

44

(jarabawa) ce, kuma lalle ne Allah, a wurinSa, akwai ijara

(lada) mai girma.‛94

Yin kyakkyawar tarbiyya ga `ya`ya na daga cikin manya-

manyan hanyoyin nuna godiya ga Allah a bisa ni’imar

haihuwa, da xaukar matakan cin wannan babbar jarabawa.

Kyakkyawar tarbiyya kuwa, tana samuwa ne ta hanyar

kiyaye qa’idodin Shari’a, da aiki da ladubbanta,

gwargwadon hali, a cikin dukkan abubuwan da za a yi wa

`ya`ya, tun kafin a haife su, da kuma bayan an haife su, har

su girma.

Abin mamaki, da yawa daga iyaye ba su damu da shiriyar

`ya`yansu ba, alhali kuwa muhimmin abu ne a cikin

tarbiyya. Saboda muhimmancinsa ne ma, Annabawa da

Manzanni suka riqa roqon Allah Ya ba su zuriya ta qwarai

tun kafin su samu haihuwa. Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ba mu labarin addu’o’in da Annabi Ibrāhīm da Zakariyya

suka yi domin samun `ya`ya nagari. Haka kuma, waxansu

iyayen ba su damu da sanin halin da `ya`yansu ke ciki ba: ba

su tambayar ina suka je, ko ina za su, ko yaushe suka je, ko

yaushe suka dawo; su wane ne abokan hirarsu ko abokan

zuwa yawonsu; `ya`yansu na zuwa makaranta ko a’a, suna

mai da hankali a wajen karatu ko a’a, suna kula da addini ko

a’a; `ya`yansu na cikin qoshin lafiya da kuzari ko a’a; sun ci

abinci ko ba su ci ba; waxanne irin tufafi suka sanya; suna

yin wanka da sauran al’amuran tsafta ko ba su yi.

Irin wannan sakaci da mafi yawan iyaye suka samu kansu a

ciki, yana haifar da tavarvarewar tarbiyya, kamar yadda a ke

gani a yau; al’umma ta rasa qima da matsayin da aka santa

da su; rashin tausayi da biyayya sun zama ruwan dare; ci

94

Anfāl 8:28

Page 45: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

45

baya da tawayar zuciya da rashin kishin kai sun dabaibaye

ta.

A vangaren iyaye, sakaci wajen tarbiyyar `ya`ya na haifar da

qiyayya a tsakanin su da `ya`yan. Haka kuma, `ya`yan da ba

su samu cikakkiyar tarbiyya ba, na zamantowa fitina ga

iyayensu, kuma su zamanto dalilin shagalar iyaye daga abin

da Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ke so. Da ma Allah

(Mai girma da xaukaka) Ya ce: ‚Ya ku waxanda suka yi

imani! Lalle ne daga matanku da `ya`yanku akwai maqiyi a

gare ku, sai ku yi hattara…‛95

Kuma Allah (Mai girma da

xaukaka) Ya ce: ‚Dukiyoyinku da `ya`yanku fitina ce

kawai. Kuma Allah, a wajenSa akwai wani sakamako mai

girma.‛96

Haka nan, Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ce:

‚Ya ku waxanda suka yi imani! Kada dukiyoyinku da

`ya`yanku su shagaltar da ku daga ambaton Allah. Kuma

wanda ya yi haka, to, waxannan su ne masu hasara.‛97

Babu

shakka, yin sakaci game da tarbiyyar `ya`ya na da haxari

mai girma.98

Ibnul Qayyim (Allah Ya jiqan shi) ya ce: ‚Wanda ya qi

karantar da xansa abin da zai amfane shi, ya bar shi haka

kawai, ya munana matuqa. Mafi yawan `ya`ya na lalacewa

ne saboda sakacin iyaye da rashin karantar da su farillai da

sunnoni na addini; ta haka, sai iyaye su tozartar da (`ya`yan)

su tun suna qanana, ta yadda `ya`yan ba za su amfanar da

kansu ba, kuma ba za su amfani iyayen ba idan sun

girma.‛99

95

Taghābūn, 64: 14 96

Taghābūn, 64:15 97

Munafiqūn, 63:9 98

Duba Tafsīrul Qur’anil Azīm na Ibn Kathīr, 4/344, da 4/47 don qarin

bayani 99

Duba littafin At-Taqsīr fi Tarbiyyatil Aulād: Al-Mazāhir, Subulul Wiqāyah wal Ilāj na Muhammad ibn Ibrahim Al-Hamd

Page 46: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

46

Abu Hāmid Al-Ghazāli (Allah Ya jiqan shi) ya ce: ‚Xa,

amana ce a wajen iyayen shi, kuma zuciyarsa tsarkakakkiya

ce, wadda babu wani zane ko hoto a cikinta; zai dace da duk

irin zanen da aka yi masa, kuma yana shirye da ya karkata

ga duk inda aka juya shi. Idan aka xora shi a kan alhairi

kuma aka karantar da shi, zai girma a kan haka, kuma ya ji

daxin rayuwa a duniya da lahira, kuma iyayensa da

malamansa su yi tarayya da shi cikin lada. Idan kuwa aka

saba masa da sharri, kuma aka yi watsi da shi kamar dabba,

zai tave, ya halaka, kuma zunubin na kan waxanda nauyinsa

ke kansu.‛100

A cikin littafin At-Taqsīr fi Tarbiyyatil Aulād, Shaikh

Muhammad ibn Ibrahim Al-Hamd ya lissafa alamomin

sakaci game da tarbiyyar `ya`ya. Daga cikinsu akwai:

1. Tarbiyyantar da `ya`ya a kan tsoro da ragwantaka da

yawan fargaba, da lalaci da kasala da jin naqasu da

tawayar zuci, da zaman banza ko rashin amfani da lokaci

yadda ya kamata, da son na banza da rashin moriya.

2. Samar wa `ya`ya duk abin da su ke so, da sayo masu duk

abin da suka nema, ko da kuwa ba su da buqatar haka,

saboda qarancin shekarunsu ko yanayinsu.

3. Sayen masu mota tun suna qanana, ta yadda za su samu

damar yin sharholiya da bin `yan mata da abokan banza,

ko kuma su rasa natsuwar yin karatu.

4. Tsananta masu, da zafafawa a gare su fiye da qima, da

rashin tausasa masu.

100

Duba littafin At-Taqsīr fi Tarbiyyatil Aulād: Al-Mazāhir, Subulul Wiqāyah wal Ilāj na Muhammad ibn Ibrahim Al-Hamd

Page 47: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

47

5. Tsananin rowa, da qanqame hannu, da tsuke bakin aljihu

wajen ciyar da su, ko xaukar nauyin karatunsu ko kuma

koyon sana’a.

6. Rashin tausasawa da tausayawa da nuna jin qai a gare su,

bisa la’akari da shekaru da yanayinsu, da kuma rashin

damuwa da halin da su ke ciki.

7. Mayar da himma ga al’amuran `ya`ya na zahiri ko kuma

ruxuwa da abin da su ke bayyanarwa a fili, ba tare da

qoqarin gyara zukatansu da kyautata al’amuransu na sirri

ba.

8. Wuce iyaka wajen kyautata zato ko munana zato ga

`ya`ya.

9. Nuna bambanci a tsakanin `ya`ya, a wajen kyauta ko

xaukar nauyin karatu, ba tare da wani sahihin dalilin

Shari’ah ba.

10. Kiransu da munanan suna ko sanya masu sunayen banza,

waxanda ba su da kyakkyawar ma’ana.101

11. Yin mummunar addu’a a kansu ko yawan la’antarsu, da

yin masu mummunar fata.

12. Doguwar hira a qofar gida ko majalisa ko dandali,

maimakon zama tare da iyali don sanin halin da su ke

ciki.

101

Karanta littafi na Ni’imar Haihuwa da Haqqoqin `Ya`ya a Musulunci don qarin bayani game da ladubban sanya suna, da

qa’idodin zaven suna.

Page 48: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

48

13. Aikata munanan abubuwa a gabansu, ta yadda za su yi

koyi da ayyukan assha waxanda suka ga iyayensu na yi.

14. Kawo munanan abubuwa a gida, ko barin abubuwan da

ke vata tarbiyya a cikin gida.

15. Tilasta wa `ya`ya maza su auri matan da ba su so, ba tare

da la’akari da abin da zai iya biyo baya ba.

16. Jinkirta aurar da `ya`ya mata, waxanda mutanen kirki

suka zo don su aura, bisa hujjar sai sun kammala

makaranta.102

102

Sanannen abu ne cewa aure ba ya hana karatu, haka kuma, karatu ba

ya hana aure. Ya kamata iyaye su hanzarta aurar da `yarsu idan ta kai

munzalin aure, matuqar mutumin kirki, wanda aka yarda da addininsa

da xabi’unsa ya fito. Kuskure ne iyaye su dage a kan sai `yarsu ta

kammala karatu, musamman idan ta nuna cewa tana buqatar

auren.Wallahi da yawa daga cikin `yan matan jami’a, da waxanda ke

sakandare, waxanda iyayensu suka hana su yin aure bisa hujjar sai sun

kammala karatu, na yin zina tare da samarin da ke nemansu. Saboda

qarancin ilmin waxansu `yan matan, har cewa su ke yi ai duk zinar da

suka yi, zunubin na kan iyayensu, tun da an hana su aure, alhali suna da

tsananin buqata.Waxansu iyayen kuma, saboda sakarci, sun yarda a yi

ta zuwa wajen `ya`yansu mata, da sunan zance, amma da zarar wani

daga cikin samarin ya nemi a ba shi damar turo wakilansa domin a yi

maganar aure, sai iyayen su ce allanbaran ba za su aurar da `yarsu a

wannan tsakani ba, bisa hujjar cewa tana yin karatu! Tambayar ita ce:

me ya sa aka bar ta tana hira da maza, tun da an san ba za a aurar da ita a lokacin ba? Sau da yawa irin waxannan `yan mata su kan fuskanci

matsaloli masu yawa idan sun kammala karatu, kasancewar waxansu

mutane za su riqa qyamar su neme su da aure, ko dai saboda tsufa ko

kuma saboda zargin cewa sun yi ballagazanci a makaranta. Ya kamata

iyaye su ji tsoron Allah!

Waxansu iyayen na kafa hujja da cewa idan sun aurar da `ya`yansu,

alhali suna karatu ko kuma suna gab da fara karatun, sau da yawa

mazajen na hana su ci gaba. Ko da ya ke hakan yana faruwa a tsakanin

matasa, wannan ba zai zame wa iyaye hujjar qin aurar da `ya`yansu ba,

musamman idan `ya`yan sun nuna buqatar yin aure. Rashin yin haka,

Page 49: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

49

17. Auren dole ga `yan mata.103

ya kan haifar wa iyaye da abin kunya, domin kuwa waxansu `yan

matan ba su iya haquri. Kafin a farga, sun yi cikin shege, ko kuma su

riqa amfani da qwayoyin hana xaukar ciki, ta yadda za su ci gaba da

holewarsu.

Babu shakka, auren wuri, ga wadda ta samu mutumin kirki, wanda

ke son ya aure ta, yana da fa’idodi masu yawa. Daga cikinsu: (1) samun

`ya`ya da wuri, ta yadda iyaye za su yi farin ciki a lokacin tsufarsu (2)

yawaita al’ummar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) (3) tsare matasa daga karkacewar tunani, da kare su daga

fitinar sha’awa (4) kiyaye mutuncin musulmi, da tsare al’umma daga

faxawa cikin yawan zinace-zinace (5) samar da aminci da tsaftataccen

yanayi ga al’umma (6) taqaita tazarar da ke tsakanin shekarun iyaye da

na `ya`yansu, domin samun damar yin kyakkyawar tarbiyya ga `ya`ya. 103

Malamai sun qara wa juna sani dangane da matsayin auren dole.

Waxansu malamai na ganin cewa za a iya tilasta wa budurwa ta auri

mutumin da ba ta so, ko da ta balaga, amma ba za a yi wa bazawara

tilasci ba, ko da ba ta balaga ba. Waxansu malamai suka ce za a iya

tilasta budurwa komai girmanta, haka nan ma, bazawarar da ba ta

balaga ba. Waxansu malamai kuma suka ce ba za a iya tilasta yarinya a

kan ta auri mutumin da ba ta so ba, ko da kuwa ba ta tava yin aure ba,

kuma ko da qarama ce, wadda ba ta balaga ba. Amma magana mafi

qarfi, wadda Ibn Taimiyyah da waxansu malamai suka qarfafa, ko da

ya ke ta sava wa mazhabar malikiyya, ita ce, ba a yi wa mace auren

dole matuqar ta balaga, ko da kuwa ba ta tava yin aure ba. Dangane da bazawara, sun dogara da hadisin Khansā Al-Ansāriyyah, wanda

Bukhari da Abu Dāwud da Nasā’i da Ibn Mājah suka ruwaito cewa

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Bazawara ita ce ke da haqqin (zavar wa) kanta (miji) fiye da

waliyyinta (uba ko waninsa).‛ Dangane da budurwa, sun kafa hujja da hadisin Ibn Abbas (Allah Ya yarda da su), wanda Abu Dāwud da Ibn

Mājah suka ruwaito, cewa wata yarinya (budurwa) ta kawo qarar

mahaifinta wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) cewa ya aurar da ita ga wanda ba ta so. Sai Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‘Idan kin amince a

zartar da auren, za a zartar; idan kuwa ba ki amince ba, za a warware

shi. Ta ce: ‘Na amince. Da ma dai ina son iyaye su san cewa `ya`yansu

na da haqqi wajen aurar da su.‛ Amma yarinyar da ba ta balaga ba a

Page 50: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

50

18. Barin `ya`ya mata su fita su kaxai, ba tare da muharrami

ba, ko su fita ba tare da sun sanya cikakken hijabi ba,

musamman daga lokacin da suka balaga.

19. Sayen wayar sadarwa ga qananan yara, ko kuma a qyale

`yan mata su yi amfani da wayar da samari suka ba su.

20. Wulaqanta `ya`ya da qasqantar da su idan sun yi

kuskure, da kuma rashin qarfafa masu gwiwa idan sun yi

abin kirki.

21. Rashin ladabtar da `ya`ya ta hanyoyin da suka dace, idan

sun yi abin da ya kamata a hore su.

22. Rashin saba masu da xaukar nauyin kansu ko xaukar

nauyin wasunsu, gwargwadon iko, tun suna qanana.

23. Rashin qoqarin fahimtar yanayinsu da xabi’unsu, ta

yadda za a san hanyoyin magance matsalolinsu na

tarbiyya.

lokacin da za a aurar da ita, ba dole ne a ba ta zavi ba, kasancewar

sayyidina Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ya aurar da A’isha (Allah

Ya yarda da ita) ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ba tare da ya shawarce ta ba. Sai dai kuma, har a hakan, idan

ta balaga, kuma ta qi yarda da matsayin da babanta ya xauka a

madadinta, waxansu malamai na ganin dole a warware auren.

Wannan ke nuna cewa iyaye ba su da damar su yi wa `ya`yansu

mata auren dole, matuqar dai `ya`yan sun balaga. Idan kuwa suka aurar

da su a bisa tilas, `ya`yan suna da damar su kai qara kotu, domin a

warware. Amma idan `ya`yan suka yi haquri da hukuncin da iyayensu

suka zartar a kansu, shi ya fi, matuqar babu cutarwa a ciki. Idan kuwa

saboda kwaxayi ko kuma wani dalili mara qarfi ne yasa iyayen suka

tilasta masu auren wanda ba su so, musamman idan ba a amince wa

aqida da xabi’ar mutumin ba, ya kamata `ya`yan su qi yarda.

Page 51: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

51

24. Rashin ba su damar gyara kuskuren da suka yi, ko

kyautata abin da suka yi shi batsa-batsa, bayan an nuna

masu yadda ya kamata su yi.

25. Rashin damuwa da irin makarantar da su ke zuwa, ko

malaman da ke karantar da su.

26. Qin haxa kai da masu karantarwa a makaranta ko kuma

hukumomi wajen tabbatar da tarbiyyar `ya`ya.

27. Barin al’amarin tarbiyya gaba xaya a hannun iyaye mata,

da watsi da haqqoqin `ya`ya, musamman `yan mata.

28. Barin tarbiyyar `ya`ya a hannun mai reno, musamman

waxanda ba musulmi ba, ko kuma musulmin da ba su

san yadda a ke yin tarbiyya ba.

29. Yawan savani a tsakanin iyaye a gaban `ya`ya, ta yadda

`ya`yan za su koya.

30. Sava wa abin da a ke tarbiyyantar da `ya`ya a kansa, ta

yadda za a nuna masu muhimmancin wani abu, amma su

ga an aikata savaninsa.

YADDA A KE YIN TARBIYYAR `YA`YA

Musulunci gamammen addini ne; babu wani al’amarin da ya

shafi addini da rayuwa, face an yi bayaninsa dalla dalla. An

rattaba dalilan da ke jawo qasqanci da lalacewa a cikin

al’umma, kamar yadda aka bayyana hanyoyin samun nasara

da kuvuta daga kowace irin matsala. An samar da tanade-

tanaden da suka shafi tarbiyya, wadda za ta kai mutane ga

cin nasara. Tanade-tanaden musulunci dangane da tarbiyya

sun haxa da:

Page 52: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

52

1. Ba da muhimmanci ga zaven uwa/uba ta/na qwarai, a

lokacin yin aure, a bisa asasin addini da kyawawan

xabi’u, kasancewar hakan na taimakawa wajen samar da

tarbiyya ga `ya`yan da za a haifa, idan Allah Ya kawo.

Uwa ta qwarai, mai riqo da addini, tana da tasiri wajen

tarbiyyar `ya`yanta. Haka kuma, uba na qwarai, mai

addini da kyawawan xabi’u, yana xaukar dukkan

matakan da suka dace, don ganin `ya`yansa sun samu

tarbiyya, da ilmin addini da ilmin sana’a.

Zaven iyaye na qwarai na daga haqqoqin `ya`ya tun

kafin a haife su, kuma yana daga kyautatawar da iyaye

za su yi wa `ya`yansu. Abul Aswad Ad-Du’ali ya ce wa

`ya`yansa:

[Na kyautata maku, kuna qanana da bayan kun girma, da

kuma kafin a haife ku. Suka ce: ‘ta wace hanya ka

kyautata mana kafin a haife mu? Ya ce: ‚Na zavo maku

uwar da ba za a zage ku ba saboda ita]

Haka kuma, Ar-Rayāshi ya ce wa `ya`yansa:

[Farkon kyautatawa ta a gare ku shi ne da na zavar maku

(uwa) mai girmar nasaba da daraja, wadda ta yi fice a

wajen kamun kai]

2. Roqon Allah (Mai girma da xaukaka) zuriyya ta qwarai,

kamar yadda Annabawa da Manzanni (tsira da aminci su

tabbata a gare su) suka kasance suna yi;104

tare da neman

taimakon Allah a cikin yin tarbiyyar `ya`ya. Misali,

104

Aal Imrān, 3:38; Furqān, 25:74

Page 53: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

53

Annabi Ibrāhīm (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya

roqi Allah (Mai tsarki da xaukaka) Ya azurta shi da

salihan `ya`ya;105

Ya nisantar da shi tare da su daga

bautar gumaka;106

kuma Ya sanya shi da zuriyyarsa masu tsai da salla.

107 Haka kuma, Annabi Ibrāhīm (amincin

Allah ya tabbata a gare shi) ya roqi Allah (Mai girma da

xaukaka) Ya sanya zuriyyarsa daga cikin masu yin

jagoranci a cikin imani da taqawa da haquri da

da’awa;108

kuma Ya sanya su masu sallamawa ga Allah

(Mai girma da xaukaka).109

Haka kuma, Annabi

Zakariya (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya roqi

Allah (Mai tsarki da xaukaka) Ya ba shi zuriyya mai

kyau,110

wadda za ta yi aiki tuquru domin yardar da

Allah.111

3. Farin cikin samun haihuwa, da nisantar yin fushi ko

kuma jin xacin rai da baqin ciki, saboda an haifi mace ko

kuma saboda tsoron talauci.112

Yin baqin ciki saboda an

haifi `ya mace, ya qunshi matsaloli guda biyar: jayayya

da qaddarar Allah; da qin karvar kyautar Allah; da

kamanceceniya da xabi’ar mutanen jahiliyya; da

bayyana alamar wawanci da sakarci da jahilci da raunin

hankali; da kuma wulaqanta matsayin `ya mace.

Iyaye su yi qoqarin kiyaye ladubban da suka shafi jariri,

tun kafin haihuwarsa, da bayan an haife shi,113

da

105

Saffāt, 37:100 106

Ibrāhīm, 14:35 107

Ibrāhīm, 14:40 108

Baqarah, 2:124 109

Baqarah, 2:128 110

Aal Imrān, 3:38 111

Maryam, 19:6 112

Isrā, 17:31; Shūrā, 42:49 113

Ladubban sun haxa da: zaven abokan zama na qwarai tun lokacin da

a ke nufin yin aure bisa asasin addini da kyawawan xabi’u; da yin

Page 54: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

54

ladubban yin tahnīk,114

da ladubban sanya suna,115

da

yanka dabbar aqiqa,116

da aski,117

da kaciya.118

Babu

addu’a a lokacin kwanciyar aure; da kula da lafiyar uwa a lokacin da ta

ke goyon ciki; da nisantar abubuwan da ke iya kawo haxari ga abin da

ke cikin mahaifa (kamar shan giya ko taba sigari); da yin kyakkyawar

addu’a da zarar an haihu; da godiya ga Allah a kan kyautar da Ya yi

masu. 114

Tahnīk na nufin tauna dabino ko dandaqa shi don sanyawa a cikin

bakin jariri/jaririya bayan haihuwa. Idan an dandaqa ko an tauna

dabinon sai a xiba da yatsar hannun dama, a sanya a cikin bakin jariri, a

jujjuya, dama da hagu, don kowanne vangare ya samu. Bayan haka, sai

a yi addu’ar alhairi da neman albarka da shiriyar Allah gare shi. An so a yi tahnīk da zarar an yi haihuwa, ba tare da dogon jinkiri ba.

Haka Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da

sahabbansa (Allah Ya yarda da su) suka kasance suna yi. Ba daidai ba

ne a jinkirta wannan aiki zuwa kwana uku, a haqqin namiji, ko kwana

huxu, a haqqin mace, bisa hujjar cewa za a yi huxuba ga jariri/jaririya. Tahnīk ne ya tabbata a cikin Sunnah, ba wai wata huxuba ba.

Ana amfani da busasshen dabino wajen yin tahnīk. Amma Ibn Hajar

ya ce: ‚Idan mutum bai samu busasshen dabino ba, sai ya yi amfani da

kowane irin dabino. Idan bai samu ba, ana iya amfani da duk wani abu

mai zaqi. Sai dai kuma ana fifita zuma a kan sauran abubuwa masu zaqi.‛ [Ahmad bn Aliyyu bn Hajar, Fat-hul Bāri Sharh Sahīh al-Bukhārī, (Dār al-Fikr, Beirut, Lebanon, 1379AH), 9/588]

Da yawa daga malamai na ganin cewa a dandaqa dabinon ya fi a

tauna. Suka ce, tauna dabino ya kevanci Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ne saboda albarkar da ke cikin

yawunsa. Wannan ya sa ba a samu sahabbai sun tauna ba bayan

rasuwar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai

dai dandaqawa.

Iyayen jariri (uwa ko uba) ko kuma wani daga cikin mutanen kirki ne ya kamata su yi wa jariri tahnīk. Ana iya neman wani bawan Allah,

mai ilmi da taqawa, wanda ya fahimci Sunnah kuma ya ke aiki da ita

gwargwadon iko, wanda a ke sa ran karvar addu’arsa saboda biyayyarsa ga Allah, ya yi tahnīk da addu’a ga jariri ko jaririya a

madadin iyayen.

Huxubar da mutane ke yi wa jarirai bayan kwana uku (a haqqin

namiji) ko kwana huxu (a haqqin mace) wadda ta qunshi kiran salla a

kunnen dama, da yin iqama a kunnen hagu, ko kuma kiran salla a

kunnen dama da hagu, ba ta da inganci. Hadisin da ke magana a kan

Page 55: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

55

kiran salla a kunnen dama, da yin iqama a kunnen hagu, ba shi da

inganci ko kaxan. Hasali ma, malamai sun tabbatar da cewa hadisi ne

na qarya (maudu’). Shi kuma hadisin da ke magana a kan kiran salla kawai, ba tare da iqama ba, mai rauni ne (da’īf). Ke nan, ba za a iya

kafa hujja ko a yi aiki da shi ba a cikin wannan muhimmiyar mas’ala.

Don haka, kiran salla da iqama, ko kuma kiran salla kawai da a ke yi

wa jarirai, da sauran abubuwan da a ke yi, da sunan huxubar haihuwa,

ba su tabbata ba. Abin mamaki shi ne yadda mutane da yawa suka jahilci Sunnar tahnīk. Mutane da yawa ba su yi, kuma ba su sanyawa a

yi wa `ya`yansu. Maimakon haka, sai su nemo liman ko wani dattijo

don ya yi huxuba, wani lokaci ma a haxa da surkulle, kai har da sanya

baki a cikin kunnen jariri, a ce: sunanka wane. 115

Wajibi ne iyaye su sanya wa `ya`yansu suna mai kyau, kuma a

lokacin da ya dace. Nazari cikin hadisai ingantattu na tabbatar da lokuta

biyu da a ke iya sanya wa jarirai suna: ranar bakwai ko kuma tun daga

lokacin da aka haihu har zuwa ranar bakwai. Dalili a kan haka yana

qunshe cikin ingantattun hadisai da yawa. Misali, Samurah (Allah Ya

yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce: ‚Kowane yaro (da aka haifa) jingina ce ga aqiqarsa

(dabbar da a ke yankawa). Za a yanka masa a ranar bakwai, a sanya masa suna, kuma a yi masa aski‛ [Ahmad da Abu Dāwud]. Haka

kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

yi umurni da sanya suna ga abin da aka haifa a rana ta bakwai, da kawar da qazanta (gashi) gare shi, da yanka masa dabba [Tirmidhī].

Haka kuma, Anas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚An haifar mani xa

namiji a daren yau, kuma na sanya masa sunan babana (kakana) Ibrāhīm‛ [Muslim]. Haka nan, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya sanya wa Abdullah ibn az-Zubair, da Abdullah ibn Abi Xalhah, da Ibrāhīm ibn Abi Mūsa al-`Ash’arī, da al-Mundhir,

suna a ranar da aka haife su [Bukhari da Muslim].

Daga hadisan da suka gabata, za a fahimci cewa Shari’a ta ba da

damar sanya suna ga jarirai tun daga lokacin da aka haife su har zuwa rana ta bakwai. Baihaqī na ganin cewa hadisan da suka yi magana

game da sanya suna a lokacin da aka yi haihuwa sun fi hadisan da ke

magana a kan jinkirtawa zuwa ranar bakwai inganci. Amma da yawa

daga malamai sun ce jinkirtawa zuwa rana ta bakwai mustahabbi ne,

saboda la’akari da maganar da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya yi. Sanya suna a ranar da aka yi haihuwa kuwa,

Page 56: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

56

halal ne saboda aikin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) ya tabbatar da hakan.

Waxansu malamai na ganin cewa jinkirta sanya suna har zuwa ranar

bakwai shi ne ya fi idan akwai halin yanka dabbar aqiqa (ragon suna).

Idan kuwa ba za a yanka dabbar ba, sai a sanya sunan tun daga lokacin

da aka yi haihuwar. Amma dai magana mafi qarfi ita ce an so a jinkirta

sanya suna zuwa rana ta bakwai, amma ya halatta a sanya sunan tun

daga ranar haihuwa, ba tare da la’akari da cewa za a yanka dabba ko ba

za a yanka ba. Wannan shi ne abin da hadisan suka tabbatar qarara.

Uba (mahaifi) shi ne ke da haqqin zavar wa xansa suna mai kyau ta

hanyar yin shawara da uwa (mahaifiya). Idan suka yi savani game da

sunan da za a sanya, haqqin sanyawar na ga uba. Idan ya so ya zava da

kansa, idan ya so ya bar uwar ta zava, ko ya yi quri’a a tsakaninsu, ko

ya ba wani mutum damar zavar sunan gare su.

Zaven suna mai kyau, na daga haqqoqin `ya`ya a kan iyayensu.

Sanya wa `ya`ya sunan da ya dace, zai haifar masu da jin daxi, kuma

zai sanya su kazarkazar duk lokacin da aka kira su da shi. Rashin sanya

suna mai kyau yana dakushe tunanin yara da tauye matsayinsu a cikin

al’umma, musamman idan suka fahimci ma’anar sunan, bayan sun

girma. Don haka, wajibi ne iyaye su sanya wa `ya`yansu suna mai

ma’ana, da kyakkyawar lafazi.

Malamai sun bayyana matakai guda biyar waxanda iyaye za su bi

wajen zaven suna mai ma’ana ga `ya`yansu. Kowane mataki ya fi

wanda ke qasan shi daraja. Matakan su ne: sanya sunan Abdullah da Abdur-Rahmān, kasancewar su ne sunayen da Allah (Mai tsarki da

xaukaka) Ya fi so [Muslim da Abu Dawud]; sanya sunan da ke nuna bauta ga Allah, kamar Abdur-Rahīm, Abdul-`Azīz, Abdul-Karīm, da

Abdur-Razzāq; sanya sunan xaya daga cikin Annabawa da Manzanni

(tsira da aminci su tabbata a gare su); sanya sunayen magabata na

qwarai (maza ko mata), kamar sahabbai da tabi’ai da shahidai da

malaman Sunnah; da sanya duk wani suna da ya qunshi lafazi da

ma’ana mai kyau, wanda ke nuna sadaukantaka, ko kamun kai, ko

taqawa. 116

Aqīqah ita ce dabbar da a ke yankawa a rana ta bakwai, ko goma

sha huxu, ko ashirin da xaya, bayan haihuwa. Yanka dabba (rago ko

tunkiya ko bunsuru ko akuya) ga wanda aka haifa, na daga ladubban

Shari’a, waxanda a ke son iyaye su aikata, saboda murna da godiya ga

Allah bisa ni’imarSa da baiwar da Ya yi masu ta samun qaruwa.

Malamai sun yi savani game da hukuncin dabbar da za a yanka wa

wanda aka haifa. Waxansu na ganin cewa wajibi ne a kan duk wanda

Page 57: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

57

ke da iko. Sun kafa hujja da maganar Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi): ‚Tare da yaro akwai aqiqar (da za a yanka

masa), don haka, ku zubar da jini a madadinsa…‛ [Abu Dawud da

Tirmidhi]; da hadisin: ‚Kowane yaro jingina ce ga aqiqarsa: za a yanka

masa a rana ta bakwai, kuma a sanya masa suna, a yi masa aski a

wannan rana‛ [Ahmad, Abu Dawud, Tirmidhi, Nasa’i da Ibn Majah].

Suka ce: a cikin hadisin farko, akwai umurnin da Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi game da yanka dabba ga

wanda aka haifa. Sananniyar qa’ida ce cewa umurni na nuna wajibci,

matuqar ba a samu wani dalilin da ke nuna savanin haka ba. Hadisi na

biyu ya nuna qarara cewa kowane yaro na matsayin jingina ce har sai

an yanka masa dabba kafin a fanshe shi. Wannan ra’ayi ya fi qarfi, in

sha Allah. Saboda haka, yanka dabba ga wanda aka haifa, wajibi ne a

kan uba, matuqar yana da iko. Ibn Hazm na daga cikin malaman da ke

ganin wajibci, kuma ya kawo dalilai masu yawan gaske don qarfafa

wannan fahimta. Haka kuma, Ibn al-Mundhir ya ruwaito daga Yahya al-Ansāri cewa salaf (sahabbai da taba’ai) ba su gushe ba, suna ganin

wajibcin yanka dabba ga wanda aka haifa.

Sunnar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ta tabbatar cewa ana yanka wa xa namiji dabbobi guda biyu,

madaidaitan shekaru; `ya mace kuma a yanka mata guda xaya. Wannan ya dace da fatawar Ibn Abbās (Allah Ya yarda da su), da mafi

yawan malamai, kamar Imam as-Shāfi’ī da Ahmad ibn Hanbal.

Hujjojinsu na qunshe a cikin hadisan da Aa’ishah da Umm Kurz da

Amr ibn Shu’aib (Allah Ya yarda da su) suka ruwaito. Ibn Umar (Allah Ya yarda da shi) da Imam Mālik na ganin cewa dabba xaya ce za a

yanka wa xa namiji ko `ya mace.

Haka kuma, Sunnah ta tabbatar da cewa ana iya yanka rago ko

tunkiya ko bunsuru ko akuya. Duk dabbar da aka yanka daga cikin

waxannan, ta wadatar. Amma ba a yin amfani da sauran nau’o’in dabbobi, kamar raquma da shanu, a wajen aqīqa.

Ana yanka dabbar aqiqa ce a ranar bakwai, ko da kuwa an sanya wa

jaririn ko jaririyar suna kafin ranar bakwai. Magana mafi qarfi ita ce za

a fara qirga ranakun ne daga ranar da aka yi haihuwa, ba wai daga

kashegarin ranar haihuwa ba. 117

Aske kan jariri/jaririya na daga cikin abubuwan da a ke son a yi a rana ta bakwai ga haihuwa. Da zarar an yanka aqīqa, sai a gabatar da

aski, a bisa hadisan da suka gabata. Malamai sun yi savani game da `ya

mace: shin za a yi mata aski kamar namiji? Magana mafi qarfi ita ce:

hukuncin wannan aski ya shafi namiji da mace, kasancewar babu wani

Page 58: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

58

shakka, kiyaye waxannan ladubba na da matuqar tasiri a

kan tarbiyyar `ya`ya.119

4. Koya masu magana ta hanya mai sauqi. An so kalmar

shahada, wato, , ta zamanto abin da za

dalili mabayyani da ya kevance xaya, ya bar xayan. Hadisan da suka zo

da lafazin ‘yaro’ ( ), na xaukar ma’anar namiji da mace, kamar yadda

kalmar ‘wanda aka haifa’ ( ), ta ke xauka. 118

Kaciya na xaya daga cikin abubuwan da a ke buqatar a yi wa jariri/jaririya a ranar bakwai da haihuwa. Kaciyar maza (khitān) ta

qunshi yanke fatar da ke kewaye da kan azzakari. Kaciyar mata kuwa

(khafd), ta qunshi rage fata ko xan tozon (clitoris) da ke kan farji, wato

tsele. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

sanya kaciya a matsayin xaya daga cikin ayyukan fixrah (xabi’un

addinin Musulunci waxanda Allah Ya halicci mutane a kansu) da a ke

buqatar kowane Musulmi ya kula da su.

Malamai sun yi savani game da hukuncin kaciya. Magana mafi qarfi

ita ce, kaciya wajibi ne a haqqin xa namiji, kuma Sunnah a haqqin `ya mace. Wannan ita ce fatawar Imam Mālik, as-Shāfi’ī da Ahmad ibn

Hanbal. Kuma wannan shi ne abin da ya shahara tun daga zamanin

sahabbai (Allah Ya yarda da su) har zuwa tabi’ai da tabi’ut-tabi’in

(Allah Ya jiqansu), da waxanda suka biyo bayansu.

Mafi yawan malamai na ganin cewa babu wani lokaci na

musamman da aka iyakance don yin kaciya. Kowane lokaci aka so, sai

a yi. Amma waxansu malamai sun ce mustahabbi ne a yi wa

jariri/jaririya kaciya a ranar bakwai. Abin lura shi ne binciken likitanci

ya tabbatar da cewa, kaciya ta fi saurin warkewa idan aka yi ta a ranar

bakwai ko kafin wannan rana, fiye da idan an jinkirta, kasancewar jiki

na samun kariya ta musamman a wannan tsakani. Haka kuma, waxansu muhimman sanadaran jiki, kamar white blood cells da anti-bodies na

yin aiki cikin sauri da sauqi, a wannan tsakani, don kare jiki daga

kamuwa da cututtuka, a sanadiyar yanka ko rauni. Bayan wannan, blood coagulation, da kuma zuciya (liver) na yin aiki sosai, kuma

vitamin K na samuwa a makon farko na haihuwa. Ke nan, yin kaciya a

ranar bakwai ya fi fa’ida, matuqar babu wata larurar da za ta hana a

gudanar da ita a wannan rana. 119

Karanta littafi na Ni’imar Haihuwa da Haqqoqin `Ya`ya a Musulunci

Page 59: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

59

a fara koya wa yaro a cikin rayuwarsa, ta yadda zai saba

da ita sosai. Kuma da zarar ya fara wayo, a sanar da shi

ma’anarta, da abin da ta qunsa. Ibn al-Qayyim ya ce:

Farkon abin da za a koya wa yara idan lokacin da za su

fara magana ya zo shi ne: , wato, ya

kasance farkon abin da zai fara shiga cikin kunnuwansu

shi ne: sanin Allah da tauhidinSa, kuma da sanin cewa

Allah Yana sama, Ya daidaitu a kan al’arshinSa;120

Yana

120

Ayoyin Alqur’ani masu yawa, da hadisai ingantattu, da maganganun

Salaf sun tabbatar da cewa Allah (Maxaukaki) Yana sama (al-Uluw), kuma Ya daidaita a kan al’arshinSa (al-Istiwā), daidaituwar da ta dace

da Shi. Daga cikin ayoyin Alqur’ani da suka tabbatar da haka, akwai:

1. Kuma Shi ne al-Qāhir (Mai rinjaya) bisa ga bayinSa…‛

[An’ām, 6:18, 61].

2. Suna tsoron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin

da a ke umurnin su‛ [Nahl, 16:50].

3. Zuwa gare Shi magana mai daxi ke hawa, kuma aiki na qwarai Yana xaukar ta‛ [Fāxir, 35:10].

4. A lokacin da Allah Ya ce: ‚Ya Isa! Ni Mai karvar ranka ne, kuma Mai xauke ka ne zuwa gare Ni..‛ [Aal Imrān, 3:55].

Daga cikin hadisan da suka tabbatar da cewa Allah (Maxaukaki)

Yana sama, kuma Ya daidaita a kan al’arshinSa, daidaituwar da ta

dace da Shi, akwai:

1. Hadisin da Bukhari ya ruwaito daga Anas (Allah Ya yarda da

shi) cewa Zainab bnt Jahsh (xaya daga cikin matan Annabi) ta

kasance tana yin alfahari ga sauran matan Annabi (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa iyayensu ne suka

aurar da su ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi); amma ita, Allah (Mai girma) ne da kanSa Ya aurar

da ita ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) tun daga bisan sama bakwai.

Page 60: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

60

2. Hadisin da Muslim ya ruwaito daga Mu’āwiyah bn al-Hakam

cewa ya zo da wata baiwarsa zuwa ga Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi). Sai Annabi (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tambaye ta: ‚Ina Allah

Yake? Sai ta ce: ‚Yana sama‛. Sai ya ce: ‚Wane ne ni‛? Ta ce:

‚Manzon Allah‛, sai ya ce: ‚`yanta ta, domin kuwa mumina

ce‛.

3. Hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito cewa Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Yanzu ba za ku amince mani ba, alhali kuwa ni ne wanda

(Allah da) ke sama Ya amince wa?‛

4. Hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Abu

Hurairah (Allah Ya yarda da shi), Annabi (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Bayan Allah Ya kammala

halitta, sai Ya rubuta a cikin littafin da ke wajenSa a saman

al’arshinSa: ‘Rahamata ta rinjayi fushina‛.

5. Hadisin da Muslim ya ruwaito daga Jābir (Allah Ya yarda da

shi), da ke magana a kan Isra’i da Mi’irajin da Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi daga

Makkah zuwa Masjid al-Aqsa, daga nan kuma, zuwa wajen

Allah a can bisan sama ta bakwai‛.

6. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

ce: ‚Ku yi jin qai ga (bayin Allah) waxanda ke qasa, sai (Allah) Wanda ke sama Ya ji qanku‛ [Tirmidhī ya ruwaito

kuma ya ce: Hasan Sahīh].

7. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

ce: ‚Babu wata macen da mijinta zai kira ta zuwa ga

shimfixarsa, amma ta qi zuwa, face (Allah) Wanda ke sama Ya

yi fushi da ita har sai mijinta ya yarda da ita‛ [Muslim].

Daga cikin bayanan da aka ruwaito daga Salaf dangane da wannan

mas’ala, akwai:

1. Maganar da ‘Abdullah bn Ahmad, da Ibn Abi Shaybah, da al-Lālakā’ī, da Ibn ‘Abdil-Barr, da al-Mundhirī suka ruwaito

Page 61: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

61

cewa Abu Bakr, da Umar, da Uthmān, da Aliyyu, da Ibn

Abbās, da Ibn Mas’ūd, da sahabbai masu yawan gaske sun

tabbatar da cewa Allah (Mai girma) Yana sama [Duba littafin Ithbāt Siffah al-Uluw na Ibn Qudāmah al-Maqdisī, shafi na 45-

73, da at-Tuhfah al-Madaniyyah fi al-`Aqīdah as-Salafiyyah na

Hamd bn Nāsir bn Uthmān Aali Ma’amar, shafi na 29-50]

2. Bayanai ingantattu da aka ruwaito daga Sufyān at-Thaurī, da

al-Hasan al-Basarī, da al-Auzā’ī, da Imām Abu Hanīfah, da

Mālik, da ash-Shāfi`ī, da Ahmad, da ad-Dahhāk, da Rabī`ah bn

‘Abdir-Rahmān, da malamai masu yawa daga cikin tabi’ai da

tabi’ut-tābi’in cewa Allah Yana sama [Duba littafin Ithbāt Siffah al-Uluw na Ibn Qudāmah al-Maqdisī, shafi na 110-132 ;

da at-Tuhfah al-Madaniyyah fi al-`Aqīdah as-Salafiyyah na

Hamd bn Nāsir bn Uthmān Aali Ma`amar, shafi na 71-101].

Dangane da daidaituwar Allah (al-Istiwa) a saman al’arshinSa,

daidaituwar da ta dace da Shi, ayoyin Alqur’ani guda bakwai sun tabbatar da haka. Ayoyin su ne: A’arāf, 7:54; Yunus, 10:3; Ra’ād, 13:2;

Xāha, 20:5; Furqān, 25:59; Sajdah, 32:4; da Hadīd, 57:4.

Daga bayanan da suka gabata, za a fahimci cewa Allah (Mai girma

da xaukaka) Yana sama, kuma Ya daidaita a kan al’arshinSa,

daidaituwar da ta dace da girmanSa. Amsar da waccan baiwa ta ba da, a

lokacin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ya tambaye ta wurin da Allah Ya ke (ta ce: Yana sama), ita ce amsar da

ya kamata kowane musulmi na qwarai ya karva, matuqar dai ba yana

ganin ya fi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

sanin tauhidi ba ne. Imam adh-Dhahabī ya tattara maganganun Sahabbai da Tabi’ai da

Tabi`ut-Tābi`īn da waxanda suka bi hanyar magabata na qwarai (Salaf) waxanda ke tabbatar da cewa Allah Yana sama, kuma Ya daidaita a

kan Al’arshinSa. Ya ruwaito irin wannan fahimta daga magabata fiye da xari biyu (200) a cikin littafinsa mai suna al-Ulū lil `Alī al-Ghaffār. Abu Ismā`īl al-Ansārī ya ruwaito, a cikin littafinsa ‘al-Furūq’, cewa

an tambayi Imam Abu Hanīfah game da mutumin da ya ce bai san inda

Allah Ya ke ba. Sai Abu Hanīfah ya amsa da cewa: ‘ya kafirta’, domin

kuwa Allah Ya ce: ‚Mai Rahama, Ya daidaita a kan Al’arshi‛ [Xāha,

20:5], kuma Al’arshinSa yana bisan sama bakwai’. Sai aka ce masa to

idan mutum ya ce Allah Yana saman Al’arshi amma kuma bai san inda Al’arshin ya ke ba (a sama ne ko a qasa) fa? Sai (Abu Hanīfah) ya ce:

Page 62: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

62

ganinsu, Yana jinsu, kuma Yana tare da su (da ilminSa,

da jinSa, da ganinSa, da ikonSa, da qudurarSa) a duk

inda su ke.‛121

5. Dasa masu imani da aqida sahihiya tun suna qanana, da

tsoratar da su daga munanan aqidu da haxarin shirka da

bidi’a a cikin addini. Idan yara suka taso da fahimtar

sahihin tauhidi da aqida ta qwarai, wadda ta dace da

Alqur’ani da Sunnah ingantacciya, bisa fahimtar

magabata na qwarai, a na fatan su kafu a cikin addini,

kuma su goge a kan karantarwarsa.

