fiqihun ibada a cikin hotuna altatoa.pdf · hadisi qudusi daga abu hurairata – allah ya yarda da...

3
Azumin Nafila

Upload: others

Post on 24-Oct-2020

9 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

  • Dr. Muhammad Sani Umar MusaShaikh Nura Sani Muhammad

    bita

    Muhammad Rabi'u Umar Musa R/lemo

    tarjama

    د. عبداهللا بن سالم باهمام

    ZakkahAzumiSallah

    Karantar da hukunce-hukuncen musulunci a sauqaqe

    Fiqihun ibada a cikin hotuna

    Azumin Nafila

    https://www.al-feqh.com/ha/category/azumihttps://www.al-feqh.com/ha/category/azumihttps://www.al-feqh.com/ha/azumin-nafila

  • 156

    Abubuwan Da Ke ciki

    Bayanin Menene Azumin NafilaKwanakin Da Aka Sunnanta Yin Azuminsu1 – Kwana shida a cikin Shawwal2 – Kwanaki Tara Na Zulhijjah3 – Azumin Ashura4 – Kwanakin Hasken Wata5 – Ranar Litinin Da Alhamis6 – Azumin Rana Xaya Da Hutun Rana Xaya7 – Azumin Watan Muharram Da Sha’aban

    Azumin Nafila4

    Azumin NafilaShi ne duk azumin da yake ba wajibi ba ne, wanda mutum

    yake yin sa don neman kusanci zuwa ga Allah Maxaukakin Sarkixx

    Azumin Nafila yana da falala mai girma da lada babba, a cikin hadisi qudusi daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص ya ce, “ Dukkan aikin xan Adam ana ninka masa shi, ana ninka kyakkyawa sau goma, har zuwa ninki xari bakwai. Allah Mai girma da buwaya ya ce, “Sai dai azumi, haqiqa shi nawa ne, ni ne nake ba da ladansa”(1).

    Kwanakin Da Aka Sunnanta Yin Azuminsu

    1 – Kwana Shida A Cikin Watan Shawwal

    Saboda faxin Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص : “Wanda ya yi azumin Ramadan, sannan ya bi shi da guda shida a cikin Shawwal, to kamar ya yi azumin shekara ne”(2). Zai iya yin su a haxe ko a rarrabe.

    2 – Kwana Tara Na Farkon Watan Zulhijjah

    Saboda faxin Annabi ملسو هيلع هللا ىلص “Babu wasu kwanaki da Allah ya fi son aikin na qwarai a cikinsu, kamar waxannan kwanaki - yana nufin kwanakin goma na Zulhijjah – sai sahabbai suka ce, Ya Manzon Allah, Ko da jihadi a cikin tafarkin Allah? Sai ya ce, “Ko jihadi a cikin tafarkin Allah, sai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, sannan bai dawo da komai ba”(3). Ranar da ta fi daga cikin waxannan kwanaki ita ce ranar Arafa, ga wanda yake ba alhaji ba ne, saboda faxin Annabi ملسو هيلع هللا ىلص “Azumin ranar Arafa ina sa rai a wurin Allah, ya kankare zunubin shekarar da take gabansa, da wadda take bayansa”(4).

    (1) Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi(2) Muslim ne ya rawaito shi(3) Bukhari ne ya rawaito shi(4) Muslim ne ya rawaito shi

    Kwana

    tara

    a ckin w

    atan

    Zulhijj

    i

    Kwana

    shida

    A cikin

    watan

    Shaww

    al

    http

    s://w

    ww

    .al-f

    eqh.

    com

    /ha/

    cate

    gory

    /azu

    mi

    https://www.al-feqh.com/ha/azumin-nafila

  • Littafin Azumi

    157

    3 – Azumin Ranar Ashura Da Ranar Da

    Take Gabaninsa

    Saboda faxin Annabi ملسو هيلع هللا ىلص “Azumin ranar Ashura, ina sa rai a wurin Allah ya kankare zunubin shekarar da ta gabace shi”(1).

    Dalilin yin azumin wannan rana shi ne abin da ya tabbata daga Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi - : “Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص ya zo Madinah, sai ya ga Yahudawa suna azumin ranar ashura. Sai ya ce, “Menene wannan?” sai suka ce, “Wannan wata rana ce mai kyau, wannan ranar ce Allah ya tseratar da Bani Isra’ila daga maqiyansu, sai Musa ya yi azuminta”. Sai Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص ya ce, “Mu muka fi cancanta da Musa fiye da ku” sai ya yi azumin wannan rana, ya kuma umarni a yi azuminta”(2). A riwayar Muslim: Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص ya ce, “Idan na kai shekara mai zuwa zan yi azumin ranar tara ga watan”(3).

    4 – Kwanakin Haske A kowane Wata

    Ya tabbata daga Abdul-Malik xan Minhal daga Babansa, wanda ya rayu tare da Annabi ملسو هيلع هللا ىلص ya ce, Manzon Allah yana umarni da azumin kwanakin haske, yana cewa : “Daidai yake da azumin shekara”(4).

    (1) Muslim ne ya rawaito shi(2) Bukhari ne ya rawaito shi(3) Muslim ne ya rawaito shi(4) Ibnu Hibban ne ya rawaito shi

    5 – Azumin Litinin Da Alhamis A Kowane

    Sati.

    Saboda da abin da aka rawaito daga Abu Hurairata – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص ya ce, “Ana bijirar da ayyuka, ranar litinin da Alhamis, ina so a bijirar da aikina ina mai azumi”(5).

    6 – Azumin Yau-gobe-babu.

    Mafificin Azumin nafila shi ne azumin Annabi Dawud, ya kasance yana azumin kwana xaya, ya huta kwana xaya. An karvo daga Abdullahi xan Amru – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص ya ce, “Mafi soyuwar azumi a wurin Allah, azumin Annabi Dawud, ya kasance yana azumin kwana xaya, kuma ya huta kwana xaya”(6).

    7 – Azumin Watan Al-Muharram

    An karvo daga Abu Huraira – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص “Mafificin azumi bayan Ramadan shi ne azumin watan Al-Muharram”(7).

    8 – Azumin Watan Sha’abanAn karvo daga Usamatu xan Zaid – Allah ya

    yarda da shi – ya ce, na ce, ya Manzon Allah ملسو هيلع هللا ىلص banga kana azumin wani wata ba cikin watanni, kamar yadda kake azumin watan Sha’aban, sai ya ce, “Wannan wani wata ne dake tsakanin Rajab da Ramadan, wanda mutane suke gafala ga barinsa. Wata ne da ake xaukaka ayyuka a cikinsa zuwa ga Ubangiji, don haka ina so a xaga ayyukana ina mai azumi”(8).

    (5) Tirmizi ne ya rawaito shi(6) Nasa’i ne ya rawaito shi(7) Muslim ne ya rawaito shi(8) Nasa’i ne ya rawaito shi

    Ashura Ita ce ranar goma ga watan Muharram

    Kwanakin haske

    Su ne, Sha uku, sha huxu, da sha xxbiyar na kowanne watan musulunci. An kira su da kwanakin haske saboda wata

    yana haske a dararensu.

    Azumin Nafila

    http

    s://w

    ww

    .al-f

    eqh.

    com

    /ha/

    cate

    gory

    /azu

    mi