Babu shakka, koya wa yara kalmar shahada da

sharuxxanta, da rukunan imani, da abubuwan da suka

qunsa, da abubuwan da ke warware kalmar shahada, da

sauran vangarorin tauhidi, waxanda mutane ke sakaci

game da su, abu ne muhimmi.122

Idan yaro ya fahimci

‘ya kafirta’, domin kuwa ya yi musun cewa Allah Yana sama. Wanda

duk ya yi musun haka kuwa, ‘ya kafirta’‛ [Duba littafin at-Tuhfah al-Madaniyyah fil `Aqīdah as-Salafiyyah na Hamd bn Nāsir bn Uthmān

Aali Ma’amar]. Imam Mālik ya tabbatar da kasancewar Allah Yana sama, kuma Ya

daidaita a kan al’arshinSa, daidaituwar da ta dace da Shi. Haka kuma, Abul Hasan ‘Aliyyu al-Ash`arī, wanda mutane da yawa ke da’awar

koyi da shi a cikin aqidar sufanci, ya tabbatar da cewa Allah Yana sama, a cikin littafansa ‘al-Ibānah an usūl ad-Diyānah’ da ‘al-Maqālāt al-Islāmīyīn’. Ban da waxannan, Ibn Abi Zayd al-Qīrawānī al-Mālikī,

ya tabbatar da daidaituwar Allah a kan al’arshinSa a sama, a cikin mashahurin littafinsa ar-Risālah. 121

Tuhfah al-Maudūd, shafi na 158 122

Vangaren farko na kalmar shahada, wato, na da sharuxxa

guda tara (9). Waxannan sharuxxa su ne mabuxin kai wa ga duk wata

falala da aka tabbatar wa kalmar shahada. Sharuxxan su ne: ilmin da

ke kore jahilci [Muhammad, 47:19; Zukhruf, 43:86]; yaqini wanda ke kore shakku [Hujurāt, 49:15]; karvar abin da kalmar ta qunsa, da kuma

yarda da abin da ta ke lazimtawa, a kan harshe, da cikin zuciya [Saffāt,

37:35-36]; miqa wuya da sallamawa da jawuwa zuwa ga kalmar, ta

Page 63: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

63

hanyar tabbatar da ita a aikace [Luqmān, 31:22; Zumar, 39:54; Nisā,

46:5; Ahzāb, 33:36]; gasgata kalmar, da karvarta, ba tare da wasa ko

yaudara ba [Ankabūt, 29:1-3; Baqarah, 2:8-10]; tsantsar ikhlasi da

kuma yarda da kalmar saboda Allah, ba tare da munafinci ba [Zumar,

39:2; Bayyinah, 98:2]; son kalmar, da kuma qin duk abin da ya sava ma ta [Baqarah, 2:165; Mā’idah, 5:54; Taubah, 9:2]; kafirce wa duk

wani xagutu, da sauran tsare-tsaren da suka sava wa na Allah [Baqarah,

2:256]; tabbatuwa da dogewa a kan kalmar, har zuwa mutuwa [Aal Imrān, 3:102]

Vangare na biyu na kalmar shahada, wato, na lazimta: (1)

imanin cewa Muhammad ibn Abdillah manzo ne daga Allah (2)

gasgata shi cikin duk abin da ya ba da labari (3) yin masa xa’a cikin

umurni da hani (4) taqaita yin bautar Allah (Mai girma da xaukaka) ga

abin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

shar’anta (5) qudurce cewa shi ne Annabin qarshe, kuma shugaban

Manzanni (6) qudurce cewa saqon da ya zo da shi daga wajen Allah

(Mai girma da xaukaka) gamammen saqo ne ga mutane da aljannu. Al-walā (soyayya da jivinta al’amari) wal Barā (qiyayya da tawaye)

na daga abubuwan da kalmar shahada ke lazimta wa kowane musulmi a cikin zuciyarsa, kuma tasirin hakan ya bayyana a gavuvvansa. Al-walā ya qunshi son `yan’uwa musulmi, da jivinta al’amari a gare su, saboda

imaninsu da xa’arsu ga Allah, ba tare da la’akari da bambancin ra’ayi ko fahimta ko jinsi ba. Al-barā ya qunshi yin qiyayya da tawaye ga

kafirai da munafikai, saboda kafircinsu ko munafincinsu, da sava wa

Allah da su ke yi, ba tare da la’akari da dangantaka ko zumunci ko

matsayi ba. Al-walā wal-barā, na daga cikin al’amuran tauhidi, wanda kafiran

duniya su ke qoqarin ganin an yi watsi da su a wannan lokaci, ta yadda

Musulmi zai daina kishin addininsa gaba xaya, kuma ya daina qyamar

kafirci ko nuna qiyayya ga kafirai. Burin su shi ne, a wayi gari,

Musulmi ya daina ganin bambanci a tsakanin xan uwansa Musulmi da

kuma arne, ko kuma ya riqa ganin cewa babu bambanci tsakanin

Musulunci da kafirci. Wannan ya sa suka xauki matakan qyamatar wa Musulmi alamomin da ke tabbatar da Al-walā ga muminai da kuma Al-barā ga kafirai.

Yana daga alamomin da ke tabbatar da al-walā ga muminai: yin

qaura daga qasashen kafirai zuwa qasashen musulmi; da taimakon

musulmi ta hanyar amfani da dukiya da jiki da harshe; da tausaya wa

musulmi a duk lokacin da wani abin baqin ciki ya same su, da yin farin

ciki a duk lokacin da wani alhairi ya same su; da yin masu nasiha da ba

Page 64: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

64

tauhidi tun yana qarami, zai taso da kyakkyawar

fahimtar addini, ta yadda zai kuvuta daga kwamacala, da

canfe-canfe, da munanan al’adu, da tsoron wanin Allah,

kamar aljannu ko dodo, da sauransu. Kuma a na sa ran

su shawara; da mutunta musulmi da girmama su, tare da nisantar

qasqantar da su ko faxin aibi game da su; da kasancewa tare da su a

cikin kowane irin hali da yanayi; da ziyartar su, da son haxuwa da su;

da girmama haqqoqinsu, da ba su haqqoqin da suka cancanta; da yin

masu addu’ar alhairi, da nema masu gafarar Allah (Mai girma da

xaukaka).

Yana daga alamomin da ke nuna soyayya ga kafirai, maimakon a yi

qiyayya da su: koyi da su wajen tufafi da kevantattun al’adunsu; da

ziyartar qasashensu don yawon shaqatawa da buxe ido; da taimakon

kafirai a kan musulmai; da kare martabar kafirai da yabonsu; da amince

masu, ta yadda za a bayyana sirrin musulmi a gare su; da amfani da

ranakun hutun da ke cikin kalandarsu; da taimakonsu wajen bikin

kirsimati ko taya su murnar kirsimati da sauran bukukuwansu na

addini; da amfani da sunayensu; da yin masu addu’ar neman gafara

bayan sun mutu; da fara yin masu sallama idan an haxu da su. Wajibin kowane Musulmi ne ya tabbatar da manufar Al-walā wal-barā a cikin rayuwarsa gaba xaya, ko da kuwa fanxararrun mutane za

su zarge shi da ta’addanci ko tsanani a cikin addini. Sanannen abu ne cewa, ba domin Al-walā wal-barā ba, ba za a bambance tsakanin

al’ummar musulmai da ta kafirai ba.

Kalmar shahada na warwarewa idan aka aikata xayan waxannan

abubuwa: (1) shirka ko munafinci babba ko kafircin da ke fitar da

mutum musulunci (2) xaukar waxansu mutane a matsayin tsani a

tsakanin bawa da Allah, da dogaro da su, da neman taimakonsu a cikin

abubuwan da babu wanda ke da iko sai Allah (Mai girma da xaukaka)

(3) rashin xaukar mushirikai a matsayin kafirai ko kuma yin shakku

game da kafircin kafirai (kamar maguzawa da kirista da yahudu da

sauransu) (4) xaukar cewa akwai wata shiriyar da ta fi shiriyar Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) (5) qin wani abu da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zo da

shi, ko da kuwa an yi aiki da shi (6) yin izgili ga wani sashe na addinin

musulunci ko wani sakamako da musulunci ya tabbatar (7) sihiri da

tsafi (8) taimakon mushirikai a kan musulmai (9) qudurta cewa akwai

waxanda ba su da buqatar bin shari’ar Allah, saboda matsayinsu a

wajen Allah (Mai girma da xaukaka) (10) juya wa addinin Allah (Mai

girma da xaukaka) baya.

Page 65: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

65

ya taso da kishin addininsa, da ganin girman Allah (Mai

girma da xaukaka) da ManzonSa (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi), da rashin damuwa, ballantana,

ruxuwa da tsare-tsaren da suka sava wa na Allah

(Maxaukaki). Wannan yasa Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana

koya wa yara mas’alolin tauhidi dabam daban,

musamman waxanda mutane suka fi yin kurakurai a kai.

Hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya tambayi wata yarinya

(baiwa): ‚Ina Allah Ya ke? Ta ce: Yana sama. Ya ce: Ni

wane ne? Ta ce: Manzon Allah. Sai (Manzon Allah) ya

ce (wa maigidanta): ‚`Yanta ta, domin kuwa mumina ce.‛

123 Haka kuma, ya ce wa Abdullah ibn Abbās (Allah

Ya yarda da su): ‚… Kuma idan za ka yi roqo, ka roqi

Allah; idan za ka nemi taimako, ka nemi taimakon

Allah…‛124

6. Fahimtar da `ya`ya wajibcin son Allah (Mai tsarki da

xaukaka), da son Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi), da sahabbai (Allah Ya yarda da

su) da mutanen gidan Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi), da sauran mutane na qwarai,

waxanda ke bin Alqur’ani da Sunnah, sau da qafa, tun

daga tabi’ai (Allah Ya jiqansu) har zuwa yau.125

Ta

123

Muslim 124

Ahmad da Tirmidhi: Sahīh 125

Karatun Alqur’ani da Sunnah da aiki da abin da suka qunsa shi ne

zaman lafiya ga kowane musulmi. Alqur’ani maganar Allah ce da aka

saukar wa Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi),

kuma a ke bauta wa Allah ta hanyar karanta shi. Sunnah ta qunshi duk

wata magana ko aiki ko tabbatarwa ko siffar halitta ko siffar xabi’a da

aka danganta zuwa ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Da yawa daga malamai na xaukar ‘Sunnah’ da ‘Hadīth’ da

‘Athar’ da ‘Khabar’ a matsayin abu xaya.

Page 66: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

66

Alqur’ani littafi ne da ya qunshi shiriya, da haske, da rahama, da

waraka. Yana qunshe da labarin al’ummomin da suka gabace mu, da

abubuwan da za su zo a bayanmu, da hukunce-hukuncen da ke

tsakaninmu: wanda ya sanya Alqur’ani a gaba, zai yi masa jagoranci

zuwa ga aljanna; wanda ya sanya shi a bayansa, zai tunkuxa shi zuwa

wuta.

Alqur’ani bayani ne na gaskiya, wanda ya qunshi hikima, da wa’azi, da hujjoji mabayyana, da ambato na dindindin [Nahl, 16:89; Isrā, 17:9;

Yunus, 10:57]. Littafi ne da bai qunshi tukka da warwara ba, kuma varna ba ta shigo masa ta kowace fuska [Nisā, 4:82; Fussilāt, 41:42].

Littafi ne da ya yi wa kansa shaidar asali, kuma ya tabbatar da

mu’ujizar kansa, sannan, ya qalubalanci wanda ke da shakku ko kokwanto a kansa [Isrā, 17:88; Hud, 11:13; Yunus, 10:38; Baqarah,

2:23]. Littafi ne da ya ke da sunaye guda biyar [Baqarah, 2:185; Kahf, 18:1; Furqān, 25:1; Hijr, 15:9; Nisā, 4:174] da siffofi fiye da hamsin,

kamar yadda ya zo a cikin littafin Al-Burhān fi Ulūmil Qur’ān na Az-

Zarkashi, kuma Abdullah ibn Fodio ya naqalo a cikin littafin Al-Farā’idul Jalīlah.

Sunnah ita ce wahayi na biyu ( ) da ba a bauta wa Allah ta

hanyar mujarradin karanta shi ( ), savanin Alqur’ani, wanda a

ke bauta wa Allah ta hanyar mujarradin karanta shi. Allah (Maxaukaki)

Ya yi wa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

wahayin Sunnah kamar yadda Ya yi masa wahayin Alqur’ani, kuma Allah Ya kira ta da suna Hikmah [Aal Imrān, 3:164; Nisā, 4:113;

Baqarah, 2:231, 129, 151; Juma’ah, 62:2; Ahzāb, 33:34].

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya saukar da Alqur’ani ga Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), kuma Ya umurce

shi da yin bayani game da abin da Alqur’ani ya qunsa [Nahl, 16:44].

Bayanin da aka umurci Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya yi, ya qunshi (1) isar da Alqur’ani da karantar da shi gaba xaya [Mā’idah, 5:67] (2) bayanin lafazi ko jumla ko aya, tare

da bayanin hukunce-hukuncen da ke cikin ayoyin Alqur’ani gaba xaya,

ta hanyar qarfafa umurni ko hani, da qarin bayani ta fuskar rarrabe abin

da ya zo a dunqule ko iyakance sakakken hukunci ko keve gamammen hukunci ko bayanin Nāsikh da Mansukh ko bayanin hukuncin da ya zo

savanin zahiri (3) zuwa da wani hukuncin da ba shi a cikin Alqur’ani,

kamar xaure mazinacin da bai tava yin aure ba bayan bulala xari, da

hukuncin saduwa da iyali a lokacin azumi, da haramcin zinare da siliki

ga maza.

Page 67: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

67

wannan hanya ce, yara za su taso a matsayin ahlus-

sunnah cikakku, waxanda za su bi hanyar magabata na

qwarai.126

Wajibi ne kowane musulmi ya yi riqo da Alqur’ani da Sunnah,

domin kuwa: (1) su ne wahayin da Allah (Maxaukaki) Ya yi wa

bayinSa umurni da su yi riqo da shi (2) su ne kawai za a riqe domin a

kuvuta daga vata da barin hanyar Allah (3) duk wanda ya bar Sunnar

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya halaka

(4) Sunnar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ta qunshi dukkan abin da ke kai mutane aljanna (5) Alqur’ani da

Sunnah ne kawai za su iya haxa kan musulmi (6) ta hanyar Sunnah ce

kawai za a iya fahimtar bidi’a da musibarta da sharrinta (7) riqo da

Alqur’ani da Sunnah a bisa fahimtar magabata na qwarai shi ne

maganin karkacewar fahimta da shiga ruxu, kuma shi ne rigakafin

bidi’a da vata. ,

126 Ahlus-Sunnah su ne waxanda ba su da wani wanda su ke yi wa

biyayya kai tsaye, ta kowane hali da yanayi, kuma a cikin magana da

aiki, sake ba qaidi, sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi), farin jakada. Su ne waxanda suka fi kowa sanin

maganganun Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi), da ayyukansa, da halayensa, kuma su ne waxanda suka fi kowa iya

bambancewa tsakanin abin da ya inganta daga gare shi, da wanda bai

inganta ba. Su ne sahabbai (Allah Ya yarda da su) da tabi’ai da

waxanda suka bi hanyarsu bisa kyautatawa, kuma suka ta’allaqa

fahimtar addini bisa fahimtarsu.

Ahlus-Sunnah su ne Salafiyyun ( ), kamar yadda Ibn Hazm [a

cikin littafin Al-Fisal] da Ibn Taimiyyah [a cikin Majmu’ul Fatāwa]

suka bayyana. Su ne Ahlul Hadīth ( ) ko As-hābul Hadīth (

), kamar yadda As-Sābunī [a cikin littafin Sharhul Aqīdatis

Salafiyyah] ya bayyana, kuma aka ruwaito irin wannan magana daga Imam Ahmad ibn Hanbal da Ibnul Mubārak. Su ne a ke kira Ahlul

Athar ( ) ko Ahlul Ittibā’ ( ), saboda riqonsu ga Sunnah a

bisa fahimtar magabata. Su ne Al-Firqatun Nājiyah ( ), kamar

yadda aka ruwaito daga Ibn Jarīr Ax-Xabarī da Ad-Dahhāk da Ibn

Baxxah. Su ne Ax-Xā’ifatul Mansūrah ( ), kamar yadda aka

ruwaito daga wajen Ibnul Madīnī da Abubakar Al-Ājurriy; su ne

Ahlus-Sunnah wal Jamā’ah ( ), kamar yadda Abdul-Qādir

Page 68: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

68

Jīlāni ya bayyana a cikin littafin Al-Gunyah. Kuma su ne Al-Gurabā

( ), kamar yadda aka ruwaito daga Abdān.

Da’awar Ahlus-Sunnah ta ginu ne a kan asasi guda takwas: (1)

tsantsar tauhidi (2) tsantsar biyayya ga Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi), da riqo da Alqur’ani da Sunnah, bisa

fahimtar magabata na qwarai (3) barin bidi’a, da nisantar ma’abota

bidi’a (4) neman ilmi mai amfani (wanda aka gina shi a kan dalili

sahihi), da aiki da shi, da karantar da shi (5) at-Tasfiyyah (tsaftace

kowane ilmi daga kwamacala, da surkulle, da hadisan qarya ko masu

rauni, da ra’ayoyin da ba a gina su a kan dalili ba, da tatsuniyoyi) da at-Tarbiyyah (aiki da tataccen ilmi, da koyar da shi ga mutane, da

tarbiyyantuwa a kan abin da ya qunsa) (6) watsi da qungiyanci da

ta’assubanci, wato, maqalqalewar ido-rufe, ga mazhabobi (7) bayyanar

da sharrin da ke cikin dokokin da suka sava wa dokokin Allah, da

qudurce aibobi da sharrin da ke cikin dukkan tsare-tsaren da suka sava

wa Shari’ar Musulunci (8) kiran mutane zuwa ga dukkan nau’o’in

jihadi don xaukaka kalmar Allah, ta hanyar amfani da harshe, da

alqalami, da dukiya, da rayuwa.

Ahlus-Sunnah na da waxansu siffofi da suka kevanta da su: (1) su

ne `yan tsaka-tsaki a cikin aqida, da ibada, da gudun duniya, da

sauransu, ba tare da wuce gona da iri, ko gazawa ba (2) sun taqaita

kansu ga Alqur’ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na qwarai (3) ba

su da wani shugaban da su ke karvar kowace magana ya yi, ko su ke

barin duk abin da ya sava masa, sai Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) (4) ba su yin husuma a cikin addini, kuma

suna nisantar jidali da musu a cikin mas’alolin fiqihu waxanda aka yi

savani a kai (5) suna girmama magabata na qwarai (salaf), kuma sun

qudurce cewa hanyar salaf ita ce hanya mafi daidai (6) suna watsi da

tawili a cikin sunayen Allah (Mai girma da xaukaka) da siffofinSa,

kuma suna sallama wa duk wani nassi ingantacce (7) ba su ware wani

nassi shi kaxai, su yi aiki da shi, ba tare da sun haxa shi da sauran

nassosin da suka sava masa ko suka qarfafe shi ba (8) ba su

dangantuwa ga wani abu, face Musulunci da Sunnah da jama’a,

savanin waxanda ke dangantuwa zuwa ga xariqun sufaye, kamar

tijjaniyya da qadiriyya (9) suna da tsananin kwaxayi wajen yaxa

sahihiyar aqida da miqaqqen addini, da karantar da mutane.

Malamai irin su Al-Asbahāni, a cikin ; da Ibn

Taimiyyah, a cikin ; da Az-Zahabi, a cikin ; da

Suyuxi, a cikin , na ganin wajibcin dangantuwa zuwa ga

Page 69: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

69

Wajibi ne a kan iyaye su cusa qauna da soyayyar Allah

(Maxaukaki) da ManzonSa (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) a cikin zukatan `ya`yansu, da karantar

da su girman Allah da matsayin Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi), da wajibcin yin

masu xa’a, a cikin tsanani ko sauqi, da qunci ko

walwala.127

Wannan zai sanya `ya`ya su fifita son Allah

, kuma sun bayyana cewa yin haka, alama ce ta . Don haka

ya halatta a siffanta wani da , kamar yadda Az-Zahabi, a cikin

ya danganta Ad-Dāra Quxnī, ko , kamar yadda Suyuxi, a

cikin ya danganta Ibn Salah. Bayan wannan, ya halatta

mutum ya kira kansa , kamar yadda Zainul Irāqī ya yi a cikin

muqaddimar littafinsa , ko kuma , kamar yadda As-

Sam’āni ya yi a cikin littafin . 127

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya girmama Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) da manzanci; Ya keve shi da isar

da saqo, Ya saukar masa da Alqur’ani, kuma Ya bayyana cewa shi ne

Manzon fiyayyar al’umma, Manzon rahama, Annabin qarshe, mai

bushara da gargaxi, wanda ba ya furuci bisa son zuciya.

Matsayin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) abu ne mai girma a wajen duk wani mumini. Allah (Mai girma da

xaukaka) Ya bayyana cewa biyayya ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) wajibi ne [Anfāl, 8:20; Nur, 24:56; Nisā,

4:64; Aal Imrān, 3:132; Nisā, 4:59; Muhammad, 47:33; Hashr, 59:36];

biyayya ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) biyayya ce ga Allah [Nisā, 4:80]; ayyukan da aka yi bisa biyayya ga

Allah (Mai girma da xaukaka) da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a na samun lada cikakke [Hujurāt, 49:14]; gafarar

zunubi da samun shiriya na rataye ne da biyayya ga Manzo [Nur, 24:54; Aal Imrān, 3:31]; biyayya ga Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ita ce alamar son Allah [Aal Imrān, 3:31];

waxanda suka yi biyayya ga Allah (Mai girma da xaukaka) da

ManzonSa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) na daga cikin waxanda aka yi wa ni’ima [Nisā, 4:69]; waxanda ba su yin biyayya ga

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ba muminai ba ne [Nisā, 4:65]; waxanda ke sava wa Manzon Allah (tsira

Page 70: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

70

(Mai girma da xaukaka) da son Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) a kan son kowa,

kuma su fifita xa’ar Allah (Mai girma da xaukaka) da

xa’ar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) a kan xa’ar kowane mutum.128

da amincin Allah su tabbata a gare shi) sakamakonsu shi ne vata da barin hanyar Allah [Ahzāb, 33:36]; waxanda ke sava wa Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) na cikin haxari, a nan duniya, kuma suna fuskantar azaba a lahira [Nisā, 4:115; Nur, 24:63;

Jinn, 72:23; Ahzāb, 33:66; Nisā, 4:42]; samun nasara da babban rabo a

duniya da lahira na cikin yin biyyaya ga Allah (Mai girma da xaukaka)

da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da sallamawa a gare su [Nur, 24:51-52; Nisā, 4:18]; Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) shi ne abin koyi ga kowane mumini [Ahzāb, 33:21]. 128

Son Allah (Mai girma da xaukaka) da son Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) na da alamomi. Da waxannan

alamomin ne a ke bambance mai soyayya ta gaskiya, daga xan boge:

wanda duk bai siffantu da waxannan alamomi ba, soyayyar da ya ke yi

wa Allah (Mai girma da xaukaka) da ManzonSa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ba gaskiya ba ne, kamar yadda Al-Qādi Iyād, da

An-Nawawi, da Ibnul Qayyim, da Ibn Hajar suka bayyana.

Alamomin son Allah su ne: (1) tsantsar biyayya ga Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) (2) tausasawa ga muminai

da tsanantawa ga kafirai (3) jihadi don xaukaka addinin Allah, ta

hanyar amfani da rai, da hannu, da harshe, da dukiya (4) rashin tsoron

zargi a wajen aikata abu domin Allah (5) ikhlasi a cikin bautar Allah

(6) fifita Lahira (7) son abin da Allah (Maxaukaki) Ya ke so (8) kiyaye

haqqoqin Allah.

Alamomin son Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) sun haxa da: (1) kwaxayin ganinsa da son sahabbantakarsa, da

damuwa a kan rashin ganinsa, da gabatar da shi, da fifita shi a kan

kowa, da koyi da shi (2) ladabi a gare shi, ta hanyar yabo, da salati, da

yawan ambatonsa, da ladabtuwa wajen ambatonsa, da ladabi a cikin

masallacinsa (3) gasgata shi a cikin duk abin da ya ba da labari (4) yin

masa xa’a, da bin hanyarsa, da shiryuwa da shiriyarsa (5) mai da

Sunnarsa a matsayin mai hukunci (6) tsare martabarsa, da matsayin

sahabbansa, da matsayin iyalinsa, da sauran mutanen gidansa (7) kare

Sunnarsa, da tsaftace ta daga abubuwan da ba su inganta ba, da karantar

Page 71: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

71

Haka kuma, ilmantar da `ya`ya matsayin sahabbai129

da

mutanen gidan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su da ita, da yaxa ta, da mai da martani ga shubuhohi da ruxanin da

maqiyanta ke shigarwa cikinta.

Zagin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ko faxin kalmomi na izgilanci ko qasqanci ko cin mutunci a gare shi,

kafirci ne. Wanda ya yi haka, ya zama kafiri, kuma jininsa ya halatta. A

cikin littafin , Ibn Taimiyyah ya naqalo maganar Ishāq ibn

Rāhawaih cewa ‚Musulmi sun yi ijma’i a kan duk wanda ya zagi Allah

(Maxaukaki), ko ya zagi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi), ko ya kore wani abu daga cikin abin da Allah

(Maxaukaki) Ya saukar, ko ya kashe wani daga cikin Annabawa, ya

kafirta, ko da ya yarda da dukkan abin da Allah Ya saukar‛. Haka

kuma, Muhammad ibn Suhnun ya ce: ‚Malamai sun yi ijma’i a kan duk

wanda ya zagi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ko ya ci mutuncinsa, kafiri ne; ya cancanci narkon azabar Allah,

kuma manyan malamai sun ba da fatawar kisa a kansa…‛

Malamai sun dogara da ayoyin Alqur’ani da hadisai masu yawan

gaske wajen tabbatar da hukuncin kafirci da kisa ga wanda duk ya yi

haka bisa ilmi. A cikin Alqur’ani, sun dogara da ayoyin Taubah, 9:29, 12; Ahzāb, 33:57; da Taubah, 9:65-66. A cikin hadisan Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), sun kafa hujja da hadisin Ka’ab ibnul Ashraf da Abdullah ibn Ubay ibn Salūl dangane da

umurnin kisa da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ba da a kansu bayan saukar ayar Taubah, 9:57 [Bukhari da

Muslim]; da banzantarwar da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya yi ga jinin Bayahudiyar da ke zaginsa, bayan

wani makaho ya maqure ta har ta mutu [Abu Dawud]; da hadisin

makahon da ya kashe baiwarsa bayan ya hana ta zagin Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), amma ba ta hanu ba [Abu Dawud da Nasā’i]; da hadisin ‘Asmā bint Marwān Al-khaxamiyyah,

wadda ta yi wa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) zambo, da cin mutunci, a cikin waqa, shi kuma ya ba da umurnin a kashe ta [Al-Qadā’iy]. 129

Sahabi shi ne wanda ya haxu da Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi), yana mai imani da shi, kuma ya mutu a

cikin musulunci. Sahabbai (Allah Ya yarda da su) su ne mazajen farko

a cikin wannan addini, kuma manya xibar fari; sun rayu da Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), suka yi imani da

Page 72: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

72

tabbata a gare shi), wato, ahlul baiti,130 da karantar da su

falalarsu, da adalcin sahabbai, da qoqarin da suka yi wa

shi, suka taimaka masa, suka aura daga gare shi, ya aura daga gare su,

suka ci tare, suka sha tare, suka fita tare, kuma suka shiga tare. Su ne

mafi gaskiya da karamcin mutane, waxanda suka fifita son Allah (Mai

girma da xaukaka), da ManzonSa (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi), da addininSa a kan rayukansu, da dukiyoyinsu, da `ya`yansu.

Sun ba da rayuwarsu da dukiyarsu da lokacinsu wajen xaukaka addinin

Allah (Maxaukaki); suka bar gidajensu da iyalinsu, suka kekketa

dazuzzuka, suka rarratsa gonaki, suka tsattsallake ramuka, suka

wurwuce tafkuna, suka hahhaye kwazazzabai, suka kukkutsa gabas da

yamma, kudu da arewa na duniya, suka qaurace wa iyalinsu da

`ya`yansu, domin su kare martabar addini kuma su xaga matsayinsa.

Babu shakka, sahabbai (Allah Ya yarda da su) sun kasance masu

gaskiya da ikhlasi, da riqon amana da cika alqawari, kuma da qoqarin

da’awa da isar da saqon Allah.

Aqidar Ahlus-Sunnah game da sahabban Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ta qunshi: (1) qudurce cewa

sahabbai (Allah Ya yarda da su) su ne mafi falalar wannan al’umma

bayan Annabinta (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi); su ne

mafi xaukakar matsayi da girma a wajen Allah (Maxaukaki); kuma su

ne farkon waxanda aka yi wa alqawarin alhairi a lahira (2) qudurce

cewa sahabbai (Allah Ya yarda da su) na da falala mabambanta: a

jumlace, Abubakar shi ne a gaba, sai Umar, sai Uthman, sai Aliyu

(Allah Ya yarda da su); kuma ana gabatar da muhajirai, waxanda suka

yi hijira daga Makka zuwa Madina, a kan ansar, waxanda suka karvi

baquncin muhajirai a Madina, daga nan, sai waxanda suka halarci yaqin Badar da waxanda suka yi mubaya’ar Bai’atul Ridwān, sannan,

sai wanda duk nassi ya tabbatar da wata falala a kansa (3) qudurce

cewa sahabbai adalai ne gaba xayansu, kamar yadda Alqur’ani da

Sunnah da Ijma’ suka tabbatar (4) kamewa daga savanin da ya faru a

tsakaninsu, da fahimtar cewa yaqin da suka yi a tsakaninsu bisa ijtihadi ne (5) qudurce cewa haramun ne a zagi sahabbai ko a soki mutuncinsu

ko a yi ishara zuwa ga abin da zai rage matsayinsu ko ya tauye

darajarsu da xaukakarsu, da qudurce cewa ba kowa ne ya ke sukar

sahabbai ko ya aibanta su ko ya zage su ba, face zindiqi, munafiki,

kuma abin tuhuma a cikin Musulunci. 130

Haqiqanin Ahlul Bait (mutanen gidan Manzon Allah – tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) su ne matansa na aure (Allah Ya

yarda da su). Amma `ya`yansa, da dangin mahaifinsa, da `ya`yan

Page 73: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

73

wannan addini, da gwagwarmayarsu, da qarfin imaninsu,

da kai-kawon da suka yi wajen taimakon addinin Allah,

na da tasiri sosai wajen samar da matasa masu kishin

addini, waxanda za su wakilci musulmi a ko’ina, kuma

su amsa sunan Ahlus-Sunnah tsantsa.

7. Ciyar da `ya`yansu yadda ya kamata, kuma a ciyar da su

halal, ba haram ba.131

Sakacin da waxansu iyaye ke yi

dangin mahaifinsa sun shiga cikin lafazin. Ke nan, Ahlul Bait na

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) su ne

waxanda sadaka/zakka ta haramta a gare su; wato: matansa da

zurriyarsa da kowane musulmi, namiji da mace, daga tsatson Abdul Muxxalib, wato, Banu Hāshim ibn Abdi Manāf, da kuma `yantattun

bayin Banu Hāshim waxanda suka musulunta.

Aqidar Ahlus-Sunnah dangane da Ahlul Bait ta qunshi: (1) qudurce

wajibcin son su, da yabo a gare su, da ajiye kowannensu a matsayin da

ya cancanta, bisa adalci (2) qudurce fifikon daraja a tsakaninsu,

gwargwadon yadda nassosi suka tabbatar (3) son Ahlul Bait gwargwadon matsayin kowannensu: Ahlus-Sunnah na son sahabbai

daga cikin Ahlul Bait saboda imaninsu, da taqawarsu, da

sahabbantakarsu ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi), da kusancinsu da shi; kuma suna son waxanda ba sahabbai ne

ba saboda imaninsu, da taqawarsu, da kusancinsu ga Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) (4) qudurce wajibcin

girmama su, da kiyaye wasiyyar da Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya yi game da mutunta su, da martaba su,

da kiyaye haqqoqinsu, da shigar da su a cikin salati (5) qudurce cewa

za a iya samun Ahlul Bait a kowane lokaci, matuqar an tabbatar da

haka ta sahihiyar hanya. 131

Musulunci ya kwaxaitar da neman na kai ta hanyar halal domin

mutum ya xauki nauyin kansa da iyalinsa, da sadar da zumunci, da yin

sadaka, da kuma taimakon al’umma. Musulunci ya shar’anta (i) saye da

sayarwa da duk abin da zai iya taimaka wa kasuwanci (ii) sana’o’in

hannu, kamar noma da saqa da qira da jima da gini da sassaqa, da

sauransu (iii) leburanci a qarqashin hukuma ko waninta.

Kasancewar Allah (Mai girma da xaukaka) Ya umurci muminai da

cin halal kamar yadda ya umurci Manzanni [Mu’uminun, 23:51;

Baqarah, 2:172], wajibi ne kowane Musulmi ya tabbatar da cewa duk

hanyar da ya xauka ta neman abin rayuwa bai faxa cikin abin da

Page 74: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

74

dangane da abincin iyalinsu ba shi da gurbi a cikin

Shari’ar Musulunci. Haka kuma, nuna halin ko in kula da

waxansu ke yi dangane da irin abin da za su kawo wa

iyalinsu (na halal ko haram), shi ma akwai haxari sosai.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Ya ishi mutum zunubi (a wajen Allah) ya

tozartar da waxanda ciyarwarsu ta ke (wajibi ne) a

kansa.‛132

Haka kuma, Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Duk wata tsoka (a

jikin mutum) da ta tsiro ta (hanyar cin) haram, wuta ce ta

fi cancantar ta qone wurin (a lahira).‛ A wani lafazin:

‚Duk jikin da ya tsiro ta (hanyar cin) haram, wuta ce ta fi

dacewa (ta qona wurin a lahira).‛133

8. Yin adalci a tsakanin `ya`ya (maza da mata) a wajen

kyauta. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) ya ce: ‚Ku yi adalci a tsakanin `ya`yanku

cikin (abubuwan da za ku ba su na) kyauta, kamar yadda

ku ke son su yi adalci a tsakaninku (mahaifi da

Shari’a ta hana ba. Misali, a cikin leburanci, haramun ne Musulmi ya yi

aiki a wajen da a ke qera kayan kixa ko a ke sarrafa giya da sauran

abubuwan da ke sanya maye, ko wajen da a ke sana’anta taba sigari; da

wuraren da aka tanada don zinace-zinace ko kuma wajen da a ke yin

mu’amala da riba a galibi. A wajen sana’o’in hannu, an haramta sana’ar

sassaqa gumaka; ko xaukar hoton abubuwa masu rai, ba tare da larura

ba; ko taimakawa wajen samar da wuraren da za a yi fasadi da masha’a.

A vangaren kasuwanci da saye da sayarwa, Musulunci ya hana duk

wani kasuwancin da ya qunshi cutarwa da yaudara ( ) da ruxi

ko rashin tabbas mai yawa ( ) ko rashin sanin haqiqanin ko adadin

abin da za a qulla ciniki a kansa ( ). Haka kuma, an rahamta hada-

hadar da ta qunshi giya da caca da mushe da alade da gunki da kare da

jini da kyanwa da hoto da kayan kixa, saboda haramta aininsu da aka

yi, kamar yadda aka haramta mu’amalar da ta qunshi riba. 132

Ahmad, Muslim da Abu Dāwud 133

Ahmad, Ibn Hibbān, ad-Dārimī da al-Baihaqī: Sahīh [Duba Sahīh al-Jāmi’ #4519]

Page 75: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

75

mahaifiya) cikin biyayya da tausasawa (da za su yi a gare ku).‛

134 Haka kuma, an-Nu’umān ibn Bashīr (Allah

Ya yarda da shi) ya ce: Babana ya tafi da ni wajen

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: Na ba wannan xa nawa kyautar wani bawa da

na ke da shi (kuma ina son ka zama shaida a kan haka).

Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce: ‚Ka yi wa duk `ya`yanka irin wannan

kyautar?‛ Ya ce: ‘a’a’. (Sai Annabi) Ya ce: ‚Ku ji tsoron

Allah, kuma ku yi adalci a tsakanin `ya`yanku.‛ Sai

babana ya qwace kyautar da ya ba ni.135

A wata ruwayar,

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Wannan bai halatta ba. Kuma ni ba na yin

shaida sai a kan (al’amari na) gaskiya.‛136

A cikin wata

ruwayar, ya ce: ‚Kada ka sanya ni yin shaida a kan

zalunci. Lallai haqqin `ya`yanka ne a kanka ka yi adalci

a tsakaninsu.‛137

Ibn al-Qayyim ya ce: ‚Magabata na qwarai (as-Salaf as-Sālih) sun kasance suna son yin

adalci a tsakanin `ya`yansu.‛138

Idan mutum ya ba xansa/`yarsa kyautar wani abu a

lokacin da ya/ta ke shi/ita kaxai, sannan daga baya, Allah

Ya ba shi qaruwar haihuwa, ba zai ba `ya`yan da aka

haifa daga baya irin wancan abu da ya ba na farko ba, ko

kuma ya ce zai qwace abin da ya ba da a can baya. Idan

yana son ya ba waxannan na yanzu, sai dai ya haxa

`ya`yansa gaba xayansu, ya yi masu kyautar. Haka

kuma, ba dole ne a daidaita su a wajen biyan buqatar

larura ba. Misali, idan yanayin wani daga cikin `ya`yan

yana buqatar abinci, ko kula da lafiya fiye da sauran, ba

134

Xabarāni: Sahīh [Duba Sahīh al-Jāmi’ #1046] 135

Bukhari da Muslim 136

Muslim 137

Ahmad: Sahīh 138

Tuhfah al-Maudūd, shafi na 155

Page 76: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

76

za a ce dole a daidaita su wajen kashe masu kuxi ba.

Haka kuma, idan bambancin jinsi ya haifar da

bambancin buqata a tsakaninsu, babu laifi a yi wa wasu

daga cikinsu xawainiyar da ta zarce ta sauran. Misali,

xawainiyar `ya`ya mata a wajen tufafi da kayan ado ta

zarce ta maza saboda bambancin yanayinsu.

Haka nan, ya kamata iyaye su saba wa `ya`yansu son

juna, da fifita juna, a kowane lokaci. Idan aka ba xaya

daga cikinsu kyauta, ko kuma ya samo wani abu a wani

wuri, iyaye su nuna masa cewa wannan abu nasu ne su

duka; su umurce shi da ba `yan’uwansa wani abu daga

ciki. Idan qarami ya ga abin wasa a hannun babba, kuma

ya nuna yana buqata, iyaye su umurci babban ya ba

qaramin aro. Lallai ne iyaye su guji nuna wa `ya`ya

bambanci saboda yanayin zamantakewarsu da iyayensu

mata. Yin haka, zai haifar da gaba, da rashin jituwa a

tsakanin `ya`yan.

9. Iyaye su kiyayi yin mummunar addu’a ga `ya`ya, domin

hakan na da haxari babba. A maimakon mummunar

addu’a, kamata ya yi iyaye su dage wajen yin addu’ar

alhairi da neman shiriya ga `ya`ya. Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Kada ku

yi mummunar addu’a ga kanku, da `ya`yanku, da

dukiyarku; don gudun kada ku dace da lokacin da Allah

Ya ke amsa addu’a, ya zamanto an amsa maku.‛139

Haka

kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce: ‚Kada ku yi wa kanku addu’a, sai ta

alhairi, domin mala’iku na faxin ‘amin’ ga abubuwan da

ku ke faxi…‛140

139

Muslim 140

Muslim

Page 77: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

77

Ke nan, addu’ar neman shiriya, da albarka, da dacewa ya

kamata iyaye su yi wa `ya`yansu a kowane lokaci, ba wai

tsinuwa da la’ana, da faxin tir, da Allah wadai ba.

Kamata ya yi, idan `ya`ya sun yi kuskure, ko sun aikata

wani abu mara kyau, a nuna masu haxarin abin, da

rashin dacewarsa, sannan, a roqi Allah Ya shiryar da su.

Idan kuwa a ka yi masu tofin Allah tsine, kuma Allah Ya

amsa wannan addu’a, za su qara fanxarewa ne. Irin

wannan ne ke faruwa a gidaje da yawa, a wannan lokaci.

Sanannen abu ne cewa Allah Yana amsa addu’ar iyaye

(kyakkyawa ko mummuna) ga `ya`yansu. Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Addu’o’i guda uku ana amsa su (kai tsaye): addu’ar

wanda aka zalunta, da addu’ar matafiyi, da addu’ar

mahaifi (uwa ko uba) ga xansa.‛141

Wannan ya sa Annabawa da Manzanni suka riqa

kyakkyawar addu’a ga kansu da `ya`yansu, kamar yadda

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ba mu labari a cikin Alqur’ani. Misali, Annabi Ibrāhīm ya ce: ‚Kuma ka

nisanta ni, ni da `ya`yana daga bauta wa gumaka.‛142

Kuma ya ce: ‚Ya Ubangijina! Ka sanya ni mai tsayar da

salla. Kuma daga zuriyyata. Ya Ubangijinmu! Kuma Ka karvi addu’ata.‛

143 Haka kuma, Annabi Ibrāhīm da

Ismā’īl sun ce: ‚Ya Ubangijinmu! Ka sanya mu,

waxanda suka sallama (al’amari) gare Ka, kuma daga

zuriyyarmu (Ka sanya) al’umma mai sallamawa zuwa

gare Ka …‛144

Don haka, wajibi ne iyaye su nisanci yin

mummunar addu’a ga `ya`yansu.145

141

Ibn Mājah: Hasan 142

Ibrāhīm 14:35 143

Ibrāhīm 14:40 144

Baqarah 2:128 145

Kalmar addu’a ( ) ta zo da ma’anoni guda bakwai a cikin

Alqur’ani: (1) Bauta [Yunus, 10:106]; (2) Neman taimako [Baqarah,

Page 78: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

78

2:23]; (3) Neman buqata [Ghāfir, 40:60]; (4) Kira [Isrā, 17:52]; (5)

Yabo [Isrā, 17:110]; (6) Magana [Yunus, 10:10]; (7) Tambaya [Baqara,

2:68]. A shar’ance, addu’a ibada ce, kuma alama ce ta bauta, wadda

bawa ke yi domin neman kulawar Allah, da qarin taimakonSa, da jawo

rahamarSa, da tunkuxe cuta da azaba, kuma bawa ya ke bayyanar da

tsananin buqata zuwa ga Allah, da neman taimakonSa saboda gajiyawa,

da rashin qarfi.

Addu’a na xaya daga cikin mafi girman ibada; kuma tana da alaqa

mai qarfi da tauhidi, da kuma aqida, domin tana daga cikin manya-

manyan hanyoyin inganta imani da havaka shi. Allah (Mai girma da xaukaka) Ya kira addu’a da suna addini gaba xaya [Ghāfir, 40:65;

Ahmad da Abu Dāwud da Tirmidhi]; kuma ya bayyana cewa yin

addu’a ga wanin Allah na daga shirka [Jinn, 72:20]. Addu’a ita ce abu

mafi girma da karamci a wajen Allah [Ahmad da Tirmidhi]; kuma ita ce ibada mafi falala [Hākim]. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya yi umurni da yin addu’a, saboda tana amfani ga abin da ya sauka da wanda bai sauka ba [Hākim]. Allah Yana fushi da

duk wanda ya qi yin addu’a, saboda tunanin ya wadatu ga barin Allah [Ahmad da Tirmidhi da Ibn Mājah]; kuma qin yin addu’a, alama ce ta

gajiyawa, kasancewar babu mai barin addu’a sai malalaci [Ibn Hibbān].

Addu’a hanya ce ta samun haquri a cikin tafarkin Allah, da mayar

da al’amura zuwa gare Shi, da tawakkali, da nisantar kasala da

gajiyawa. Addu’a ibada ce mai sauqi, wadda a ke yinta a cikin dare da

rana, a kan tudu, a cikin teku, a sama, a halin tafiya da zaman gida, a

halin wadata da talauci, a halin lafiya da rashin lafiya, a bayyane da

asirce. Lazimtar addu’a na daga sababin xaukewar bala’i, da

tunkuxewar tavewa da rashin arziqi; kuma tsari ne da kariya daga

mahassada da sharrin maqiya. Addu’a na daga abubuwan alhairi,

waxanda ke kai wa ga mamaci; kuma ita ce makamin wanda ke da

rauni, da kuma wanda aka zalunta.

Addu’a na da ladubba da sharuxxa guda ashirin (20): (1) tabbatar da

cikakken tauhidi da kuma nisantar shirka (2) roqon abin da Shari’a ta

yarda da shi, da barin yin addu’a a kan abin da Shari’a ba ta yarda da

shi ba (3) qudurta cewa Allah ne kaxai Ya ke da ikon amsar addu’a, da

kawo amfani, da tunkuxe cuta (4) ikhlasi, da koyi da Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da nisantar bidi’a a cikin

addu’a (5) fuskantar Allah, da qanqan da kai, tare da bayyanar da

gajiyawa da kasawa (6) tabbatar da cewa abinci da abin sha da tufafi da

muhalli duk na halal ne (7) rashin qetare dokokin Allah ko cuxanyar

zunubi da savon Allah, kamar yanke zumunta da sava wa iyaye (8)

Page 79: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

79

kada a roqi wani abu na savon Allah (9) rashin qosawa ko tunanin an

samu jinkiri wajen amsa addu’ar, ballantana ma a kai ga dainawa (10)

farawa da yabo ga Allah (Mai girma da xaukaka) da salati ga Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) (11) sakankancewa

da qudurce za a amsa addu’ar, matuqar ta cika sharuxxa (12) yin

tawassuli da sunayen Allah mafi kyawu da siffofinSa mafi xaukaka ko

tawassuli da kyawawan ayyukan da aka yi saboda Allah ko tawassuli

da halin da a ke ciki na qasqanci ko talauci ko tsananin buqata (13)

zaven gajejjerun addu’o’i, waxanda ke da cikakkiyar ma’ana (14)

kammala addu’ar da wani suna daga cikin ingantatun sunayen Allah,

wanda ya dace da buqatar da a ke nema wajen Allah (15) xaga

hannuwa a wuraren da suka dace (16) yin alwalla, da kallon alqibla, da

yin kuka wajen addu’a (17) nacewa da maimaitawa sau uku, da kuma

rashin yanke qaunar cewa za a amsa addu’ar (18) asirtawa (19) faxin ‘amīn’ (20) fara yi wa kai addu’a kafin wani.

Yana daga ladubban addu’a a yi amfani da duk wani lokaci ko wuri

ko wani hali, waxanda nassosin Alqur’ani da Sunnah suka tabbatar da

cewa ana amsa addu’a. Daga cikin lokutan da a ke sa ran amsa addu’a,

akwai: ranar arfa; da lokacin ayyukan Hajji; da watan Ramadan,

musamman a cikin goman qarshe; da daren lailatul qadr; da ranar

Juma’a, daga lokacin da liman ya hau kan munbari zuwa lokacin da za

a kammala salla; da cikin dare, musamman kashi xaya bisa ukun

qarshe; da bayan fitowar alfijir; da bayan sallar la’asar a ranar Juma’a.

Daga cikin wuraren da a ke fatan amsa addu’a, akwai: masallaci,

musamman masallacin haramin makka da madina da masallacin qudus da quba; da al-multazām; da maqama Ibrāhīm; da arfa; da safa da

marwa; da mash’arul harām. Haka kuma, nassosi sun tabbatar da cewa

ana sa ran amsa addu’a a waxannan halaye: lokacin haxuwa da abokan

gaba; da lokacin saukan ruwan sama; da lokacin kiran salla; da tsakanin

kiran salla da iqama; da halin sujuda; da bayan sallar farilla; da lokacin

da a ke yin azumi; da lokacin buxa baki; da lokacin da aka zalunci

mutum; da addu’ar iyaye ga `ya`yansu; da lokacin da aka ji carar

zakara; da addu’a ga wanda ba ya nan; da addu’ar matafiyi, da wanda

ke cikin tsanani; da addu’a bayan an kammala alwalla; da addu’a a

lokacin da za a sha ruwan zamzam.

An hana yin abubuwa guda goma sha biyu (12) a cikin addu’a: (1)

nisantar yin addu’a gaba xaya (2) yin addu’a a lokacin talauci ko

tsanani, amma idan wadata ta samu, a watsar da yin addu’a (3) kasala

da nuna gajiya wajen addu’a (4) yin shisshigi ta fuskar iyakance adadi

ko wuri ko yanayi ko hali ko siffa, ba tare da ingantaccen nassi ba (5)

Page 80: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

80

10. Nisantar da `ya`ya daga wuraren da a ke aikata zunubi

da nau’o’in savon Allah,146

da bidi’a,147

da sauran

yin mummunar addu’a ga kai ko ga iyali ko ga dukiya (6) addu’ar

savon Allah da yanke zumunci (7) qosawa, da kuma yin gaggawa game

da addu’a (8) jingina addu’a ko sanya wa addu’a sharaxi, kamar a ce:

‚Allah Ka gafarta mani idan Ka so‛ (9) gaggauto da uquba a nan

duniya, kamar a ce: ‚Ya Allah! Azabar da Ka yi nufin yin mani a

lahira, Ka yi mani a nan duniya domin in huta‛ (10) quntata addu’a, da

iyakance ta, ba tare da wani sahihin nassi ba (11) amfani da bayan

hannuwa wajen roqon Allah (12) canza addu’a mai iyakantaccen lafazi. Duba littafin Tashīhud Du’ā na Bakar Abdullah Abu Zaid, da Ad-Du’ā wa Manzilatuhu minal Aqīdatil Islāmiyyah na Jilān Al-‘Arūsi, da

Shurūxul Ibādah wa Mawāni’ul Ijābah na Sa’īd ibn Wahf Al-

Qahaxāni, da Kitābud Du’ā na Husain Al-Awāyishah, da Du’ā: the Weapon of the Believer na Abu Ammār Yāsir Qādi, domin samun

cikakken bayani game da addu’a. 146

Kalmar zunubi ta zo da sigogi, da kuma ma’anoni masu yawan

gaske a cikin Alqur’ani. Haka kuma, kalmomin da sigogin sun

maimaitu a wurare da yawa. Misali, kalmar zanb – savawa, ta zo sau

talatin da biyar (35); ma’asiya – tsaurin kai, da fita daga umurnin Allah,

da qetare iyakokin bauta, ta zo sau talatin da uku (33); Ithm – laifi, sau

arba’in da takwas (48); sayyi’ah – mummunar aiki, sau xari da sittin da biyar (165); Jurm – laifi, sau sittin da xaya (61); Khaxī’ah – kuskure ko

babban zunubi, sau ashirin da biyu (22); Fisq – fita daga hanyar xa’a, sau hamsin da uku (53); Fasād – fita daga madaidaicin yanayi, da yin

varna, sau hamsin (50); Munkar – abin qi, sau goma sha shida (16); Fujūr – keta suturar kunya da halin girma da addini, sau shida (6);

Fāhishah – mummunar magana da ayyukan da ba su da kyau, sau

ashirin da huxu (24); Lamam – kusantar zunubi, sau xaya (1); da Wizr – babban sharri ko aibi, sau ashirin da shida (26).

Zunubi ya kasu gida biyu: babba da qarami. Babban zunubi shi ne

duk wani zunubi ko savon Allah da aka samu nassin da ya nuna

tsananin haramcinsa da haxarin aikata shi; ko dai ta hanyar bayyana

la’ana ko fushi a kan wanda ya aikata, ko narkon azaba ko shiga wuta a

lahira, ko kuma haddi a duniya. Daga cikin manyan zunubai akwai:

shirka, da sihiri, da kisan kai, da barin salla, da hana zakka, da sava wa

iyaye, da zina, da luwaxi, da cin riba, da shan giya, da cin dukiyar

maraya, da girman kai, da taqama, da giba, da annamimanci, da jiji da

Page 81: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

81

kai, da shaidar zur, da sata, da rantsuwa a kan qarya, da qazafi, da fashi

da makami, da hana wa mutane aminci a kan hanya, da kashe rai ba da

haqqin Shari’ah ba, da yin hukunci da savanin abin da Allah Ya saukar,

da rashin damuwa game da varna ko fasiqancin da matar aure ke yi, da

kamanceceniya da maza/mata, da ha’inci, da rashin tsarkaka daga

fitsari.

Qananan zunubai su ne waxanda ba su shiga cikin manyan zunubai

ba. Irin wannan zunubi ya haxa da qin amsa gayyatar walima ba tare da

uzuri ba, da qin amsa sallama, da qin gaishe da wanda ya ce ‘Alhamdu Lillah’ bayan ya yi atishawa. Qananan zunubai na komawa manya idan

aka nace ana aikatawa, kuma aka riqa yin farin ciki saboda an aikata,

musamman idan ya zamanto mai aikatawar na daga cikin mutanen da a

ke koyi da su.

Ana sava wa Allah, a aikata zunubi ne saboda jahilci ko bin son

zuciya ko mummunar xabi’a ko rashin imani da lahira. Yawancin

savon Allah na kasancewa ne ta hanyar idanu, da harshe, da hankali, da

gavuvva.

Zunubi da savon Allah na da shu’umanci mai yawa ga wanda ke

aikatawa: yana haifar da baqar zuciya, da la’ana daga zukatan

muminai, da baqin ciki, da hana albarkar ilmi, da hana albarkar arziqi,

da kaxaici a cikin zuciya, da qyama a cikin mutane, da tsanani a cikin

al’amura, da duhun zuciya, da duhun qabari, da raunin jiki, da rashin

albarka a cikin rayuwa, da dabaibayin shaixanun aljannu, da qasqanci

da wulaqanci, da qasqanci a wajen Allah, da lalacewar hankali da

tunani, da jawo wa zuciya karkata da rashin lafiya da tsatsa da

bushewa, da rashin samun addu’ar Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) da mala’iku, da kuma gushewar ni’ima.

Bayan wannan, savon Allah na haifar wa al’umma yawan cututtuka da

annoba, da rashin aminci, da qarancin ruwan sama ko kuma ruwa mai

yawan gaske wanda zai yi masu varna, da bayyanar girgizar qasa da

yaqe-yaqe, da qasqanci, da ci baya. 147

Imam Shāxibi ya fassara bidi’a da cewa: ‚Hanya ce da aka qago a

cikin addini, wadda ta yi kama da hanyar Shari’ah, kuma a ke binta bisa

irin niyyar da a ke bin hanyar Shari’ah‛. Wannan fassarar ta samu goyon bayan Ibn Rajab, da Ibn Hajar, da Az-Zarkashi, da Al-Haithumī,

da waxansu malamai masu yawa. A harshen larabci kuwa, bidi’a na

nufin duk wani abu sabo ko qagagge.

A Shar’ance, idan aka ce bidi’a, ana nufin ma’ana ta Shari’a, ba

ma’ana ta harshe ba, kasancewar Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi) ya zo ne don tabbatar da Shari’ah, ba harshen

Page 82: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

82

larabci ba. Bidi’a a cikin Musulunci haramun ne bisa nassin Alqur’ani

da Sunnah da Ijma’in sahabbai da Tabi’ai da sauran mutanen kirki.

Bidi’a na gudana ta hanyoyi guda biyar: (1) aqida, kamar qin yarda

da qaddara, da vata siffofin Allah ko tawilinsu; (2) zuciya, kamar

tsoron qabarin wane ko qaunar samun wani abu daga wani matacce; (3)

furuci, kamar zikirin bidi’a da `yan xariqa ke yi, da roqon matacce, da

neman agaji daga waxanda ke cikin qabari; (4) jiki, kamar durquso a

wajen gaisuwa, da sujuda ga wani waliyyi, da yin taron maulidi; (5)

dukiya, kamar kuxin da `yan Shi’ah ke ba limamansu da sunan

khumusi. Bidi’a na faruwa ne a cikin al’umma idan mutane suka jahilci yadda

za a fahimci addini; ko suka jahilci manufofin Shari’ah; ko suka

kyautata zato ga mujarradin tunaninsu, suka dogara ga hankali,

maimakon nassi; ko suka bi son zuciya; ko aka samu waxanda ke yin

magana a cikin addini ba tare da ilmi ba; ko suka jahilci Sunnah; ko

suka yi shisshigi da wuce qa’ida a cikin addini; ko suka bi mutashābihāt. Bidi’a za ta yaxu a cikin jama’a idan malamai suka yi

shiru; ko malamai suka yi aiki da bidi’ar; ko sarakuna suka qarfafa

mata gwiwa, suka ba ta goyon baya; ko mutane suka yi taqalidanci ga

malamai ko shugabanni, a cikin abubuwan da babu dalili a Shari’ah.

Bidi’a na da illoli masu yawa ga wanda ke aikatawa: (1) `yan bidi’a

na zargin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

da yin ha’inci wajen isar da saqo, shi ya sa ma su ke aikata abin da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya qi

bayyana wa al’ummarsa a bisa zarginsu; (2) suna cikin vata; (3) sun bar

hanyar Allah; (4) sun bijiro da kawunansu ga fitinar duniya da lahira;

(5) sun lalata ayyukansu; (6) sun bi son zuciya; (7) suna kawo rarraba a

cikin al’umma; (8) suna haifar da mutuwar Sunnar Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) a cikin al’umma.

`Yan bidi’a na da siffofi guda goma sha huxu (14): yawan savani a

cikin addini; watsi da gaskiya da bin son zuciya; tsarkake waxansu

mutane, da sunan waliyyai ko malamai, da yin shisshigi da wuce iyaka a cikin al’amarin shaihunnai da waliyyai; bin mutashābihāt; sava wa

sahihiyar Sunnah, ta hanyar amfani da mutashābihātul Qur’ān; qiyayya

da gaba ga masu riqo da hadisi; juya wa littafan salaf baya; rashin

komawa ga fahimtar salaf wajen yin aiki da Alqur’ani da Sunnah;

aibanta malaman Sunnah da kiransu da munanan suna; juyar da

gaskiya; alfahari da taqama game da yawan mabiya; cuxanya gaskiya

da qarya; gandara qarya wajen qoqarin kare bidi’arsu; neman suna da

samun yarda a wajen shugabanni da mawadata.

Page 83: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

83

wuraren da ba su dace ba, musamman, wuraren alfasha,

da batsa, da munanan maganganu, da kaxe-kaxe, da

raye-raye, da wasannin da ke shagaltarwa, kamar karta,

ludo, caca, da sunuka. Ibn al-Qayyim ya ce: ‚Haka nan

Bayan wannan, `yan bidi’a na da xabi’ar amfani da shubuhohin

qarya wajen ruxar da mabiyansu da sauran jahilai, ta yadda ba za su

fahimci Sunnah ba. Misali, a Nijeriya, ana cewa, ‘Ahlus-Sunnah (`yan

Izala/Salafiyya) ba su yin zikiri da salati, kuma ba su son Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).’ Ana faxin irin wannan

maganar ce, don kada a gane kurakuran da ke cikin waxansu bidi’o’in

da a ke yi, bisa da’awar son Allah (Maxaukaki) da ManzonSa (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi). Manufar ita ce a tsoratar da

mutane, kuma a nisantar da mabiya daga fahimtar Sunnah, da kuma

riqo da Alqur’ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na qwarai.

Sanannen abu ne cewa idan aka ce `yan Izala na yin salatin Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) irin wanda ya zo a

cikin ingantattun hadisai, amma ba su yin salatul fatihi, wadda aka ce

Allah (Maxaukaki) Ya yi wa Muhammadul Bakari wahayinta, kuma

wai karanta salatul fatihi sau xaya dai dai ya ke da saukar Alqur’ani sau

dubu shida, babu wani mai hankali da zai yi qiyayya da `yan Izala, ko

kuma ya yarda cewa `yan Izala ba su yin salati. Haka kuma, idan aka ce

`yan Izala ba su yin zikirin wazifar tijjaniya ko qadiriyya ko

naqashabandiyya ko shaziliyya, kuma ba su yin zikirin rawa ko zikirin

dukan qirji da kaxa ganga, amma suna yin duk wani nau’in zikiri da ya

zo a cikin Alqur’ani ko ingantaccen hadisi, mabiya ba za su qullaci

`yan Izala da gaba ba, ko kuma su yarda cewa ba su yin zikiri. Dangane

da son Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

kuwa, an qi fitowa valo-valo a bayyana wa muridai cewa rashin yin

maulidi ne (wanda aka qago bayan shekara xari shida da wafatin

Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi –) ya sa

aka ce `yan Izala ba su son Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi), ba wai domin ba su yin masa biyayya da xa’a, ko

kuma koyi da shi ba. Mene ne dalilin da yasa a ke voye wa muridai

gaskiyar al’amari? Wajibi ne iyaye su tabbatar da cewa `ya`yansu sun bi Sunnah sak,

kuma su nema wa `ya`yansu rigakafin bidi’a ta hanyar (1) riqo da

Alqur’ani da Sunnah (2) xabbaqa Sunnah a cikin rayuwa gaba xaya (3)

yin da’awah (4) rushe dalilan bidi’a da shubuhohin `yan bidi’a (5)

wadatuwa da fahimtar magabata na qwarai.

Page 84: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

84

ma, wajibi ne a nisantar da yaron da ya fara hankali daga

wuraren wasanni na varna, da kixe-kixe, da sauraren

alfasha da bidi’a da munanan maganganu. Domin kuwa,

idan ya saba da waxannan abubuwa tun yana yaro, da

wuya ya barsu bayan ya girma, kuma iyaye za su wahala

matuqar gaske kafin su raba shi da su.‛148

Daga cikin wuraren da ya kamata a nisantar da `ya`ya

daga gare su, akwai wuraren bikin kirsimati (christmas),

kasancewar laifi ne yin tarayya ko taimakawa ko ba da

haxin kai, ta kowace irin hanya, wajen wannan biki. A

da’awar kirista, bikin kirsimati biki ne na tunawa da ranar haihuwar Annabi Isā (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi). Annabi Isā (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi), a irin qaryarsu da kafircinsu, wai xan

Allah ne, ko kuma ma shi Allah ne. To yanzu Musulmi

na gaskiya zai yarda `ya`yansa su yi murnar zagayowar

ranar haihuwar Allah ko xan Allah? Sanannen abu ne,

hatta a wajen kiristoci da yawa, cewa babu wani dalili ko

bayani sahihi da ya tabbatar da cewa haihuwar Annabi Isā (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ta

kasance ne a wannan rana ta 25 ga Disamba, da a ke yin

wannan biki. Bai kamata Musulmi ya bar `ya`yansa su

taya kirista murna, ko su kai yawon ziyara, ko su ba da

kyauta gare su ko karvar wani abu daga gare su, a

wannan rana ba. Yin haka, girmamawa ce ga shirkar da

su ke yi da Allah, kuma taimakawa ce a gare su cikin

kafircinsu.149

Ibnul Qayyim ya bayyana cewa yin

gaisuwar taya kirista murnar kirsimati ya fi tsananin

muni a wajen Allah fiye da gaisuwar taya murna ga

wanda ya sha giya ko ya yi kisan kai ko ya yi zina. Ya

qara da cewa, ‘wanda duk ya yi gaisuwar taya murna ga 148

Tuhfah al-Maudūd, shafi na 162 149

Ibn Taimiyyah, Majmū’ al-Fatāwā (Maktabah Ibn Taimiyyah),

25/332

Page 85: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

85

mai savon Allah ko wanda ke aikata bidi’a ko aikin

kafirci, to, haqiqa, ya bijiro wa fushin Allah’.150

Haka kuma, ya kamata a nisantar da `ya`ya daga xabi’ar

nan ta bikin murnar zagayowar ranar haihuwa (birthday).

Wannan biki an samo shi ne daga waxanda ba Musulmi

ba. Malamai sun yi rubuce-rubuce da dama, kuma sun ba

da fatawoyi iri-iri dangane da wannan mas’ala.

Dukkansu sun yi ittifaqi a kan rashin dacewar wannan

biki, musamman da ya ke ya qunshi rashin fahimtar

manufar rayuwa a Musulunci, kuma ya qunshi

almubazzarancin dukiya, da koyi da xabi’un kafirai, da

vata lokaci a banza.151

Yana daga wuraren da ya kamata a nisantar da `ya`ya

daga gare su, wuraren da a ke yin bikin maulidi,

kasancewar maulidin da mutane ke yi a cikin watan

Rabi’ul Awwal, da sunan tunawa da haihuwar Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), a

kowace shekara, ba shi da asali a cikin Alqur’ani da

Sunnah, da ayyukan magabata na qwarai, kuma da yawa

daga manyan malamai magabata sun tabbatar da cewa

bidi’a ce da aka qago a cikin qarni na bakwai, wato

bayan hijira na da shekara fiye da xari shida.152

Wannan

150

Ibnul Qayyim, Ahkāmu Ahliz Zimmah, (Dārul Hadīth, Al-Qāhirah,

2003), shafi na, 154 151

Umm Muhammad, The Observance of Mawlid an-Nabawi and other Birthdays, (Abul-Qāsim Publishing House, Jeddah, Saudi Arabia,

1994), shafi na 41-50 152

Akwai bidi’o’i dabam daban waxanda a ke yi a cikin shekara. Mafi

shahara daga cikinsu su ne:

Al-Muharram: (1) bidi’ar baqin ciki, da marin fuska, da kekketa

tufafi, da zagin sahabbai (Allah Ya yarda da su) da yin qazafi ga A’isha

(Allah Ya yarda da ita), da ihu da kururuwar da zindiqai, maqiya

addinin Musulunci ke yi, a ranar Ashura (goma ga watan Muharram),

da sunan tunawa da ranar karbala, wato, ranar da Sayyidina Husain ibn

Page 86: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

86

ya sa ba a samu bayani a kan falalar maulidi ko

Abi Xālib (Allah Ya yarda da shi) ya yi shahada; (2) bidi’ar cika-ciki

da maqiyan Ahlul Bait suka qago don qalubalantar zindiqan da ke yin

baqin ciki, kuma waxansu jahilai da masu qarancin fahimtar addini

suka qaqaba wa kawunansu; (3) bidi’ar taron murnar shiga sabuwar

shekarar Musulunci.

Safar: bidi’ar canfi, da kuma da’awar cewa akwai ranakun da ba a

yin tafiya ko xaurin aure ko aikata waxansu abubuwa a cikinsu.

Rabi’ul Awwal: bidi’ar maulidi, da sunan tunawa da ranar da aka

haifi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi). Al-Fākihāni, da Ibnul Hāj, da Ash-Shāxibi, da Ibn Taimiyyah, da Ibn

Kathīr, da As-Sakkhāwi, da Ibn Hajar, da Ibnul Haffar, da An-

Nafarāwi, da As-Sāwi, sun tabbatar da cewa taron maulidi bidi’a ne.

Rajab: bidi’ar keve watan Rajab da yin azumi ko tsayuwar dare, don

neman samun lada da falala na musamman. Ibn Dihyah, a cikin littafin Adā’u mā wajab min Bayāni wad’il Waddā’īn fi Rajab, da Ibn Hajar, a

cikin Tabyīnul ‘Ajab bimā warad fi Fadli Rajab, sun tabbatar da cewa

duk hadisan da aka ruwaito dangane da falalar yin azumi ko qiyamul laili a cikin watan Rajab masu tsananin rauni ne, ko kuma hadisan qarya. Haka kuma, Al-Harwi, da Ibn Kathīr, da Al-Fairūza Ābādi, duk

sun tabbatar da rashin ingancin hadisan. Wannan ya sa, Umar ibnul Khaxxāb (Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana bugun waxanda ke

yin azumin watan Rajab da qwarangamar da ke hannunsa, kuma Ibn Umar da Ibn Abbās (Allah Ya yarda da su) sun kasance suna hana

mutane yin wannan azumi, saboda mutanen jahiliyya ne suka kasance

suna yin azumin. Sha’abān: bidi’ar raya daren sha biyar ga wannan wata.

Ramadān: bidi’ar yin sallar tarawihi bayan sallar magriba, maimakon

bayan sallar isha’, da `yan Shi’a ke yi, don ganin sun sava wa sauran

musulmi na duniya. Shawwāl: bidi’ar canfi game da yin aure.

Dhul Hijjah: bidi’ar Yaumu Ghadīr Khum (ranar sha takwas ga

wata) da `yan Shi’a ke yi, bisa da’awar cewa a wannan rana ce Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ayyana Aliyyu ibn Abi Xālib (Allah Ya yarda da shi) a matsayin wanda zai zamanto

halifar musulmi, bayan shi. Duk da cewa wannan magana qarya ce

tsagwaro, amma `yan Shi’a na amfani da ita wajen kafirta Abubakar da

Umar da Uthman da A’isha da sauran sahabbai (Allah Ya yarda da su),

saboda wai sun ci amanar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi), suka ba Abubakar halifanci, maimakon Aliyyu.

Page 87: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

87

shar’ancinsa a cikin Alqur’ani ko wani littafi daga cikin

littafan hadisi da fiqihu, waxanda musulmi ke karantawa

a duniya ba. Maimakon haka, an samu manyan malamai,

musamman `yan mazhabar malikiyya, tun fiye da

shekara xari bakwai, sun qyamaci bidi’ar maulidi, kuma

sun tabbatar da cewa taron maulidi ba shi da asali a cikin

Alqur’ani da Hadisi da maganganun magabata na

qwarai. Daga cikin manyan malaman da suka soki bidi’ar maulidi tun tali-tali, akwai: Tājuddīn Umar ibn

Aliyyu Al-Lakhamī Al-Fākihāni Al-Māliki,153

da Abu

Ishāq Ash-Shāxibi Al-Māliki,154

da Ibnul Hāj Al-

Māliki,155

da Abu `Amr ibn Al-Alā,156

da Abu Abdillah

Muhammad Al-Mihdār,157

da Abu Zur’ah Al-Irāqi,158

da

Zahīruddīn Ja’afar At-Tazamnati,159

da Abu Abdillah Al-

Haffār Al-Māliki,160

da Abux Xayyib Muhammad

Shamsulhaq Al-Azīm Ābādi,161

da Bashīruddīn Al-

153

A cikin littafinsa Al-Maurid fi Amalil Maulid, ya bayyana cewa

maulidi bidi’a ce wadda `yan zaman kashe wando suka qago, kuma

sha’awar rai ce wadda masu son cin na banza ke ba muhimmanci. Ya

mutu a shekara ta 734 AH. 154

A cikin littafin Al-I’itisām da Fatāwal Imāmish Shāxibi, shafi na

203-204, ya tabbatar da bidi’ancin taron maulidi. Ya rasu a shekarar

Hijira 790 155

A cikin littafin Al-Madkhāl, 2/2-10. Ya rasu a shekarar 732 AH 156

Jalāluddīn As-Suyuxi ya naqalo maganarsa a cikin littafin Al-Hāwi lil Fatāwa, 1/190 157

A cikin littafin Al-Mi’iyārul Mu’urib,7/ 99-101 158

A cikin littafin Tanshīful Aazān 159

Duba Al-Mi’iyārul Mu’urib, 7/99 160

Duba Al-Mi’iyārul Mu’urib, 7/99 161

Duba littafin Ar-Raddul Qawiy alar Rufā’i wal Majhūl wabni Alawi wa Bayānu Akhxā’ihim fil Maulidin Nabawi na Hamud ibn Abdillah

At-Tuwaijiri, shafi na 235

Page 88: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

88

Qanūji,162

da Abdussalām Khidir Ash-Shuqairi,163

da

Muhammad Ulaish Al-Māliki,164

da Rashīd Rida.165

Abin mamaki, duk waxannan malamai babu xan izala ko

bawahabiye, ballantana waxanda ke qoqarin kare bidi’ar

maulidi su ce maqiyan Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ne suka nuna rashin asalin

bidi’ar maulidi a cikin Musulunci. Hasali ma, malamai irinsu Ibnul Hāj da Ulaish da Al-Haffār masu bin hanyar

sufaye ne.166

Haka kuma, lallai ne iyaye su nisantar da `ya`yansu daga

wuraren da a ke kaxa mandiri ko a ke yin rawa da bugun

qirji da haniniya da hargowa a wajen zikiri, kasancewar

waxannan abubuwa ba su da asali cikin addinin Allah.

Babu shakka, yin haniniya da ihu, da shessheqa, da

kyakkyarma murya, da yin tafi da rawa a yayin da a ke

zikiri, ba shi daga cikin karantarwar Musulunci. Wajibi

ne a kan iyaye su tabbatar cewa `ya`yansu ba su je kallon

irin waxannan ayyukan bidi’a ba, waxanda mutane ke yi,

wai da sunan addini.167

162

Duba littafin Ar-Raddul Qawiy alar Rufā’i wal Majhūl wabni Alawi wa Bayānu Akhxā’ihim fil Maulidin Nabawi na Hamud ibn Abdillah

At-Tuwaijiri, shafi na 235 163

Karanta littafinsa As-Sunan wal Mubtadi’āt 164

A cikin littafin Fat-hul Aliyyil Māliki 165

A wurare da dama cikin Al-Manār, 9/96; 2/74-76; 17/111; 29/664-

668 166

Duba littafina Nau’o’in Ibada a cikin Watannin Musulunci da Bidi’o’in da a ke yi a kowane Wata. Allah Ya ba ni ikon kammala shi,

da kuma fitar da shi ga jama’a. 167

Babu wani malami daga cikin malaman Sunnah, tun daga zamanin

sahabban Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

zuwa yau, da ke ganin halaccin irin wannan mummunan aiki da `yan bidi’a ke yi, da sunan bautar Allah. Hasali ma, Imam Ax-Xurxūshi Al-

Māliki, wanda ya rasu a shekarar hijira 520, a cikin littafinsa Al-Hawādith wal Bida’u, na ganin cewa zindiqai, mutanen As-Sāmiri,

Page 89: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

89

waxanda suka yi wa Annabi Musa (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) tawaye, su ne suka fara yin bauta ta hanyar kewaye xan

maraqi, suna rawa, suna tafi, suna layi, da sauransu. Wannan ya sa Al-Qurxubi, a cikin Al-Jāmi’u li Ahkāmil Qur’ān, da Ibnul Jauzi, a cikin

Talbīs Iblīs, da Ash-Shāxibi, a cikin Al-‘I’itisām, da Ibnus Salah, a

cikin Al-Fatāwā, da Ibn Taimiyyah, a cikin Majmū’ul Fatāwā da

Mas’alatus Sama’, da Ibnul Qayyim, a cikin Ighāthatul Lahfān da

Madārijus Sālikīn, da Ibnul Hāj, a cikin Al-Madkhal, da As-Sayyid

Mahmud Al-Alūsī, a cikin Rūhul Ma’āni, da Ibn Hajar Al-Haithumī, a

cikin Kaffur-Ra’a’ ‘Anistimā’i’ Ālātis Samā’ suka nuna bidi’ancin yin

rawa ko layi ko rausaya ko tafi ko kixa ko ihu da haniniya wajen zikiri.

Da yawa daga malamai sun danganta yin tsuwwa da tafi wajen zikiri

ga mutanen jahiliyya, kuma suka danganta rangwaxa da jan sauti a wajen zikiri ga kirista [duba tafsirin Al-Alūsī, Rūhul Ma’āni, a

qarqashin faxin Allah ‚ ‛; da littafin

Risālatus Sama’ na Ibn Taimiyyah]; suka bayyana cewa yin tafi wajen

zikiri, kamanceceniya ce da mata, domin kuwa, mata ne kawai ke yin tafi idan larura ta auku a cikin salla [duba Talbīs Iblīs na Ibnul Jauzi, a

qarqashin ; da Kaffur-Ra’a’ ‘Anistimā’i’

Aalātis Samā’ na Ibn Hajar Al-Haithumī]; suka bayyana cewa yin rawa

da rausaya ko layi da mommotsa jiki da sunan bauta a lokacin zikiri, varna ce babba [duba Kaffur-Ra’a’ ‘Anistimā’i’ Aalātis Samā’ na Ibn

Hajar Al-Haithumī]; Izz ibn Abdis-Salām ya ce wanda ke yin tafi da

rawa a lokacin zikiri ‘xan daudu’ ne, kuma babu wanda ke yin haka, sai wawa ko jahili [duba Kaffur-Ra’a’ ‘Anistimā’i’ Aalātis Samā’ na Ibn

Hajar Al-Haithumī]; Az-Zamakhshari ya ce, a addinance, layi da

rausayawa, addinin yahudawa ne wajen karanta littafin At-Taurah

[duba tafsirin Al-Kash-Shāf, a qarqashin faxin Allah ‚

‛]; Ax-Xurxūshi ya ce, asalin rawa da layi ko tafi ko

rausaya wajen ibada, addinin kafirai ne waxanda suka yi bautar xan

maraqi, kuma hanya ce ta sufaye wajen zikiri, kuma hakan ya qunshi zaman kashe wando da jahilci da vata [duba Al-Jāmi’ li Ahkāmil

Qur’ān na Al-Qurxubī, a qarqashin faxin Allah ‚

‛ a cikin suratu Xāha, 20:88; da Al-Madkhal na

Ibnul Hāj, juz’i na biyu; da Kaffur-Ra’a’ ‘Anistimā’i’ Aalātis Samā’ na

Ibn Hajar Al-Haithumī]; Ash-Shāxibī ya bayyana cewa rawa da

rausayawa ko layi, da sufaye ke yi a wajen zikiri, bidi’a ce da ta sava

wa hanyar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

da sahabbai (Allah Ya yarda da su) da tabi’ai (Allah Ya jiqansu) da

Page 90: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

90

11. Iyaye su riqa nema wa `ya`ya tsari da kariya tare da

nisantar da su daga duk wani abu mai cutarwa, kamar

shaixanun aljannu da mutane. Hakan zai samu ne ta

hanyar yin masu rigakafi irin na Musulunci da ya qunshi

addu’o’i, da nisantar waxansu abubuwa ko aikata

waxansu abubuwa.168

Manzon Allah (tsira da amincin

sauran magabata na qwarai [duba littafin Al-I’itisām]; Abux-Xayyib

Ax-Xabarī ya ce, waxanda ke yin kixa wajen zikiri sun sava wa

jama’ar musulmi, domin sun mai da waqa a matsayin addini da xa’a,

kuma suna ganin dacewar bayyana wannan abu a cikin masallaci da wuraren qaburbura [duba Risālatux Xabarī]; Ibn Salāh ya ce waxanda

ke yin zikiri da kixa sun yi wa Allah (Maxaukaki) qarya, kuma sun sava wa ijma’in musulmi [duba Fatāwā Ibn Salāh]. 168

Kashi na 13 (4) na dokar haqqoqin yara, Child’s Right Act, wadda

tsohon shugaban qasar Nijeriya, Obasanjo ya rattaba wa hannu a ranar

31 ga watan Yuli, 2003, ya wajabta wa iyayen kowane yaron da bai kai

shekara biyu ba, cewa su tabbatar an yi masa allurar rigakafi. Idan ba

haka ba, akwai tara ta kuxi da za a yi masu, wadda ba ta wuce N5000

ba, a karo na farko. A karo na biyu, za a iya yanke masu hukuncin

xaurin da bai wuce wata xaya ba, sannan, a tursasa su yin rigakafin.

Wannan sashi na dokar yara, na qoqarin kore dukkan xari-xarin da

musulmi ke yi game da allurar rigakafin da a ke yi wa yara, musamman

rigakafin cutar shan inna (polio). Binciken da aka gudanar a kan

maganin rigakafin shan inna da a ke xiga wa yara a wannan qasa, wato, Oral Polio Vaccination (OPV), ya nuna cewa, an gurvata maganin

rigakafin da qwayoyin hana xaukar ciki, da waxanda ke kashe

qwayayen halitta. Wannan ta’addanci na daga cikin shirin kisan qare

dangi da qasashen yammacin Turai suka daxe suna shiryawa a kan

musulmin Nijeriya. Da yawa daga manyan likitoci, da qwararru a

harkar harhaxa magunguna, da masana tattalin arziqi da gudanarwar

mulki da siyasa, na qasashen duniya, sun tabbatar da makircin da

qasashen yammacin duniya ke qullawa ga qasashen da ke tasowa,

musamman Nijeriya.

Waxanda ba su fahimci siyasar da ke cikin rigakafin polio ba, gani

suke, neman tayar da zaune tsaye a ke yi, duk lokacin da aka soki tsarin

rigakafi. Haka kuma, wasu daga cikin malamai, sukan yi qoqarin

danganta jahilci ko tsattsaurar ra’ayi ga waxanda ke qorafi a kan

Page 91: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

91

maganin rigakafin polio, duk da cewa malaman ne ba su fahimci

al’amarin ba yadda ya dace.

Sanannen abu ne cewa, babu wanda ke jayayya game da halaccin

yin rigakafi a Musulunci, ta hanyar karanta addu’o’i, ko yin zikirori, ko

cin dabinon ajwah, ko kuma xaukar waxansu matakan da Shari’ah ta

yarda da su don tsare kai, da kuma samun kariya daga cututtuka. Kace-

nace a tsakanin mutanen Nijeriya ya auku ne a dalilin matsaloli da

illolin da aka gano game da maganin rigakafin. Matsaloli da illolin da

ke tattare da maganin rigakafin sun dace da makircin qasar Amurka da

`yan kanzaginta, da kuma mummunar kaidinsu ga Musulunci da

musulmi, da sauran baqar fata, ko da ba musulmi ba ne.

Tun da aka fara kace-nace dangane da rigakafin polio, akwai wanda

ya tabbatar da rashin sahihancin sakamakon binciken da aka gudanar a

wannan qasa, wanda ya tabbatar da cewa akwai illoli a cikin maganin?

Ina sakamakon binciken da Farfesa Haruna Kaita ya gudanar? Ina sakamakon binciken da Jamā’atu Nasril Islām ta sa aka gudanar? Ina

sakamakon binciken da ma’aikatar lafiya ta tarayya tare da haxin

gwiwar hukumar NAFDAC ta gudanar? Sakamakon binciken da

waxannan vangarori guda uku suka gudanar, ya tabbatar da cewa, an

gurvata maganin rigakafin polio da a ke xiga wa yara, kuma an shigar

da waxansu abubuwa masu haxarin gaske a cikinsa. Mene ne ya hana a

bayyana sakamakon binciken ga `yan Nijeriya? Me ya sa a ke ci gaba

da amfani da shi, duk da cewa an hana xiga wa `ya`yan Amurkawa, a

jihar Lagos? Kuma ko da ya ke daga baya, hukumar Nijeriya ta yi

da’awar magance matsalar gurvacewar maganin, har ma aka tursasa wa

jihohin Kano da Zamfara amfani da shi, wane tabbaci Musulmin

Nijeriya ke da shi game da sahihancin sabon maganin rigakafin? Idan

da gaske ne, mene ne ya hana a nemi su Farfesa Haruna Kaita domin a

sake yin gwaji a kan sabon maganin? Wannan kawai ya isa ya haifar

wa mafi yawan Musulmin Nijeriya xari-xari game da ingancin

rigakafin polio.

Ban da wannan, mene ne yasa qasar Amurka ta yi barazanar qaqaba

takunkumi a kan Nijeriya idan ba a yi rigakafi a jihohin Zamfara da

Kano ba, alhali cibiyar hana yaxuwar cututtuka ta Amurka (Centre for Disease Control), ta ba da shawarar dakatar da xiga maganin rigakafin

polio ga `ya`yan Amurkawa, a ranar 1 ga watan Janairu, 2000, saboda

an gano cewa maganin na haddasa cutar shan inna? Mene ne dalilin

tursasa qasar Saudi Arabia ta yi barazanar hana musulmin Nijeriya

zuwa aikin Hajji, idan ba a yi polio ba, tare da cewa, cutar, ba ta kama

manya, sai dai qananan yara?

Page 92: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

92

Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Idan dare ya yi (wato

rana ta faxa) ku tsare `ya`yanku (kada ku barsu su fita

gida), domin a wannan lokaci shaixanu (daga cikin

Ina hikimar kururuta al’amarin rigakafin polio, da qungiyar lafiya ta

duniya (World Health Organisation) ke yi, duk da cewa, a jerin gwanon

cututtuka masu saurin kisa, polio ba shi daga cikin cututtuka guda

goma, mafi haxari; amma a xaya vangaren, qungiyar, ba ta kuzuzuta

cutar qyanda (measles), da zazzavin cizon sauro (malaria) ko zazzavi

mai sanya tsananin zafin jiki (typhoid), duk da cewa sun addabi `yan

Nijeriya, kuma suna sanadiyyar mutuwar dubban mutane, a kowace

shekara? Wace hovvasa qungiyar lafiya ta duniya ke yi, wajen kawar

da waxannan cututtukan da ke sahun farko a jerin cututtuka masu kisa?

Ashe ba a wannan qasar ba ce, jaridar Daily Trust, ta ranar 7 ga

Oktoba, 2003, ta bayyana cewa, kusan kashi arba’in bisa xari (40%) na

xaruruwan miliyoyin `yan Afrikan da ke fama da matsalar zazzavin

cizon sauro, `yan Nijeriya ne? Mene ne gwabnatin Nijeriya, da

hukumomin qasashen qetare, da qungiyoyin ba da agaji suka yi, a kan

wannan? A yayin da a ke xiga maganin rigakafin cutar polio kyauta,

duk da yawan kuxin da a ke kashewa, da qyar `yan Nijeriya ke iya

sayen maganin zazzavin cizon sauro, da maganin cutar qyanda! Abin

tambaya a nan shi ne: mene ne yasa gwabnati ke kashe wa kowane

yaron da aka xiga wa maganin rigakafin polio fiye da N300, amma ba

ta iya samar da maganin zazzavin cizon sauro da maganin cutar qyanda

kyauta duk da cewa kuxin da a ke buqata don yin hakan bai taka kara

ya karya ba? Haka kuma, mene ne yasa a ke bi gida-gida domin yin

rigakafin cutar polio har sau huxu a shekara, ba tare da la’akari da

yaran da aka yi masu rigakafin, da waxanda ba a yi wa ba? Sau nawa

ya kamata a yi wa yaro rigakafin cutar shan inna a rayuwarsa? Sau

nawa ya kamata a yi wa yaro rigakafin polio a kowace shekara? Daga

shekara nawa ne ya kamata a daina yi wa yara allurar rigakafin polio?

Bayan wannan, ashe, ba qungiyar lafiya ta duniya ba ce, tare da

taimakon gwabnatin Amurka, ta sa aka qago qwayoyin cutar sida (HIV/AIDS), aka zuba qwayoyin a cikin maganin allurar rigakafin

ciwon agana, aka kai wa mutanen qasar Zaire, Zambia, Tanzania,

Uganda, Malawi, Rwanda, Brundi, Brazil, da Haiti ba, kamar yadda

jaridar The London Times, ta qasar Ingila, ta bayyana, a ranar Litinin,

11 ga Mayu, 1987, kuma Dr. William Doglas, wani qwararren likita, a

Amurka, ya tabbatar da hakan, a cikin mujallar Amurka, mai suna

Health Consciousness, ta watan Disamba, 1987? [Duba littafina

Ni’imar Haihuwa da Haqqoqin `Ya`ya a Musulunci don qarin bayani]

Page 93: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

93

aljannu) ke warwatsuwa (don zuwa yawo). Idan aka

samu wani lokaci (bayan faxuwar rana), to ku sake

su…‛169

A wata ruwayar, Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Kada ku saki

dabbobinku da `ya`yanku (qanana) idan rana ta faxi, har

sai duhu ya shiga; domin shaixanu na yawo daga wannan

lokaci zuwa lokacin da duhu zai fara shiga.‛170

Haka

kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya kasance yana yi wa al-Hasan da al-Husain

addu’ar neman tsari, da kiyayewar Allah a gare su. Kuma ya kan ce, Kakanku (Annabi Ibrāhīm) ya kasance

yana nema wa Ismā’īl da Ishāq tsari da irin wannan

addu’ar da nake muku:

[Ina neman muku tsari da kalmomin Allah cikakku daga

dukkan shaixan da wata dabba (ko qwaro) mai dafi, da

kuma dukkan wani mai kambin baka, mai cutarwa]171

.

Haka kuma, yana da matuqar muhimmanci, iyaye su

koya wa `ya`yansu nau’o’in zikirin da a ke yi domin

samun kariyar Allah (Mai tsarki da xaukaka) daga

dukkan wani abu mai cutarwa, musamman bayan sallar

asuba da magriba, da lokacin barci, da lokacin fita gida,

da lokacin shiga bayi.172

169

Bukhari da Muslim 170

Muslim 171

Bukhari 172

Zikiri shi ne abin da ke gudana a kan harshe da zuciya, wanda ya

qunshi tasbihi da hailala da tahmidi, da yabo ga Allah (Maxaukaki), da

karanta Alqur’ani, da yin addu’a, da zartar da umurnin Allah, da tunani

a cikin ni’imominSa da halittarSa. Zikirin Allah igiya ce mai qarfi,

wadda ke qulla kyakkyawar alaqa a tsakanin bawa da Mahaliccinsa,

kuma ta ke sanya bawan Allah ya rayu a cikin kulawa da kariyar Allah,

ta yadda Allah zai tsai da shi a kan alhairi, kuma Ya tabbatar da shi a

kan hanya madaidaiciya.

Page 94: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

94

Zikiri shi ne abin da ke yaye wa zukata baqqan ciki, kuma ya goge

zukata fyas. Zikiri shi ne buxaxxiyar qofar Allah (Maxaukaki) mafi

girma, wadda ke tsakanin Allah (Maxaukaki) da bawanSa, matuqar dai

bawa bai gafala ko ya rafkana ga barinta ba. Zikiri shi ne ruhin ayyuka;

idan bawa ya bar zikiri, zai zamanto kamar jiki ne da ba shi da ruhi.

Wannan yasa Allah (Maxaukaki) Ya umurci musulmi da su kasance

daga cikin waxanda ke yin zikirin Allah a cikin dare da rana, a zaune

da tsaye da kwance, a asirce da bayyane, a halin zaman gida da tafiya, a

ruwa ko a tudu, a halin rashin lafiya da lokacin qoshin lafiya.

Ibnul Qayyim ya bayyana fa’idodi da falalar zikiri har guda xari (100) a cikin littafinsa Al-Wābilus Sayyib, (Al-Maktabuth-Thaqāfi, Al-

Qāhirah, 2003), shafi na 41-93. Daga cikin falalar zikiri, akwai: (1)

zuciya na samun babban rabo da natsuwa a cikin duniya da lahira (2)

zikiri na daga mafificin xa’a, kuma yana daga mafi girman ayyukan

samun kusanci zuwa ga Allah (3) waxanda ke yin zikiri, su ne ke

amfana da ayoyin Allah, kuma su ne masu hankali da tunani (4) zikirin

Allah shi ne katangar qarfe da bawa ke tsare kansa da ita daga shaixan

(5) zikiri na daga dalilan samun xaukaka a duniya da lahira (6) zikiri na

daga dalilan da ke jawo arziqi a duniya da lahira ga xaixaikun mutane,

da kuma al’umma baki xaya (7) wanda ke yin zikiri, Allah Yana

ambatonsa a cikin mala’iku (8) dawwama a kan zikiri na wajabta wa

bawa samun aminci daga mantawa da Allah (9) yana kawo wa bawa

kiyayewa da kulawar Allah (10) zikiri alama ce ta kuvutar bawa daga

munafinci (11) zikiri yana yardar da Allah (12) yana gusar da baqin

ciki da damuwa da vacin rai daga zuciya (13) yana jawo wa zuciya

farin ciki da walwala da nishaxi da jin daxi (14) yana qarfafa zuciya da

gangar jiki (15) yana haskaka zuciya da fuska (16) yana jawo wa mai

yinsa kwarjini da girma (17) yana gadar wa bawa da soyayyar Allah

(18) yana kankare zunubi, ya saryar da laifi (19) yana gadar da lada mai

yawa (20) yana gusar da kaxaici (21) yana tserar da mutum daga azabar

Allah (22) dalili ne na saukar natsuwa da lulluvewar rahama da samun

kariya (23) yana shagaltar da harshe daga barin giba da gulma da qarya

da alfasha da tsogararo (24) yana daga mafi sauqin ibada (25) yana

daga cikin ibada mafi falala (26) wuraren da a ke yin zikiri, wurare ne

da mala’iku ke zuwa (27) yana sauqaqe abu mai wahala kuma ya

kawar da tsoro (28) yana maye gurbin taxawwu’in da ba a samu damar

yi ba (29) yana daga cikin nau’o’in ibada mafi karamci a wajen Allah

(30) yana gadar wa bawa xabi’ar mai da al’amura zuwa ga Allah.

Zikiri na da nau’o’i dabam daban. Nau’o’in zikiri sun haxa da: (1)

karatun Alqur’ani (2) zikirin da a ke yi da harshe, kamar tasbīh (

Page 95: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

95

), tahlīl ( ), tahmīd ( ), takbīr ( ), hawqala (

), da istirjā ( ), da sauran nau’o’in zikirin da suka

tabbata a ckin Alqur’ani da Sunnah sahihiya (3) addu’a (4) istigfari (5)

tunani a cikin halittun Allah (6) ayyukan xa’a, kamar salla da azumi da

sadaka da ziyara da neman ilmi.

Zikiri na da lokuta iri biyu: sakakken lokaci ( ) da iyakantaccen

lokaci ( ). Duk wani zikirin da ba a iyakance masa lokaci ko wuri ko

adadi ko siffa ba, a cikin Alqur’ani da Sunnah, za a iya yinsa a ko’ina,

kuma a kowane lokaci ko yanayi ko siffa, in ban da abin da nassi sahihi

ya hana. Zikirin da aka qayyade shi da wani lokaci ko hali ko wuri ya

haxa da: zikirin safe (daga fitar alfijir zuwa kafin rana ta fito) da

yamma (bayan la’asar zuwa faxuwar rana), da lokacin barci, da bayan

farkawa daga barci, da shiga gida ko fita, da shiga masallaci ko fita, da

shiga ban xaki ko fitowa daga ban xaki, da lokacin rashin lafiya, da

lokacin baqin ciki ko damuwa, da lokacin aukuwar musiba, da halin

tafiya, da lokacin saukar ruwan sama, da bayan sallar farilla, da bayan

kammala alwalla.

Akwai kurakurai da dama da aka shigar cikin zikiri. Daga cikin

kurakuran akwai: (1) qayyade sakakken zikiri da wata siffa ko adadi ko

yanayi ko lokaci ko wuri, ko kuma rashin iyakance zikirin da nassi ya

qayyade (2) zikiri a cikin jam’i, alhali kuwa ba shi daga cikin Sunnah, kamar yadda Ibn Abi Shaibah ya ruwaito daga Umar ibnul Khaxxāb,

kuma Ad-Dārimi ya ruwaito daga Ibn Mas’ud (Allah Ya yarda da su)

cewa sun yi tsananin inkari ga waxanda ke yin zikiri cikin jam’i (3) yin

kixa da rawa da tafi da rausayawa ko layi wajen zikiri, kasancewar manyan malamai irin su Ax-Xurxūshi a cikin Al-Hawādith wal Bida’, da Al-Qurxubī, a cikin Al-Jāmi’u li Ahkāmil Qur’ān, da Ibnul Jauzī, a

cikin Talbīs Iblīs, da Ash-Shāxibī, a cikin Al-‘I’itisām, da Ibnus Salāh,

a cikin Al-Fatāwā, da Ibn Taimiyyah, a cikin Majmū’ul Fatāwā da

Mas’alatus Sama’, da Ibnul Qayyim, a cikin Ighāthatul Lahfān da

Madārijus Sālikīn, da Ibnul Hāj, a cikin Al-Madkhal, da As-Sayyid

Mahmud Al-Alusi, a cikin Rūhul Ma’āni, da Ibn Hajar Al-Haithumī, a

cikin Kaffur-Ra’a’ ‘Anistimā’i’ Aalātis Samā’ sun nuna haramcin yin

haka (4) xaga murya fiye da buqata, in ban da wajen kiran salla da iqama, da kabbarorin liman a cikin salla, da faxin ‘amīn’ a qarshe

fatiha ko a wajen addu’a, da faxin ‘sami’allahu liman hamidah’ ko

‘rabbana walakal hamd’, da karatun sallar da a ke bayyanawa, da

kabbarorin isarwa ga mamu idan akwai buqata, da sallamewa daga

salla, da yin sallama ko amsa sallama ga musulmi, da faxin ‘Alhamdu

Page 96: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

96

Ke nan, wajibi ne iyaye su kula da `ya`yansu, kuma su

tsare su daga dukkan abubuwa masu cutarwa ko

firgitarwa, ta hanyar yin masu addu’a, da hana su zuwa

wuraren haxari. Ibn al-Qayyim ya ce: ‚Ya kamata a

nisantar da yaro daga dukkan wani sauti ko wani abin

kallo mai firgitarwa da tsoratarwa, domin (rashin yin)

hakan na iya cutar da qwaqwalwarsa tun yana

qarami.‛173

Amma abin mamaki shi ne, waxansu iyayen,

tsoratar da `ya`yansu su ke yi ta hanyar kiran sunan dodo

ko kyanwa (mage) ko kura ko kare ko vera ko wani sauti

mai firgitarwa da tsoratarwa, a duk lokacin da su ke son

yara su daina kuka, ko kuma su daina yin wani abu mara

kyau. Ta haka, sai yaro ya taso da tsoron dodo ko aljannu

a cikin zuciyarsa, maimakon ya ji tsoron Allah kuma ya

saba da jarumta da sadaukantaka. Lallai ne iyaye su ji

tsoron Allah game da wannan al’amari.

12. Karantar da `ya`ya ilmin Shari’ah da ilmin sana’a, ko

kuma a tura su makaranta don su koyo. Ta hanyar ba su

ilmin addini, da zaburar da su a kan aiki da shi, iyaye za

su kare kawunansu da na iyalinsu daga wuta, kamar

yadda Allah Ya yi umurni. Haka kuma, ta hanyar ilmin

sana’a ne, `ya`ya za su zama masu kishin zuci, da dogaro

da kai, da amfani ga al’umma.174

lillah’ bayan atishawa ko kuma addu’a ga wanda ya yi atishawa, da kabbarbarin īdi, da zikirin bayan sallar farilla, da talbiyya, da

kabbarbari wajen aikin hajji, da karatun Alqur’ani, da faxin ‘Bismillah’

wajen yanka. Ban da waxannan wurare, ba a buqatar xaga murya da

qarfi a cikin zikiri. 173

Tuhfah al-Maudūd, shafi na 158 174

Ilmi shi ne mafificin abin da ya kamata a yi amfani da dukiya wajen

nemansa, domin kuwa babu abin da ya kai shi daraja. Da ilmi ne a ke

sanin Allah domin a bauta maSa; kuma da ilmi ne a ke sanin haqqoqin

kowa domin a ba shi. Ilmi haske ne da a ke shiryuwa da shi; yana gadar

da taqawa; kuma yana jawo daraja da xaukaka ga wanda ya mallake

Page 97: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

97

shi. Ilmi shi ne ma’aunin halal da haram; kuma shi ne maganin cutar

jahilci da rarraba a tsakanin mutane.

Neman ilmi ibada ce, kuma bitarsa tasbihi ne; bincike a kansa jihadi

ne; koyar da shi ga wanda bai sani ba sadaka ce, kuma yaxa shi a cikin

masu shi aikin lada ne. Ilmi mai xebe wa mai shi kewa ne a lokacin

kaxaici, kuma aboki ne a halin tafiya; da shi ne a ke sanin Allah kuma a

bauta maSa; da shi ne a ke sanin matsayin Allah kuma a girmama Shi.

Lafazin ilmi ( ) ya zo a cikin Alqur’ani fiye da sau saba’in da

bakwai, a bisa yanayi dabam daban na jujjuyawar kalmomi a harshen

larabci. Haka kuma lafazin ya zo da ma’anoni mabambanta a wurare

masu yawa a Alqur’ani. Ya zo da ma’anar: sanin abu bisa haqiqanin yadda ya ke [Baqarah, 2:77, 216]; gani [Aal Imrān, 3:142; Baqarah,

2:143]; izni [Hud, 11:14]; addini [Baqarah, 2:120]; dalili da hujja [An’ām, 6:148]; Annabta [Yusuf, 12:22]; rarrabewa/tantancewa [Aal

Imrān, 3:166-167]; falala [Qasas, 28:78]; da kuma ma’anar abin da a ke

zaton cewa ilmi ne alhali kuwa a haqiqa ba shi ba ne [Ghāfir, 40:83;

An’ām, 6:148].

Ilmi na da falala mai yawa da matsayi mai girma. Ilmi haske ne da

ke nuna wa mai shi bambancin gaskiya da qarya [Saba, 34:6]; yana gadar da tsoron Allah [Isrā, 17:107-109]; shi ne mafificin jihadi

[Furqān, 25:52]; alama ce ta masu imani [Munafiqun, 63:8]; ba ya

yankewa saboda mutuwa [Sahīh Muslim]; la’ana ba ta sauka a kan ilmi

[Tirmidhi]; alama ce ta alhairi [Baihaqi]; kuma yana shigar da mutane

hanyar aljanna [Muslim]. Saboda falalar ilmi, Allah (Mai girma da

xaukaka) Ya yi wa Annabi Yusuf da Musa da Isa da Muhammad (tsira

da aminci su tabbata a gare su) gori a kan ilmin da Ya ba su [Yusuf, 12:22; Qasas, 28:14; Mā’idah, 5:110; Nisā, 4:113].

Ilmi ya kevanta da abubuwa guda shida: (1) shi ne gadon Annabawa

(2) shi ne kaxai aka yi wa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) umurni da yin addu’ar Allah (Mai girma da

xaukaka) Ya qara masa (3) Allah Ya siffanta kanSa da ilmi (4) kowane

mutum yana farin ciki idan aka danganta ilmi gare shi, ko da kuwa ba

shi da ilmin; haka nan kowane mutum ba ya son a danganta shi zuwa

ga kishiyar ilmi, ko da kuwa jahili ne (5) shi ne kaxai abin da ba ya

raguwa daga mai shi saboda ya ba wani (6) ilmi ba ya qarewa saboda

yawan karantarwa, shi yasa ba a tava samun wanda aka ce, ‘Allah

sarki, wane ya kasance mai ilmi, amma yanzu ilmin ya qare’, duk da

cewa a kan ce, ‘wane mai kuxi ne, amma yanzu ba shi da komai’ ko

kuma ‘wane mai mulki/sarauta ne, amma yanzu ba shi da komai’.

Page 98: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

98

Masu ilmi manyan mutane ne a cikin Musulunci domin su ne

malamai waxanda ke koyo kuma su koyar, su karanta kuma su

karantar. Malamai su ne ke yi wa al’umma tarbiyya a kan ilmi [Aal Imrān, 3:79; Mā’idah, 5:44]; su ne ke yi wa al’umma shugabanci,

matuqar sun lazimci haquri da taqawa [Baqarah, 2:248; Sajdah, 32:24]; suna daga cikin Ulul Amr da aka ce a yi wa xa’a [Nisā, 4:59]; su ne

Ahluz Zikr da aka ce a yi wa tambaya [Nahl, 16:43; Anbiyā, 21:7]; su

ne Allah Ya ce a koma gare su a lokacin da wani abu mai girma ya auku [Nisā, 4:83]; su ne waxanda Allah Ya gwama shaidarsu da

shaidarSa [Aal Imrān, 3:18]; su ne waxanda bin hanyarsu ke kai mutum

ga shiriya [Maryam, 19:43]; su ne magadan Annabawa [Abu Dāwud da

Tirmidhi]; su ne waxanda ke tsoron Allah [Fāxir, 35:28]; suna daga

cikin waxanda Allah Ya ke xaukaka darajarsu [Mujādalah, 58:11];

kuma suna daga cikin waxanda Allah Ya ke nufi da alhairi [Bukhari da

Muslim]; su ne mafi hasken fuska kuma mafi xaukakar mutane saboda

addu’ar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) gare su [Ahmad, Abu Dawud, Tirmidhi da Ibn Mājah]; Allah (Mai

girma da xaukaka) Ya hore masu komai don ya nema masu gafarar Allah kuma ya yi masu addu’a [Abu Ya’alā]; su ne waxanda Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya bar wasiyya game da su [Ibn Mājah].

Neman ilmin Shari’ah domin aikata abin da Allah Ya xora wa kowane bawa wajibi ne [Nahl, 16:43; Anbiyā, 21:7; Muhammad,

47:19; Xabarāni]; idan kuwa wajibin kowa da kowa ne, nemansa wajibi

ne a kan al’umma gaba xayanta [Ibn Abdil-Barr, a cikin At-Tamhīd;

An-Nawawi, a cikin Al-Majmū’; da Ibn Taimiyyah, a cikin Majmū’ul Fatāwā]. Haka kuma, neman ilmin sana’a da kimiyya da fasaha da

sauran na’o’in ilmin rayuwa, wajibi ne al’umma ta samu wakilci,

saboda yana daga cikin tattali da kintsin da Allah (Maxaukaki) Ya yi

umurni [Anfāl, 8:60], kuma ya shiga cikin qa’idar

. Don haka, dole ne Musulmi su shiga makarantar boko domin

samun ilmin fannoni dabam daban, gwargwadon buqatar kowane

zamani, da kuma kowace al’umma.

Ilmi na da muhimmanci a rayuwar Musulmi. Da ilmi ne a ke

tabbatar da tsantsar bauta ga Allah. Sanin halal da haram ba zai yiwu ba

sai da ilmi. Ba za a iya sanin kevance-kevancen Musulunci da falalarsa

ba sai da ilmi. Tunkarar qalubalen da ke fuskantar al’ummar Musulmi,

musamman munanan aqidodi, da al-gazwul fikriy, da koma bayan

Musulmi a fagen ilmi da tattalin arziqi da gudanarwa, ba za ta yiwu ba

sai da ilmi. Bayan wannan, kyakkyawar wakilci ga Musulmi a kowane

Page 99: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

99

Mutum zai yi takaici idan ya dubi yadda waxansu iyaye

ke nuna halin ko in kula game da ilmin `ya`yansu.

Waxansu ba su damu da koyar da su, ko tura su

makaranta don koyon ilmin addini ba. Waxansu kuma,

suna tura su, amma ba su ba karatun muhimmanci ba,

kamar yadda suka ba na boko. Wannan yasa waxansu

yaran ke yi wa ilmin addini ko malaman addini kallon

biyu ahu, kuma suna fifita duk wani abin da ya shafi

karatun boko a kansa. Wannan irin qasqanci da iyaye ke

jawo wa ilmin addini, babban bala’i ne. Ya kamata a

nuna wa yara cewa girmama ilmi da malamai bisa

qa’idodin Shari’a, wajibi ne a kan kowa. Sanannen abu

ne cewa malamai su ne magadan Annabawa. Allah (Mai

girma da xaukaka) Ya ce: ‚Ka ce, ‚Ashe, waxanda suka

sani, suna daidaita da waxanda ba su sani ba?‛ Masu

hankali kawai ke yin tunani.‛175

Kuma Allah (Mai girma

da xaukaka) Ya ce: ‚Allah na xaukaka waxanda suka yi

imani daga cikinku da waxanda aka bai wa ilmi, wasu

darajoji masu yawa, kuma Allah Mai qididdigewa ne ga

dukan kome.‛176

A vangaren ilmin zamani, ko koyon sana’a, da yawa

daga iyaye (musamman a qauyuka) na sakaci wajen tura

`ya`yansu. Za ka ga `ya`ya na wasa a gida, ko a kan titi,

a lokacin da ya kamata su je makaranta, ko wajen koyon

sana’a. A qarshe, idan `ya`yan suka taso ba tare da ilmin

vangaren rayuwa ta dogara ne a kan ilmi. Haka kuma, bin umurnin

Allah (Mai tsarki da xaukaka) da ManzonSa (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) yana yiwuwa ne kawai idan akwai ilmi. 175

Zumar, 39:9

176 Mujādalah, 58:11

Page 100: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

100

zamani ko ilmin sana’a ba, sai su zama mabarata, ko

`yan bangar siyasa, ko `yan daba.177

177

Tarihi ya tabbatar da cewa al’ummar Musulmi ta kasance abar

alfahari saboda bunqasar da ta yi a fagen ilmi, da shugabanci, da

tattalin arziqi, da tsarin zamantakewa, irin waxanda duniya ba ta tava

gani ba. Haka kuma, ta kasance al’ummar da ta yi fice wajen dogaro da

kai, da kishin zuci, kamar yadda ta shahara wajen kawo amfani da ci

gaba ga duniya baki xaya.

Amma a yau, abubuwa da dama sun canza a cikin wannan al’umma.

Xaukakarta ta yi qasa, haskenta ya dushe, shahararta ta wuce,

jagorancinta ya kuvuce, darajarta ta ragu, kuma matsayinta ya faxi. A

fagen ilmi, sauran al’ummomi sun yi mata fintinkau. A vangaren

tattalin arziqi da ci gaban rayuwa, an bar ta a baya. Wannan yasa

talauci da jahilci suka addabe ta, kuma rashin sanin ciwon kai ya yaxu

a cikinta. Hakan, ya haifar da ci baya sosai a gare ta.

Rashin kishin kai da wadatar zuci sun sanya waxansu daga cikin

`ya`yan wannan al’umma sun xauki zaman kashe wando da xumama

benci a matsayin alamar wayewa; barace-barace da roqo da maula da

bambaxanci a matsayin sana’a; kuma zaman ludo da karta da tsegumi a

matsayin hanya mafi dacewa ta amfani da lokaci. Wannan xabi’a ta

jawo wa al’ummar Musulmi koma baya, da qorafi da tsana da kushe

daga sauran al’ummomi.

Daga cikin waxannan munanan xabi’u, yawon maula ya fi haifar da

illoli da sharri a cikin al’umma, kasancewar masu yin maula sun tattaro

aibobin da suka zarce saura. Galibin masu yawon maula na da’awar

wayewa da sanin inda duniya ta sa gaba. Suna yin kyakkyawar shiga, ta

hanyar sanya manyan rigunar da ke bayyana su a matsayin manyan

mutane. Xabi’arsu ita ce, bin gidajen masu kuxi, da ofisoshin manyan

ma’aikata, da wajen hirar manyan `yan siyasa, don samun abin cefane.

Sana’arsu ita ce neman abin hannun mutane ta hanyar da ba ta dace ba.

Maula ta qunshi neman abin hannun mutane, ba tare da haqqi ba, ta

hanyar qarya ko naci ko bambaxanci ko zamba. Manufar xan maula ita

ce samun biyan buqata daga waninsa ta kowace irin hanyar da za ta

jawo masa qasqanci, da wulaqanci, da mutuwar zuciya, da xabi’ar

samun na banza. Mutanen da ke yin maula, na xaukar wannan xabi’a, a

matsayin sana’a, kasancewar ba su da wata hanyar samun biyan

buqatar rayuwa da ta wuce ta. Don haka, su ke yin takakkiya zuwa gida

ko ofis ko wajen sana’ar wanda za su yi wa maular, ko dai da sunan

siyasa ko malanta ko kuma wani abin daban.

Page 101: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

101

Haqiqa, Musulunci ya hana bin irin waxannan hanyoyi da `yan

maula ke amfani da su don samun biyan buqata a hannun jama’a. A

cikin hadisai da dama, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) ya tsawatar game da roqo (idan babu tsananin larura) ko

naci, don a raba wani da abin hannunsa, ko zaqewa cikin yabo, ko

zamba domin a karvi wani abu a hannun mutane. Haka kuma, Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi kyakkyawar

addu’a ga waxanda ke kamewa daga roqo ko bambaxanci.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce wa Hakīm bn Hizām (Allah Ya yarda da shi):

‚Ya Hakīm! Dukiya, na da daxi: to wanda ya karve ta (a hannun wani)

bisa daxin rai (daga wanda ya ba da), za a sanya masa albarka a cikinta.

Wanda kuwa ya karva ta hanyar naci (ko bambaxanci), ba za a sanya

masa albarka a ciki ba. Kuma zai zamanto kamar wanda ke cin abinci,

amma ba ya qoshi‛ [Bukhari].

Dangane da raba mutane da abin hannunsu ta hanyar naci, Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Wanda ya roqi mutane (abin hannunsu) alhali yana da abin da ya kai qimar Uqiyah, to haqiqa ya yi naci‛ [Abu Dawud da Nasā’i].

Dangane da amfani da hanyar zamba ko kushe don kai wa ga biyan

buqata, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

ce:

‚ Tir da bawan dinare da dirhami da bargo da riga: idan an ba shi (abin

da ya nema) sai ya gamsu (ya yi yabo). Amma idan bai samu ba, ya qi

gamsuwa (ya yi zamba)‛ [Bukhari].

Haka kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya bayyana irin haxari da halin qasqanci da mai maula ke ciki, da

kuma mummunar makomarsa idan bai tuba ba. Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Mutum ba zai gushe yana tambayar mutane dukiyarsu ba, har sai ya zo

a ranar Qiyama, ba tare da ko tsoka xaya a fuskarsa ba‛ [Bukhari].

Malamai sun ce hadisin zai iya xaukar cewa mai roqo zai zo a

qasqance, ba tare da mutunci ko qima ba a ranar lahira (saboda neman

Page 102: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

102

abin hannun mutane da ya riqa yi), ko kuma hadisin na nufin za a yi

masa azaba a fuskarsa har sai naman ya zaganye gaba xaya.

Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ya ce:

‚Roqo magurji ne da mutum ke gurje fuskarsa da shi. Don haka, wanda

ya so, ya ci gaba da gurje fuskarsa ko ya bari, sai dai idan mutum zai

roqi sarki ne, ko (zai yi roqo) cikin abin da ba shi da makawa‛ [Abu Dawud, Tirmidhi da Nasā’i].

A cikin wani Hadisin, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce:

‚Wanda ya roqi mutane wani abu alhali ya wadata daga gare shi, zai zame masa wani abin qasqanci a fuskarsa‛ [Dārimi da Ahmad].

Dangane da mummunar makomar xan maula ko mai sana’ar roqo

idan bai tuba ba, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce:

.

‚Wanda ya yi roqo alhali yana da abin da zai wadace shi, to yana

yawaita (rabonsa ne) daga wutar Jahannama.‛ Suka ce: Ya Manzon

Allah, mene ne zai wadace shi? Ya ce: ‘Abin da zai ishe shi yin kalaci

ko abincin dare‛ [Ahmad]. A ruwayar Abu Dawud: ‚Ya kasance yana

da abincin yini da dare (kwana xaya).‛

A cikin wani Hadisin, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya ce:

‚Wanda ke roqon mutane dukiyarsu don yawaita abin da ya mallaka,

yana roqon garwashin wuta ne. Don haka (ya rage gare shi) ya roqi

kaxan ko mai yawa‛ [Muslim].

Bayan wannan, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya yi yabo ga waxanda ke kamewa daga roqo ko maula, kuma

ya lamunce masu shiga aljanna a ranar qiyama. Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

Page 103: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

103

‚Ya samu babban rabo: wanda ya musulunta, kuma aka azurta shi da

(gwargwadon) abin da ya ke buqata, kuma Allah Ya sanya masa

wadatar zuci a cikin abin da Ya ba shi‛ [Muslim].

Haka kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce:

‚Wane ne zai lamunce mani cewa ba zai nemi komai a hannun mutane ba, ni kuwa in lamunce masa shiga aljanna? Sai Thaubān (Allah Ya

yarda da shi) ya ce: ‘Ni ne’. Don haka ya kasance ba ya neman komai a hannun wani‛ [Nasā’i da Baihaqi].

Babu shakka, maula na haifar da matsaloli ga wanda ke yinta, da

wanda a ke yi wa, da al’umma baki xaya. Daga cikin matsalolin da

maula ke haifarwa ga mai maular, akwai: jawo mutuwar zuciya; da

zama talasuru; da jawo qasqanci, da qyama, da zubewar mutunci a

cikin jama’a; da tauye tattalin arziqi; da mummunar makoma a lahira

idan ba a tuba ba.

Wanda a ke yi wa maula bai kuvuta daga sharri da aibobinta ba.

Daga cikin aibobinta ga wanda a ke yi wa, akwai: tauye tattalin arziqi,

domin yana vatar da kuxi ta hanyar abin da bai tanada ba; da haifar da

girman kai da riya; da yin xabi’ar xan hali don a cike gurbin abin da

aka rasa ta hanyar biyan buqatar masu maula.

Sharrin maula bai tsaya a kan xaixaikun mutane ba. Gaba xayan

al’umma ba su kuvuta daga musifarta ba, domin tana haifar da koma

baya gare su ta hanyar: rashin ba da gudummuwa wajen samar da

buqatun al’umma; da jawo tsana da kushe ga al’umma daga sauran

qasashen qetare; da yaxa aqidar zaman kashe wando; da jawo wa

gwabnati hasarar kuxin shiga; da jawo wa gwabnati qarin kashe kuxi

don samar da abubuwan more rayuwa, kamar magani a asibiti da ruwan

sha ga mutanen da za su iya tallafa wa kansu, ba domin suna yin maula

ba.

Ban da maula, xabi’ar barace-barace na daga cikin matsalolin da ke

addabar al’ummar Musulmi, musamman a arewacin Nijeriya. Mabarata

sun xaukar wa kansu xabi’ar roqon mutane abin hannunsu, ta hanyar

qasqanci da wulaqantar da kai, da jawo wa Musulunci da Musulmi

gori, musamman a idanun kafirai. Mutuwar zuci da rashin kishin kai

sun sanya waxansu mutane sun xauki bara a matsayin sana’a, duk da

cewa mafi yawansu suna da lafiyar jiki, da ikon yin aiki don dogaro da

kai, ba tare da sun zame wa al’umma matsala ba. Abin baqin ciki shi

ne, maimakon a qyamaci xabi’ar barace-barace a tsakanin Musulmi,

mafi yawan mutane ba su damu ba. Hasali ma, waxansu azzaluman

Page 104: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

104

malamai na qarfafar wannan mummunar xabi’a, kuma suna goyon

bayan mabarata, har ma suna nuna cewa Musulunci bai hana xaukar

bara a matsayin sana’a ba. Bayan haka, wasu daga cikin irin waxannan

azzaluman malamai na da’awar cewa karatun Alqur’ani ba zai yiwu ba

sai an yi bara, duk da cewa su ba su tura `ya`yansu almajiranci.

Kasancewar maula da barace-barace alamomi ne waxanda ke nuna

ci baya, da rashin sanin ciwon kai a cikin al’umma, Musulunci ya

tanadar da hanyoyin magance su. Hanyoyin da Musulunci ya bi wajen

magance matsalar maula da bara sun kasu gida biyu. Kashi na farko ya

qunshi saitin tunani da zaburarwa game da dogaro da kai. Kashi na

biyu ya shafi matakan tattalin arziqi da havaka dukiya.

Musulunci ya xauki matakin yin saiti ga tunanin mabiyansa dangane

da haxarin maula da barace-barace da zaman kashe wando da

bambaxanci da rashin kishin zuci ko dogaro da kai, kuma ya zaburar da

su a kan tsare mutunci ta hanyar yin sana’a. Matakan da Musulunci ya

xauka a wannan vangare sun haxa da:

1. Tunatar da su yalwar qasa da abin da ke cikinta, da hore ta da aka

yi gare su, ta yadda za su yi fafutukar neman na kansu. Kuma aka

tabbatar masu da cewa neman arziqi da alhairan da ke cikin qasa, ibada ce ga Allah [A’arāf, 7:10; Mulk, 67:15].

2. Sanya fafutukar neman na kai ta hanyar halal a matsayin alama ta tawakkali ga Allah [Ahmad da Tirmidhī].

3. Kwaxaitarwa game da yin noma, da kasuwanci, da sana’o’in

hannu, da sauran ayyuka (na albashi ko lada) [Bukhari da

Muslim].

4. Xaukar yin aiki don samun abin biyan buqatar rayuwa a matsayin

sadaka, da kuma hanyar ba da sadaka [Bukhari da Muslim].

5. Rashin yarda da duk abin da aka samu ta hanyar da ba ta dace ba.

Wannan yasa Musulunci ya haramta qwace, da fashi, da sata, da

caca, da kuxin ruwa (riba), da duk wata harkar kuxi da ke da

alaqa da su. Kuma ya tanadi uquba dabam daban ga waxanda

suka aikata xayansu. Ta wannan hanyar, Musulunci ya kallafa wa

mabiyansa neman na kai da rashin zaman xumama benci [Mā’idah, 5:33; Mā’idah, 5:38; Baqarah, 2:275-276, 278-279;

Baqarah, 2:219; Mā’idah, 5:90].

Page 105: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

105

Ilmin addini wajibi ne a kan kowane Musulmi. Da shi ne

a ke sanin Allah, kuma a ke sanin dokokinSa, da yadda

za a bauta maSa. Ilmi shi ne maganin cutar jahilci da

6. Tsawatarwa game da roqo, da maula, da barace-barace, da

yaudara [Bukhari da Muslim].

7. Hana ba da sadaka ga mawadata, da waxanda ke da lafiyar jiki da ikon yin aiki don dogaro da kai [Tirmidhī].

Bayanan da suka gabata na nuna wa kowane Musulmi wajibcin

dogaro da kai gwargwadon iko, don tsare mutunci, da nisantar zaman

kashe wando, da baxala, da aqidar cima zaune. Alqur’ani da Sunnar

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sun nuna

wa kowane mutum muhimmancin yin gwagwarmayar neman abin kai

ta hanyar kasuwanci da sana’o’in hannu ko aikin da za a biya lada.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Mutum bai ci abinci mafi alhairi ba fiye da wanda ya samu ta hanyar

aiki da hannunsa‛ [Bukhari]. Haka kuma, Alqur’ani da Sunnah sun

karantar da cewa Allah (Maxaukaki) Ya tarbiyyantar da fiyayyun

halittarSa, Annabawa, a kan yin aiki, domin su zama abin koyi.

Wannan yasa suka yi sana’o’i dabam daban, waxanda suka haxa da

kasuwanci, da kiwon dabbobi, da qira. Bayan wannan, an umurci

kowane Musulmi ya nemi ilmin bauta wa Allah da ilmin harkokin

rayuwa don samun damar amfanar da kansa, da sauran al’umma,

gwargwadon iko, kamar yadda aka hana shi zaman banza, da aqidar

maula da bara, da zame wa al’umma nauyi.

A taqaice, wajibi ne kowane Musulmi ya nemi abin yi, wanda zai

taimaka masa wajen dogaro da kansa, da nisantar neman abin hannun

mutane, ba tare da haqqi ba, ta hanyar naci ko roqo ko bambaxanci ko

qarya ko zamba. Kuma wajibi ne ya ji tsoron Allah a cikin dukkan

al’amuransa.

A vangaren al’umma kuma, Musulunci ya wajabta mata taimaka wa

mutanen da ke da kishin koyon sana’a don magance zaman kawai. Za a

yi hakan, ta hanyar koya masu sana’o’i, da samar da ayyukan yi ga

waxanda ke da ilmin yin ayyukan hukuma. Haka kuma, akwai buqatar

samar da tallafi ga waxanda suka qware a kan waxansu sana’o’in

hannu, amma ba su da kayan aiki. Manufar ita ce a ba su damar amfani

da qwarewarsu da hazaqarsu wajen dogaro da kansu, da tallafa wa

waxanda za su yi aiki a qarqashinsu.

Page 106: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

106

cutar savanin da ke tsakanin al’umma. Shi kuma ilmin

zamani ko ilmin sana’a, gishirin zaman duniya ne.

Wanda ba shi da ilmi, ya rasa komai, ko da kuwa yana

da mulki ko dukiya. Kowane mutum yana buqatar ilmin

addini da na zamani/sana’a, kamar yadda ya ke buqatar

qosasshiyar lafiya, da abinci, da abin sha, da tufafi, da

wajen kwana. Domin kuwa babu yadda za a yi al’umma

ta samu ci gaba, matuqar mafi yawan jama’arta na cikin

jahilci. Wannan ya sa aka ce: ‚wanda ke neman lahira,

ya nemi ilmi; wanda ke neman duniya, ya nemi ilmi;

haka kuma, wanda ke neman duniya da lahira gaba xaya,

to ya nemi ilmi.‛178

Don haka, lallai ne iyaye su ji tsoron Allah game da

ilmin `ya`yansu. Su sani, Allah zai tambaye su a ranar

Qiyama, domin kuwa `ya`ya amana ce a gare su. Su yi

amfani da dukiyar da Allah Ya ba su (komai

qanqantarta) wajen ilmantar da `ya`yansu. Su fifita

neman ilmi ga kansu, da `ya`yansu, da sauran waxanda

ke qarqashinsu a kan komai. Babu hasara ko kaxan a

cikin dukiyar da aka ciyar wajen neman ilmin addini da

na zamani.

Sannan, wajibi ne a kan iyaye su zava wa kansu, da

`ya`yansu makarantun da suka dace, don koyon ilmin

addini da na zamani. Ilmin da babu tarbiyya a cikinsa

akwai matsala. Sanannen abu ne cewa akwai makarantun

islamiyya da dama a wannan lokaci waxanda ba su da

alqibla ko tsarin karantarwa mai kyau. A waxansu

makarantun ma, ba a karantar da yara sahihin addini,

kamar yadda ya ke qunshe cikin Alqur’ani da hadisai

ingantattu bisa fahimtar magabata na qwarai. Maimakon

178

Ana danganta wannan magana ga Imam Ash-Shāfi’ī (Allah Ya

jiqansa)

Page 107: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

107

haka, za ka ga ana koyar da waqe-waqe, da hadisan

qarya, da sauran abubuwan da ba su da wani ingantaccen

dalili a cikin Shari’ah. Abin mamaki, waxansu iyayen

ma, suna kai `ya`yansu makarantun islamiyyar `yan

bidi’a ne, ko ma makarantun `yan shi’a, inda za su koyo

zagin Sahabbai, da cin mutuncin matan Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da aqidar

qiyayya ga Musulmi. Babu shakka, wanda duk ya yi

haka, haqiqa ya ha’inci amanar kulawa da `ya`ya, wadda

Allah (Mai girma) Ya xora masa.

A vangaren ilmin boko ko koyon sana’a ma, akwai

matsaloli dabam daban. Sau da yawa, iyayen da ba su

kishin addininsu na tura `ya`yansu makarantu ko

wuraren koyon sana’a da ke da haxari ga addini da

tarbiyya. Sau da yawa, mun ji labarin yaran da ke rufe

idanu don yin addu’ar coci wajen cin abinci, ko kuma su

riqa maimaita waqoqin kirista waxanda suka koya a

makaranta. Yaran da ke da hazaqa ma, har na xaya su ke

yi a darasin addinin kirista. A wajen koyon sana’a ma,

ana samun matsaloli, musamman idan abin ya haxa da

waxanda ba musulmi ba. Da yawa matasa na qorafi

game da yadda mutanen da ke koya masu aiki ke hana su

yin salla a kan lokaci, ko su tursasa su a kan munanan

al’adunsu, kamar durquso ko kwanciya wajen gaisuwa,

ko a umurce su da sayen giya a lokacin da za a yaye su.

Saboda haka, tilas ne iyaye su sanya ido a kan harkar

ilmin `ya`yansu. Su tabbata sun zavar masu makarantu

ko wuraren koyon sana’a da suka dace. Ta haka ne za a

samu ilmi mai kyau, kuma mai amfani, sannan a gina

al’umma ta qwarai.

13. Wajibi ne iyaye su koya wa `ya`yansu yin salla, da zarar

sun kai shekara bakwai. Kafin wannan lokaci, iyaye su

Page 108: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

108

koya wa `ya`yansu ma’anar kalmar shahada, da

hukunce-hukuncen tsarki da alwalla, da sauran hukunce-

hukuncen da ya kamata yara qanana su sani. Idan `ya`ya

mata ne, za a sanar da su hukunce-hukuncen jinin al’ada

(jinin haila) da zarar sun kusa balaga.179

Haka kuma, an

179

Jinin al’ada shi ne jinin da ke fito wa da kansa daga al’aurar mace

wadda za ta iya xaukar ciki, kuma yana daga manya-manyan alamomin

balaga a haqqin mace. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) ya bayyana wa A’isha (Allah Ya yarda da ita) cewa jinin

al’ada wani abu ne da Allah (Maxaukaki) Ya hukunta shi a kan mata daga cikin `ya`yan Adam [Bukhari]; kuma Abdullah ibn Abbās (Allah

Ya yarda da shi) ya ce, ‘farkon wadda ta fara yin jinin al’ada ita ce Hauwa, bayan an saukar da su daga aljanna’ [Hākim da Ibnul Munzir].

Mafi yawan mata na fara jinin al’ada ne daga shekara goma sha biyu

(12) har zuwa shekara hamsin (50), ko da ya ke waxansu na farawa

kafin su kai shekara goma sha biyu, waxansu kuma na wuce shekara

hamsin kafin su daina. Maganganun da aka ruwaito cewa an iyakance

shekarun jinin al’ada zuwa 55 ko 70 ko 60 ko 50, duk ba su inganta ba, kamar yadda Ad-Dārimi da Ibn Taimiyyah suka bayyana. Amma a mafi

yawan lokaci, `yan mata na fara jinin al’ada ne daga shekara goma sha

biyu, idan suna zaune a cikin qasashe masu zafi, ko kuma shekara

goma sha huxu, idan suna zaune a cikin qasashe masu sanyi. Abdul-Muta’ālī Jabrī, a cikin littafinsa Fiqhul Ukhtil Muslimah fix Xahārah wal Haid, ya bayyana cewa duk macen da ta ga jini ya zubo mata kafin

ta kai shekara tara (9), to, wannan jinin cuta ne, ba jinin haila ba.

Jinin al’ada ba shi da qarancin kwanaki ko mafi yawan kwanaki. A

duk lokacin da mace ta ga jini ya zubo mata, a tsakanin lokacin da ta ke

sa ran jinin al’adarta zai zo, kuma ta fahimci cewa ba jinin cuta ba ne,

tana nan a matsayin mai haila, ko da ya xauki kwanaki da yawan gaske.

Babu wani hadisi ingantacce da ya iyakance kwanakin haila, kamar

yadda Ibnul Munzir da Ibn Taimiyyah da Ibnul Qayyim da Ash-Shaukāni da Sadīq Khān suka tabbatar. Hadisin da ke magana a kan

qarancin lokacin haila kwana uku, kuma mafi tsawancinsa kwana goma

sha biyar, hadisi ne na qarya, a bisa ittifaqin malamai. Haka kuma,

hadisin da ya yi magana a kan kwana shida ko bakwai, yana magana ne

a kan jinin istihadha (jinin cuta) ba jinin al’ada ba.

Jinin al’ada na da launi guda uku, matuqar babu wata illar da ta

cuxanye shi: (1) launin ja (2) launin fatse-fatse (kamar ruwan qwai) (3)

launin qasa-qasa (kamar gurvataccen ruwa). Jinin al’ada na yankewa

Page 109: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

109

ne ta hanyoyi guda biyu: (1) bushewar kafar da jinin ke zubowa, wato,

mace ta sanya wani abu kamar farin qyalle ko audugar mata a cikin

al’aurarta, ta fito da shi ba tare da jini ba (2) fitowar farin ruwa daga

mahaifa.

Mafi yawan mata ba su yin jinin al’ada a lokacin da su ke da juna

biyu. Hasali ma, babbar alamar da ke nuna cewa mace ta xauki ciki, ita

ce, jinin al’adarta ya qi zuwa a lokacin da ya kamata. Idan mace mai

ciki ta ga jini ya zubo mata, ta garzaya asibiti, kasancewar wannan jinin

alama ce ta haxari. Amma kuma, an ce `yan kaxan daga matan da ke da

juna biyu na yin jinin al’ada, ko da ya ke binciken likitoci yana nuna

shakku a kan haka. Ke nan, idan mai ciki ta ga jini ya zubo mata, irin

wanda ta saba yi na al’ada, kuma ta je asibiti, aka tabbatar da cewa ba

vari ne za ta yi ba, sai ta xauke shi a matsayin jinin al’ada.

An haramta wa macen da ke al’ada: (1) sallar farilla da ta nafila (2)

azumin farilla da na nafila (3) saduwa, wato, kwanciyar aure da miji (4)

xawafi a xakin ka’aba, matuqar ba a kai ga larurar da dole sai ta yi

xawafin a haka ba. Idan an kai ga wannan larura, misali, kamar ya

zamanto za ta rasa aikin hajjin wannan shekara idan ba ta yi ba, Ibn

Taimiyyah da waxansu malamai na ganin za ta iya yin qunzugu, ta

gabatar da xawafinta, a cikin jinin al’ada (5) sakin aure, wato, haramun

ne mijinta ya sake ta a lokacin da ta ke cikin jinin al’ada.

An halatta wa matar da ke cikin jinin al’ada: (1) zikirin Allah da karatun Alqur’ani, a bisa fahimtar Abu Hanīfah da Shāfi’ī da Ahmad

ibn Hanbal da Ibn Hazm (2) sujudar tilawa a cikin karatun Alqur’ani,

kasancewar babu wani sahihin dalili da ya hana yin haka (3) xaukar

Alqur’ani, kasancewar babu wani nassi sahihi wanda qarara ya hana ta

xaukar Alqur’ani ko ya hana ta tava shi (4) miji ya kwanta a kan

cinyarta, ya karanta Alqur’ani (5) halartar filin sallar idi, ko da ya ke ba

za ta yi sallar ba (6) shiga masallaci (7) a ci abinci tare da ita (8) yin ma

mijinta hidima (9) kwanciya tare da ita, amma ban da saduwar aure

(10) rungumarta da sumbantarta.

Idan jinin al’ada ya qi tsayawa, har na tsawon lokacin da aka

fahimci ya zamanto na cuta, ko kuma mace ta zamanto tana yin jinin

al’ada fiye da sau biyu a cikin wata xaya, ko kuma jinin ba ya wuce

kwana xaya ko biyu a cikin kowane wata, wannan jini ya zamanto na

istihadha (jinin cuta). Idan tana da sanannen adadin kwanakin haila,

kafin ya fara mata gardama daga baya, za ta yi amfani da kwanakin da ta saba yi a can baya, kamar yadda hadisin Ummu Habībah ya tabbatar.

Idan ba ta tava samun iyakantaccen kwanaki ba tun da ta fara haila,

amma za ta iya bambancewa a tsakanin jinin la’ada, da jinin istihadha,

Page 110: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

110

so iyaye su riqa zuwa da `ya`yansu masallaci, kuma su

koya masu azumi tun suna qanana, don su saba. Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Ku umurci `ya`yanku da yin salla idan sun kai shekara

bakwai; kuma ku buge su a kanta (idan suka qi yi) idan

sun kai shekara goma; kuma ku raba su a wajen

kwanciya (ta yadda kowanne daga cikinsu zai samu

gado/katifa ko kuma mayafi daban).‛180

Kuma Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi sallar jam’i a cikin masallaci yana riqe da Umāmah bint

Zainab181

, kamar yadda ya yi salla tare da al-Hasan ko

al-Husain a hannunsa.182

Bayan wannan, Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Na

kan fara salla da niyyar tsawaitawa a cikinta, amma idan

na ji kukan yaro (a cikin masallaci), sai in gajarta sallar

don (gudun) kada in takura mahaifiyarsa (da ke salla tare

da mu).‛183

Dangane da koya masu azumi, ar-Rabi’ bint Mu’awwidh

(Allah Ya yarda da ita) ta ba da labarin cewa sun kasance suna koya wa qananan yara azumin āshura a zamanin

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi). Har ma su kan tafi da su masallaci tare da kayan

wasa, ta yadda idan sun fara kuka saboda yunwa, sai su

ba su kayan wasa.184

Bugu da qari, hadisi ya tabbata

za ta yi amfani da launin baqi a matsayin haila, launin ja a matsayin

istihadha; ko kuma mara kauri a matsayin haila, shi kuma mai kauri a matsayin istihadha, kamar yadda hadisin Fāximah bint Abi Hubaish ya

nuna. Idan kuwa ba za ta iya bambancewa a tsakaninsu ba, sai ta xauki

kwana shida (6) ko kwana bakwai (7) a matsayin al’adarta, bisa la’akari

da kwanakin da tsararrakinta ke yi. 180

Abu Dāwud: Sahīh 181

Bukhari da Muslim 182

Ahmad da Nasā’i: Sahīh 183

Bukhari 184

Bukhari da Muslim

Page 111: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

111

cewa wata mace ta ce wa Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi), bayan ta xaga wani

yaron da ke hannunta: ‚ya halatta wannan (yaron) ya yi

aikin hajji‛? Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Na’am, kuma ladan (aikin

hajjin da ya yi) naki ne (tunda shi bai balaga ba).‛185

Waxannan hadisai na nuna yadda Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) da sahabbansa

(Allah Ya yarda da su) suka kasance suna ba da

muhimmanci ga tarbiyyar `ya`ya, da koya masu addini

tun suna qanana, ta yadda ba zai yi masu wuya ba idan

sun balaga. Haka kuma, hadisan na nuna halaccin zuwa

da yara masallaci, da shigar da su cikinsa. Ke nan,

maganar da ta shahara cewa ba a zuwa da yara masallaci,

ba ta da inganci. Haka nan ma, xabi’ar korar yara, ko

zaginsu idan sun shiga masallaci, ba ta da kyau. Hadisin

da ke cewa: ‚Ku nisantar da `ya`yanku daga masallaci‛, mai rauni (da’īf) ne.

186

14. Wajibi ne a koya wa `ya`ya kyawawan xabi’u, da

halayen girma da karamci, don su taso da cikakkiyar

tarbiya.187

A sanar da `ya`ya muhimmancin faxin

185

Muslim 186

Duba Da’īf al-Jāmi’ # 2636; da Da’īf Ibn Mājah #164 187

Kyawawan xabi’u ( ) su ne abu mafi nauyaya mizanin

mumini [Abu Dāwud da Tirmidhi]; xaya daga cikin abubuwan da suka

fi shigar da mutane aljanna [Tirmidhi]; kuma suna daga cikin abubuwa

guda huxu waxanda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce idan mutum na da su, kada ya yi baqin ciki a kan duk

wani abin duniya da ya rasa [Ahmad].

Waxanda ke da kyawawan xabi’u su ne mafi cikar imani [Tirmidhi];

mafi alhairi a cikin mutane, kuma daga cikin zavavvu [Bukhari da Muslim]; suna daga cikin mafi soyuwar bayi a wajen Allah [Hākim];

suna kai wa ga darajar mai azumi da rana, kuma ya raya dare [Abu Dāwud]; su ne mafi kusa da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

Page 112: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

112

gaskiya da riqon amana; da cika alqawari; da girmama

manya, da tausayin qanana; da biyayya ga iyaye; da son

`yan’uwa da dangi; da kiyaye haqqin maqwabta, da

girmama baqi; da son `yan’uwa Musulmi, da kare

mutuncinsu; da sauransu. Haka kuma, a sanar da su

haxari, da kuma sakamakon munanan xabi’u.188

Lallai

tabbata a gare shi); kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya lamunce masu wani gida a qololuwar aljanna [Abu Dāwud].

Daga cikin kyawawan xabi’u waxanda ya kamata iyaye su koya wa

`ya`yansu, akwai: taqawa (tsoron Allah, da kiyaye dokokinSa); da

dagewa a kan bauta wa Allah; da juriya; da dauriya; da yafewa da

haquri; da kyauta da ciyarwa; da sadaukantaka; da sauqin kai; da

kyakkyawar mu’amala; da tausayi; da rahama; da soyayya da qiyayya a

kan gaskiya; da adalci; da riqon amana; da faxin gaskiya; da cika

alqawari; da sadar da zumunta; da kyautatawa; da qanqan da kai; da

kunya da kawaici; da gudun duniya (zuhudu); da natsuwa; da tunani

game da halittun Allah (tafakkuri). 188

Munanan xabi’u na hana mutane kai wa ga nasara; suna haifar da

rashin walwala, da rashin aminci da yarda ga waxanda ke da su. Haka

kuma, waxanda ke nuna mummunan hali, na zama abin qyama a cikin

mutane. Munanan xabi’u na da hanyoyi guda uku: (i) zuciya (ii)

harshe; da (iii) gangar jiki.

Ta hanyar zuciya a ke yin munafinci; da hassada; da qiyayya; da

mugunta; da jiji da kai. Ta hanyar halshe a ke faxin magana ba tare da

ilmi ba; da cutar da musulmi ta hanyar cin naman mutane; da shaidar

zur; da qazafi; da qarya; da annamimanci; da vatanci; da izgili; da

tonon asiri; da gori; da batsa; da jayayya a kan varna; da yabon mutane

ba bisa qa’ida ba; da kururuwar mutuwa; da tsinuwa; da waqa. Ta

hanyar gangar jiki a ke taqama; da nuna raini ga mutane; da girman kai;

da nuna isa; da cutarwa ta zahiri; da algushu; da mummunar

zamantakewa.

Munafinci na daga mafi haxarin dukkan munanan xabi’u. Munafinci

ya qunshi bayyanar da savanin abin da aka voye. A shar’ance,

munafinci shi ne bayyanar da Musulunci da voye kafirci da sharri [Baqarah, 2:8-20; Mujādilah, 58:14-19; Nisā, 4:88, 72-73, 136, 142,

145; Aal Imrān, 3:168-169].

Munafinci nau’i biyu ne: munafinci na aqida ko quduri ( )

da munafinci na aiki ( ). Munafincin aqida ya qunshi (i) qaryata

Page 113: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

113

ne iyaye su guji koya wa `ya`ya munanan xabi’u, kamar

zagi, da qarya, da sava alqawari, da yaudara, da ha’inci.

Abin mamaki, da yawa daga cikin iyaye na koya wa

`ya`yansu qarya, ba tare da sun sani ba. Misali, za a aiko

ana sallama da mahaifin yaro a qofar gida; amma sai

mahaifin ya ce wa xansa: ‘je ka ce babanka ba ya nan, ko

yana barci’. Ta haka, ya koya wa xansa qarya, ba tare da

ya sani ba. Ko kuma iyaye su kira `ya`yansu qanana da

sunan za su ba su wani abu, alhali kuwa ba komai a

hannunsu. Wannan ma, koyar da qarya da yaudara ce ga

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) (ii) qaryata

wani abu daga cikin abubuwan da Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya zo da shi (iii) qin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) (iv) qin wani sashe na abin da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zo da shi (v) farin ciki game da qasqanci ko tawaya ko rashin ci gaban

addinin da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zo da shi (vi) qin duk wata nasara da addinin Musulunci zai samu.

Wanda duk ya ke da xaya daga cikin waxannan siffofin munafinci,

ya fita daga cikin Musulunci kuma ya shiga cikin waxanda aka siffanta

su da mafi sharrin siffofi, kamar kafirci, da rashin imani, da izgilanci ga

addini, da karkata gaba xaya zuwa ga maqiyan addini. Nau’in munafinci na biyu ya qunshi (i) qarya a wajen bayar da

labari (ii) ha’inci bayan an amince wa mutum (iii) yaudara idan an yi

yarjejeniya (iv) wuce iyaka a wajen husuma (v) sava alqawari (vi)

kasala wajen bauta (vii) riya (viii) rashin ambaton Allah (ix) gaggawa a

cikin salla (x) zunxen waxanda ke yin ayyukan alhairi (xi) izgilanci ga

Allah da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da Sunnah (xii) rantsuwa a kan qarya (xiii) rashin son ciyarwa saboda

Allah (xiv) watsi da Musulunci (xv) yaxa jita-jita da varna (xvi) aibanta

dokokin Allah (xvii) qasqantar da mutanen kirki (xviii) qin yin sallar

farilla a cikin jam’i (xix) kawo varna, wai da sunan gyara (xx) ba da

uzurin qarya (xxi) umurni da mummuna da yin hani ga kyakkyawa

(xxii) mantawa da Allah (xxiii) qaryata alqawarin Allah ko alqawarin

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) (xxiv) ba

da himma wajen gyara zahiri, amma kuma a yi watsi da baxini (xxv)

rashin fahimtar addini.

Page 114: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

114

`ya`ya. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) ya ce: ‚Wanda ya ce wa yaro: zo ka karva,

sannan, ya qi ba shi komai, to za a rubuta masa

(zunubin) qarya.‛189

Haka kuma, ‘Abdullah ibn ‘Aamir

(Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‚Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya zo gidanmu,

lokacin ina qarami. Sai na kama hanya zan fita don yin

wasa. Sai mahaifiyata ta ce: ‘Abdullah, zo ka karva. Sai

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Me ki ke son ki ba shi?‛ Sai ta ce: dabino.

Sai (Manzon Allah) ya ce: ‚Da ba ki ba shi komai ba, za

a rubuta maki (zunubin) qarya.‛190

Waxansu iyayen na koya wa `ya`yansu darussa dabam

daban na zagi da tsinuwa, ba tare da sun sani ba. Kuci-

kuci kaxan sai su zage su, ko su tsine masu. Wani

lokacin ma, iyayen da ba su da tarbiyya, kan sanya

`ya`yansu qanana su zagi yayyensu, ko su yi masu

daquwa (zagi da hannu). Irin wannan mummunar xabi’a

na da haxari ga yaro, domin kuwa zai qware da zagi fiye

da yadda zai qware da karatun fatiha. A vangaren iyaye

ma, akwai babbar illa, kasancewar duk lokacin da

`ya`yan suka yi zagi (a gida ko a waje), iyayen ne aka

zaga. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce: ‚Lallai yana daga mafi girman zunubi,

mutum ya la’anci mahaifansa. Sai aka ce: Ya Manzon

Allah, ta yaya mutum zai la’anci mahaifansa? Ya ce:

Mutum ya zagi uban wani, shi ma (wancan) ya zagi

ubansa; kuma ya zagi uwar wani, shi ma a zagi tasa

uwar.‛191

189

Ibn Wahab: Sahīh al-Isnād [Duba littafin as-Sahīhah 2/385] 190

Ahmad da Abu Dāwud: Sahīh 191

Bukhari

Page 115: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

115

Ban da wannan, waxansu iyayen na koya wa `ya`yansu

ha’inci da algushu a wajen sana’a. Za ka ga an koya wa

yaro/yarinya tauye mudu ko qara ruwa ko yin amaja a

cikin kayan sayarwa. Waxansu `ya`yan kuma, ana koya

masu husuma, da rashin qimanta juna, da yadda savani

ke aukuwa a tsakanin miji da mata, tun suna qanana.

Domin kuwa, waxansu iyayen su kan yi faxa a

tsakaninsu, wani lokaci ma har da dambe, ko murxe

wuyar riga, ko zage-zage da doke-doke a tsakaninsu, a

gaban `ya`yansu. Haka kuma, waxansu iyayen na koya

wa `ya`yansu nau’o’in savon Allah tun suna qanana.

Misali, sai ka ga mutumin da ke shan taba sigari192

ko

192

A zamanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) da sahabbansa (Allah Ya yarda da su) da waxanda suka biyo bayansu daga cikin tabi’ai da tabi’ut-tābi’īn, babu taba sigari irin wadda

a ke gani a yau. Saboda haka, ba a samu wani bayani ko hukunci qarara

daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ko

sahabbansa (Allah Ya yarda da su) da sauran malaman farko dangane

da ita ba. Wannan ya sa, a lokacin da taba sigari ta bayyana, malamai

sun yi qiyasin hukuncinta daga hukuncin albasa da tafarnuwa, waxanda

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya hana

duk wanda ya ci su, zuwa masallaci, saboda cutuwar da sauran mutane

da mala’iku (waxanda ke cikin masallacin) za su yi daga warin

bakinsu. Suka ba da fatawar cewa taba sigari makaruhi ne, wato, abin

qi, gwargwadon abin da suka fahimta game da ita, a wancan lokaci. Ke

nan, a wancan lokaci, malamai sun dubi hukuncin taba sigari ne daga

vangaren cutarwar da ta ke yi ga mutanen da ke kusa da mai shan

sigari, ba wai illarta ga wanda ke sha ba. Amma daga baya, binciken

likitanci ya tabbatar da cewa taba sigari na da illoli, da haxari ta fuskar

wanda ke sha, da dukiyarsa, da sauran jama’a. Nan take, malamai suka

tabbatar da haramcinta.

A taqaice, shan taba sigari haramun ne, ba makaruhi ba. Shan sigari

ya qunshi almubazzarancin dukiya, da sakarci wajen kashe kuxi, da

cutar da lafiya, da cutar da sauran mutane waxanda za su ji warinta a lokacin da a ke zuqa ko busa ta. Alqur’ani da Hadisi da Ijmā’i duk sun

nuna haramcin waxannan abubuwa gaba xaya. Haka nan ma, sayar da

taba ko sayo ta, duk haramun ne, domin kuwa yin hakan, ya qunshi

taimakawa a cikin savon Allah.

Page 116: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

116

giya, ya tura xansa ya sayo masa, ko ya sanya shi ya

xauko masa daga wani wuri, don ya sha. Yaro zai taso a

haka, kuma ya riqa zaton cewa waxannan abubuwa babu

laifi a aikata su.

15. Lallai ne iyaye su koya wa `ya`yansu ladubban da suka

shafi cin abinci ko shan wani abu, da yin sallama, da

shiga cikin gida ko cikin xaki, da magana, da zama a

cikin jama’a, da atishawa, da hamma, da sanya takalmi,

da kwanciya da tashi daga barci, da shiga cikin

masallaci, da shiga ban xaki, da sauransu. Waxannan

ladubba na da matuqar muhimmanci. Ya kamata iyaye

su sansu, kuma su ilmantar da `ya`yansu. Su koya masu

wanke hannu, da faxin ‘Bismillah’, da amfani da hannun

dama a lokacin cin abinci ko shan wani abu. Idan sun

kammala kuma, su ce ‘Alhamdu Lillah’, daga nan su

wanke hannu. A umurce su da yin sallama kafin su shiga

gida ko xaki, da neman izni idan za su shiga xakin

iyayensu kafin sallar asuba, da tsakiyar rana da bayan

sallar isha’i. Su koya masu rufe baki da hannun dama

idan sun yi hamma, da rufe hanci da hannun hagu tare da

faxin ‘Alhamdu Lillah’ idan sun yi itishawa. A koya

masu shiga masallaci da qafar dama, da fita da qafar

Abin mamaki shi ne, har yanzu waxansu mutane ba su yin la’akari,

kuma ba su lura da haxarin taba sigari. Su kan yi biris da kiraye-

kirayen da malaman addini, da kuma likitoci ke masu, dangane da

illolin sigari. A nan qasar misali, duk lokacin da aka yi tallar taba a

rediyo ko talabijin, za a bayyana wa mutane cewa ‘ma’aikatar lafiya ta

tarayya na faxakar da mutane cewa shan taba sigari na da haxari ga

rayuwa, kuma yana gaggautar da mutuwar mutum.

Tare da wannan bayani, daga cikin ribar dimokaraxiya a Nijeriya,

akwai gayyato kamfanin tabar sigari mai suna British-AmericanTobacco Company (BATC) da gwabnati ta yi, don su ci

karensu ba babbaka. Abin da waxansu ba su sani ba, shi ne, kamfanin

BATC yana daga kamfanonin da aka koro daga Turai, saboda musiba

da bala’in da ya ke yaxawa a cikin jama’a.

Page 117: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

117

hagu. Haka kuma, a koya masu shiga ban xaki da qafar

hagu, da fita da qafar dama. Sannan, a koya wa `ya`ya

addu’o’in da a ke yi idan za a shiga masallaci ko za a

fita, da addu’o’in kwanciya da tashi daga barci, da

waxanda a ke yi a lokacin shiga ban xaki ko fitowa, da

addu’ar fita gida, da wadda a ke yi idan za a shiga gida.

Bayan wannan, a umurci yara su gabatar da dama wajen

sanya takalmi da riga da wando. Kuma a hana su yin

tafiya da takalmi qafa xaya, kasancewar xabi’a ce ta

shaixan.193

Bugu da qari, a koya masu yanke qumba da

gyara gashin kai, da nisantar wuraren qazanta, da

qoqarin kawar da abubuwan da ke cutarwa a kan hanya.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya kasance yana koya wa qananan yara ladubban

addini. Misali, lokacin da Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ga hannun ‘Umar

ibn Abi Salamah (Allah Ya yarda da shi) yana kai-kawo

a cikin akushi, ya ce masa: ‚Ya kai yaro! Ambaci sunan

Allah (ka ce: ‘Bismillah’ idan za ka fara cin abinci),

kuma ka ci da (hannun) dama, kuma ka ci (abin da ke) gabanka.‛

194 Haka kuma, lokacin da ‘Abdur-Rahmān ibn

Sahl da Huwaisah da Muhaisah `ya`yan Mas’ūd (Allah

Ya yarda da su) suka zo wajen Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ‘Abdur-Rahmān

(wanda shi ne qaraminsu) ya yi nufin ya fara magana, sai

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Ka bar babba daga cikinku ya fara

magana.‛195

Kuma ya ce: ‚Na ganni a cikin barci

(mafarki) ina asuwaki, sai waxansu mutane biyu - xaya

daga cikinsu ya girmi xayan - suka zo wuri na. Sai na

miqa wa qaramin cikinsu asuwaki. Sai aka ce mani: ‘fara 193

Bukhari 194

Bukhari 195

Bukhari da Muslim

Page 118: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

118

da babba’. Sai na miqa wa babban na su.‛196

Ke nan, ana

la’akari da fifikon shekaru idan falala da daraja cikin

ilmi da jagoranci suka zama iri xaya, kamar yadda Ibn Hajar ya tabbatar a cikin Fat-hul Bārī. Dangane da

sallama, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ya kasance yana yin sallama ga

qananan yara, kuma idan sun yi masa sallama, yana

amsawa, kamar yadda hadisai suka nuna.197

Yin haka,

zai sa yara su san muhimmancin sallama, da kuma

ladubban da ke tattare da ita.198

Dangane da neman izni

kafin shiga xaki a lokuta uku, waxanda Alqur’ani ya

bayyana199

, ‘Abdullah ibn ‘Umar da ‘Abdullah ibn

Suwaid (Allah Ya yarda da su) sun kasance suna hana

`ya`yansu shiga xakunansu a waxannan lokuta, ba tare

da izni ba.200

16. Iyaye su koya wa `ya`yansu ladubban amfani da dama da

hagu, da wuraren da a ke amfani da kowannensu, ko

kuma a ke gabatar da xaya kafin xayan. Bayani ya

gabata cewa ana amfani da hannun dama wajen cin

abinci ko shan wani abu. Haka kuma, ana fara amfani da

dama wajen shiga masallaci, da fita daga ban xaki, da

sanya takalmi, da sanya tufafi; kamar yadda a ke gabatar

196

Muslim 197

Bukhari da Muslim 198

Ba a yin sallama ga wanda ba musulmi ba, kamar yadda hadisai

ingantattu suka nuna. Idan kuwa su ne suka fara yin sallama ga

musulmi, shin zai amsa ko ba zai amsa ba? Idan zai amsa, wace siga zai

yi amfani da ita wajen amsawa? Magana mafi qarfi ita ce, zai amsa

sallamar yahudawa da kirista; kuma zai amsa masu da lafazin da ya

dace, matuqar sun yi amfani da sahihan kalmomi wajen yin sallamar,

kuma bisa yadda Shari’ah ta tabbatar da lafazin. Duba littafin Ibnul Qayyim, Ahkāmu Ahliz Zimmah, shafi na 149 don qarin bayani. 199

Nūr, 24:58 200

Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī, Sahīh al-Adabil Mufrad #803 da

808

Page 119: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

119

da hagu wajen fita daga masallaci, da shiga ban xaki.

Bayan waxannan, an so a yi amfani da dama cikin duk

wani abu mai kyau da tsafta, kamar sanya zobe ko

agogo, da kwanciya, da miqa wani abu ko karvar wani

abu. A wajen abubuwan qazanta kuwa, kamar wanke

bayan gida (kashi) ko fitsari, an so a yi amfani da hannun

hagu. Idan za a yi aski ko yanke qumba ko gyara suma

(gashin kai) ko wankan tsarki, an so a fara da vangaren

dama kafin hagu.

Hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) yana gabatar da dama wajen

cin abinci, da shan abin sha, da alwalla, da sanya tufafi,

da miqawa, da karva. Yana amfani da hagu cikin sauran

abubuwa.201

Haka kuma, Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Idan xayanku zai ci

abinci, to ya ci da (hannunsa na) dama, kuma ya sha da

dama, kuma ya karva da dama, kuma ya miqa da dama;

domin shaixan na ci ne da hagu, kuma yana sha da hagu,

kuma yana ba da wa da hagu.‛202

Dangane da tsarki,

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Idan xayanku zai yi fitsari, kada ya riqe

zakarin shi da (hannun) dama. Kuma idan ya shiga ban

xaki, kada ya yi amfani da (hannun) dama wajen

tsarki.‛203

A wata ruwayar: ‚Idan xayanku zai yi tsarki,

kada ya yi amfani da (hannun) dama; ya yi amfani da

(hannun) hagu wajen tsarkinsa.‛204

Dangane da sanya

201

Ahmad: Sahīh [Duba littafin Muhammad Jamīl Zainū, Quxūf min as-Shamā’il al-Muhammadiyyah, shafi na 88; da Sahīh al-Jāmi’ ,

#4912 na Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī] 202

Ibn Mājah da al-Hasan ibn Sufyān: Sahīh [Duba Sahīh al-Jāmi’ #384; da as-Sahīhah #1236] 203

Ahmad, Bukhari, Muslim, Abu Dāwud da Tirmidhi [Duba Sahīh al-Jāmi’ #410] 204

Baihaqī, Ahmad da Abu Dāwud: Sahīh [Duba Sahīh al-Jāmi’ #322]

Page 120: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

120

takalmi, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) ya ce: ‚Idan xayanku zai sanya takalmi, ya

fara da (qafar) dama; kuma idan zai cire, to ya fara da

(qafar) hagu: qafar dama ta zamanto ita ce farko wajen

sanyawa, amma ta zamanto a qarshe wajen cirewa.‛205

A

cikin wani hadisin, Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Ka cire (takalmanka)

gaba xaya, ko ka sanya su gaba xaya; kuma idan za ka

sanya, ka fara da dama; idan kuma za ka cire, ka fara da

hagu.‛206

Dangane da kwanciya, Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚… sannan ka

kwanta a tsagin jikinka na dama…‛207

Dangane da

wanka, da gyaran suma (gashin kai), hadisi ya tabbata

cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) yana sha’awar farawa da (vangaren) dama

wajen sanya takalmi, da gyara sumarsa, da wanka.‛208

Dangane da alwala, Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Idan za ku sanya

tufafi ko za ku yi alwala, ku fara da (vangaren) dama.‛209

Dangane da shan ruwa, Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya hana shan ruwa a tsaye.210

17. Lallai ne iyaye su ilmantar da `ya`yansu game da

haqqoqin zamantakewa, musamman haqqoqin iyaye, da

`yan’uwa, da shugabanni, da maqwabta, da sauran

musulmi. Kafin wannan, wajibi ne iyaye su sanar da

`ya`yansu haqqoqin Allah (Mai girma da xaukaka) da

haqqoqin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

205

Ahmad, Muslim, Abu Dāwud da Tirmidhi 206

Ibn Hibbān: Sahīh 207

Bukhari da Muslim 208

Bukhari da Muslim 209

Abu Dāwud da Ibn Hibbān: Sahīh [Duba Sahīh al-Jāmi’ #787] 210

Bukhari

Page 121: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

121

tabbata a gare shi), kasancewar su ne mafi girman

haqqoqi a kan kowane mutum.

Haqqoqin Allah (Mai tsarki da xaukaka) a kan bayinSa

guda bakwai (7) ne: (1) imani da Shi a vangaren

rububiyyah da uluhiyyah da sunayenSa mafi kyawu da

siffofinSa mafi xaukaka211

(2) tsarkake bauta gare Shi

(3) bin umurninSa da barin haninSa (4) girmama Shi da

tsarkake Shi daga dukkan aibobi da tawaya, da girmama

umurni da haninSa, da tsayuwa a inda Ya iyakance (5)

bauta Masa a bisa asasin soyayya da tsoron azabarSa da

kwaxayin rahamarSa (6) gode maSa bisa ni’imominSa,

ta hanyar yarda da qudurce cewa dukkan ni’ima daga

gare Shi ta ke, kuma da bayyanar da ni’imar a fili, tare

da yabonSa a kanta, da sarrafa ni’imar, tare da juyar da

ita zuwa ga abin da Ya ke so (7) sallama wa qaddararSa

da yarda da duk abin da Ya hukunta.

Haqqoqin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) a kan al’ummarsa guda bakwai (7) ne:

(1) gasgata shi a cikin abin da ya ba da labari, da bin

umurni da haninsa, da imanin cewa shiriyarsa da Shari’ar

da ya zo da ita su ne mafi cika da dacewa (2) gabatar da

shi da fifita shi a kan kowa (3) mai da shi abin koyi (4)

ladabi a gare shi, da ladabi ga Sunnarsa (5) kare

martabarsa, da kiyaye matsayi da mutuncin sahabbansa

da matansa da sauran iyalan gidansa (6) kare Sunnarsa

da yaxa ta (7) yawaita salati a gare shi.212

211

Karanta littafina, The Most Beautiful Names of Allāh from the Qur’ān and Authentic Sunnah, domin qarin bayani game da sunayen

Allah. 212

Allah (Maxaukaki) Ya bayyana cewa Shi da mala’ikunSa suna yin

salati ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), kuma Ya umurci muminai da yin salati a gare shi [Ahzāb, 33:56].

Sahabbai (Allah Ya yarda da su) sun tambayi Manzon Allah (tsira da

Page 122: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

122

amincin Allah su tabbata a gare shi) game da yadda za su yi masa

salatin da Allah (Mai girma da xaukaka) Ya umurci muminai su yi.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce, ‘Ku

ce:

Wannan yana nuna cewa babu wani salatin Annabi (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) da ya kai inganci, da matsayi, da falala, da

darajar wannan nau’in da ya karantar da sahabbansa (Allah Ya yarda da

su). Hadisai ingantattu sun tabbatar da sigogi guda bakwai na wannan

salati. Ana iya karanta kowace siga daga cikinsu a sallar farilla ko ta

nafila. Sigogin da suka tabbata daga bakin Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) kai tsaye su ne:

Idan kuwa ba a cikin salla ba ne, waxansu malamai sun ba da

fatawar halaccin karanta kowane irin salati ga Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi), matuqar yana da lafazi mai daxi,

da ma’ana mai kyau, kuma ba a fifita shi, ko aka daidaita shi da

waxanda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ya karantar da kansa ba. Sun dogara da sigogin salati da aka ruwaito

Page 123: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

123

cewa Ibn Mas’ud da Aliyyu ibn Abi Xālib da waxansu daga cikin

tabi’ai da atbā’ut tābi’īn suna yi, maimakon waxannan sigogi da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

karantar.

Salati ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) na da falala da fa’idodi masu yawan gaske. Ibnul Qayyim, a cikin Jilā’ul Afhām fis Salāti Wassalāmi ‘ala Khairil Anām, (Al-Maktabatut

Taufīqiyyah, Egypt), shafi na 284-291, ya bayyana fa’idodi da falalar

salati har guda arba’in (40). Daga cikinsu, akwai: (1) biyayya ga

umurnin Allah (2) yin muwafaqa da Allah a cikin salati, duk da cewa

salatin Allah yana da bambanci da salatin mutane (3) yin muwafaqa da

mala’iku a cikin salati (4) dacewa da lada guda goma (5) samun

xaukakar daraja sau goma (6) dacewa da saryarwar laifuffuka guda

goma (7) qaunar amsa addu’ar da aka fara gabatar da godiya da yabo

ga Allah, da salati ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata

a gare shi) (8) dalilin samun ceto a ranar qiyama (9) dalilin samun

kusanci ga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

a ranar qiyama (10) kuvuta daga kaucewa hanyar aljanna (11) dacewa

da mai da gaisuwa daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) (12) kuvuta daga wari da xoyi (13) kuvuta daga

addu’ar turmuje hanci da nisantarwa daga rahama (14) kuvuta daga

hasara da nadama (15) dalili ne na korewar baqin ciki da damuwa da

tsanani (16) dalili ne na dawwamar soyayyar Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) (17) hanya ce ta sauke mafi

qaranci daga cikin haqqoqin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) a kan mabiyansa.

Akwai lokuta da wuraren da aka wajabta yin salati ga Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), kuma akwai wurare da

lokutan da yin salati mustahabbi ne. Wuraren da aka fi son a yi salati ga

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), a matsayin

wajibi ko mustahabbi sun haxa da: (1) bayan tahiyar qarshe a cikin

sallolin farilla ko sallar nafila (2) bayan tahiyar farko (3) a cikin sallar

jana’iza bayan kabbara ta biyu (4) a cikin huxubar Juma’a ko Idi ko

roqon ruwa (5) bayan kwaikwayon mai kiran salla (6) a wajen addu’a

(7) lokacin shiga masallaci da lokacin fitowa daga cikinsa (8) lokacin

da mutane suka zo tashi daga wani majalisin da suka zauna (9) a duk

lokacin da aka ambace shi (10) ranar Juma’a (11) lokacin baqin ciki da

damuwa da tsanani.

Page 124: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

124

Haqqoqin iyaye a kan `ya`yansu guda shida (6) ne: (1)

kyautata masu, da yin masu xa’a a cikin abin da bai sava

wa Shari’ah ba (2) tausasa magana da yin tawali’u a gare

su, da saurarensu a lokacin da su ke yin magana, da

rashin qosawa ko nuna gajiya ga maganarsu, da rashin

xaukaka murya a kan ta su (3) yin addu’a a gare su,

musamman bayan mutuwarsu, da rashin jawo dalilin

tsinuwa a gare su (4) sadar da makusantarsu da

abokansu, musamman bayan rasuwarsu (5) rashin

kiransu da sunayensu, ko zaunawa a wuri kafin su zauna

ko yin tafiya a gabansu (6) ilmantar da su, da yin masu

nasiha, a bisa fuska mafi dacewa.

`Yan’uwa da maqwabta na da haqqoqin da Shari’a ta ba

su. Haqqoqin `yan’uwa makusanta da `yan’uwa na nesa

guda biyu (2) ne: (1) sadar da zumunci, da rashin yanke

zumuntarsu (2) fifita su a kan sauran mutane wajen

kyauta da sadaka da zakka da jawo amfani.

Maqwabci na da haqqoqi guda uku (3) a kan

maqwabcinsa: (1) rashin cutar da shi (ta hanyar magana

ko aiki), ko cin mutuncinsa, ko vata wani abu da ya

mallaka (2) girmama shi, gwargwadon yadda Shari’a ta

ce (3) kyautatawa a gare shi. Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya bayyana cewa

mutumin da maqwabcinsa bai amintu daga sharrinsa ba,

bai da cikakken imani.

Shugabanni na da haqqoqi a kan waxanda su ke yi wa

shugabanci, kamar yadda a ke da haqqoqi a kansu.

Haqqoqin shugabanni guda shida ne a kan jama’arsu: (1)

kyautata wakilci gare su a duk lokacin da suka sanya

wakili (2) yin addu’ar shiriya da kyakkyawar jagoranci

gare su (3) tausasawa gare su a cikin magana da

mu’amala (4) yin masu xa’a cikin abin da bai sava wa

Page 125: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

125

Shari’a ba (5) taimakonsu wajen sauke nauyin da aka

xora masu (6) yin haquri a kan cutarwar da za ta zo ta

hanyarsu.

Waxanda a ke yi wa shugabanci na da haqqoqi guda

biyar: (1) kiyaye masu larurori guda biyar ( ),

wato, addini, da rayuwa, da dukiya, da mutunci, da

hankali (2) yin masu adalci (3) tausasawa gare su da

qoqarin jawo masu amfani da tunkuxe cuta gare su (4)

rashin ha’intarsu da yaudararsu da satar dukiyarsu ko yin

almubazzaranci da ita (5) rashin shamakancewa daga

gare su (6) neman shawara daga zavavvun cikinsu kafin

a zartar da hukunci a kan muhimman abubuwan da suka

shafe su

Kowane musulmi na da haqqoqi guda goma sha uku

(13) a kan xan’uwansa musulmi: (1) yin masa sallama

idan sun haxu (2) amsa gayyatarsa, matuqar babu larurar

da za ta hana, kuma babu savon Allah a wurin (3) yin

masa nasiha, da basa shawara mai kyau idan ya nema (4)

faxin yarhamukallah idan ya ce Alhamdu Lillah bayan

ya yi atishawa (5) gaishe shi idan ya yi rashin lafiya (6)

halartar jana’izarsa idan ya mutu (7) kuvutar da shi a kan

rantsuwar da ya yi (8) rashin yin hijira daga gare shi (9)

tsare harshe da idanu daga cutar da shi (10) mutunta shi

da rashin cutar da shi, ta hanyar magana ko aiki (11)

taimakonsa ta kowace hanyar da ta dace, gwargwadon

iko (12) yin masa da’awa.

Karantar da `ya`ya waxannan haqqoqi, da nuna masu

wajibcin kiyaye su yadda ya kamata, za su taimaka

wajen tarbiyyar da ta shafi zamantakewa. Idan `ya`ya

suka taso a kan wannan turba, babu shakka, za a samu

zaman lafiya, da walwala, da kwanciyar hankali, da

martaba juna a cikin al’umma. Haka kuma, ana sa ran

Page 126: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

126

irin waxannan `ya`ya za su zamanto masu son

`yan’uwansu Musulmi, da nuna qauna da haxin kai, da

tabbatar da `yan’uwantakar Musulunci,213

da nisantar

213

`Yan’uwantaka ita ce mafi girma daga cikin ginshiqan da Musulunci

ya dogara kansu wajen gina al’umma. Lokacin da Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya samar da al’ummar farko a

Madina, ya mai da `yan’uwantaka a matsayin ginshiqi na biyu, bayan

tabbatar da kaxaituwar manufa ta hanyar gina masallacin Quba.

`Yan’uwantaka wata irin alaqa ce da ke tsaye a bisa asasin imani da

Allah (Maxaukaki), domin kuwa imani ne ya haxa tsakanin muminai.

Musulunci ya girmama `yan’uwantaka, kuma ya qarfafata, sannan ya

tabbatar da kyakkyawar sakamako a nan duniya da can lahira ga

waxanda suka tabbatar da ita.

Allah (Maxaukaki) Ya ba da labarin aukuwar `yan’uwantaka a tsakanin muminai [Hujurāt, 49:10]; Ya sanya `yan’uwantaka a

matsayin ni’imar da Ya ke yi wa bayinSa gori a kanta [Aal Imrān,

3:103]; Ya sanya ta a matsayin dalilin da zai sa Allah (Maxaukaki) Ya so bawansa [Muslim; Mālik da Ahmad]; Ya sanya ta a matsayin igiyar

imani mafi qarfi [Bazzār]; Ya sanya matsayin masoyi iri xaya da na

wanda a ke so [Muslim]; Ya tabbatar da lada mai yawan gaske ga

waxanda suka tabbatar da `yan’uwantakar Musulunci a tsakaninsu

[Muslim]; Ya sanya ta a matsayin dalilin samun lagwadar imani

[Bukhari da Muslim] da kai wa ga kammalallen imani [Abu Dawud]

wanda ke kai mutum ga shiga aljanna [Muslim da Abu Dawud da

Tirmidhi], da samun matsayin da ya fi wanda mutum ya cancanta

[Bukhari da Muslim].

`Yan’uwantaka na da sharuxxa guda huxu: (1) ta kasance saboda

Allah (2) gwama ta da imani da taqawa (3) lazimtar manhaji da tsarin

Musulunci wajen tabbatar da ita (4) gina ta a bisa asasin nasiha ga

Allah da bayinSa.

Musulmi za su iya tabbatar da `yan’uwantaka a tsakaninsu, kuma su

qarfafeta ta waxannan hanyoyi: (1) idan mutum yana son wani, ya

sanar da shi; (2) idan zai yi balaguro, a nemi ya yi wa `yan’uwansa

Musulmi addu’a, a kan hanya (3) idan ya haxu da xan’uwansa

Musulmi a wani wuri, ya sakar masa fuska; (4) idan ya haxu da

Musulmi, ya yi gaggawar yin masu sallama, da yin musafaha da su; (5)

yawaita ziyara lokaci zuwa lokaci; (6) taya murna a lokacin farin ciki,

da yin jaje a lokacin baqin ciki; (7) taimakekeniya, musamman a

lokacin tsananin buqata; (8) kiyaye wa juna haqqoqin `yan’uwantaka.

Page 127: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

127

yawan savani.214

Haka kuma, ana fatan cewa `ya`yan da

suka taso a kan irin wannan tarbiyya za su zamanto masu 214

Savani shi ne rashin daidaituwa a kan al’amarin addini, da ya ke da alaqa da asalin addini (usūluddīn) ko reshe (furu’ah). Idan savanin yana

da alaqa da asalin addini ne, wato, kamar mas’alolin tauhidi da aqida,

ana kiransa , kuma shi ne mafi sharrin nau’o’in savani. Idan kuwa

yana da alaqa ce da furu’a, wato, kamar mas’alolin fiqihu, ana kiransa

ko ko .

Savani a tsakanin Musulmi wani abu ne da aka qaddara, kuma dole

ne ya auku. Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ce: ‚Kuma da

Ubangijinka Ya so, da Ya sanya mutane al’umma xaya. Kuma ba za su

gushe ba suna masu sava wa juna. Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa

rahama, kuma domin wannan ne Ya halicce su…‛ [Hud, 11:118-119].

Kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

bayyana cewa ya roqi Allah (Maxaukaki) kada Ya sanya savani a

tsakanin al’ummarsa, amma Allah bai amsa ba [Muslim]. Haka kuma,

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tabbatar

da cewa al’ummarsa za ta kasu gida saba’in da uku (73), kashi saba’in

da biyu (72) daga cikinsu `yan wuta ne [Abu Dawud da Ahmad].

Duk da cewa aukuwar savani dole ne a cikin wannan al’umma, an

nemi musulmi da yin riqo da sabubban da za su kawo qarshen duk

wani irin savani a tsakaninsu, domin su zamanto al’umma guda xaya,

wadda za ta yi gwagwarmayar tabbatar da dokokin Allah da tsare-tsarenSa a doron qasa [Anbiyā, 21:92]. Wannan ya sa Allah

(Maxaukaki) Ya umurce mu da haxin kai, da yin riqo da igiyarSa, kuma Ya hana mu rarraba, wadda savani ke haifarwa [Aal Imrān,

3:103]. Ya bayyana mana cewa jayayya da savani na haifar da rauni da rashin qarfi a gare mu [Anfāl, 8:46]. Ya tsawatar da mu daga bin

hanyar waxanda suka rarraba, suka yi savani a tsakaninsu [Aal Imrān,

3:105], kasancewar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ba shi a kan irin wannan hanya [An’ām, 6:159], domin kuwa

son rarraba, da kuma son yin savani na daga cikin xabi’un mushrikai [Rūm, 30:31-32]. Haka kuma, Allah (Mai girma da xaukaka) Ya

shar’anta mana bin addini sahihi, wanda aka yi wa Annabawa da Manzanni wasiyya da shi [Shūrā, 42:13].

Savani ya kasu gida biyu: abin zargi ( ) da wanda babu zargi (

). Savanin da a ke yin zargi a kansa na da fuskoki guda huxu:

1. Savani a cikin mas’alolin aqida waxanda aka yi ittifaqi a kansu a

tsakanin ahlus-sunnah wal jamā’ah ( ). Idan kuwa

Page 128: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

128

mas’alolin da ba a yi ittifaqi a kansu ba ne, saboda rashin hujjoji

qaxa’i, babu zargi a kansu, matuqar ba an karkata ga son zuciya ba.

Irin wannan nau’in, kamar yadda Ibn Taimiyyah ya bayyana a cikin littafin Majmū’ul Fatāwā, ya haxa da (i) zai yiwu mamaci ya ji

muryar waxanda ke raye? (ii) shin ana azabtar da mamaci a cikin

qabarinsa saboda kuka ko kururuwar iyalansa a dalilin mutuwarsa?

(iii) shin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ga Ubangijinsa kafin ya bar duniya? Kasancewar babu

ittifaqin magabata a kan waxannan mas’aloli, savani a cikinsu ba

ya jawo zargi ko inkari a tsakanin Musulmi, matuqar ba a gina

savanin a kan son zuciya ba. Amma babu laifi mutum ya yi qoqarin

gamsar da abokin savaninsa game da fahimtar da ta fi qarfi, da

fatawar da ta fi rinjaye a tsakanin malamai, gwargwadon binciken

da ya yi, da kuma hujjojin da ya dogara da su. Yin bayanin hujjoji,

da kuma rinjayar da fahimtar da ta fi qarfi, ba xaya ya ke da yin

inkari ba.

2. Savani a cikin mas’alolin da suka tabbata bisa dalilan da babu

kace-nace a kansu, kamar rukunan musulunci, da haddin sata, da

wajibcin sanya hijabi ga mata, da haramcin shan giya.

3. Duk wani savani da ke aukuwa a dalilin alfahari da qabila ko

qungiya ko mazhaba, da son zuciya.

4. Sava wa abin da al’umma ta yi ijma’i a kan shi.

Savanin da babu zargi a kan shi yana da alaqa ce da mas’alolin

furu’a, kuma ya kasu gida biyu:

1. Savanin da ke zuwa a dalilin nassosin da ba su yi karo da juna ba,

amma sun qunshi siffofi ko adadi ko lokaci dabam daban. Irin

wannan savanin a cikin nassosi ana kiran shi savanin nau’o’i (

). Misalinsa ya haxa da: siffar yadda a ke kiran salla da iqama;

da sigogin tahiyya da sallamewa daga salla da salatin Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi); da sigogin

addu’ar da a ke yi kafin a fara karatun salla bayan an yi kabbarar

harma; da nau’o’in azkarun da a ke yi a cikin ruku’u da sujuda; da

adadin tasbihi da a ke yi bayan sallar farilla; da siffofin sallar tsoro;

da adadin kabbarbarin da a ke yi a sallar jana’iza; da siffar yadda a

ke yin ishara da yatsa a wajen tahiya.

2. Savanin da ke zuwa a cikin nassosin da suka yi karo da juna, kuma

babu yadda za a yi a haxa su gaba xaya. Irin wannan savanin ana

kiran shi savanin da ke kishiyantar juna ( ). Misalinsa ya

Page 129: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

129

haxa da: wajen da a ke yin ibadar i’itikafi; da hukuncin yin azumin

nafila a ranar Asabar; da hukuncin yin azumin arfa ko azumin

ashura idan ya kasance ranar Juma’a ko Asabar.

Savani irin wannan ba a yin zargi a kansa, matuqar ba a gina shi a

kan son zuciya ko yin yadda aka so ba. Hasali ma, irin wannan savani,

yana nuna yalwar addini ne idan ya shafi , ko kuma rashin

dalilin da a ke kira , domin kuwa sahabban Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sun yi savani a kan irin

waxannan mas’aloli na furu’a, saboda bambancin fahimta, da rashin

yiwuwar kiyaye dukkan maganganu da ayyukan Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) a xaixaikunsu, ko kuma saboda

bambancin ijtihadi a wajen da babu nassi qarara. Duk da cewa ba a yin

zargi a cikin irin wannan savani, hakan ba ya nuna cewa ba za a yi wa

juna nasiha a kan abin da ya fi dacewa ba. Ya kamata a yi nasiha, tare

da faxakarwa ga juna a kan fahimtar da ta fi qarfi, da kuma fatawar da

ta fi rinjaye. Haka kuma, za a iya xaukar hujjojin wanda aka yi savani

da shi a kan mas’alar, don a bayyana rauninsu, ko rashin dacewarsu.

Abin da Shari’a ta hana shi ne aibanta juna ko cin mutuncin juna a

dalilin irin wannan savani.

Dalilan da ke kawo savanin da ba a yarda da shi ba, wato, ,

musamman a cikin mas’alolin aqida, sun haxa da:

1. Makircin abokan gaba, kamar yadda Yahudawa irinsu

Abdullah ibn Saba’in suka haifar da qiyayya da gaba a tsakanin

musulmi, tun daga lokacin da aka samu savani a tsakanin Aliyyu ibn Abi Xālib da Mu’āwiyyah (Allah Ya yarda da su).

2. Jahiltar addinin musulunci, da qa’idodinsa, da usūl xin da a ke

bi wajen tabbatar da hukunce-hukunce.

3. Varaka a cikin hanyar da a ke bi wajen fahimtar addini (

), musamman idan aka nemi fahimtar Alqur’ani ko Sunnah

a bisa savanin yadda sahabbai da tabi’ai da sauran magabata na

qwarai suka fahimta.

4. Tsanantawa, da zurfafawa, da son wuce gona da iri a cikin

addini.

5. Bidi’a, da qage a cikin sahihiyar aqida, kamar yadda aka samu khawārij da murji’ah da mu’utazilah sun qago sababbin

abubuwa, kuma sun sava wa fahimtar sahabban Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).

Page 130: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

130

6. Tasirantuwar da waxansu musulmi suka yi ga tunani da kuma

falsafar da ke gangarowa daga qasashen kafirai, da kuma

mummunar farfagandar maqiyan Musulunci.

7. Barin da’awa, da kuma yin sakaci a kan neman ilmin addini.

Shi kuwa , wato, savanin furu’ah, dalilan da ke kawo shi sun

haxa da: kasancewar xan Adam mai kuskure ne tun asali, don haka

babu mamaki idan ya sava wa waninsa bisa kuskure; da zalunci, da

qiyayya, da qin gaskiyar da ke kai mutane ga yin jayayya da qin karvar

gaskiya; da hassada, da girman kai; da ta’assubanci ga waxansu mutane

ko qungiya; da vacin tunani, da raunin tasawwuri; da lazimta wa

mutane abin da ba ya lazimtuwa, domin a cinma wata manufa; da son

yin savani domin a samu shahara; da bin son rai, da qoqarin biye wa

zuciya; da qarancin bincike a cikin littafan magabata; da qarancin

fahimtar , wato, hukunce-hukuncen savani, da yadda a ke yin

mu’amala da abokin savani; da kuma bidi’a a cikin addini, da nacewa

wajen qoqarin kare ta, da tallata ta, tare da qoqarin ciyar da ita gaba.

Alqur’ani da Sunnah sun karantar da ladubban da suka dace a

kiyaye a kan waxanda suka yi savani. Ladubban sun haxa da:

1. Ikhlasi, da koyi da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) da sahabbansa wajen mu’amala da wanda

aka yi savani da shi ( ).

2. Fatar shiriya, da dawo wa hanyar qwarai ga wanda ya sava wa

gaskiya.

3. Sauraron hujjar wanda aka yi savani da shi, da kuma ba shi

damar kawo fahimtarsa a kan mas’alar.

4. Ba da dalili da hujja a kan mas’alar da aka yi savani game da

ita, ba wai amfani da ra’ayi ko ta’assubanci ba.

5. Tausasawa wajen tattaunawa, da kuma mai da martani a cikin

natsuwa. 6. Tawāli’u, da qanqan da kai wajen raddi, matuqar yin hakan ba

zai haifar da qasqanci ba.

7. Mai da hukunci zuwa ga Alqur’ani da Sunnah a bisa fahimtar

magabata na qwarai, musamman sahabbai da tabi’ai da tabi’ut-tābi’in.

8. Zuwa ga na gaba wajen ilmi da fahimta domin ya warware

mas’alar, idan ba a samu fahimta ba a tsakanin masu savani.

Page 131: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

131

kulawa da haqqoqin Musulmi, kuma masu son zaman

lafiya da jawo amfani ga al’umma.

18. Wajibi ne iyaye su riqa tausasawa ga `ya`yansu, tare da

nuna masu qauna da rashin gajiya ko qosawa da su,

musamman idan sun yi tambaya a kan abin da ba su sani

ba. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya ce: ‚Mafi alhairin mata a cikin larabawa, su

ne matan quraishawa: (kasancewar) su ne mafi

tausasawa (da nuna qauna) ga `ya`ya a lokacin da su ke

9. Tantance nau’in savani, ta yadda za a bambance a tsakanin

wanda ke da alaqa da aqida, da kuma wanda ya shafi furu’a, ko

kuma wanda a ke da hujja qarara a cikin nassi, da kuma wanda

babu hujja qarara, kasancewar kowannensu na da yanayinsa

daban.

10. Adalci ga abokin savani, ko da kuwa maqiyi ne mabayyani.

11. Kyautata zato ga abokin savani a tashin farko, kasancewar

akwai yiwuwar ya yi kuskure ne, amma bisa kyakkywar niyya

ko kuma qoqarin fahimtar gaskiya.

12. Yin mu’amala da abokin savani irin yadda a ke son shi ma ya

yi mu’amalar.

Domin rage yawan savani a tsakanin Musulmi, musamman a cikin

mas’alolin aqida, dole ne a bi hanyoyin da Shari’a ta tanadar, waxanda

suka haxa da:

1. Yin kowane abu domin Allah, ba tare da yarfiya ko qazafi ko

qage ba ga abokan savani, ko kuma yin abu don kawai a vata

masu rai.

2. Riqo da Alqur’ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na

qwarai, da kuma xabbaqa hukunce-hukuncensu a cikin adini da

rayuwa gaba xaya.

3. Bin hanyar magabata na qwarai da qoqarin fahimtar addini irin

yadda suka fahimta.

4. Koyon karatu daga waxanda suka dace, da kuma nisantar

girman kai ga dukkan musulmi.

5. Kwaxayi da kuma fatan shiriya da samun dacewa ga kowane

musulmi.

Page 132: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

132

qanana.‛215

An so iyaye su riqa sumbantar `ya`yansu, da

yin masu wasa, da shafa kansu, da xora su a kan cinya

ko qirji, da yawaita yin masu addu’a. Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance

yana sumbantar yara,216

yana rungume su,217

yana yin

masu wasa,218

yana xaukarsu ya xora a kan cinya219

ko

qirji,220

yana shafa kan yara,221

musamman marayu,222

kuma yana yi wa yara addu’ar Allah Ya sanya masu

albarka.223

Haka kuma, ya kasance ya kan xora hannunsa

a kan kafaxar yara, idan zai yi masu magana.224

Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

kasance yana yin waxannan abubuwa ne ga yara saboda

tausayawa da tausasawa da girmamawa da nuna qauna

gare su. Hasali ma, Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ya nuna cewa rashin

sumbantar `ya`ya, alama ce ta rashin tausayi da jin qai

gare su.225

Amma waxannan abubuwan da aka bayyana, ba su nuna

cewa iyaye su qyale `ya`yansu haka nan sakaka, ba tare

da yin masu tarbiyya ba. Dole ne iyaye su ladabtar da

`ya`yansu, kuma su riqa kwavonsu a duk lokacin da suka

ga sun karkace hanya. Ba shi daga qauna ko tausasawa

ko soyayya, a bar `ya`ya ba tare da ladabi, da sanin ya

kamata ba. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

215

Muslim 216

Bukhari da Muslim 217

Bukhari a cikin al-Adabul Mufrad: Sahīh 218

Bukhari da Muslim 219

Bukhari da Muslim 220

Bukhari da Muslim 221

Bukhari 222

Ahmad: Hasan 223

Ahmad, Bukhari da Muslim 224

Bukhari 225

Bukhari

Page 133: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

133

tabbata a gare shi) bai tava ganin yaro ya yi wani abin da

ba dai dai ba, face ya shiryar da shi zuwa ga dai dai, ko

ya kwave shi. Wannan ya sa, a lokacin da aka kawo

zakkar dabino wajen Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi), al-Hasan ibn Ali (Allah Ya

yarda da shi) ya xauki xaya ya sanya a bakinsa don ya ci.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) yana ganinsa, sai ya ce masa: ‚Kikh, kikh,226

don ya

fito da shi (daga bakinsa)‛. Sannan ya ce: Ba ka san (mu banu Hāshim da banu Abdil-Muxxalib) ba mu cin

sadaka ba?‛227

Haka kuma, a lokacin da Zainab bint Abi Salamah

(Allah Ya yarda da ita)228

ta shiga wajen Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) alhali yana

wanka, ya xebi ruwa a hannunsa ya watsa mata a fuska,

kuma ya ce: ‚Tafi ki bani wuri, sakaryar yarinya!‛229

Bayan wannan, hadisi ya tabbata cewa, lokacin da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ga hannun ‘Umar ibn Abi Salamah (Allah Ya

yarda da shi) – a lokacin yana yaro – na yawo a cikin

akushin abinci, sai ya ce masa: ‚Kai yaro! Ka ce:

Bismillah, ka ci da (hannun) dama, kuma ka ci

gabanka.‛230

Bugu da qari, lokacin da Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ga al-Fadl ibnul Abbās (Allah Ya yarda da shi) na kallon wata

mace, ita ma tana kallonsa (a lokacin aikin hajji), sai ya

226

Kalmar farisanci wadda ke nuna tsawatawa da neman a bar abin da a

ke aikatawa 227

Bukhari da Muslim 228

A lokacin tana qarama 229

Xabarāni: Hasan 230

Bukhari

Page 134: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

134

riqa juyar da fuskarsa, don gudun kada ya ci gaba da

kallonta.231

A taqaice, soyayya da qaunar da ya kamata iyaye su

nuna wa `ya`yansu ba su nufin a bar `ya`ya ba tare da

jawo hankali da kwavo ba, a duk lokacin da buqatar

haka ta taso. Wajibi ne iyaye su tabbatar da cewa

`ya`yansu sun samu kyakkyawar tarbiyya, ta hanyar

kwavo, da jawo hankali, da nasiha, da tsawatarwa, da

nuna fushi, da tsoratarwa, da kau da fuska, wani lokaci

ma, har da duka, gwargwadon yadda ya dace. Illa iyaka,

dole ne a lura da abin da ya fi dacewa a duk lokacin da

buqatar yin wani abu ta taso. Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance idan ya ji

wani daga cikin mutanen gidansa (babba ko yaro) ya faxi

qarya, yana kau da fuskarsa daga gare shi (don nuna

masa vacin rai) har sai (wanda ya yi qaryar) ya tuba.‛232

Haka kuma, ya yi umurni da dūkan yara idan suka qi yin

sallar farilla, daga shekara goma.233

Don haka, lallai ne iyaye su sanya ido sosai game da

al’amuran `ya`yansu. Yana daga abin takaici, ka ga

waxansu iyayen sun yi biris da `ya`yansu, a lokacin da

su ke abubuwan da bai dace ba. Misali, uwa ko uba na

kallon yara suna cin abinci da hannun hagu, ko a ji suna

zage-zage, amma ba za a kwava masu ba, wai da hujjar

cewa qananan yara ne; ko kuma a ji suna yawaita

rantsuwa, ko suna rantsuwa da sunan wanin Allah, kamar kwarankwatsa, ko tarnatsa, ko yāsin, ko qabarin

tsoho, ko rawanin tsoho, amma a qyale su, saboda wai

yara ne. To wannan dai ba qauna ba ce a ma’aunin

231

Bukhari da Muslim 232

Ahmad da Hākim: Sahīh [Duba Sahīh al-Jāmi’ #4675 da as-Sahīhah

#2051] 233

Abu Dāwud da al-Bazzār: Sahīh

Page 135: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

135

Shari’a. Bayani ya gabata cewa Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance mai

tausasawa, da nuna qauna, da soyayya, da jin qai ga

qananan yara. Amma duk da haka, ba ya barinsu, ba tare

da ladabtarwa ko faxakarwa ba, idan ya ji/ga sun yi abin

da ba daidai ba. Wannan ne ma ya sa Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ‚Ku

rataye bulala a wajen da iyalinku za su riqa gani, domin

kuwa (yin haka) ladabi ne a gare su.‛234

19. Wajibi ne iyaye su nisantar da `ya`yansu daga abokan

banza don gudun kada su koyi munanan xabi’u daga

gare su. Babu shakka, Musulunci ya ba abota da

qawance muhimmanci sosai, saboda irin tasirin da su ke

da shi a cikin rayuwar mutane.

Allah (Maxaukaki) Ya yi umurni da a lazimci masu

gaskiya;235

Ya zaburar da muminai a kan yin abota da

mutanen da ke yawaita ibada;236

Ya kwaxaitar da bin

hanyar waxanda ke komawa gare Shi;237

Ya hana yin

abota da azzalumai, saboda yin hakan, na haifar da

nadama, da hasara a lahira;238

Ya sanya sakamakon

abotar da ba a gina ta a kan asasin taqawa ba, shi ne,

samun qiyayya a tsakanin abokai;239

kuma Ya tsawatar

game da yin abota tare da wanda ya bar hanyarSa.240

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Mutum yana kan addinin (halaye da xabi’un)

234

Xabarāni, da Khaxīb da Ibn Asākir: Hasan [Duba as-Sahīhah #1447;

da Sahīh al-Jāmi’ #4022] 235

Taubah, 9:116 236

Kahf, 18:28 237

Luqmān, 31:15 238

Furqān, 25:28 239

Zukhruf, 43:67 240

Najm, 53:29

Page 136: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

136

abokinsa, don haka, kowannenku ya duba wanda ya dace

ya yi abota da shi.‛241

Don haka, lallai ne kada iyaye su bar `ya`yansu su riqa

yin mu’amala da yaran da ba su da tarbiyya, a wajen

wasa ko wajen zuwa makaranta. Haka kuma, ya kamata

iyaye su tabbatar da cewa, waxanda ke yin abota da

`ya`yansu, masu hankali ne, da sahihin addini, da

kyawawan xabi’u. Wajibi ne su nisantar da `ya`yansu

daga jahilai ko fasiqai, da wawaye ko masu xabi’un

banza.

20. Wajibin iyaye ne su kula da irin tufafi da kayan adon da

za su sayo wa `ya`yansu don su sanya. Rashin sanya ido

a kan nau’o’in tufafin da yara ke amfani da su a yau da

kullum, na da haxari a kan tarbiyya. Abin mamaki,

waxansu iyayen na yin sakaci game da wannan al’amari,

ta yadda `ya`yansu za su riqa sanya tufafin da ba su dace

ba, wani lokaci ma, su sanya tufafin da Shari’a ta hana

sanyawa, amma ba su kula ba. Misali, waxansu iyayen

su kan sayo wa `ya`yansu kayayyakin da ke xauke da

hotunan manya-manyan kafirai, ko mawaqa, ko `yan

qwallo, ko gumaka, ko karuwai, da sauran manya-

manyan ashararan duniya, ko kuma tufafin da aka yi

rubutun batsa, ko surkulle, ko rashin tarbiyya, a jikinsu.

Haka kuma, waxansu kan sayo wa `ya`yansu mata

nau’o’in tufafin da ke nuna tsiraici da rashin mutunci,

tun suna qanana. A ganin irin waxannan iyayen, abin da

su ke yi daidai ne, kuma wai nuna qauna ce ga `ya`ya.

Ta haka, sai `ya`yan su taso da tsananin son kafirai, irin

su Lenin, Bob Marley, Michael Jackson, Ronaldo,

Okocha, da Kanu, fiye da yadda su ke son Allah (Mai

241

Abu Dāwud da Tirmidhi: Hasan li ghairih [Duba as-Sahīhah #927]

Page 137: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

137

girma da xaukaka) da ManzonSa (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi), da sahabban Manzon Allah (Allah

Ya yarda da su) da sauran bayin Allah na qwarai. Sau da

yawa an ji yara na cewa suna son zama Bob Marley ko

Micheal Jackson ko Ronaldo da sauransu. Wannan, babu

shakka, bala’i ne mai girma, a cikin al’umma.

Wajibi ne iyaye su tabbatar cewa `ya`yansu na sanya

tufafin da bai sava wa Shari’a ba. Kuma ya kamata su

saba wa qananan yara maza sanya dogon wando a

lokacin da za su yi salla. Domin kuwa salla ba ta inganta

ga wanda ya buxe cinyarsa da gangan (alhali yana da

ikon rufewa), kamar yadda Ibn Taimiyyah ya tabbatar. A

qarqashin wannan magana ta Ibn Taimiyyah, Shaykh Muhammad Nāsiruddīn Al-Albānī ya ce: ‚Ya kamata a

koya wa yara maza sanya dogon wando. Bai halatta

iyaye su riqa sanya masu gajeren wando (a lokacin da za

su yi salla), kuma su riqa tafiya da su masallaci a haka

ba, saboda hadisin: ‘Ku umurci `ya`yanku da yin salla

idan sun kai shekara bakwai…’ Babu shakka umurnin da

za a yi masu ya haxa da sharuxxanta, da rukunanta

(kasancewar sallar ba ta inganta sai da su).‛242

Sai dai kuma, lallai ne iyaye su nisantar da `ya`yansu

daga sanya dogon wandon da tsawonsa ya wuce idon

sawu; wanda sai an take shi a qasa, saboda tsawo. Irin

wannan wando, bai dace da Musulmi ba. Hadisai sahihai

sun iyakance tsawon gyauto (kamar wando) zuwa wurare

uku: (i) tsakiyar qwauri;243

(ii) tsakanin saman qwauri

zuwa qasar gwiwa;244

(iii) daga tsakiyar qwauri zuwa

242

Ibn Taimiyyah, Hijābul Mar’ah wa libāsuha fis-Salah, Ta’alīq

Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī, (al-Maktabul Islāmī, Beirut, 1985),

shafi na 28 243

Ahmad, Muslim da Xabarāni 244

Ahmad, Tirmidhi, Nasā’i da Ibn Mājah

Page 138: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

138

idon sawu.245

Idan doguwar riga ce, Sunnah ta iyakance

tsawonta zuwa idon sawu.246

Tufafin da ya wuce

wannnan haddi, bai dace da karantarwar Sunnar Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ba,

Allahumma, sai dai idan akwai mantuwa, ko kuma wata

larura, kamar rauni ko mikin da a ke da buqatar

rufewa.247

Malamai sun bayyana aibobin da ke tattare da sakin

tufafi, har ya ja qasa, a haqqin maza. Waxannan aibobi

sun haxa da: sava wa Sunnar Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi); da faxawa cikin

abin da Shari’ah ta hana; da almubazzaranci; da taqama,

da alfahari da girman kai; da kamanceceniya da mata; da

yiwuwar aukuwar najasa; da haxari ga ibada; da aukawa

cikin haxarin rashin samun kallo da rahama daga Allah;

da faxawa cikin uqubar Allah.248

Don haka, wajibi ne

kowane musulmi ya nisanci sakin tufafi, har ya ja qasa,

ko da kuwa ba da niyyar girman kai ba.249

245

Ahmad, Abu Dāwud da Ibn Mājah 246

Bakar Abdullah Abu Zaid, Hadduth-Thaub wal Uzrah wa Tahrīmul Isbāl wa Libāsish-Shuhrah, (Maktabah as-Sunnah, Egypt, 2001), shafi

na 7-14 247

Bakar Abdullah Abu Zaid, Hadduth-Thaub wal Uzrah wa Tahrīmul Isbāl wa Libāsish-Shuhrah, shafi na 23-24 248

Bakar Abdullah Abu Zaid, Hadduth-Thaub wal Uzrah wa Tahrīmul Isbāl wa Libāsish-Shuhrah, shafi na 19-21 249

Akwai mutanen da ke da’awar cewa, hadisan da suka tsawatar game

da sakin tufafi ya wuce idon sawu, duk suna magana ne a haqqin

wanda ya yi haka da nufin girman kai ko taqama. Hujjarsu mafi qarfi,

ita ce, bayan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya bayyana wa sahabbansa (Allah Ya yarda da su) irin uqubar da

aka tanada ga wanda ya saki tufafinsa, ya ja qasa, saboda girman kai,

Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ya ce, ‘tufafina yana jan qasa, duk da

cewa ina qoqarin xaga shi’. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi) ya ce: ‘ba ka daga cikin masu sakin tufafi saboda

girman kai’. Haka kuma, Abu Hurairah (Allah Ya yarda da shi) ya

Page 139: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

139

ruwaito daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Allah ba zai dubi wanda ya ja tufafinsa a qasa, saboda

taqama ba, a ranar qiyama.‛ Waxanda ke ganin halaccin sakin tufafi ya

ja qasa, sun bayyana cewa, duk wanda ya saki tufafi ya ja qasa ba da

nufin girman kai ba, bai shiga cikin narkon da aka bayyana a hadisan

ba.

Sai dai kuma, wannan fahimtar kuskure ne. Hadisan Abubakar, da

Abu Hurairah, da wata ruwaya daga Ibn Umar (Allah Ya yarda da su)

na nuna irin haxarin da ke cikin sakin tufafi, saboda girman kai ko taqama; amma hadisan Ibn Abbās, da Abu Sa’īd al-Khudrī, da

Huzaifah (Allah Ya yarda da su) sun tabbatar da azaba ga wanda ya

saki tufafinsa, ba tare da qayyade wani dalili ba, ko la’akari da

niyyarsa. Ke nan, ayyuka ne guda biyu mabambanta, waxanda ke

qunshe da sakamako dabam daban: wanda ya saki tufafi, da niyyar

taqama da girman kai, Allah ba zai kalle shi ba, a ranar qiyama, ba zai

tsarkake shi ba, kuma yana da azaba mai raxaxi, kamar yadda hadisan

Abubakar da Abu Hurairah da Ibn Umar (Allah Ya yarda da su) suka

nuna. Idan kuwa ya saki tufafin har ya wuce idon sawu, ba tare da

niyyar girman kai ko taqama ba, Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi) ya bayyana cewa za a qona qasan idon sawunsa, saboda mujarradin wannan mummunar aiki, kamar yadda Ibn Abbās,

da Abu Sa’īd al-Khudrī, da Huzaifah (Allah Ya yarda da su) suka

ruwaito.

Kuma idan ma an qaddara cewa duk hadisan na magana ne a kan

wanda ya saki tufafi, saboda girman kai ko taqama, shi Abubakar

(Allah Ya yarda da shi) ya bayyana wa Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi), cewa hakan na faruwa a gare shi, duk da

qoqarin da ya ke yi wajen tattare shi, da xaga shi sama. Waxanda ke

sakin tufafinsu a yanzu, suna yin haka? Ban da wannan, Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya tabbatar da cewa,

Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ba shi daga cikin waxanda ke sakin

tufafi, saboda girman kai. Idan mutum ya saki tufafinsa a yanzu, wane

ne zai ba shi tazkiyya ko lasisin cewa, ba don girman kai ya ke yi ba?

Haka kuma, idan Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ya saki tufafinsa a

qasa, kasancewar ya sayo shi ne a haka, me za a ce game da waxanda

ke sayen yadi, su ba tela, ya auna su, sannan, su ce masa ga yadda su ke

son tsawon tufafin? Bayan wannan, hadisai sun tabbata daga Ibn Umar da Jābir ibn Salīm (Allah Ya yarda da su) cewa mujarradin sakin tufafi

a qasa, girman kai ne da taqama [Ahmad da Ibn Mani’]. Wace hujja ta

rage wa waxanda ke sakin tufafinsu har ya ja qasa?

Page 140: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

140

Haka kuma, ya kamata a nisantar da qananan yara maza

daga amfani da zinare ko sanya tufafin alhariri. Idan ma

aka ga sun sanya, a umurce su da cirewa, tare da yin

masu bayanin matsayinsa, a haqqin maza. Abdullah ibn

‘Amr (Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‘Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ga tufafi

(mai launin) fatse-fatse a jikina, sai ya ce: ‚Mahaifiyarka ce ta umurceka ka sanya!?‛

250 Kuma Jābir ibn Abdullah

(Allah Ya yarda da shi) ya ce: ‚Mun kasance muna fisge

shi (zinare ko tufafin alhariri) daga (jikin) yara maza,

amma muna barinsa ga mata.‛251

Bayan wannan, wajibi

ne iyaye su hana `ya`yansu maza sanya abin wuya

(sarqa) da abin hannu (warwaro) da xan kunne, kamar

yadda waxansu matasan da ba su da tarbiyya ke yi, a

matsayin koyi da arna. Haka nan ma, wajibi ne a hana su

yin irin askin nan na banza, wanda ke kamanta musulmi

da kafirai, ko kuma a aske wani vangaren gashin kai, a

bar saura, wai saboda gayu.

Don haka, duk da cewa mafi yawan malaman mazhabobi guda

huxu, na ganin cewa makaruhi ne sakin tufafi ya ja qasa, ba haram ba,

fahimtar da ta fi qarfi, da rinjaye, bisa tabbatattun dalilai, ita ce

haramci. Kuma idan ma an xauka cewa makaruhi ne, mene ne amfanin

aikata makaruhi, musamman idan za a iya kauce masa? Ballantana ma,

waxansu malamai na ganin cewa hadisan da suka yi magana a kan haramcin sakin tufafi, sun kai matsayin mutawātir ma’anawi, domin an

ruwaito daga Ibn Abbās, da Ibn Umar, da Ibn Mas’ud, da Abu

Hurairah, da Anas, da Abu Zar, da A’ishah, da Hubaib ibn Mugaffal, da Abu Sa’īd al-Khudri, da Huzaifah, da Mughīrah, da Samurah ibn

Jundub, da Sufyān ibn Sahl, da Abu Umāmah, da Ubaid ibn Khālid, da

Jābir ibn Salīm, da Ibnul Hanzaliyyah, da Amr ibn ash-Sharīd, da Amr

ibn Zurārah, da Amr ibn Fulān, da Kharīm ibn Fātik (Allah Ya yarda da

su). Duba littafin Bakar Abdullah Abu Zaid, Hadduth-Thaub wal Uzrah wa Tahrīmul Isbāl wa Libāsish-Shuhrah, shafi na 18-19 250

Muslim 251

Abu Dāwud: Hasan

Page 141: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

141

Su kuma `ya`ya mata, lallai ne a saba masu da sanya

hijabi (ko mayafi) cikakke idan za su fita gida zuwa

makaranta ko kasuwa ko gidan biki ko asibiti ko ziyara

ko wani wuri daban. Kuskure ne a qyale `yan mata su

riqa sanya tufafi shara-shara ko kuma su fita ba tare da

hijabi cikakke ba, da zarar sun balaga, wato, sun fara

jinin al’ada. Maganar cewa hijabi wajibi ne kawai a kan

matar aure, ba ta da asali a cikin Alqur’ani da Sunnah.

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya ce: ‚Kuma ka ce wa

muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare

farjojinsu, kuma kada su bayyana qawarsu face abin da

ta bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a

kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna qawarsu face

ga mazansu, ko ubanninsu…‛252

Kuma Ya ce: ‚Ya kai

Annabi! Ka ce wa matanka na aure da `ya`yanka da

matan muminai su kusantar da manyan tufafin da ke

kansu qasa.‛253

Hadisi ya tabbata cewa Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Daga qarshen al’ummata, za a samu waxansu mata (na

yawo) sanye da tufafi (amma kuma saboda shara-

shararsa), tsirara (su ke a zahiri)… Ku la’ance su, domin

kuwa la’anannu ne.‛254

A cikin wani hadisin, Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce:

‚Ba za su shiga aljanna ba, kuma ba za su ji qamshinta

ba.‛255

Ke nan, da zarar yarinya ta balaga (ko da ba ta yi

aure ba), wajibi ne ta sanya hijabi irin na Musulunci,

idan za ta fita.256

252

Nūr, 24:31 253

Ahzāb, 33:59 254

Xabarāni: Sahīh 255

Muslim 256

Nazari a cikin Alqur’ani da Sunnah na tabbatar da cewa akwai

sharuxxa guda takwas da a ke buqatar lulluvi ko mayafin da mace za ta

sanya (a lokacin da za ta fita) ya cika, kafin a kira shi hijabi. Sharuxxan

su ne: (1) ya zamanto ya rufe jikinta gaba xaya (2) kada ya kasance shi

Page 142: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

142

Haramun ne ga mace ta yi wa iyayenta ko mijinta xa’a,

idan suka hana ta sanya hijabi cikakke, a lokacin da za ta

fita ko kuma suka taqaita mata sanya hijabi ga lokacin da

za ta yi salla kawai, kamar yadda waxansu ke yi.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya ce: ‚Babu xa’a ga wata halitta a cikin savon

Mahalicci‛.257

Kuma ya ce: ‚Ana yin xa’a ne a cikin

abin da aka sani a Shar’ance.‛258

Tun da sanya hijabi

umurni ne daga Allah da Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi), ba daidai ba ne ga wata

mace ta qi sanyawa saboda mijinta ko iyayenta ba su so.

Idan ta qi sanyawa, ta yi laifi; idan kuwa ta sanya, ba ta

da laifi a wajen Allah (Maxaukaki), ko da iyayenta ko

mijinta sun yi fushi. Haqiqa, xa’a ga Allah (Mai girma

da xaukaka) da ManzonSa (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) na gaba da xa’a ga miji ko iyaye. 259

A

kansa tufafi ne na ado (3) kada ya riqa nuna wani vangare ko wata gava

na jikinta, saboda shara-shara da shafa-shafarsa (4) kada ya zamanto

matsattse ta yadda zai siffanta jiki (5) kada a sanya turare a lokacin da

za a fita ko kuma tun kafin lokacin fitan bayan an san za a fita daga

baya (6) kada ya yi kama da tufafin maza (7) kada ya yi kama da

tufafin mata kafirai (8) kada ya kasance tufafi ne na shahara (saboda tsada ko arharsa, sai dai ya kasance matsakaici). [Duba littafin Jilbāb al-Mar’ah al-Muslimah na Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī]. 257

Muslim 258

Muslim 259

Akwai savani mai tsanani, a tsakanin malamai, a wannan zamani,

dangane da hukuncin rufe fuska da tafin hannu. Misali, a yayin da Shaykh Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī da al-Qaradāwi ke ganin

halaccin bayyanar da fuska da tafin hannu, ko da ya ke rufewar mustahabbi ne; Shaykh Muhammad ibn Sālih al-‘Uthaymīn da At-

Tuwaijiri da mafi yawan malaman Saudia da malaman Yemen da

malaman Sunnah na qasar Masar na ganin wajibcin rufe fuska da tafin hannu. [Duba littafin Jilbābul Mar’atil Muslimah fil Kitāb was Sunnah da Ar-Raddul Mufhim na Al-Albānī; Risālatul Hijāb na Al-‘Uthaymīn;

Risālatul Hijāb na At-Tuwaijiri; Hirāsatul Fadīlah na Bakar Abdullah

Page 143: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

143

Abu Zaid; da Al-Hijāb na Musxafa Al-Adawi don ganin maganganun

malamai, da savanin da suka yi].

Abin lura shi ne, duk malaman sun tabbatar da Shar’ancin sanya

niqabi da safar hannu, domin rufe fuska da tafin hannu. Hasali ma,

savanin da suka yi, ba wai a kan halacci ba ne. Sun yi savani ne

dangane da wajibci ko mustahabbancin niqabi. Kuma wannan savani

ba yanzu aka fara ba; tun daga lokacin sahabban Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi) da tabi’ai da sauran magabata

aka samu bambancin fahimta. Bambancin lokacin magabata (salaf) da abin da ke faruwa a yanzu shi ne: magabata ba su qulla al-walā wal barā, wato, qiyayya da soyayya, a kan mas’alar ba; amma waxansu

xaliban ilmi a yanzu, suna neman kafirta juna saboda niqabi. Duk da irin zafafa wa juna da aka yi a tsakanin Al-Albānī, musamman a cikin

Ar-Raddul Mufhim, da At-Tuwaijiri da magoya bayansa, ba su qulla

soyayya da qiyayya a kan wannan mas’ala ba. Abin mamaki, waxansu

`yan zafi a Nijeriya, sun mai da mas’alar niqabi, kamar xaya daga cikin

rukunan Musulunci, ta yadda su ke qulla qiyayya da soyayya ( )

a kanta. Irin waxannan xaliban ilmi, ba su da wani magabaci a kan

haka, daga cikin malaman da suka gabata, da malaman wannan zamani.

Lallai ne xaliban ilmi da masu da’awa su ji tsoron Allah.

Kwatsam, sai ga waxansu `yan bidi’a na da’awar cewa niqabi bidi’a

ne, kuma wai ba a fara sanya shi ba, sai bayan shekara hamsin (50) da

barin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

duniya. Wannan qarya ce tsantsa, wadda ba ta buqatar a yi kace-nace a

kanta. Waxannan mutane, galibinsu `yan boko ne waxanda suka

tasirantu da shubuhohin , waxanda ke raddin hadisan Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ingantattu saboda

wai sun sava wa abin da kimiyyar zamani ta tabbatar. Bayan waxannan

`yan boko aqida, an samu waxansu daga cikin shehunnan xariqa na

sukar hijabi da niqabi, kuma suna umurtar matan Musulmi da sanya

gyale ko xigilgilallen mayafi, maimakon hijabi, wai don kada su yi

kamanceceniya da matan `yan izala.

Daga baya-bayan nan, sai ga wani malami a jami’ar Ahmadu Bello,

Zaria, Issa Hasan Tikuma, ya rubuta wani littafi, yana sukar xalibai

mata waxanda ke sanya niqabi, kuma yana kira ga malaman jami’a da

su hana irin waxannan xalibai zama a cikin aji, a lokacin karatu. Bai

tsaya nan ba, Tikuma ya jahiltar da malamai, kuma ya zarge su da

jumudi, wato, daskarewar fahimta, da sakarci da kuma rashin faxin

gaskiya. Hujjarsa a cikin wannan littafi mai suna The Abuse of Islam and the Dormancy of Islamic Scholars: Evidence from the Misuse of

Page 144: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

144

vangaren miji kuma, haramun ne a gare shi ya bar

matarsa ta fita, ba tare da hijabi cikakke ba. Idan ba za ta

sanya tufafin da ya dace ba, a lokacin da za ta fita, kada

ya yi mata iznin fita.260

Niqab (Face Veil) in the Nigerian Society ita ce wai waxansu mata na

yin amfani da niqabi a matsayin kariya wajen satar jarabawa ko sace-

sace a kasuwa, da sauran nau’o’in varna.

Tir da wannan mummunar famita, da kuma qarfin halin rashin

kunya (jara’a) a kan malamai. A ina aka tava aibanta wani tabbataccen

abu a cikin Shari’ah saboda waxansu `yan tsirarun mutane da ke sakaci

da shi? Wane tabbaci Tikuma ya ke da shi cewa xalibai mata suna

fakewa da niqabi wajen yin varna? Shin, Tikuma ba ya jin cewa yana

qoqarin jawo wani bala’i ne ga kansa da hukumar jami’ar Ahmadu

Bello, a dalilin kiraye-kirayen da ya yi cewa a xauki qwaqqwarar

mataki a kan masu sanya niqabi? Ba ya tunanin cewa varna ya ke yi wa

Musulunci da musulmi, maimakon gyara? Allah Ya shiryar da mu.

Kwanan nan aka ce Issa Hasan Tikuma ya sake rubuta wani littafi a

kan niqabi. Ko da ya ke ba a buga littafin ba, waxanda suka tattauna da

shi, sun ce littafin ya qunshi bayanan da ke nuna cewa wai niqabi

wajibi ne kawai a kan matan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi). Duk da cewa babu wani xalibin ilmi da ya ruxu da

shirmensa, da yawa daga mutanen da ke mu’amala da shi, suna zaton

cewa wai shi Ahlus-Sunnah ne! Bincike ya nuna cewa Issa Hasan

Tikuma na fama da karkatacciyar aqida, da kuma ra’ayin xariqar

sufaye, duk da cewa ba ya son a gane hakan. Allah Ya kyauta. 260

Waxansu mata na da’awar cewa ba su sanya hijabi saboda ba shi ne

ya ke tabbatar da tsoron Allah ba, kuma wai ai zuciya a ke dubawa ba

tufafi ba. Haka kuma, su kan yi da’awar cewa akwai matan da ke sanya

hijabi, wataqila ma har da niqabi, amma ayyukansu munana ne.

Wannan shubuhar na nuna jahilci da son zuciyar irin waxannan mata,

duk da cewa suna samun goyon bayan waxansu malaman da ke da

karkatacciyar fahimtar Musulunci. Sanannen abu shi ne, kamar yadda

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya yi umurni da yin salla, da azumi, da

zakka, da hajji, da biyayya ga iyaye, da kyautata wa maqwabta da `yan’uwa, haka kuma, Ya umurci mata da sanya hijabi [Nūr 24:31;

Ahzāb 33:59]. Ke nan, biyayya ce ga Allah, mace ta sanya hijabi, ko da

sanya hijabin bai hana ta yin waxansu munanan abubuwa ba. Shin

akwai musulmin da zai ce ba a buqatar yin aure a yanzu, tun da dai bai

hana waxansu ma’aurata yin zina ba!? Ko kuwa, za a ce ba dole ne

Page 145: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

145

Haka kuma, kasancewar itace ana tanqwara shi ne tun

yana xanye, ya kamata iyaye su himmatu wajen koya wa

`ya`yansu sanya hijabi, da saba masu amfani da shi, tun

suna qanana, musamman a lokacin da za su fita,

maimakon gyale ko abin tatan qullun koko.261

Shaykh Muhammad Sālih ibn al-‘Uthaimīn ya ce: ‚Ya ku

`yan’uwa, iyayen `ya`ya mata! Sanya wa `ya`ya mata

gajejjerun tufafi ko matsattsun tufafin da ke siffanta jiki

ko tufafin da ke bayyana launin jiki saboda shara-

shararsa, abu ne da ya yaxu a tsakanin mutane kuma aka

xauke shi da sauqi. (Ku sani cewa) wanda duk ya sanya

wa `ya`yansa mata irin waxannan tufafi ko kuma ya

qyale su idan sun sanya da kansu, to yana sanya masu

tufafin `yan wuta ne, kamar yadda ya tabbata daga

Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).262

Ya kai uba musulmi! Yanzu za ka so wa `yarka, kuma

masoyiyarka, shiga wuta? Ka yarda ka riqa sanya wa

`yarka tufafin da zai nuna rashin kunyarta, bayan kuwa

kunya na daga imani? Ka yarda `yarka ta mai da kanta

kamar wata hajar (kayan) sayarwa…?‛263

Wajibi ne iyaye su sanya ido a kan `ya`yansu mata don

tabbatar da cewa ba su yin amfani da kayan ado na

haram. Sanannen abu ne cewa qarin gashi, da tsaga wani

mutane su yi salla ba, tun da dai sallar ba ta hana waxansu musulmi

aikata alfasha ba? 261

Sanya hijabi na da fa’idodi masu yawa: (1) tsare mutunci; (2)

tsarkake zuciya; (3) samun kyawawan xabi’u; (4) alama ce ta kamewa;

(5) hanya ce ta karya kwaxayi da tunanin shaixan; (6) yana taimakawa

wajen tsare kunya da kishi; (7) yana hana tabarruj. [Duba littafin Hirāsatul Fadīlah na Bakar Abdullah Abu Zaid]. 262

Imām Muslim da Xabarāni suka ruwaito hadisin, kuma ya gabata. 263

Samīr Abdul-‘Azīz, Manhaj al-Islām fi Tarbiyyatil Aulād, shafi na

247-248

Page 146: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

146

vangare na jiki don ado,264

da aske gashin gira, da

amfani da duk wani sanadarin da ke canza fatar jiki

(bleaching), haramun ne a musulunci. Hasali ma,

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya roqi Allah (Mai girma da xaukaka) Ya la’anci

waxanda ke yin haka, kamar yadda hadisai suka

tabbatar.265

Amma abin mamaki, waxansu iyayen ne ke

umurtar `ya`yansu su tsaga jikinsu, su yi zane-zane ko

hotunan abubuwa masu rai (bayan an tsattsaga jikin), da

sunan ado. Wani lokaci ma, iyayen ne ke yin haka da

kansu. Idan iyaye suka tsaga fuska ko wani vangare na

jikin `ya`yansu, laifin yana kansu, tun da dai `ya`yan ba

su da ikon hanawa a wannan lokaci.266

Wannan shi ne abin da Imām Nawawī da mafi yawan malamai suka

tabbatar.267

21. Haqqin `ya`ya ne a kan iyayensu a sanar da su

muhimmancin lokaci da yadda za su yi amfani da shi, da

fahimtar da su cewa an halicce su ne don bauta, da

tunatar da su wajibcin tattali don zama sojojin

Musulunci, da faxakar da su qalubalen da ke gabansu, a

matsayinsu na yara manyan gobe, da karantar da su irin

264

Wannan ya haxa da tsagar al’ada da a ke yi wa yara a fuska, kamar

bille, fashin goshi, kwale, tsagen kananci, mallanci, gobiranci, nufanci,

yarbanci da sauransu. Dukkansu laifi ne, kuma canza halittar Allah ce,

da cutar da jiki ba tare da larura ba. Waxanda aka yi wa irin wannan

tsaga tun suna qanana, ba su da laifi, domin kuwa ba su da ikon hanawa

a wancan lokaci. Sai dai kuma wajibi ne su nisantar da nasu `ya`yan

daga irin wannan aiki mara kyau nan gaba. 265

Bukhari da Muslim 266

Wannan hukuncin bai haxa da huda kunne don sanya wa yara mata

xan kunne, da sauran kayayyakin ado ba. Shi kam babu laifi, tun da dai

larura ce, kamar yadda malamai, irin su Ibn al-Qayyim, suka tabbatar. Duba littafin Tuhfah al-Maudūd, shafi na 143-144 267

Samīr Abdul-‘Azīz, Manhaj al-Islām fi Tarbiyyatil Aulād, shafi na

245

Page 147: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

147

gudummuwar da a ke sa ran su ba da wajen kawo ci gaba

da xaukaka ga al’umma. Waxannan abubuwa za su

tabbata ne kawai idan `ya`ya sun taso da kishin zuci, da

son karatu da aiki da shi, da son dogaro da kai, da

kyakkyawar mu’amala, da son taimakon jama’a, da sanin

muhimmancin lokaci, bayan sun samu kyakkyawar

tarbiya.268

268

‘Lokaci’ yana daga abubuwa mafi tsada waxanda Allah (Mai girma

da xaukaka) Ya yi wa bayinSa kyautarsu. Babu wata kasuwa da a ke

sayar da ‘lokaci’; shi ne farkon abin da a ke nema daga kowane

musulmi, kasancewar jihadi, da da’awah, da karatun Alqur’ani, da tsai

da salla, da yin ziyara, da koyon karatu da karantarwa duk suna buqatar

lokaci. Wannan ya sa a ke xaukar ‘lokaci’ a matsayin rayuwa. Saboda

matsayin ‘lokaci’, Allah (Mai girma da xaukaka) Ya goranta wa bayinSa ni’imar ‘lokaci’ [An’ām, 6:13; Ibrāhīm, 14:32-34; Nahl, 16:12;

Isrā, 17:12; Fussilāt, 41:37], kuma Ya rantse da ‘lokaci’ gaba xayansa

ko sashensa [‘Asr, 103:1; Lail, 92:1-2; Fajr, 89:1-4; Duha, 93:1-2; Inshiqāq, 84:16-17; Takwir, 81:17-18].

‘Lokaci’ na da matuqar muhimmanci a rayuwar musulmi: shi ne

rayuwa gaba xaya, kamar yadda Al-Hasan Al-Basari ya ce, ‘Ya kai xan

Adam, rayuwarka gaba xaya ta qunshi kwanaki ne, idan wata rana ta

wuce, sashenka ne ya wuce.’ ‘Lokaci’ na daga asalin ni’imomin da

Allah Ya yi wa bayinSa; yana daga cikin abubuwan da za a yi hisabi a

kansu a ranar qiyama; kuma shi ne uwar dukiya da jarin kowane

mutum.

Wajibi ne musulmi ya yi amfani da lokacinsa, yadda ya dace. Haka

kuma, laifi ne a tozarta ‘lokaci’, domin yin hakan, na jawo nadama,

kuma butulci ne ga Allah. A wannan zamani, rashin amfani da ‘lokaci’

yadda ya dace, alama ce ta ci baya ga al’umma.

Amfani da ‘lokaci’ yadda ya dace na buqatar: (i) tsattsara abubuwan

da za a gabatar (ii) samar da manufa, da abin da a ke son a cimma, tun

gabanin a gudanar da abu (iii) shirya abubuwa a bisa tsarin cancanta, da gwargwadon muhimmanci (iv) shirya jadawalin ayyukan da za a yi a

cikin yini (v) amfani da lokacin da ya fi daxi, da kuma karsashi ga

mutum (vi) sabawa da qin xaukar nauyin abubuwan da ba su zama dole

ba (vii) watsi da aqidar sai komai ya yi daidai, xari bisa xari, domin

kuwa kyautatawa da ingantawa kawai a ke buqata, ba wai kamala ba.

Malamai sun bayyana cewa kowane mai hankali yana buqatar raba

‘lokacinsa’ gida huxu: (1) ambaton Allah ta hanyar nau’o’in ibada na

Page 148: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

148

Wajibi ne iyaye su tsawata wa `ya`yansu, a duk lokacin

da suka ga suna amfani da lokaci wajen aikata abubuwan

da ba za su amfane su ba, duniya da lahira. Zaman

xumama benci, da zaman kashe wando, ko zaman kalle-

kallen finafinan wasan kwaikwayo269

da wasannin `yan

farilla da nafila (2) yi wa kai hisabi (3) tunani a cikin halittar Allah (4)

biyan buqatar duniya, kamar neman abinci. 269

Bincike ya tabbatar da cewa kallon finafinai na da illoli ta fuskar

aqida, da al’ada, da tarbiyya, da tarihi, da tunani, da lafiya, da tattalin

arziki. Ta vangaren aqida, finafinai na da illolin da suka shafi nuna

muhimman alamomin kafirai da vataccen addininsu; da nuna cewa

waxansu mutane, musamman matsafa, da shugabannin kiristoci,

waxanda ke yin amfani da karama ta qarya ko gicciye (cross), suna iya

yin tarayya da Allah wajen yin halitta da kashewa da rayawa; da haifar

da shakku a cikin zukatan waxansu, game da ikon Allah da qarfinSa;

da koyar da sihiri da bokanci; da koyar da yin wasa da sunan Allah. A

vangaren yanayin zamantakewa, waxanda ke kallon finafinai, su kan yi

sha’awar gwanayen `yan fim, ko mawaqa daga cikin kafirai da karuwai

da kangararru, da irin xabi’un da su ke nunawa a lokacin wasan fim, da

son koyi da su; da yaxa halayen banza; da koyar da zinace-zinace, da

fyaxe, da kisan kai; da nau’o’in rashin gaskiya, kamar qarya, da zamba

da karvar rashawa. A vangaren tarbiyya kuma, kallon finafinai na

vavvako wa samari sha’awar mata, da son yin jima’i; da raye-raye; da

maganganun batsa; da bayyana tsiraici; da rashin son sanya tufafin da

ya dace; da sauransu. A vangaren ibada, kallon finafinai na haifar da

sakaci da jinkiri wajen ibada; da jawo tauye lada; da wulaqanta hijabi.

A tarihance, finafinan da a ke shiryawa, musamman daga qasashen

Turai, na kawo tarihi a hagungunce domin a gurvuta sahihin tarihin

Musulunci; da nuna azzalumai a matsayin masu gaskiya; da rashin

qimanta baraden Musulunci; da tsoratar da musulmi game da qarfin

kafirai. A fagen lafiya, kallon finafinai na jawo matsala ga idanuwa; da

haifar da rashin barci.

Abin baqin ciki da takaici shi ne, duk waxannan matsaloli da

aibobin da ke tattare da finafinan Turanci (Nigerian Films), da finafinan

India, da waxanda a ke shigo da su daga qasashen Turai, ana samunsu a

cikin finafinan Hausa. Hasali ma, varnar da `yan fim xin Hausa ke yi

wa Musulmin Nijeriya da Musulunci ta fi wadda waxancan ke yi,

saboda mutane na fahimtar halshen da `yan fim xin Hausa ke amfani da

Page 149: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

149

aljannu (cartoon), ba su da amfani a cikin rayuwar

musulmi (yaro da babba, mace da namiji), Allahumma,

sai dai idan cartoon xin da aka shirya bisa tsarin

Musulunci. Ibn al-Qayyim ya ce: ‚Kuma ya kamata

waliyyin yaro (iyaye ko waninsu) ya nisantar da shi daga

karvar abin hannun mutane, domin kuwa da zarar ya

saba karva, hakan zai zame masa xabi’a; sai ya zamanto

maimakon ya riqa ba da wa, sai dai ya karva. Kuma ya

kamata (uba) ya koya wa yaronsa yin kyauta da

taimakon jama’a (gwargwadon hali). Idan zai ba da

kyautar wani abu, an so ya ba da ta hannun yaron, don ya

saba masa da ayyukan alhairi. Haka kuma, ya kamata ya

nisantar da shi daga kasala, da zaman kashe wando da

xumama benci, domin kuwa abubuwa ne waxanda ke

haifar da tawaya ga wanda ke yinsu.‛270

22. Lallai ne iyaye su riqa karantar da `ya`yansu sahihin

tarihin Musulunci, da irin gwagwarmayar da sahabban

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) suka yi wajen tsare martabar addinin Musulunci, da

yaxa shi a duniya. Haka kuma, lallai ne a karantar da su

martabar sahabbai da tabi’ai da tabi’ut tabi’in da sauran

malaman Sunnah, da irin abubuwan koyi da suka yi a

cikin rayuwarsu. Idan yara suka ilmantu a kan matsayin

sahabban Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi); suka fahimci daraja da matsayin

matan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) da `ya`yan Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) da jikokin Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi); da

shi. Haka kuma, ana ganin irin fitsara, da ballagazanci, da sakarci, da

shashanci, da kwaikwayon al’adu da addinin kafirai, da rashin kamun

kai, da munanan xabi’un da mafi yawan `yan fim ke koyarwa ta

fuskoki dabam daban. Allah Ya kiyaye mu. 270

Tuhfah al-Maudūd, shafi na 162

Page 150: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

150

matsayin tabi’ai da manyan malaman Sunnah, ana sa ran

su girmama su, irin girmamawar da ta dace da su, kuma

su yi tsayuwar daka wajen tsare martabarsu da bayyana

falalarsu, tare da tona asirin wanda ke adawa da su. Haka

kuma, ana sa ran su xauki waxannan manyan mutane a

matsayin abin koyi gare su, maimakon `yan qwallo da

`yan rawa ko kangararrun matasan da ke yin finafinai.

23. Ya kamata iyaye su tarbiyyantar da `ya`yansu a kan yin

da’awa, da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna,

domin su san muhimmancin qoqarin tabbatar da gyara a

cikin al’umma.271

Haka kuma, ya kamata iyaye su nemi

271

Da’awah ta qunshi yin kira zuwa ga imani da Allah, da abin da

ManzanninSa suka zo da shi, ta hanyar gaskata abin da suka ba da

labari, da yin masu xa’a cikin umurninsu. Kira zuwa ga addinin Allah

farilla ce da Allah (Maxaukaki) Ya xora a kan al’ummar Musulmi baki xaya [Aal Imrān, 3:110]; sai dai kuma tana zama farillar dole a kan

shugaba [Hajj, 22:41], sannan sai malamai, kasancewar sun xauki

alqawari ga Allah (Maxaukaki) cewa za su bayyana littafinSa, ba tare da voyewa ba [Aal Imrān, 3:187].

Ayoyin Alqur’ani da ingantattun hadisai sun zo da umurni game da yin da’awah [Aal Imrān, 3:104; Nahl, 16:125; Taubah, 9:71; Bukhari

da Muslim;]. Haka kuma, hadisan Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) sun yi umurni da yin da’awa, da umurni da

kyakkyawa da hani da mummuna [Bukhari da Muslim]. Malamai da

yawa sun tafi a kan cewa yin kira zuwa ga hanyar Allah, da umurni da

kyakkyawa da hani da mummuna wajibi ne a kan kowane Musulmi gwargwadon iko. Misali, Ibn Kathīr, a cikin tafsirinsa, a qarqashin Aal

Imrān, 3:104, ya bayyana cewa yin da’awa wajibi ne a kan kowane

mutum, gwargwadon ikonsa. Haka kuma, Ash-Shaukāni, a cikin

tafsirinsa, a qarqashin Yusuf, 12:108, ya bayyana cewa ayar na nuna

wajibcin koyi da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) a cikin da’awah.

Ahlus Sunnah na yin da’awah saboda dalilai guda tara:

1. Lada mai girma wanda Allah (Maxaukaki) Ya tanadar wa

mai yin da’awah, kasancewar wanda ke yin da’awah: yana

daga cikin mafi kyautata magana [Fussilat, 41:33]; shi ne mafi alhairin mutane [Aal Imrān, 3:110]; yana daga cikin

Page 151: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

151

masu babban rabo a duniya da lahira [Aal Imrān, 3:104];

yana da ladan kwatankwacin mutanen da suka bi shi

[Muslim]; yana samun lada wanda ba ya yankewa bayan

mutuwarsa [Muslim]; yana samun addu’ar neman gafarar

Allah (Maxaukaki) daga waxanda ke sama da qasa, har da

tururuwar da ke cikin rami, da kifin da ke cikin teku [Xabarāni]; yana samun matsayin da alhairinsa ya fi duniya

da abin da ke cikinta [Bukhari].

2. Yin biyayya da xa’a ga umurnin Manzon Allah [Ahmad da

Bukhari] da yin koyi da Annabawa [Yusuf, 12:108].

3. Samun uzuri wajen Allah (Maxaukaki) a ranar qiyama [A’arāf, 7:164].

4. Neman tsira da kuvuta daga fitinar duniya da lahira [Anfāl,

8:25].

5. Al’umma ta gyaru kuma al’amarinta ya kyautatu.

6. Qalubalantar varnar `yan bidi’a, da bayyana wa al’umma gaskiya, da kare martabar sahihin addini [Nisā, 4:104].

7. Mutane su fahimci gaskiya, kuma su iya bambancewa a

tsakanin gaskiya da qarya [Nur, 24:54].

8. Samar da aminci a cikin al’umma [Hud, 11:117].

9. Tabbatar da manufar da’awar Sunnah, da yaxa ta, da kare

muradunta.

Ana kiran mutane ne zuwa ga sanin Allah (Mai girma da xaukaka)

da sunayenSa da siffofinSa, da sanin Shari’arSa da ke kai mutane zuwa

ga aljanna, da sanin sakamakon yin maSa xa’a ko kangarewa, kamar

yadda Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

koyar da Mu’azu ibn Jabal (Allah Ya yarda da shi) a lokacin da ya tura

shi zuwa Yemen [Bukhari da Muslim]. Za a yi wa mutane da’awah a

kowane lokaci, gwargwadon yanayi da iko: dare da rana, kamar yadda

Annabi Nuhu (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi [Nuh,

71:5]; a cikin halin tsanani da qunci ko yalwa, kamar yadda Annabi

Yusuf (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi a cikin

kurkuku [Yusuf, 12:39-40]; hatta a cikin ciwon ajali, kamar yadda

Annabi Ya’aqub (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi ga

`ya`yansa [Baqarah, 2:133]; da lokacin gargarar mutuwa, kamar yadda

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi

wasiyya game da kiyaye salla da haqqoqin bayi [Ahmad, Abu Dawud, Nasā’i, Baihaqi, Ibn Hibbān da Xabarāni].

Ana gina da’awa ce a bisa asasin ilmi, da fahimtar hali, da yanayi da

matakin ilmin wanda za a yi wa da’awar, da fahimtar halin da a ke ciki,

Page 152: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

152

taimakon dattawan qwarai, da sauran mutanen kirki

wajen ganin `ya`yansu sun samu tarbiyya. Babu laifi su

haxa `ya`yansu abota da `ya`yan da aka san suna da

tarbiyya, ko kuma su tura su gidajen mutanen da suka

shahara da xabi’un qwarai domin su koyi tarbiyya. Idan

an yi baqon malamin Sunnah, iyaye su tafi da `ya`yansu

wajensa domin ya yi masu nasiha tare da jawo hankali,

kuma ya kwaxaitar da su a kan shiga cikin harkokin

da’awa. Idan an samu hali, iyaye su tafi da `ya`yansu

ziyarar malaman Sunnah a wasu garuruwan domin a

saba wa yara lazimtar mutanen kirki da son jin alhairi.

QALUBALEN DA KE FUSKANTAR TARBIYYA

A yau, tarbiyya a cikin al’ummar musulmi na fuskantar

matsaloli, da qalubale iri-iri. Waxannan matsaloli sun shafi

cikin gida da waje, kuma suna yin karen-tsaye ga tarbiyyar

`ya`yan musulmi.

da fahimtar hanyoyin isar da da’awar, waxanda suka haxa da rediyo da

talbijin da yanar gizo da wayar hannu da jarida da mujalla da allon

masallaci. Za a iya gudanar da da’awa ta hanyoyin shirya darussan ilmi,

da muhadarori, da buxe makarantun islamiyya ko boko, da makarantun

hardar Alqur’ani, da ziyarar asibiti ko gidan yari, da ziyarar gidan

marayu, da filin idi, da sauran wuraren da a ke taruwa.

Ya kamata mai da’awah ya fara gyara kansa saboda tasirin yin haka a cikin da’awah [Hud, 11:88; An’ām, 6:14]; daga nan sai makusantan

shi, kamar ma’aura da `ya`ya da `yan’uwa da dangi [Shu’arā, 26:214];

daga nan sai maqwabta na kusa da na nesa [An’ām, 6:92]; sannan

sauran mutanen duniya gwargwadon iko da halin da a ke ciki [Ibrahim,

14:1].

Lallai ne mai da’awa ya mallaki siffofi guda takwas: taqawa; da

ikhlasi; da gwargwadon ilmin da ya ke buqata don yin da’awar; da

zamantowa kyakkyawar abin koyi; da qanqan da kai; da juriya; da

la’akari da halin wanda za a yi wa da’awar.

Page 153: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

153

Daga cikin manyan qalubalen da ke fuskantar tarbiyya,

akwai:

1. Talauci272

272

Talauci ya qunshi yanayin rashin mallakar abin da a ke buqata a

cikin rayuwa, da ya haxa da abinci, da abin sha, da muhalli. Masana

ilmin tattalin arziki sun kasa talauci gida biyu: (1) mai dama-dama, da

ke haifar da yanayin da mutane za su rasa abincin da ke gina jiki, da

abubuwan more rayuwa (2) mai tsanani, da ke haifar da yanayin da

mutane da qyar za su rayu, yanayin daga shi sai mutuwa, saboda rashin

abinci, da ruwan sha tsaftatacce, da wajen kwana, da ilmi, da abubuwan

da za su kyautata tsaftar muhalli.

A yau, matsalar talauci na xaya daga cikin matsalolin da suka fi

addabar mutane. A qididdigar da cibiyar ICPD ta yi a shekarar 2002, an

qiyasta cewa fiye da mutane biliyan xaya ne ke rayuwa a cikin

matsanancin talauci. A Nijeriya, binciken da aka gudanar a tsakanin 2006 zuwa 2007 ya gano cewa kusan kashi biyu bisa uku (⅔) na ‘yan

Nijeriya na fama da matsanancin talauci, kuma suna rayuwa a kan qasa

da dalar Amurka guda xaya ($1) a kowace rana, duk da cewa Nijeriya

ta samu fiye da dala biliyan xari uku ($300 billion) daga man fetur da

iskar gas, tun daga 1960 zuwa yau.

Ba da daxewa ba, a cikin shekarar 2008, tsohon gwabnan babban

bankin Nijeriya (CBN), Farfesa Soludo, ya bayyana cewa kimanin

kashi saba’in bisa xari (70%) na mutanen da ke zaune a arewacin

Nijeriya, na rayuwa a kan qasa da naira dubu huxu (N4000) a kowane

wata. A qiyasin da aka yi wa mutanen da ke rayuwa a cikin jihohin

arewa, an bayyana cewa kashi 95% a jihar Jigawa, kashi 89.7% a jihar

Kebbi, kashi 88.6% a jihar Kogi, kashi 86.3% a jihar Bauchi, kashi

85.2% a jihar Kwara, kashi 83.3% a jihar Yobe, kashi 80.9% a jihar

Zamfara, kashi 77% a jihar Gombe, kashi 76.8% a jihar Sokoto, da

kashi 71.7% a jihar Adamawa na rayuwa a kan qasa da naira xari da

talatin (N130) a kowace rana, ko kuma naira dubu huxu (N4000) a

kowane wata.

Bayan wannan, duk da irin rawar da ilmin boko ke takawa a wajen

kawar da talauci da kawo ci gaba ga al’umma, musamman a wannan

zamani, mutanen arewa, waxanda galibinsu Musulmi ne, an bar su a

can baya. Misali, tsohon gwabnan CBN xin, ya bayyana cewa a cikin

fiye da xalibai miliyan xaya (1,000,000) waxanda suka zauna wa

jarabawar share fagen shiga jami’a a shekarar 2008, xalibai dubu

saba’in da uku (73,000) ne kawai daga dukkan jihohin arewa in ban da

jihohin Kogi da Kwara da Benue, a yayin da a jihar Imo kawai, an

Page 154: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

154

2. Saxaxowar munanan aqidu da hanyoyin vata273

samu fiye da xalibai dubu xari (100,000). Wannan na nuna cewa babu

mamaki idan talauci ya yi wa Musulmin Nijeriya kaka-gida,

musamman waxanda ke zaune a arewa.

Musulunci na kallon talauci a matsayin musiba, wadda ke auka wa

mutane, kuma ya kamata a nemi tsarin Allah (Mai girma da xaukaka)

daga gare ta, kuma a yaqe ta, saboda mummunar tasirinta a kan aqidar

mutane, da mu’amalarsu. Talauci ba abin so ba ne, kuma ba a yin tutiya

ko qafafa da shi, ballantana ya zamanto abin alfahari. Talauci na da

haxari mai yawan gaske a kan aqida, da xabi’a, da mu’amala, da

tunanin mutane. Talauci na xaya daga cikin manya-manyan dalilan

yaxuwar munanan xabi’u da ayyukan alfasha, kamar sata da zina da

kisan rai.

Talauci na xaya daga cikin abubuwan da ke yin karen-tsaye ga

tarbiyya. Da yawa daga `yan matan da ke yin talla a cikin kasuwa ko a

tashar mota ko a gidajen mai, suna yi ne saboda talaucin iyayensu. Ba

wani abu ne voyayye ba cewa irin wannan tallace-tallace na daga cikin

abubuwan da ke gurvata tarbiyyar `ya`ya. Haka kuma, wani lokaci,

waxansu iyayen ba su iya kwava wa `ya`yansu, musamman `yan mata,

a lokacin da su ke yin abubuwan da ba su dace ba, kasancewar sun kasa

xauke wa `ya`yan nasu larurorin rayuwa.

Musulunci ya xauki matakan yin faxa da talauci, da magance

matsalolinsa ta hanyoyin da suka haxa da: (1) ilmantar da mutane

sahihiyar aqidar cewa arziqi daga Allah (Maxaukaki) ya ke; abin da

Allah Ya raba wa bawa, shi ne nasa, kuma wajibin kowane musulmi shi

ne ya yi haquri da musibar talauci, sannan ya xauki matakan kawar da

shi (2) neman tsari daga talauci ta hanyar addu’o’i (3) zaburar da

mutane a kan yin aiki, da neman na kai, da dogaro da kai, da kai-kawo

wajen neman abin rayuwa (4) haramta zaman banza, da barace-barace,

da maula, da sana’ar roqo (5) tabbatar da taimakekeniya a cikin

al’umma, ta hanyar tallafi daga iyali da `yan’uwa da dangi, da tallafi

daga mutanen gari, da kuma tallafi daga hukuma. 273

Daga cikin munanan aqidun da ke yin karan-tsaye, da barazana ga

tarbiyyar Musulunci a wannan zamani, akwai:

1. Aqidar Shi’a, wadda ke karantar da zagin sahabban Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da kafirta su, musamman Abubakar da Umar da Uthmān da Mu’āwiyah da Amr

ibnul ‘Āss da Mughīrah ibn Shu’ubah da Xalha da Zubair da

Abdur-Rahmān ibn ‘Auf da A’isha da Hafsah (Allah Ya yarda da

Page 155: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

155

su). Haka kuma, `yan shi’a na da aqidar cewa sahabban Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) gaba xayansu

sun yi ridda bayan rasuwar Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi) in ban da waxansu `yan tsirarun da ba su

wuce guda ashirin da biyar ba.

Waxanda ke bin aqidar shi’a na ganin cewa A’isha (Allah Ya

yarda da ita), matar Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi) ta yi zina, kuma ta cancanci zagi da la’ana, duk

da cewa Allah (Maxaukaki) Ya tsarkake ta; Ya wanke ta daga

zargin da munafukai suka yi mata; Ya yi kashedi ga waxanda ke

yaxa labarin; Ya qarya ta su; kuma Ya tabbatar da cewa waxanda

ke faxin haka ba mutanen kirki ba ne [Nur, 24:11-25]. `Yan shi’a na da aqidar cewa Abubakar da Umar da Uthmān

(Allah Ya yarda da su) ba halifofin Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi) ba ne, domin wai sun ha’inci Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), kuma wai sun qi zartar da wasiyyar da ya yi masu cewa wai Aliyyu ibn Abi Xālib

(Allah Ya yarda da shi) shi ne zai zamanto halifa a bayansa. Bayan

wannan, `yan shi’a sun soki Abu Hurairah (Allah Ya yarda da shi),

kuma sun zarge shi da cewa wai yana qirqiro hadisan qarya. Amma

a nasu vangaren, `yan shi’a sun qirqiro hadisan qarya valo-valo

domin su kare munanan aqidunsu, da kaidinsu game da Musulunci

da musulmi; kuma suna da xabi’ar watsi da duk wani hadisin da ya

sava wa ra’ayoyin da suka gina addininsu a kai.

`Yan shi’a na ganin halaccin auren wacin gadi (auren mutu’a), da al’adar ba da aron farjin mace (i’āratul furūj), da halaccin jin

daxi da jaririyar da ke shan nono, da halaccin saduwa da mace a

duburarta, da ganin rashin wajibcin sallar Juma’a, har sai

Mahadinsu ya bayyana, da sauransu. Haka kuma, suna ganin

halaccin voye wa mutane gaskiyar abin da ke cikin zukatansu, tare

da bayyanar da savanin haka a fili, wai da sunan tuqiyyah. Bayan

wannan, `yan shi’a sun sava wa musulmin duniya a cikin

mas’alolin Alqur’ani, da rukunan Musulunci, da shugabanci. Suna

da aqidar cewa Alqur’anin da ke hannun Musulmi bai cika ba, wai saboda Abubakar da Umar da Uthmān da waxansu sahabbai (Allah

Ya yarda da su) sun yi qari da ragi a cikinsa. A wajen `yan shi’a,

Alqur’anin gaskiya yana hannun Mahadinsu, wanda ya shige rami

tun yana rarrafe, yau fiye da shekara dubu xaya, bai fito ba. A

da’awarsu, idan Mahadinsu ya fito, zai bayyanar da Alqur’anin

gaskiya. Amma a babin tuqiyya, `yan shi’a na karanta Alqur’anin

Page 156: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

156

da ke hannun sauran Musulmin duniya a halin yanzu, kuma suna

bayyana shi a cikin jama’a, sannan suna qaryar cewa ba su da wani

Alqur’ani savanin wanda ke hannun sauran Musulmi.

A vangaren rukunan Musulunci, `yan shi’a sun qara rukunin yarda da limanci, da kuma shugabancin Aliyyu ibn Abi Xālib da

Al-Hasan da Al-Husain (Allah Ya yarda da su) da sauran mutane

guda tara, waxanda suka ga damar zave daga zuriyyar Al-Husain, a

matsayin xaya daga cikin rukunan Musulunci/imani. Dangane da

shugabanci, `yan shi’a ba su yarda da halifancin Abubakar da Umar da Uthmān (Allah Ya yarda da su) ba. Hasali ma, suna xaukarsu

kafirai, kuma maciya amanar Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi). A wajen `yan shi’a, waxancan limaman nasu

guda goma sha biyu, su ne halifofin Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi). Kuma suna da aqidar cewa

limamansu guda goma sha biyu, suna da matsayin da ya fi na

kowane mala’ika ko Annabi a wajen Allah; kuma wai sun san

gaibu; kuma ba su yin kuskure, ba su rafkannuwa; ba su mantuwa;

sannan kuma, ba su mutuwa sai lokacin da suka so.

Bugu da qari, `yan shi’a na da xabi’ar fakewa a qarqashin

da’awar son mutanen gidan Manzon Allah (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi) domin ganin sun yaudari mutanen da ba su da

ilmin sharrin addinin shi’a, ta yadda ba za a yi saurin fahimtar

bala’in da ke tattare da su ba. Yana daga hanyoyin da su ke bi

wajen yaudarar mutane, xabi’ar bayyana cewa wai an zalunci Nana Fāximah (Allah Ya yarda da ita), aka hana ta gadon dukiyar

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi); da kuma xabi’ar bayyana baqin ciki a ranar āshura, wato goma ga

watan Muharram, wai don tunawa da ranar da aka yi wa sayyidina Husain ibn Abi Xālib (Allah Ya yarda da su) kisan gilla, duk da

cewa su ne suka yi masa alqawarin qarya, kuma suka gayyace shi zuwa Kūfa, sannan, suka bar shi a hannun maqiyansa. Abin

mamaki shi ne, `yan shi’a na kururuta maganar gadon Fāximah ce

kawai, amma ba su yin maganar gadon matan Manzon Allah (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi), da kuma sauran

`yan’uwansa daga vangaren mahaifinsa, tun da dai suna da gado a cikin dukiyar, kamar yadda Fāximah ta ke da shi. Mene ne dalilin

da ya sa `yan shi’a ba su yin magana a kan gadon waxannan, sai dai na Fāximah kawai?

Bala’i da fitinar `yan Shi’a ba su qyale kowane Musulmi ba,

domin kuwa har Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

Page 157: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

157

gare shi) ma bai tsira ba. Littafansu na cike da maganganun rashin

kunya da rashin mutuntawa ga Manzon tsira (tsira da amincin Allah

su tabbata a gare shi). Misali, ya zo a cikin littafin

na As-Sayyid Husain Al-Musawiy, wanda `yan Shi’a

suka kashe daga baya, kamar yadda suka kashe Musa Al-Musawiy da Ahmad Al-Kātib saboda sun tona masu asiri, cewa: (i) Manzon

Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kalli Zainab

bint Jahash (Allah Ya yarda da ita) tana wanka tsirara, har ta ba shi sha’awa, kafin Zaid ibn Hārithah (Allah Ya yarda da shi) ya sake

ta; (ii) Aliyyu (Allah Ya yarda da shi) ya zauna a kan cinyar Nana

A’isha (Allah Ya yarda da ita), kuma da ta yi masa magana, sai

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce

mata kada ta cutar masa da xan’uwa; (iii) Aliyyu (Allah Ya yarda

da shi) ya kwanta a tsakanin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita); (iv)

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) na

sumbantar Nana Faxima (Allah Ya yarda da ita), kuma ya sanya fuskarsa a tsakanin nononta; (v) za a qona al’aurar Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) saboda ya yi kwanciyar aure da Nana A’isha (Allah Ya yarda da ita); (vi)

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya

voye wasiyya game da shugabancin Aliyyu (Allah Ya yarda da shi)

saboda tsoron Abubakar da Umar (Allah Ya yarda da su). Domin

qarin bayani, a karanta na As-Sayyid

Husain Al-Musawiy, da na Abu Khalīfah

Aliyyu ibn Muhammad Al-Qudaibiy, waxanda dukkansu malaman

shi’a ne a lokacin da suka rubuta littafan.

Babu shakka, waxannan miyagun aqidun shi’a na karan-tsaye

ga tarbiyyar al’ummar musulmi, domin kuwa ta wace hanya

kyakkyawar tarbiyya za ta samu ga `ya`yan da suka taso a kan

aqidar cin mutuncin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi), ko watsi da hadisan Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi), ko zagin sahabbai da qudurce

cewa sun yi ridda, ko zagin A’isha (Allah Ya yarda da ita) da

qudurce ta yi zina, ko auren mutu’a, ko ba da aron mace domin a

kwana da ita?

Saboda munin aqidar shi’a da haxarinta ga Musulmi, malamai

sun ba da fatawoyi iri-iri a kansu. A cikin littafin

, Dokta Ibrahim ibn `Aamir Ar-Ruhailiy, ya ciro

Page 158: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

158

fatawoyin malamai fiye da ashirin dangane da `yan shi’a. Daga

ciki: (a) An tambayi Imām Mālik ibn Anas (Allah Ya jiqan shi)

dangane da waxanda ke zagin sahabban Annabi (tsira

da amincin Allah su tabbata a gare shi), sai ya ce:

.

[Ba su da rabo a cikin Musulunci]

Kuma an ruwaito ya ce:

[Kada ku yi masu magana, kuma kada ku yi ruwayar (Hadisi)

daga gare su, domin suna yin qarya (a matsayin addini)]

(b) Imām Shā’fi’i (Allah Ya jiqan shi ) ya ce:

[Daga cikin waxanda ke bin son zuciyarsu, ban ga waxanda suka kai Rāfidah (masu zagin sahabbai) qarya da shaidar zur a

cikin da’awarsu ba]

(c) Al-Qāsim ibn Salām (Allah Ya jiqan shi) ya ce:

[Na zauna da mutane (dabam daban), kuma na tattauna da `yan

falsafa, amma ban ga qazamai, kucakai, masu raunin hujja, kuma wawaye ba, kamar Rāfidah (masu zagin sahabbai)]

(d) An tambayi Imām Ahmad ibn Hanbal (Allah Ya jiqan

shi) game da wanda ya zagi Abubakar da Umar (Allah

Ya yarda da su), sai ya ce:

[Ina ganin ya fita Musulunci]

(e) Ibn Taimiyyah (Allah Ya jiqan shi) ya ce:

[Babu waxanda suka kai `yan shi’a sharri da jahilci da zalunci da

kusanci ga kafirci da fasiqanci da savon Allah, daga cikin dukkan

qungiyoyin bidi’a da vata waxanda ke dangantuwa zuwa

Musulunci]

Page 159: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

159

Duk da irin munin aqidun shi’a, da fatawoyin da malaman farko

suka ba da a kansu, sai ga wani matashin xariqar tijjaniyya daga

Kaduna yana bayyana cewa wai `yan shi’a ba su zagin sahabbai,

kuma ma wai idan ma sun zagi sahabbai, ba a ga suna yin maulidi

ba, saboda son Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi)? Ya faxi wannan maganar a cikin lakcar da ya gabatar wa

`yan shi’a a garin Zaria, a lokacin taronsu na makon haxin kai,

kuma ya maimaita irin wannan mummunar magana a xakin taron

musabaqar Alqur’ani wanda ke Kinkinau, Kaduna, a wajen taron

qara wa juna ilmi dangane da ganin wata da haxin kai, a ranar Asabar, Rabi’uth-Thāni 2, 1430 (March 28, 2009). A nan take,

kusan dukkan mahalarta taron, waxanda suka haxa da shaihunnan

Tijjaniya, suka yi Allah wadai saboda qaryar da ya sharara. Bayan

shi, a cikin tafsirin Ramadan na shekarar Hijira 1429, da a ke sanya

wa a NTA, Zaria, daga wata zawiyyar Tijjaniyya, a Tudun Wada,

Zaria, wani matashin da a ke yi wa zaton wayayye ne, ya bayyana

cewa aqidodin shi’a wai sahihai ne, kuma wai ba su da matsala.

Abin da ya xaure wa mutane kai shi ne: shin waxannan matasan

tijjaniyya sun fi shehunnansu ilmi ne? Ashe babban Shehi bai yi

kaca-kaca da `yan shi’a ba, a cikin tafsirin Ramadan na shekarar

1428 da 1429? Ashe `yan shi’a ba su yi barazanar kashe wani

Shehin da ke yin tafsiri a Chikaji, Sabon Gari, Zaria ba, saboda ya

bayyana sharrinsu, da bala’in da ke cikin aqidunsu? Ko kuma sun fi

shehunnansu bincike ne game da aqidar shi’a? Ko kuwa sun raina

shehunnansu ne? Anya, babu wata alaqar sirri da ke tsakanin

waxannan matasan tijjaniya da `yan shi’a? Ko kuwa dai duk a

babin haxa qarfi da qarfe ne domin a yaqi Ahlus-Sunnah (`yan

Izala, Salafiyyah)? Shi dai matashin tijjaniyyar da ke Kaduna an

fahimci cewa an turo shi ne domin ya qalubalanci babban Shehi,

kuma ya share fagen zama halifan tijjaniya idan ya rayu bayan

rasuwar babban Shehi, tun da dama waxanda ke xaukar nauyin

yaxa karatunsa abokan hamayyar babban Shehin ne. Shi yasa ya ke

ta yin vavatu da qarerayi dabam daban, da tavargaza iri-iri, a

rediyo, don ya ci kasuwar muridai, kuma ya bayyanar da

matsayinsa a cikin tijjaniyyar.

Shi kuwa matashin Zaria, muna zargin cewa son zuciya ne

kawai ya ke damunsa, da baqar qiyayya ga Sunnah, da mummunar

hassada ga Ahlus-Sunnah, domin kuwa ya daxe yana faxin cewa

kalmar ko isxilahin (aqida) ba a san ta ba a zamanin

Page 160: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

160

magabata. A cewarsa, Wahabiyawa ne, wato, `yan Izala, suka fara

amfani da kalmar aqida. Ba domin hassadar da ya ke yi wa Ahlus-

Sunnah ba, mene ne yasa zai ce: `yan shi’a na da

(sahihiyar aqida), bayan kuwa ya ce kalmar sabon isxilahi ne

da Wahabiyawa suka qirqiro? Kuma shin da gaske aqidar `yan

shi’a sahihiya ce a wajensa? Dangane da isxilahin , shin

gaskiya ne cewa magabata ba su yi amfani da shi ba? Mene ne zai

ce game da waxannan littafai: na Abu Yālā; da

na Al-Lālakā’iy; da na Ibn Hanbal; da

na Abu Uthmān As-Sābūniy; da

na Abu Bakr Al-Ismā’īliy; da na Ax-Xahhāwiy; da

na Ibn Qudāmah; da na As-Safārīniy?

Marubutan waxannan littafai ba su yi amfani da isxilahin aqida ba?

Ko kuwa ba su a cikin magabata? Ashe ba shi ne ya ke da’awar

cewa yana karanta littafan Ibn Taimiyyah, da littafan Ibnul Qayyim, kuma ya mallaki kaset-kaset xin Nāsiruddīn Albāni da

rubuce-rubucensa domin ya bayyana kurakuransu ba? Mene ne ya

sa bai karanta littafan shi’a domin ya fahimci munin aqidunsu ko

kuma sahihancinsu ba? Allah Ya shiryar da mu.

2. Aqidar Khawārij, waxanda suka yi tawaye ga Aliyyu ibn Abi Xālib

(Allah Ya yarda da shi) saboda yarda da sulhun da ya yi a tsakaninsa da Mu’awiyah ibn Abi Sufyān (Allah Ya yarda da su).

Khawārij sun kafirta waxanda suka yarda da wannan sulhu; sun

zarge su da yin ridda; suka yi da’awar cewa Aliyyu ibn Abi Xālib

da A’isha da Xalha da Zubair da Amr da Abu Musa sun yi ridda;

kuma suka xaura yaqi da sayyidina Aliyyu (Allah Ya yarda da shi);

sannan suka halatta wa kansu zubar da jinin wanda duk ya sava wa

da’awarsu. Aqidar khawārij ta ginu ne a kan kafirta musulmi a dalilin

manyan zunubai, da yin tawaye ga shugabannin musulmi, da

janyewa daga cikin jama’a. Ana gane khawarijawa ta hanyoyi guda

uku: (1) kafirta musulmi saboda sun aikata manyan zunubai

waxanda ba su kai matsayin shirka ba (2) yin tawaye ga

shugabanni, da yin fito-na-fito da su (3) kare aqidunsu ta kowace

hanya, da ganin halaccin zubar da jinin musulmi, wai da sunan

jihadi ko gusar da abin qi.

Page 161: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

161

Daga cikin siffofin khawārij a wannan zamani, akwai: yin

tawaye ga shugabanni, da yin fito-na-fito da su; da tsanani a cikin

addini; da zurfafawa a cikin ibada; da raina manyan malamai, da

wulaqanta su, da zarginsu da munafunci, da kuma ganin halaccin

kashe su; da qarancin karatun addini da rashin aiki da fahimtar

magabata na qwarai; da kafirta musulmi saboda zunubin da bai kai

matsayin shirka ba; da yin kira zuwa ga jahilci; da kushe karatun

boko ko kuma ganin kafircin karatun boko, da kira zuwa ga

janyewa daga aikin gwabnati; da ganin halaccin qwace dukiyar

musulmi; da ganin halaccin kashe duk wanda bai yarda da aqidarsu

ba; da kuma ganin wajibcin yin hijira zuwa gare su.

Babu shakka, idan yaro ya taso a kan wannan mummunar aqida,

zai zamanto barazana ga tarbiyyar `ya`yan musulmi. Haka kuma,

waxanda ke da aqidar khawarijanci a yau, na jawo wa musulmi

gori, da ci baya, da kuma qauyanci.

3. Aqidar Istishrāqiyyah, wato, masu bin Orientalism, waxanda

galibinsu ba musulmi ba ne, amma suka karanta addinin musulunci,

bisa mummunar manufar haifar da shubuhohi game da fahimtar

addini; da sanya shakku game da aikin Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) na isar da Alqur’ani da

Sunnah; da jefa tunanin cewa tanade-tanaden musulunci ba za su

iya wadatar da mutanen wannan zamani ba saboda ci gaba da

wayewar da aka samu a duniya; da jefa wa musulmi shakku

dangane da sahihancin hadisan Manzon Allah (tsira da amincin

Allah su tabbata a gare shi); da qoqarin amfani da tsukakken tunani

da taqaitacciyar qwaqwalwa wajen tabbatar da inganci ko rashin

ingancin hadisai; da zargin manyan malaman hadisi, irin su Imam

Az-Zuhri, da cewa sun qirqiro hadisan qarya; da zargin sarakuna

da halifofin musulmi cewa sun sanya malamai sun qirqiro hadisan

da za su goyi bayan zaluncinsu; da sauransu.

Waxanda ke da irin wannan mummunar kaidi game da

karantarwar musulunci sun samu nasarar gurvata tunanin irin su Xāha Husain (a qasar Masar), da Abdullah Chakralawi da Ghulām

Ahmad Pervaiz (a India) da Zia Gogelup (a Turkiyyah). A dalilin

haka, sai aqidar istishrāqiyya ta shigo cikin qasashen musulmi, ta

hanyar rubuce-rubucen da irin waxancan malamai suka yi bayan

sun tasirantu da ra’ayoyin mustashriqai irin su Sprenger, da

Edward, da Salisbury, da Houdas, da Goldziher, da Wensinck, da

Watt, da Schacht, da Robson.

Page 162: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

162

Aqidar istishraqiya na da mummunar tasiri a kan tarbiyyar

`ya`yan musulmi, musamman a vangaren aqidarsu da tunaninsu

game da Shari’ar Musulunci, kamar yadda mu ke gani a wannan

zamani. Haka kuma, mummunar tasirin aqidar istishraqiya ya

sanya waxansu `yan bokon zamani na yin dakon aqidar , wato,

aqidar amfani da sakamakon binciken kimiyyar zamani a matsayin

ma’aunin inganci ko raunin Hadisi, zuwa cikin Musulmi.

4. Aqidar Qala-qato, wadda ta qunshi da’awar amfani da Alqur’ani

kaxai, a cikin dukkan wani abin addini, tare da watsi da hadisi, da

kuma sukar littafan fiqihu. `Yan qala-qato na da’awar cewa Allah

(Maxaukaki) Ya umurci musulmi da yin riqo da Alqur’ani kawai,

kuma babu inda aka ce a yi amfani da hadisi ko kuma ra’ayin

waxansu mutane. Wannan ya sa a ke kiransu da suna `yan qala-qato, ko kuma qur’aniyyun, wato, waxanda ke da’awar riqo da

Alqur’ani zalla, kuma su ke xaukar hadisai da littafan fiqihu a

matsayin maganar wani qato.

`Yan qala-qato ba su amfani da wani hadisin Manzon Allah

(tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai idan ya yi dai-dai

da zahirin ayar Alqur’ani; kuma sun sava wa dukkan musulmin

duniya a wajen tauhidi, da sallolin farilla da na nafila, da zakka, da

azumin farilla da na taxawwu’i, da aikin hajji, da aure, da saki, da

idda, da hukunce-hukuncen tsarki, da jana’iza, da sallar idi, da

sallar juma’a, da sauransu.

`Yan qala-qato na ganin cewa haramun ne a ci kifi idan ba a

yanka ba; kuma suna ganin cewa wajibi ne macen da ke yin haila ta

yi salla da azumi. Waxansu daga cikin `yan qala-qato ba su yarda

cewa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana da

sahabbai (Allah Ya yarda da su) ba, in ban da Zaid (Allah Ya yarda

da shi), kasancewar shi kaxai ne Allah (Maxaukaki) Ya ambaci

sunansa valo-valo a cikin Alqur’ani.

Wannan mummunar aqida, ta ci karo da aqidar Musulunci,

kuma ta sava wa abin da musulmin duniya suka fahimta. Malamai

da yawa sun kafirta waxanda ke da irin wannan bamagujiyar aqida.

Misali, Muhammad ibn Nasr Al-Marwazi, a cikin As-Sunnah, ya ce

waxanda ke raddin sahihan hadisan Manzon Allah (tsira da

amincin Allah su tabbata a gare shi) sun fita daga cikin jama’ar musulmi; Al-Ājurri, a cikin Ash-Sharī’ah, ya ce kasancewar ba za a

iya fahimtar Alqur’ani ba sai ta hanyar Sunnah, waxanda ke qin yarda da Sunnah, sun yi ridda; Ibn Hazm, a cikin Al-Ihkām fi

Page 163: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

163

Usulil Ahkām, ya kafirta su; Ibn Taimiyyah, a cikin Al-Wasiyyatul Kubrah da Ibn Daqīqil ‘Eid, a cikin Sharhul Ilmām, sun kafirta su;

As-Suyuxī, a cikin Miftāhul Jannah fil Ihtijāj bis Sunnah, ya ce

waxanda ke inkarin ingantattun hadisai, kafirai ne, kuma Allah (Maxaukaki) zai tayar da su tare da Fir’auna da Hāmān a ranar

qiyama.

Babu shakka, aqidar `yan qala-qato na yin barazana ga tarbiyyar

`ya`yan musulmi, musamman a Nijeriya, da qasar Nijer, kuma tana

dankwafe qwaqwalwar waxanda ba su san inda aka sa gaba ba,

sannan, tana nisantar da mutane daga Musulunci gaba xaya, ba tare

da sun sani ba.

5. Aqidar , wato, aqidar kore bambanci a tsakanin Musulunci

da kiristanci ko yahudanci (interfaith) bisa hujjar cewa mabiyansu

sun yarda da Allah Ubangiji a matsayin abin bauta, kuma suna

iqirarin bin littafin da aka saukar daga sama. Wannan mummunar

aqida ta shigo Nijeriya ta hanyar waxansu matasa masu kishin

addini, amma ba tare da ilmi ba. Da yawansu ba su yi karatun

addini ba sai ta hanyar jaridu da mujallu da littafan da aka fassara

addinin Musulunci bisa fahimtar abokan gaban Musulmi.

Mabiya wannan aqida na bi lungu-lungu don tallata

bamagujiyar aqidarsu, wai da sunan qoqarin wanzar da zaman

lafiya, ko sasantawa a tsakanin Musulmi da mabiya addinin kirista.

Domin abin na su ya yi masu armashi, qungiyoyin da ke tallata

wannan varna suna zaven shugabanni guda biyu: Imam, domin ya

wakilci Musulmi, da Pastor, da ke wakiltar kirista. A galibi, wanda

a ke kiransa Imam xin, bai yi karatun a zo a gani ba game da

addinin Musulunci, kuma bai san makircin maqiyan Musulunci ba.

Malaman Musulunci sun ba da fatawar haramcin wannan

yunquri, da haxarin shiga cikin wannan baqar harka, sai dai idan za

ta samar da damar tattaunawar ilmi a tsakanin Musulmi da kirista

domin a nuna masa varnar da kiristanci ya qunsa. Abin mamaki, a

cikin `yan dakon wannan bamagujiyar aqida a Nijeriya, akwai

wanda a ke yi wa zaton ilmi da wayewa a nan Kaduna, shi kuwa

shugaban nasu, dama can bai da ilmin a zo a gani.

Aqidar daidaituwar mabiya addinai dabam daban na da

mummunan tasiri a kan tarbiyyar al’umma. Idan yaro ya taso a

kanta, ko kuma ya yi karo da waxanda ke yaxa ta, za a cire masa aqidar Al-wala’u wal barā daga zuciyarsa, duk da cewa tana daga

cikin abubuwan da tauhidi ke lazimta wa Musulmi.

Page 164: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

164

3. Savani a tsakanin iyaye ko kuma rabuwar aure 274

274

Aure aya ce daga cikin ayoyin Allah, kuma ni’ima ce daga cikin

ni’imominSa. An shar’anta aure a Musulunci, aka qarfafe shi, aka

kwaxaitar da yin shi, aka hana yin tabattul (aqidar rashin yin aure

saboda a samu damar bauta wa Allah sosai), kuma aka bayyana cewa

barin yin aure domin a samu damar yin ibada ya sava wa Sunnar

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).

Aure na da manufofi da fa’idodin da suka haxa da: (1) biyayya ga

Allah (Maxaukaki) da nisantar savo (2) samun ladan ciyar da iyali (3)

kamewa daga zina, da tsare mutunci (4) samar da iyali da taimakawa

wajen yawaita al’umma (5) xorewar jinsin xan Adam (6) samun xa na

qwarai da zai yi wa iyayensa addu’a bayan mutuwarsu (7) samun

natsuwa da sukuni da kwanciyar hankali (8) biyan buqatar sha’awa ta

xabi’a (9) samun ladan yin tarbiyya da xaukar xawainiyar `ya`ya (10)

kai wa ga matsayin kamala a cikin mutane (11) dacewa da abin da

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ke so (12)

raya Sunnar Annabawa (13) dacewa da samun taimakon Allah idan aka

yi aure saboda kange kai daga zina.

Abubuwan lura a wajen zaven abokiyar zama su ne: (1) riqo da

addini [Baqarah, 2:221] (2) sahihiyar aqida [Tirmidhi] (3) kyawawan

xabi’u [Tirmidhi] (4) iya soyayya da kuma haihuwa [Ahmad da Abu

Dawud] (5) budurci, matuqar babu wata maslahar da za ta sa a fifita bazawara [Bukhari] (6) kyau [Nasā’i da Ahmad; Muwaxxa Mālik;

Ahmad]. A wajen zaven abokin zama, mace ta yi tarayya da namiji a

cikin mafi yawan waxannan xabi’u. Don haka, wajibin iyaye ne su

zava wa xiyarsu miji na qwarai bisa lura da waxannan siffofi.

Yana daga abubuwan da aka hana a cikin neman aure: (1) kaxaita da

wadda za a aura, ko yin tafiya tare da ita, ko fita yawon shaqatawa ba

tare da wani muharrami ba, ko da kuwa an biya sadaki [Bukhari da

Muslim; Ahmad da Tirmidhi] (2) tava jikin wadda za a aura, ko rungumarta, ko sumbantarta, ko da an biya sadaki [Xabarāni] (3)

maganganun batsa a wajen hira, ko aikawa da saqon da ke xauke da

maganganun batsa ko hotunan tsiraici ko sakarci ko motsar da sha’awa

ta cikin wayar tafi da gidanka (4) kwanciya (jima’i) da wadda za a aura

tun kafin a xaura auren, ko da an biya sadaki.

Fatawar da ke nuna cewa idan aka amince za a aurar da yarinya ga

mutum, kuma iyayenta ko wakilansu suka karvi sadaki, wannan

saurayin wai zai ci gaba da sha’aninsa da ita, har ma da yin jima’i,

fatawa ce da aka ginata a kan kuskure, da rashin la’akari da tasirin urf,

Page 165: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

165

wato, al’adun da ba su yi karo da nassosin addini ba, a cikin

mu’amaloli. Duk mutanen da urfinsu ya nuna cewa ba a xaukar aure ya

tabbata a tsakanin mace da namiji har sai an tara jama’a don xaura

auren, dole ne a jinkirta zuwa wannan lokaci. Maganar cewa tun da an

kammala dukkan sharuxxan aure, ta hanyar biyan sadaki, bayan

waliyyai sun yarda za su ba da `yarsu kuma saurayi da budurwa sun

daidaita kansu, sannan an karvi sadaki a gaban a qalla mutane biyu

zuwa uku, aure wai ya tabbata a tsakaninsu, kasancewar taron xaurin

aure al’ada ce kawai, magana ce mai tsananin rauni. Daga cikin

abubuwan da ke nuna rauninta shi ne, su kansu mutane ba su yarda

cewa abubuwan da aure ke lazimtawa a tsakanin ma’aura sun tabbata a

cikin irin wannan shiri ba. Misali, idan saurayin ya mutu kafin ranar

xaura aure, ko kuma ita budurwar ta mutu, ba za a yarda wanda ke da

rai a cikinsu ya ci gadon xayan ba. Haka kuma, idan aka samu canjin

ra’ayi a tsakaninsu, saurayin ba zai ce ya fasa auren ba ta hanyar rubuta

takardar saki ko furtawa, ko kuma ita budurwar ta yanke alaqarta da shi

ta hanyar khul’i, domin za a danganta hauka ga duk wanda ya yi hakan

a cikinsu, kasancewar mutane ba su xaukar cewa sun zama ma’aurata.

Don haka, waxanda ke ba da irin wannan fatawar su ji tsoro.

Saboda muhimmancin aure, da kuma babban tasirinsa a kan

tarbiyyar `ya`ya, Musulunci ya xauki matakai na dawwamar da aure, a

tsakanin miji da mata, matuqar babu wata larurar da ta bijiro. Daga

cikin hanyoyin da Musulunci ya bi domin dawwamar da aure, akwai:

(1) fifita addini da kyakkyawar xabi’a a wajen zaven miji/mata (2)

halatta kallon wadda a ke son a aura domin kada a yi kitso da

qwarqwata (3) sharxanta yardar wadda za a aura, matuqar ta balaga (4)

hana wa miji neman kamala daga wajen matarsa, da bayyanar da

muhimmancin yin haquri da juna (5) halatta wa mutane shiga cikin

al’amarin ma’aura domin yin gyara da sulhu a tsakaninsu, idan akwai

buqatar haka (6) halatta qarya (ba yaudara ba) a tsakanin ma’aura

domin zamantakewa ta qara danqo (7) wajabta wa ma’aurata

zamantakewa kyakkyawa a tsakaninsu, ta hanyar bayyana wa

kowannensu haqqoqinsa, da kuma haqqoqin da ke kansa.

Haqqoqin ma’aurata sun kasu gida uku: waxanda suka yi tarayya a

ciki; da waxanda miji ke da su a kan matarsa; da waxanda mace ta ke

da su a kan mijinta. Haqqoqin da suka yi tarayya a kai guda uku ne: (1) haqqin jima’i da jin daxin juna [Nisā, 4:20-21; Baqarah, 2:223;

Bukhari] (2) haqqin gadon dukiyar wanda ya riga mutuwa [Nisā, 4:11-

12] (3) haqqin dangantuwar `ya`ya [Bukhari da Muslim].

Page 166: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

166

Haqqoqin mace a kan mijinta sun haxa da: biyan sadaki [Nisā, 4:4];

xaukar nauyi da xawainiya, da ciyarwa da tufatarwa, da kula da lafiya, da wajen zama [Baqarah, 2:223; Nisā, 34]; kyakkyawar mu’amala

[Nisā, 4:19]; jima’i, gwargwadon ikonsa da yanayinsa [Bukhari da

Muslim]; rashin duka, sai in ya zama dole [Nisā, 4:34; Bukhari]; kiyaye

sirrin jima’i [Abu Dawud]; adalci a tsakaninta da kishiyarta [Nisā,

4:129; Abu Dawud]; karantar da ita addini [Tahrīm, 66:6; Bukhari];

tsare mutunci da rashin cin mutunci [Bukhari da Muslim]; rashin

watsarwa ko wofintarwa [Ahmad da Muslim].

Haqqoqin miji a kan matarsa sun haxa da: samar masa da sukuni da natsuwa a cikin gida [A’arāf, 7:189; Rum, 30:21]; yarda da

shugabancinsa ga gida [Nisā, 4:34]; biyayya cikin duk abin da ba savon

Allah ba [Hākim]; biya masa buqatar jima’i, matuqar babu larurar da

za ta hana [Tirmidhi]; rashin barin wani ya shiga gidan idan mijin ya

hana [Bukhari da Muslim]; rashin fita daga gida ba tare da izini ba [Ahzāb, 33:33]; yin masa abinci, da gyara shimfixarsa, da yin masa

dukkan nau’o’in hidama, gwargwadon iko, kuma gwargwadon urf [Ahmad; Bukhari da Muslim]; taimaka masa da nuna masa goyon baya

da qarfafa gwiwa a cikin dukkan abubuwan da Shari’ah ba ta hana ba [Nasā’i]; gode wa qoqarinsa, da rashin matsawa a kan buqatun da babu

larura [Bukhari da Muslim; Nasā’i; Hākim]; rashin yin azumin nafila

ba tare da izininsa ba, matuqar bai yi tafiya ba [Bukhari da Muslim].

Allah (Mai tsarki da xaukaka) Ya albarkaci wannan al’umma ta

hanyar ba ta cikakkiyar Shari’ah, da dokoki, da tsare-tsare waxanda ke

yin mata jagoranci a cikin dukkan al’amura, kuma su ke ba ta mafita

daga kowace irin matsala. Kasancewar savani a tsakanin ma’aura wani

abu ne na xabi’a, kuma dole ya auku, a lokaci zuwa lokaci, Shari’ar

Musulunci ta tanadar wa Musulmi hanyoyin warware matsalolin aure,

ko kuma savani a tsakanin ma’aura: idan matsalar daga gefen matar ce,

an tsara wa miji irin matakan da zai bi domin ganin ta dawo kan hanya kuma ta yi masa xa’a [Nisā, 4:34]; idan bijirewar ko tawayen daga

vangaren miji ne, an tsara wa mace hanyar da za ta bi wajen samar da gyara a tsakaninsu [Nisā, 4:128]; idan kuwa kowannensu na da hannu a

cikin bijirewar, ko kuma yin tawayen ga juna, kuma warware matsalar

a tsakaninsu ya ci tura, Allah (Mai tsarki da xaukaka) Ya ba da

umurnin a samu wakilai daga vangarorin ma’aura don zaman sulhu [Nisā, 4:35].

Bijirewa ko tawaye daga mace na xaukar fuskoki mabambanta: (1)

qin yin ado ga miji a lokacin da ya ke buqata; (2) qin zuwa shimfixarsa

ko yarda da shi a lokacin da ya ke buqatar jima’i; (3) fita gida ba tare

Page 167: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

167

da izininsa ba; (4) qin yin masa hidima a gida; (5) qin kula da

`ya`yansa; (6) sakaci wajen bautar Allah (Mai tsarki da xaukaka) da

kiyaye dokokin Musulunci. A vangaren miji, tawaye na xaukar: (1)

girman kai a gare ta, da qin kiyaye haqqoqin da Allah (Mai tsarki da

xaukaka) ya xora masa, dangane da ita; (2) zaluntarta ta hanyar duka

ko zagi ko cin mutunci ko qin jima’i ko hana ta abinci da sauran

buqatun larura; (3) kau da kai daga gare ta; (4) qin magana da ita, da

sauransu.

Duk da waxannan matakai, akwai yiwuwar a samu savani a tsakanin

ma’aura, kuma akwai yiwuwar wannan savani ya haddasa rabuwar

aure. Savani a tsakanin iyaye, da kuma rabuwar aure, suna da

mummunar tasiri a kan tarbiyyar `ya`ya. Lallai ne iyaye su yi qoqarin

ganin sun magance savanin da ke tsakaninsu, ba tare da `ya`yansu sun

sani ba. Haka kuma, ya kamata su xauki dukkan matakan da suka dace

domin ganin rabuwar auren ba ta auku a tsakaninsu ba. Rabuwar aure a

tsakanin miji da mata na daga cikin abubuwan da ke kawo matsala ga

`ya`yan da aka haifa.

Galibi, savanin da ke aukuwa a tsakanin ma’aura na da dalilai guda

biyar: (1) yanayi da xabi’ar zuciya, ta yadda wani lokaci mutum zai

samu canjin tunani game da abokin zama; soyayya ta koma qiyayya,

qauna ta koma rashin qauna (2) rashin ikhlasi, da rashin tsarkake

zuciya game da alaqar aure, da rashin xaukar aure a matsayin ibada (3)

sakacin mace a vangaren tattalin miji da haquri da qana’a da karvar

gyara (4) matsala daga miji, a dalilin rashin adalci a tsakanin mata, da

rashin kishi, da rashin kulawa da tarbiyyar `ya`ya, da rashin zama a

gida (5) tsadar rayuwa, da rashin cikakken abin yi.

Idan savani ya auku a tsakanin iyaye, kuma iyayen suka bari

`ya`yansu suka fahimci akwai wannan savani, musamman idan

al’amarin ya kai su ga cacar baki ko zage-zage ko cin mutuncin juna ko

dambe ko cin kwalar riga ko dukar mace a gaban `ya`yan, wannan zai

sanya `ya`yan su rasa kwanciyar hankali ko kuma su xauka cewa haka

ya kamata a gina rayuwar aure. Ke nan, lallai iyaye su nisanci yin

savani a gaban `ya`yansu ko kuma tattauna matsalolin da suka shafi

zamantakewarsu a gaban `ya`yan. Yawan yin savani a tsakanin

ma’aura yana hana iyaye samun natsuwa da kwanciyar hankalin da za

su yi tarbiyyar `ya`yansu yadda ya kamata.

Mutuwar aure musiba ce ga `ya`ya, domin kuwa za su iya shiga

mummunan hali, kasancewar mahaifiyarsu ba ta a cikin gidan, kuma ba

lallai ne a dace da wadda za ta kula da su, ta xauki amanar yin masu

tarbiyya ba yadda ya dace. Haka kuma, idan ma `ya`yan na hannun

Page 168: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

168

4. Da’awar kare `yancin mata, da kururuta haqqoqin

yara275

uwarsu ce, ko suna hannun dangin uwa, akwai yiwuwar su rasa

cikakkiyar tarbiyya, kasancewar ubansu na nesa da su; ballantana kuma

idan rashin mutunci ya shiga a tsakanin ma’aura, a lokacin rabuwa, ta

yadda uban zai yi watsi da al’amarin `ya`yansa gaba xaya.

Dalilan da ke kawo mutuwar aure sun haxa da: (1) rashin fahimtar

manufar aure a Musulunci ko yadda a ke zamantakewar aure (2) auren

dole (3) rashin tattaunawa a tsakanin ma’aura (4) talauci da sauran

matsalolin rayuwa (5) rashin ba da muhimmanci ga rayuwar aure (6)

canjin tunani game da abokin zama ko rashin samun yadda a ke zato

daga abokin zama (7) rashin kula da haqqoqin aure (8) ha’intar abokin

zama, da rashin kamun kai (9) shaye-shayen barasa ko abubuwan da ke

gusar da hankali (10) cin mutuncin abokin zama, ko wulaqanta surukai

(11) yawan duka ko zagi (12) rashin sanya ido daga iyaye ko kuma

rashin tarbiyya tun daga gida, kafin aure (13) rashin sanin hanyoyin

warware matsala idan ta auku (14) rashin agaji daga al’umma (15) son

kai, ko bin son zuciya a tsakanin ma’aura.

Ya kamata iyaye su ji tsoron Allah (Maxaukaki) game da tarbiyyar

`ya`yansu, kuma su danne zukatansu, su yi haquri da juna, su kyautata

wa juna, su kiyaye haqqoqin juna, kuma su riqa tuna makomar

tarbiyyar `ya`yansu. 275

Allah (Mai girma da xaukaka) Ya halicci namiji da mace a matsayin

vangare guda biyu na nau’in mutum, domin su yi tarayya wajen raya

duniya, kowannensu a bisa abin da ya kevanta da shi, kuma su yi

tarayya a cikin bauta wa Allah (Mai girma da xaukaka), ba tare da

bambanci a tsakaninsu ba a cikin tauhidi, da aqida, da haqiqanin imani

da miqa wuya, tare da sallamawa ga Allah; da ayyukan lada ko uquba;

da ayyukan kwaxaitarwa ko tsawatarwa; da ayyukan falala; da sauran

ayyukan wajibi. Haka kuma, an kevance wa kowannensu ayyukan da

suka dace da yanayinsa, domin a samu zaman lafiya da walwala da

kwanciyar hankali.

Ana cikin wannan hali, sai shaixan ya qawata wa mutane yin shirka

da Allah (Mai girma da xaukaka), da canza tsarin Allah, da yin zalunci

da varna a cikin qasa. Wannan ya sanya mace ta shiga cikin

mummunan hali, kuma ta fuskanci yanayi mai tsanani da mu’amala

mara kyau daga maza. Mace ba ta fita daga wannan halin qaqanikayin

ba, har sai bayan an aiko Manzon Allah (tsira da amincin Allah su

Page 169: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

169

tabbata a gare shi). Misali, kafin zuwan Musulunci: (1) Girkawa (Greek) na xaukar mace a matsayin bishiya mai guba; qazantar

shaixan; dalilin tashe-tashen hankula da rikice-rikicen duniya; kuma

hajar sayarwa (2) Romawa (Romans) na xaukar mace a matsayin

wadda ba ta da ruhi, kuma za a iya kashe ta bisa duk wata tuhumar da

aka yi mata; ana ladabtar da ita ta hanyar zuba mata tafasasshen mai a jikinta (3) Mutanen qasar Sīn (China) na ganin cewa mace ruwan zafi

ne mai wanke nasara da walwala, kuma ruwan najasa ce da ke tafiyar

da farin ciki da dukiya; ana gadon mace, kamar yanda a ke gadon

dabbobi; kuma za a iya rufe ta da ranta (4) Yahudawa (Jews) sun ce

mace tsinanniya ce kuma ita ce dalilin vacewa da halakar namiji, kuma

ubanta na da damar ya sayar da ita, sannan, yahudawa na xaukar duk

wadda ke cikin jinin al’ada a matsayin najasa (5) Hindu (mutanen qasar

India) na xaukar cewa munin mace da haxarinta sun fi mutuwa, da

guba, da wuta, da maciji, kuma suna ganin wajibcin qonata tare da

mijinta idan ya riga ta mutuwa (6) Farisawa (mutanen Iran) na ganin

halaccin auren muharramai, da yanke wa mace hukuncin kisa, ba tare

da wani dalili qwaqqwara ba; kuma da nisantar da ita daga mutane a

lokacin da ta ke yin jinin al’ada (7) Nasara (Kirista) na xaukar mace a

matsayin mutum wanda ba shi da ruhi, kuma an halicce ta ne don kawai

ta yi wa maza hidima; ita ce qofar da shaixan ya ke bi domin ya vata

mutane; kuma tana rusa dokokin Allah, ta sanya maza su fanxare wa

mahaliccinsu (8) Larabawa a lokacin jahiliyya suna wulaqanta `ya`ya

mata ta hanyar bizne su da ransu ko kuma su bar su da rai, amma a

cikin wulaqanci da qasqanci, kuma suna auren matan da iyayensu suka

bari, sannan ba su ba mace gadon komai daga cikin abin da iyayenta ko

mijinta ya bari.

Musulunci na zuwa, sai ya ruguje waxannan tsare-tsare na

maguzanci, kuma ya tabbatar da adalci ga `ya mace, ta hanyar dawo

mata da mutuncinta da martabar da aka halicce ta a kansu. Allah

(Maxaukaki) Ya tabbatar da cewa mace cikakken mutum ne, wadda ta

cancanci bauta wa Allah, da yabo da zargi, da lada da zunubi, da

aljanna da wuta, gwargwadon imaninta da ayyukanta na qwarai ko

munana. Haka kuma, an ba ta damar mallakar dukiya, da yin

kasuwanci, da cin gado, da `yancin yin kyauta ko barin wasiyya. Aka

wajabta mata neman ilmi, kamar yadda aka wajabta a kan namiji, aka

ba ta damar yin musharaka da maza a wajen sallar idi da halartar jam’i.

Musulunci ya wajabta biyan sadaki a gare ta kafin a aure ta, ya tabbatar

mata da haqqoqi a matsayinta ta uwa ko matar aure ko `ya. Bayan

wannan, Musulunci ya bayyana mata cewa a vangarorin shugabancin

Page 170: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

170

aure ko shugabancin al’umma, da annabta ko manzanci, da haila ko

jinin biqi, da xaukar ciki ko shayarwa, da rabon gado, da karvar shaida

a kotu, da sanya hijabi, tana da bambanci da namiji, bisa la’akari da

yanayin kowannensu, domin gudun kada ta xauka cewa sun yi

musharaka da tarayya a cikin kowane abu, ba tare da togaciya ba.

Musulunci ya nuna wa mace irin rawar da za ta taka, da

gudummuwar da za ta ba da wajen gina qaqqarfar al’umma.

Gudummuwar mace wajen gina al’umma na da fuskoki guda uku: (1)

haihuwa da tarbiyya domin samar da nagartattun tubalan gida al’ummar

da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) zai yi

alfahari da ita a ranar qiyama (2) samar da natsuwa da sukuni ga

mazajensu, da qarfafa wa mazajensu gwiwa a kan gwagwarmayar

rayuwa wadda ba ta sava wa manufar halitta ba (3) taimakon al’umma

a vangaren kare martaba da matsayin mata, ta hanyar ilmartarwa da

wakilci kyakkyawa, da shiga cikin ayyukan da suka dace da yanayinsu,

kamar likitanci, da jinya, da unguwar zoma, da karantarwa, da fannin

harhaxa magani.

Ganin irin matsayin da `ya mace ke da shi a Musulunci, da kuma

irin gudummuwar da mace za ta ba al’ummar musulmi, sai abokan

gaban Musulunci, musamman yahudawa da munafukai da sauran masu

mugun qulli da hassada da karkacewar tunani da fanxewar jima’i suka

fara xaukar matakin kawo varna a cikin al’amarin mace, domin su keta

suturar da Allah (Maxaukaki) Ya yi wa mace, kuma su tozarta ta, tare

da jawo mata hasarar duniya da lahira. Kuma suka kururuta `yancin

mata, wai da sunan kuvutar da su daga bautar da su ke yi a gidan aure.

Manufarsu ita ce:

1. `Yantar da mace daga ladubban Musulunci, da xaukar matakan

ganin ta yi tawaye ga dokokin Allah.

2. Watsar da hijabi, kamar yadda ya kasance a qasar Masar, a inda

mata suka jefar da hijabinsu a ranar 20/03/1919, kuma daga baya abin ya yaxu zuwa qasashen Turkiyya da Shām da Irāq, sannan, a

shekarar 1995, mata suka yi taron gangami na duniya a Peking,

domin su yi Allah wadai ga danniyar da a ke yin masu, da sunan

addini. Irin wannan farfaganda, da kiraye-kirayen shaixan, sun

sanya wa mata, musamman `yan boko, qyamar hijabi, kuma suna

xaukar sanya shi a matsayin alamar rashin wayewa.

3. Cuxanya a tsakanin maza da mata, da rashin kunya, da rashin

kamun kai, da qin yin auren wuri, duk da cewa ana yin zinace-

zinacen wuri.

Page 171: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

171

5. Hulxa da mutanen banza da kangararrun yara da

mutanen da suka shahara da sharri, da lazimtar wuraren

da ke vata tarbiyya, kamar gidajen sinima ko wuraren

kallon finafinai da qwallon qafa.276

4. Tawaye ga mazan aure, ta hanyar fita ba tare da iznin miji ba, da

yin yadda aka so, ba tare da kiyaye haqqoqin aure da matsayin miji

ba.

5. Qirqiro kundin mata, da neman kafa dokokin da ke wa Musulunci

karen-tsaye, wai da sunan kare haqqoqin mata. Irin waxannan

kundaye da qudurorin da munafukai da sauran abokan gaban

Musulunci ke qoqarin tabbatarwa sun haxa da: tabbatar wa mace

haqqin sakin mijinta, kamar yadda maza ke da ikon sakin matansu;

da tabbatar wa mace damar yarda ko qin yarda da duk matar da za

a auro a matsayin kishiya; da taqaita adadin iyalin kowane mutum

zuwa ga matarsa ta farko da `ya`ya guda huxu; da kuma samar da

rijistar ma’aurata wadda za ta ba da damar a bibiyi halin da

ma’aura ke ciki don tabbatar da cewa ba a sava wa kundin ma’aura

ba.

Bayan wannan, kasancewar addinin Musulunci ya lulluve `ya`ya da

goma ta arziqi, ya samar da tanade-tanaden da za su kyautata

al’amarinsu, kuma ya tabbatar masu da haqqoqi a kan iyayensu,

maqiya Musulunci da sauran `yan barandarsu, sun kai gwauro da mari,

don ganin sun vata tsarin zamantakewar iyali a Musulunci. Suna bin

hanyoyi dabam daban don ganin sun jefa ruxani a cikin zukatan

Musulmi game da dacewar tsare-tsaren Musulunci, da sahihancin

karantarwarsa, da kyawun tsari, da tattalin da Musulunci ya yi wa yara.

Daga cikin hanyoyin da suka xauka, akwai nuna kamar Musulunci wai

bai kare wa yara haqqoqinsu ba, yadda ya kamata. Wannan ya sa suka

qirqiro dokar haqqoqin yara, suka yi qoqarin qaqaba wa qasashen

musulmi [duba littafi na Ni’imar Haihuwa da Haqqoqin ‘Yaya a Musulunci domin samun cikakken bayani].

Ba sai an faxa ba, irin waxannan kururuwar shaixan da kiraye-

kirayen banza waxanda maqiyan Musulunci ke yi, suna da mummunar

illa, da haxari mai girma a kan makomar al’umma da kuma tarbiyyar

`ya`yanta. 276

Bayani ya gabata dangane da haxarin abokan banza, da mummunar

tasirinsu a kan tarbiyyar `ya`ya.

Page 172: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

172

6. Mummunar mu’amalar da iyaye ke nuna wa `ya`ya.277

277

Mummunar mu’amalar da waxansu iyaye ke yi tare da `ya`yansu na

taimakawa wajen rashin tarbiyya. Idan mahaifi ya zamanto ba ya jawo

`ya`yansa kusa da shi, akwai yiwuwar ya kasa fahimtar halayensu da

qoqarinsu ko gazawarsu. Haka kuma, mummunar mu’amala da `ya`ya

na janyo wa `ya`ya dakushewar qwaqwalwa da rashin saitin tunani, da

kuma yin hulxa da mutanen banza.

Ya kamata iyaye su jawo `ya`yansu a jiki domin su saba da juna; su

riqa yin hira da su domin su ba su shawarwari ko su yi masu gyara a

wuraren da suka dace; su yi qoqarin fahimtar matsalolinsu domin su

san hanyoyin magance su; su riqa sauraron abubuwan da yara ke faxi a

cikin maganganunsu domin su yi masu saiti; su riqa yin kawaici ga

waxansu kura-kuran da `ya`yansu za su yi a gabansu a wani lokacin

domin su samu damar faxakar da su daga baya. Muhammad ibn Abdillah Al-Habdān, a cikin littafin Al-Usrah Baynal Islām wal Garb, shafi na 54-60, ya bayyana matakai guda goma

sha biyu (12) waxanda ya kamata iyaye su bi domin kyautata

mu’amalarsu da `ya`yansu. Matakan su ne:

1. Samar wa yara wajen ajiye littafan karatu (maktabah) na

musamman, wanda zai qunshi littafai masu ma’ana, tare da yin

tarayya da su wajen karatu, lokaci zuwa lokaci.

2. Keve wa yara lokacin wasa, da nuna masu wajibcin kammala

ayyukan da ke gabansu kafin su tafi wajen wasa. 3. Fita da yara domin shaqatawa, kamar yadda Aliyyu ibn Abi Xālib

(Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana yi da Al-Hasan da Al-

Husain (Allah Ya yarda da su).

4. Tarayya da yara a cikin wasanninsu domin a samu damar yin masu

gyara. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)

ya guntsa ruwa a bakinsa, sannan, ya fesa wa Al-Husain (Allah Ya

yarda da shi), shi kuma Al-Husain na gudu yana dariya. Bayan

wannan, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya kasance yana xora yara a kan bayansa domin ya yi masu

wasa. Haka nan, ya tabbata cewa yana fitar da halshensa ga Al-

Husain, shi kuma Al-Husain sai ya yi ta yin dariya.

5. Samar da darasin Alqur’ani a cikin gida ko masallaci domin a riqa

karanta Alqur’ani kuma ana qoqarin hardace shi.

6. Qarfafa masu gwiwar halartar daurah ko kevantattun tarurrukan da a ke shiryawa a waxansu lokutan musamman (kamar irin su IVC da

qungiyar xalibai musulmi ta qasa, MSS, ke shiryawa).

Page 173: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

173

7. Kallon finafinan banza, waxanda ke vata tarbiyya.278

8. Zaman banza da rashin aikin yi.

9. Sakaci da al’amarin tarbiyya.279

10. Mutuwar iyaye.280

7. Shigar da su cikin ayyukan kasuwanci ko sana’ar da mahaifi ke yi

domin su saba tun suna qanana.

8. Kwaxaitar da su yin bincike a cikin harkar ilmi, da tafiya da su

wajen da’awa da sauraren ilmi, da tafiya da su masallaci.

9. Ba su labarai game da musulmi da Musulunci a duniya da irin

wayewa da ci gaban Musulunci.

10. Ziyartar asibiti da maqabarta tare da su.

11. Sanya masu kaset xin karatun Alqur’ani ko wa’azi, sannan, a yi

masu tambayoyi a kan kaset xin daga baya.

12. Kawar da kai daga kurakuransu a wani lokacin, domin a samu

damar yin masu gyara cikin hikima daga baya. 278

Bayani ya gabata dangane da haxarin kallon finafinai, da yadda

finafinai ke qalubalantar tarbiyyar al’ummar musulmi. 279

Bayani ya gabata dangane da yadda waxansu iyaye ke yin sakaci

game da al’amarin tarbiyya, da alamomin sakaci, da kuma haxarin irin

wannan sakaci a kan `ya`ya da iyaye da al’umma baki xaya. 280

Mutuwar iyaye na daga matsalolin tarbiyya, musamman idan iyaye

suka mutu a lokacin da `ya`yansu ke qanana, kuma ya zamanto ba a

dace da `yan’uwa ko dangi waxanda za su ji tsoron Allah game da

waxannan marayu ba.

Maraici abu ne da ke samun yara, a dalilin mutuwar iyayensu,

musamman mahaifi, a lokacin da yaran ba su kai matsayin da za su

kula da kansu ba. Idan Allah (Maxaukaki) Ya xauki ran mahaifi, kuma

aka dace da `yan’uwa na qwarai waxanda za su ci gaba da xaukar

nauyi da xawainiyar marayun, ana sa ran waxannan marayu ba za su

tozarta ba. Idan kuwa waxanda za su ci gaba da kulawa da marayun,

azzalumai ne ko kuma waxanda ba su ba al’amarin tarbiyya

muhimmanci ba, akwai yiwuwar waxannan marayu su tozarta a

vangaren addininsu da rayuwarsu.

Al’amarin maraici na da girma a cikin Musulunci. Akwai ayoyin

Alqur’ani fiye da guda ashirin da kuma ingantattun hadisai masu tarin

Page 174: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

174

yawa waxanda suka yi magana a kan marayu, da irin haqqoqin da su

ke da shi a cikin al’umma, da muhimmancin kulawa da su, da falalar da

ke cikin xaukar nauyinsu. Misali, Allah (Maxaukaki) Ya hana a zalunci maraya ko a nuna masa fin qarfi [Dhuhā, 93:9]; kuma Ya tsawatar

game da cin dukiyar marayu bisa zalunci [Nisā, 4:10], haka nan, Ya yi

umurni da a kyautata masu, a ciyar da dukiya wajen xaukar nauyinsu

[Baqarah, 2:215]. Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a

gare shi) ya bayyana cewa kulawa da marayu da xaukar xawainiyarsu,

nau’i ne na jihadi [Bukhari a cikin Al-Adabul Mufrad], kuma kyautata

masu da kulawa da tarbiyyarsu, na jawo albarkar dukiya [Bukhari da Muslim] da taushin zuciya [Xabarāni da Silsilah As-Sahīhah, 854].

Haka kuma, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi) ya bayyana cewa yana tare da waxanda ke kula da marayu, da

xaukar nauyinsu, da yin masu tarbiyya, a ranar qiyama [Bukhari].

Babu shakka, maraici na daga qalubalen da ke fuskantar al’amarin

tarbiyyar `ya`ya. Kuma ko da ya ke abu ne da ba a son aukuwarsa, dole

ne ya faru ga waxansu daga cikin mutane, tun da dai babu shakka,

kowa zai mutu.

Rayuwa a cikin wannan duniyar na da iyakantaccen lokaci, kuma

lallai ne lokacin zai zo. Wannan rayuwar kuma, lokaci ne na jarabawa

domin a bambance a tsakanin waxanda ke yin qoqarin ganin sun

rabauta a nan duniya da can lahira, da kuma waxanda za su gina

rayuwarsu a kan sharholiya [Mulk, 67:2].

Mutuwa ita ce matakin farko na zuwa lahira, kuma babu makawa sai mutum ya mutu. Mutuwa babbar musiba ce [Mā’idah, 5:106], wadda ke

yanke jin daxi [Tirmidhi], kuma tana da raxaxin gaske [Qāf, 50:19].

Babu wani rai face sai ya xanxani mutuwa [Aal Imrān, 3:185]; babu

wanda zai kuvuce mata [Juma’ah, 62:8]; kuma ko’ina mutane suka shiga, kowa sai ya mutu [Nisā, 4:78] har sai duniyar ta qare gaba

xayanta, in ban da fuskar Allah [Rahmān, 55:26-27; Qasas, 28:88].

Kowane rai na da iyakantaccen lokacin da zai mutu [Aal Imrān, 3:145],

kuma babu wanda ya san lokacin mutuwar sai dai Allah [Luqmān,

31:34], to amma, idan lokacin ya zo, za a mutu, ba tare da qarin lokaci ko ragi ba [Munāfiqun, 63:11; A’arāf, 7:34], sannan, da zarar an mutu,

babu dawowa cikin wannan duniya [Mu’uminūn, 23:99-100].

Kusan kowane xan Adam yana zullumin mutuwa, galibi, saboda

rashin sanin abin da za a tarar bayan an mutu, ko da ya ke ana buqatar

mumini ya kyautata zato ga Allah (Mai girma da xaukaka). Wani

lokaci, zullumin na da alaqa da makomar `ya`ya bayan iyayen sun

mutu, musamman idan babu manyan `ya`yan da za su kula da qanana.

Page 175: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

175

KAMMALAWA

Wannan shi ne abin da Allah (Mai tsarki da xaukaka) Ya

bani ikon rubutawa game da tarbiyyar `ya`ya a Musulunci.

Ina roqon Allah Ya karvi wannan xan aiki nawa, kamar

yadda ni ke roqonSa falalarSa, da karamcinSa, da

rangwamenSa, da gafararSa.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu

Muhammad, da mutanen gidansa da Sahabbansa da

waxanda suka bi hanyarsa har zuwa ranar Qiyama.

Alhamdu lillah.

Sau da yawa, ana samun mugayen `yan’uwa ko dangi waxanda ke

tozarta haqqin maraya, da nuna masa bambanci, da rashin xaukar

nauyin karatunsa yadda ya kamata, da rashin damuwa da tarbiyyarsa,

da rashin kulawa da lafiyarsa, da yin rib da ciki a kan dukiyarsa, ta

yadda maraya zai shiga cikin wani mummunan hali. Irin waxannan

azzalumai, ba su tunanin mutuwa? Sun manta cewa za su mutu? Za su

so a yi wa nasu `ya`yan irin wannan zalunci bayan mutuwarsu? Ba su

tsoron haxuwarsu da Allah (Mai girma da xaukaka) a ranar qiyama? Ba

su gudun kunyata tun a nan duniya?

Page 176: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

176

DAGA CIKIN LITTAFAN DA AKA YI AMFANI DA SU

Alqur’ani Mai Girma da Littafan Hadisi Abdullah Nāsih Ulwān, Mas’uliyyatut Tarbiyyatil Jinsiyyah

min Wijhati Nazaril Islam, Dārus-Salām lix-Xibā’ah

wan-Nashr wat-Tauzi’ wat-Tarjamah, Al-Qāhirah,

2003 Abdullah Nāsih Ulwān, Tarbiyyatul Awlād fil Islām, Dārus-

Salām lix-Xibā’ah wan-Nashr wat-Tauzi’ wat-

Tarjamah, Al-Qāhirah, 2005

Abdullahi Qādiriy Al-Ahdal, Daurul Masjid fit Tarbiyyah,

Dārul Mujtama’, Jeddah, 1407

Abdur-Rahmān An-Nihlāwiy, Usūlut Tarbiyyatil Islāmiyyah Wa Asālībuhah, Dārul Fikr, Dimashq, 1983

Ahmad Bello Dogarawa, Ni’imar Haihuwa da Haqqoqin `Ya`ya a Musulunci, Amanah Printing Limited,

Kaduna, 1426AH Ahmad ibn Abdil-Halīm ibn Taimiyyah, Hijābul Mar’ah wa

libāsuha fis-Salāh, Ta’alīq Muhammad Nāsiruddīn

al-Albānī, Al-Maktab Al-Islāmī, Beirut, 1985

Ahmad ibn Abdil-Halīm ibn Taimiyyah, Majmū’ul Fatāwā,

Maktabah Ibn Taymiyah, Al-Qāhirah, 1980

Ahmad ibn Abdil-Halīm ibn Taimiyyah, Iqtidā’us Sirāxil Mustaqīm, Wizārah ash-Shu’ūnil Islāmiyyah, Saudi

Arabia, 1999 Ahmad ibn Abdil-Halīm ibn Taimiyyah, As-Sārimul Maslūl

alā Shātimir Rasūl, Dārul Hadīth, Al-Qāhirah, 2003

Ahmad Musxafa Mutawalli, Al-Mausū’atul Āmm fi Tarbiyyatil Aulād fil Islām, Dār Ibnil Jauziy, Al-

Qāhirah, 2005

Al-Lajnah ad-Dā’imah lil Buhūth al-`Ilmiyah wal Iftā, al-

Idārah al-`Aamah lix-Xibā’i wat-Tarjamah, Saudi

Arabia, 1411AH As’ad Ismā’īl Aliyy, Usūlut Tarbiyyatil Islāmiyyah, Dārus

Salām, Al-Qāhirah, 2005

Page 177: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

177

Bakar Abdullah Abu Zaid, Hadduth-Thaub wal Uzrah wa Tahrīmul Isbāl wa Libāsish-Shuhrah, Maktabah as-

Sunnah, Egypt, 2001 Bakar Abdullah Abu Zaid, Hirāsatul Fadīlah, Dārul Āsimah,

Riyād, 2005

Bakar Abdullah Abu Zaid, Tas-hīh Ad-Du’ā, Dārul Āsimah,

Riyād, 1999

Khālid Hāmid Al-Hāzimiy, Usūlut Tarbiyyatil Islāmiyyah,

Dār `Aalamil Kutub, Riyadh, 1421

Khālid Shantūt, Daurul Bait fi Tarbiyyatix Xifl Muslim, Dārul Maxbū’atil Hadīthiyyah, Jeddah, 1990

Laylā Bint Abdir-Rahmān, Kayf Turabbiy Waladak,

http://www.islamhouse.com/files/ar/ih_būks/single/ar

_How_raising_and_son.doc.

Mājid Arsān Al-Kailāniy, Ahdāfut Tarbiyyatil Islāmiyyah,

Mu’assasatur Rayyān, Beirut, 1998

Miqdād Yālijn, Ahdāfut Tirbiyyatil Islāmiyyah, Dārul

Hudā, Riyadh, 1989

Muhammad Abdus-Salām Khidir as-Shuqairī, As-Sunan wal Mubtadi’āt, Dār al-Fikr, 1352AH

Muhammad Ad-Duwaysh, Al-Asālibut Tarbawiyyah inda Rasūlil Bashariyyah,

www.quran.maktūb.com/vb/quran22761

Muhammad As-Suhaim, Min Akhxā’inā fi Tarbiyyati Aulādinā, Dārul `Aasimah, Riyadh, 1415

Muhammad ibn Abdillah al-Habdān, Al-Usrah baynal Islām wal Garb, Dār Ibn Khuzaimah, Riyadh, 2001

Muhammad ibn Abi Bakr ibn al-Qayyim al-Jawziyyah, Ahkām Ahliz Zimmah, Dārul Hadīth, Al-Qāhirah,

2003

Muhammad ibn Abi Bakr ibn al-Qayyim al-Jawziyyah, Al-Wābilus Sayyib, Al-Maktabuth-Thaqāfi, Al-Qāhirah,

2003

Page 178: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

178

Muhammad ibn Abi Bakr ibn al-Qayyim al-Jawziyyah, Jilā’ul Afhām fis Salāti Wassalāmi ‘ala Khairil Anām, Dārul Arubah, Kuwait, 1987

Muhammad ibn Abi Bakr ibn al-Qayyim al-Jawziyyah, Tuhfah al-Maudūd bi Ahkām al-Maulūd, Maktabah

al-Qur’ān, al-Qāhirah, 1987

Muhammad ibn Ibrahim Al-Hamd, At-Taqsīr fi Tarbiyyatil Aulād: Al-Mazāhir, Subulul Wiqāyah wal Ilāj, http://www.sāid.net/būk/open.php?cat=82&būk=809

Muhammad Munīr Marsī, At-Tarbiyyatul Islāmiyyah: Usuluhā wa Taxawwuruhā fil Bilādil ‘Arabiyyah,

‘Ālamul Kutub, Al-Qāhirah, 1421

Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī, Jilbābul Mar’atil Muslimah fil Kitāb was Sunnah, Dārus Salām, 2002

Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī, Sifah Salātin Nabiyy,

Maktabah Al-Ma’ārif, Riyād, 1991 Muhammad Nūr Suwaid, Manhajut Tarbiyyatin

Nabawiyyah Lix Xifl, Maktabatul Manāril

Islāmiyyah, Kuwait, 1988

Muhammad Sa’īd Maulawiy, Kayf Yurabbil Muslim Waladah? Maxba’ah Ramādiy, Damām, 1995

Najīb Al-`Aamir, Min Asālībir Rasūl fit Tarbiyyah, Al-

Bushral Islāmiyyah, Kuwait, 1990

Sālih As-Sadlān, Al-Masjid Wa Dauruh fit Tarbiyyah Wat Taujih, Dār Bilansiyyah, Riyadh, 1994

Sālih ibn Aliyyu Abu ‘Arrād, At-Tarbiyyatul Islāmiyyah: Al-Musxalah wal Mafhum, 1426, http://sāid.net/Doat/arrad/17.htm

Sālim Aliyyu Rāshid ash-Shabalī da Muhammad Khalīfah

Muhammad ar-Rabāh, Ahkāmul Maulūd fi as-Sunnah al-Muxahharah, Al-Maktab Al-Islāmī,

Beirut, 1994 Samīr Abdul-Azīz, Manhaj al-Islām fi Tarbiyyatil Awlād,

Dār Ibn Rajab, Egypt, 1999

Page 179: Tarbiyyar `Ya`Ya a Musulunci

179

Shamsuddīn Az-Zahabī, Mukhtasār Al-`Uluw lil Aliyyil Ghaffār, Tahqeeq Muhammad Nāsiruddīn al-Albānī,

Al-Maktab Al-Islāmī, Beirut, 1991

Sihām Mahdiy Jabbār, Ax-Xifl fish-Sharī’atil Islāmiyyah Wa Manhajut Tarbiyyatin Nabawiyyah, Al-

Maktabatul Asariyyah, 1997 Ummu Hassān Al-Hulw, Akhxā Tarbawiyyah Shā’i’ah, Dār

Ibn Hazm, Beirut, 1994